Showing 255001 words to 258000 words out of 288345 words

Chapter 86 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

710

zauna da ya'yana har abada ba. domin nasan Ishaq bazai bani ko daya Daga ciki ba.
Sai bayan La'asar su Mama suka wuce katsina an rabu zukata ba Dadi,kamar kada mu rabu da Amir da yaga ma Ina Damuwa sai yace"Umma ki daina damuwa fa zan lallashi su Anum kuma ma ai Baba yace zai rika kawo ki,kina ganin mu muma yace zamu rika zuwa muna ganin ki"
Sai na rumgumesa ina kuka Kaunar Engr da ta boye acikin raina ta sake Fitowa a cikin zuciyata,ance mai d'a wawa daman ya Fad'amin shi baya son ya'yansa su kirasa wani Daddy yafi son Baba na gargajiya.
Nasan Engr na da kirki ammh sai da Amir ya kalleni yace"Umma ki daina Damuwa shi Baba na da kirki bazai rika sakaki kuka kamar Daada ba"
Har suka tafi da na tuna da mganarsa sai naji hawaye sun kawo min Allah Sarki ya'ya Rahma ne Allah ya bama wadanda ba su da ya'ya masu albarka mu kuma da muke da su Allah ya tsare mana su sannan ya kara shiryawa,katsina zasu kwana Gobe su tafi kano Jamal Dole zai siya musu Tiket zuwa lagos tunda Uban gayyar ya watsar da su ya yi gaba.
Tunda dai na tabbatar da cewa Engr na aura sai duk wani Fargaba na ya kare na saki jikina da yammah Nana Fatima na cewa na sake wanka ba Gaddama na Sake yin wanka na sauya kaya zuwa atamfa Doguwar riga.
Da naga bata ce zatamin kwalliya ba kai Tsaye nace"Fatin mu kwalliyar fa..?
Cikin shagwaba na fada ai sai ta rike baki tana fadin"Eyee lalle na yarda ana son Engr ammh ai dazu har kina mana Boren baki so"
Ina Dariya nace"Dazu kika ce. yanzu ai komai ya sauya".
Duka ta D'akamin tana fadin"Zaki sani ne bazan yi kwalliyar ba".
Dariya na fara ina bata Hakuri sai ta rumgumeni tana fadin"Naji dadin ganin ki cikin farinciki Fa'in mu Allah ya saka ki yi farinciki fiye da yadda kike Tsammani, Allah yasa Engr ya juyar dake Dadin da sai kin manta sunan ki"
Tsungulinta nayi ina fadin"Ba'a gasa bakin nan naki ba"
Na fad'a ina dariya ni da ita ina tuna Dazu da Yaya Mariya tace gwara da Ishaq? ya furta haka akansa wasu hallayansa tasa Inno ta mata dakuwa tana fadin bakin ki kamar bai ji gashi ba Mariya, muna ta dariya shine na tuna na fad'ama Nana Fatima"
Sai da mukayi sallar mangariba sannan Nana Fatima ta min kwalliya mai sauki sai tunani nake yi ko Engr yayi Fushi ne bai nemeni ba.
Abunda ban sani ba suna tare da su Abba har Dr.Lawal sai washegari zai koma Abuja,bazai iya barin su ba,kuma wayata ban kunna ba amnh yafi kowa son ganina da jin muryata.
Abincin har sai da aka bama almajirai tunda ba wasu jama'a ni ko su Sa'adatu hana su dawowa yau nayi alokacin bansan lamarin zai sauya ba Ammi ko bakinta har kunne ammh da Safe ko Fara'a batayi.
Taruwa suka yi Nana Fatima da Raliya suna min tsiya Badariya na taremin daman tana nan bata koma ba,Yusuf din zai turo Direba yazo ya Dauketa jibi.
Muna cikin hakane Abba ya kira wayar Nana Fatima akace a bani ina karba yace"Fa'i ki kunna wayarki Engr na son mgana da ke"
Cikin sanyin jiki na amsa mai da toh wayar na cikin karamar jakata ta hannu na fiddota na kunna,naga tarin sakonnin Engr ban bude ba sai na goge su nasan ma magiyane tun a baya yanzu kuma mun taka wani mataki basai mun koma baya ba.
Ina kunna wayar kamar yana jira sai ga kiransa gabana ya fadi ga su Badariya sai na lallaba na fice ashe suna Lura dani sai suka kwashi shewa na fice ina girgiza kai kawai.
Tsakar gida na fita sai naji akwai sanyi sai na shige dakin Karikitan goggo da nawa ni kaina,na samu saman Freezer na haye har kiran ya katse sai ya kara kira ina Dagawa bai jira nayi mgana ba yace"Alhamdulillah Faa'iza ta zama ta Tosin har Abada"
Mirmishi nayi ban yi mgana ba sai ya cigaba da fad'in "Ki ce wani abu mana karo na farko da aurane na akan ki Faa'iza"
Dakyar na iya fadin"Ina mana Fatan alheri"
Ina jin Sautin mirmishinsa kafin yace"Kin gama mgana gabadaya..?
To Ameen ykk..?kin ci abinci kuwa..?kin daina kuka..?
Ina dariya nace"Duk ni kadai wanne zan fara amsa maka..?
Kai tsaye yace"Duka nake bukata"
Cikin karya murya da bansan na iya ba nace"ina lafiya kamar yadda kake. abinci kuma ban ci ba kila sai an jima kuka kuma na daina tun daga Lokacin da naji Labarin na zama matarka"
Ni kaina in ina tare da Engr bana sanin ma ina sakin baki ina mgana.
Sai da naji yace"Da gaske Faa'iza..?
Ni kaina bansan adadin Halin da na shiga ba nayi ma Allah godiya Sosai har Umra zamu Faa'iza domin mu kara godema Allah"
Jin nayi shuru yasa ya cigaba da fadin"Papa da sweetheart sun ce na gaishe ki sosai tare da Sister dina. Suna ta min magiyan gobe na taho dake Abuja"
Da sauri nace"Ni kuma..?
Sai ya marairaice kafin yace"Eh suna so su ganki ne. Ni dayake ma kinga jibi zan? yi tafiyata bama ganina zaki rika yi ba"
Dariya ya bani kafin nace"Ai sai jibi ne Tafiyar goben bazan ganka ba ne..?
Sai ya yi saurin fadin"Nufina daga goben nake so nace"
Yafad'a yana sosa keya kamar ina ganinsa yana jina ina yar Dariya wani irin farinciki ya mamayesa kafin yace"Wlh da na son da auran? nan Visa zan yi miki kafata kafarki zuwa America Faa'izaa"
Ina mirmishi nace"Ayya sai kuma ga shi kafarka kafarka zaka tafi"
Kai ya kada kafin yace"Kin ci ba shi. Zakuma ki sha wahala wajen biya'
Ni dai dariya nayi masa hira ya dinga min yana bani labarin granny din su ta kirashi tana fadan meyasa aure cikin gaggawa haka? bai fad'ama kowa ba yana cemin"Kinsan me na gayamata..?
Sai na girgiza kai cikin Danne Dariyansa yace"Ce mata nayi gaggawan na rabo? ne,gwara ayi ayi auran kada na haifa mata yaran da take son gani a titi"
Sai na rufe baki ina salati shi kuma yana Dariya kafin yace"To karya nayi..?haka tsohon mijin ki yace nawa na biyaki kika bani jikin ki..?
Ni wlh ban ji haushinsa ba ga shi Sanadin mganarsa ya sa jikin ya zama nawa har Abada, in a baya ina biya ne yanzu a?kyauta ma za'a bani sai ma ina yanga"
Kasa mgana nayi ina toshe bakina kada nayi dariya shi ko ajikinsa cikin Kada harshe yace"Wayyo na tausaya masa sosai"
Kai kawai na girgiza kafin nace"Ba kai kayi masa kwacen mata ba"
Da sauri yace"A'a daman ai Faa'iza ta Abdulbasit ne shi kadai ban cika neman abu na rasa ba Faa'iza,ni da kika ganni nan ina da sa'a duk abunda na nema ban Samu ba to ki tabbatar da ba Alherina ba ne"
Cigaba ya yi da bani labarin sa kad'an da wasu abubuwa na shi,ya yi mganar yana dawowa zan tare na zabi in da nake so na zauna kaduna ko Abuja,ko Edo
Saboda na Zolayesa nace"Lagos nake so"Da sauri yace"Ban da nan. Ni bana zuwa Lagos"
Yafada har da hade rai sai na kyakyalce da dariya shima tayani yayi kafin yace"In domin yaran mu ne kada ki damu tare zamu rika zuwa ganin su bazan lamunta da barin ki ke kad'ai ba. gwara ki zabi kusa dani wlh kika zabi nesa korata za'ayi a aiki Tunda wajen ki zan tare kinsan makale mata manne mata'?
Ina Dariya nace"Eh.."
Shi kuma sai yace"To ai irina kenan so gwara ki neman mana masalaha"
Hiran ce tayi dadi cikin wasa da Dariya da barkwanci har bansan Dare ya yi ba,sai da wayata ta dauke,ashe ba Chaji na fito naga duhu ya yi sosai har mallan ya dawo dukkanmu bamu yi sallar isha'i da wuri ba.
Koda na koma Daki ina Sadda kai Badariya batayi barci ba Nana Fatima kuma na wanka Raliya na Dayan dakin Goggo.
Kallona tayi kafin tace"Uhm za'a kwashi kallon kauna agidan ki Anty Fa'iza.."
Kai na Sadda kasa sai naji ina jin kunyarta dariyanta naji tana Fadin"ni ce fa.
Badariya ce Anty Fa'iza.
Wlh ina miki murna na jima ina addu'aan Allah ya baki miji mai sonki wanda zai kasheki da Soyayya kuma Daga gani Allah ya baki"
Sai na kwashe da Dariya a raina ina Tuna Engr duk da ba'a son maci Tuwo ba sai miya ta kare,ammh alaman karfi yana ga mai kiba Engr karshe ne a sanin kan mace to ya shiga ko'ina meye bai gani ba..?
Nasan ba domin wayar ta mutu ba bazai kyaleni ba chaji na sakata da Nana Fatima ta fito nashiga nima nayi wanka na Dauro alwala nazo nayi sallah ranar raba Dare muka yi muna Hira suna ta bani sharwari Badariya tace"Yaushe ne tarewar.?
Ina kauda Fuskata nace"Wai fa yace da ya dawo"
Nafada kamar zan yi kuka suka kwashe da Dariya har da tafawa.
Nan fa suka fara min mganar gyara nace bazan yi ba Nana Fatima tace"Zaku gamu da Ammi"
Ina jin haka na zaro ido nasan Halin Ammi mutumcina zata ci.
Sai wajen uku na Dare suka kwanta ni dai sai da nayi raka'a biyu nayi ma Allah Godiya sannan na kwanta,shiyasa muka makara sallar asuba sai da aka rika bugamana kofa da karfi.
Da safe ma daganan akayi abun karyawa aka kaima su Abba,kuma sai da Safen na kunna Wayata da Sakon Engr na fara cin karo.

"Fatan kin tashi lafiya Amaryan Abdulbasit?
"I love u"

Na lura baya son yana yi min Turanci Saboda kada na rika jin kamar zai kureni Allah Sarki Engr sai ya koma Daidai dani mun taba mganar karatu da shi nace masa bana ra'ayi kai Tsaye yace"Bokon banza Bokon wofi kin burgeni wlh meye a bokon ban da wahala.?ke ce mai ilimin duk duniya Tunda kinsan Qur',ani da Hadisai ni kaina kamar na kwashe bokon kaina na Kona haka nake ji"
Alokacin bansan Dariyan da nayi ba,Shi komai nawa ya gama yi masa ba shi da wata matsala.
Tun Safe nayi wanka na cakare da Wani materil Doguwar riga ya kuma yi min cif mayafi dai suka yi sukayi na saka nace Hijabina zan saka.
Yace min daman kafin ya tafi zamu yi mgana,bamu yi waya da Safe ba na dai yi kokari na tura masa amsar da cewa"Lau na tashi Ya Tosin din Faa'iza shima ya tashi.?
Sai bai bani amsa ba kuma bai kirani ba nafi Tunanin ko yana waya ko kuma wanu uzuri ya rikesa.
Wayar tana hannuna ina jiran kiransa sai naji kira na dauka jikina na rawa na zata shine sai naga bashi ba ne Zainab.
Sai da jikina ya yi sanyi ina Dauka ko sallamata bata amsa ba tace"Shikenan sai ki yi mana haka Maman Amir..?
Ta fada a sanyaye cikin wani yanayi nace"Ba haka ba ne Zainab shi bai fad'amiki yace baya son Datti a gidansa ba..?kinga kuwa tunda ni Datti ce ya kamani da kwarto bai kamata kuma na koma masa ba"
Cikin damuwa tace"Duk ya fad'amin komai wlh yace kishin ki ne ya rufaimai ido ammh ba har zuciyarsa ba haka ba ne,ga shi nan da zazzabi ya Dawo sai rawan sanyi yake yi yana kuka yana Kiran sunan ki"
Sai naji dadi ko banza shima zai ji abunda naji acikin raina.
Cikin Mirmishi nace"Allah ya ba shi lafiya bani da abunda zan yi masa bakin Alkalami ya riga da ya Bushe zainab.."
Cikiin wani irin sanyu tace"Yanzu shikenan Maman Amir..?
Sai naji nima Tausayin ta ya kamani Cikin karfin hali nace"Shikenan ba shikenan ba. akwai amanar ya'yana a wajen ki zainab ki kularmun da su ki yi kuma Hakuri da su ki yi musu Gyara a inda suka yi kuskure, Allah me ya had'amu ba Ishaq ba saboda haka bai isa ya rabamu ba zamu cigaba da waya da zumuncin mu in sha Allah"
Cikin Tausaawa tace"Hakane ina yi miki Fatan Alheri Allah ya bada zaman Lafiya"
Na amsa mata da Ameen ina so na tambayeta yaran sai kuma na kasa haka muka rabu zukata ba Dadi.
Ita kanta Zainab tasan Alhakina ke Bibiyan Ishaq,daman tun kafin dawowarsa Daddy ya kirata ya fad'amata ga yadda abun ya kaya ta sani har ga Allah bata bakinciki da Dawowar Fa'iza ammh tayi farinciki da ya rasa ta, ko domin haka ya zame masa izina gobe ko kashi ya aura sai ya san yadda zai iya Daraja shi.
Ni ko muna gama waya na bama Nana Fatima Labari daman tana Dakin cikin Tausayawa tace"Allah sarki. Sai ta bani Tausayi,ai yaran suna gidan Anty Fadila tace jiya tana gidan Baban zainab din ya kira yake fadin abunda ke Faruwa, sai ta tafi da su kada su ji labari su fara kuka tunda suna ta Murnan Umman zata dawo"
A raina nace"Ai ko Umma bazata Dawo ba har Abada"
Naji ma damu ammh jin suna tare da Anty Fadila sai naji na samu natsuwa.
Sai wajen sha Daya su Abba suka shigo muna daki Badariya tazo tana Fadin ga su Abba chan har da Engr sun zo gai da su Inno da su Goggo.
Ni dai leke nayi ta yi ta Labule har da Dr.Lawal mahaifin Zainab ko kunya.
Ni dai gwanina na rika d'age ina son gani a chan na hangosa kasa gaban su Inno kansa duke ya sanya Shadda mai ruwan kasa hular kansa na hango duk da yana Duke ne ammh duk yafi su Abba tsawo shiyasa na hangosa.
Sun jima ana ta dai yan nasihu kafin Naji ana cigiyata kamar an jefoni haka na fito daman na saka Hijabina har kasa,nasan idanuwansa na kaina shiyasa ban yarda na Dago mun hada ido ba. har kasa na duka na gaida su Abba.
Inno ce ta kalli Engr tana fadin"To kai Ango an ce kuma zaka yi tafiya kasashen Turawa wa zaka bar ma amanar amaryan taka..?
Tafada cikin zolaya kai tsaye yace"Nan zan bar muku ita Hajiya har sai na dawo sai ayi shirin tarewar nata in sha Allahu"
Sai inno tace"Au to na zata ai wayau zakayi mana ka dauketa kai kaita cikin yan'uwan ku yarbawa"
Gabadaya aka saka dariya tunda cikin Sigar wasa tayi mganar shi ko sai so yake mu hada ido naki yarda ina zan yarda ya bani kunya gaban su Abba.
Sallama ya yi musu bayan ya sauke ma su Inno kudi suna ta saka albarka Abba ya gabatar da Dr.lawal sai kika ji Allah Sarki na tashi.
Da suka fice kasa fita nayi ina kunyar Abba sai da Ammi tace naje mu yi sallama da mijina,ko alokacin kasa bin shi nayi sai da ya kirani a waya yana Fadin"Kuna shikenan zan tafi ban yi sallama da iyalina ba Faa'iza.?
Dole na fita yana zaure su Abba kuma na waje jikina ke kyarma na zata zai rikeni ammh wlh ko Tafin hannuna bai Taba ba,sallama kawai mukayi ana ta kiransa a waya yace zamu tattauna in ya samu natsuwa haka ya tafi yana Dagamin hannu ina Dagamai kamar kada ya tafi.
Koda na dawo cikin gida sai naji kewa sai dai fa har suka isa Abuja muna waya kamar ta bakinsa manne mata makale mata kenan..

? Washegari Litini su Abba suka koma Kaduna Yaya Asiya ma ta koma kano,Badariya ma Direba yazo ya Dauketa ta Dau Hanya Gida ya rage dagani sai Nana Fatima sai baba Ati,Inno an tafi da ita Saboda zuwa asibiti.
Nana Fatima sai talata ta tafi Ammi taso na bisu nace mata zan taho Daga baya tace gyara zatamin na sosai,Nima ina son na gyara din Domin Farincikin Engr shi kadai nake so tunda nima yake sakani Farinciki shima ina son saka shi,100k ya turomin yace kada na kara tambayan Abba komi shi zai yi min yanzu sannan bai ce nacigaba da wannan sana'ar na wahala ba, sai mun tare sannan zamu zauna? mu zamanantar da al'amarin yadda bazan rika wahala ba., Yana chan fa bai barni ba daya samu Sarari sai ya taboni,sai dai ko in aiki ya yi masa yawa na rasa wani irin so Engr ke yi min haka Mamansa da Yan'uwansa ya basu lambata haka zasu kirani suna gaisheni Mamanshi kuwa ba dai kirki ba in ta kirani haka zata rika ce min"Ba dai matsalan komai ko..?
In nace mata babu sai tace Allah ya yi muku albarka dukkan ku Allah ya baku zaman lafiya"
In na fad'amai sai yace"Sweetheart haka take bata da? damuwa Faa'izaa"
Yana chan mun yi mganar Lefe sau daya yace dai sai ya Dawo mganar in da zan zauna ma yace ya fasa bani Zabi yaga in ya Biyemin zan cuceshi ne.
Saboda zan zabi nesa da shi, shikuma wlh kara'in Holewa zai yi ba ruwansa.
Engr. Uhmm sai da na had'u da shi na farajin ashe nima macece kamar sauran mata..?
Shi d'in ya wuce namiji,gwarzo ne ta kowani Fanni.





*Janafty*
[7/31, 2:45 PM] +234 803 654 7511: *KNKB3016*


*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

*ENGINEAR ABDULBASIT ABDULGHAFFAR OLUWATOSIN*

Sheik Abdulbasit Abdulfattah Oluwatosin shine asalin sunan kakan Engr wanda ya haifi mahaifinsa.
Su asalin su tun tale talen kakan kakannin su yarbawan Ilorin ne, ammh aiki da kasuwanci ya sa suka tashi garin Benue ,ammh ba Haifafun nan ba ne, nan dai suka girma suke kuma gudanar da Rayuwarsu a tsakiyar Birnin Beneu State.
Sai dai aiki da karatu na fidda wasu Daga garin ammh kusan dukkan su ba su da tushe ko asalin daya wuce garin,Ilorin kuma shine Tushen su.
Sheik Abdulbasit Abdulfattah ba bahaushe ba ne iyaye da kakkaninsa duka yarbawa ne,ammh sun fito daga Tsatson gidan malamai ahalin sunna Shiyasa ba sa kyamtar Hausawa ko wasu yarukan, suna auran junan su sannan sukan yarje ma mutum ya auro dukkan yaren da ya yi masa ma'ana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login