Showing 165001 words to 168000 words out of 288345 words

Chapter 56 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

732

mata ban dauka zai iya kallonta ba, ammh dayake Namiji sunnsa Namiji sai ga shi sun shirya an shiga kurya an yi lamo,Daganan na san sha'anin mata da miji sai Allah Shi da har masifa ya rikamin wai na ce ta tafi nace dayake ni na kawo ta ba,Bata koma ba sai da suka Daidaita da juna kwananta Biyar ta koma Abuja,motar Haya ta shiga abunda bata tayi ba ammh ga shi Namiji ya sakata acikin wani Hali.
Ni daman tunda yace na cire bakina na kama kaina, ko da tazo ta zaunar dani tana gayamin har abunda ma bansani ba iyakata da ita hakuri kawai Domin kamar yadda yace ba ruwana to ba ruwana din.
Mun yi azumi sha biyar Hafsah suka samu Huta,Washegari Yaya Abdul'Ahad yazo wajen Raliya shi ya wuce da ita Tare da Anum da Laila ta matsa sai an zo mata da ita haka kurum Allah ya hada kaunarta da Anum da taji ma dagantarkar dake Tsakani sai tace daman ba haka kawai take kaunar Anum ba ashe jini d'aya muke da mijinta.
Musty har da kuka akan sai ya bi Anum Dakyar Babansa ya Lallashesa akan zamu je da sallah sannan ya Hakura,Azumi nada ashirin da Biyar sakon Abba na kayan sallarmu ya iso karofi aka kai,Yaya Isa ya kawo min nawa har gida duka da ni da yara.
Har da Babansu,kala biyar biyar,harda na Anum data ke chan Da na Hafsah kenan wasu za'a sake dinka musu Yaya mariya haka aka kai mata nata ita da Yaya Asiya,Bakina yaki Rufuwa na kira Abba ina masa godiya sai yace"Ba godiya tsakanimu Fa'iza duk abunda nayi muku ba komai ba ne, ku ya'ya na ne kamar yadda zan yi ma Nana Fadila haka zan yi muku"
Sai na kasa mgana,Saboda farinciki ya gamamin komai ganin ba na Mama aciki sai na saka kudi na siya mata kala uku har da Hijabi da takalmi ta karba Karo na farko da Mama ta taba godemin bayan nayi mata wani abun alheri..
Shi kuma Yaya ishaq da nace ya kira Abba yayi masa godiya sai yace"Ba kin kira shi ba?sai na Dagamai kai cikin basarwa yace"Ya wadatar kin hada da godiyata da naki godiyar"daganan ban kara mai mganar ba,na lura ba duka halinsa ba ne ya sauya wani Lokacin rashin Mutumcinsa na nan bai tafi ba,Wannan karon dai mun yi sallah cikin Farinciki da wadata Jamal ya Dawo gida sallah shima nayi masa kayan sallah har da Hula da takalmi,Badariya a kano tayi sallah Tace Hajiyar Dala ta mata kala Daya nima na tura mata kudi tayi guda Biyu ta kara da shi Saboda yanzu ina samun kudi sosai tunda bana taba kudin sana'ata tunda Abba ya karamin jari abubuwa suka daina Cushemin ga shi muna da kayan abinci sosai,wannan sallar ko Anty Binta bata kawo mana komai ba ganin bana neman komai,Naman salla kuma Abba sa ya saka aka siya aka yanka a karofi aka raba mana Nama,Ni kuma na siya mana kaji,sai bayan na siya ma Hajiya ta aiko mana da shi,Sai dai ma muka rika kyautarwa,Ranar sallah na uku naje Karofi ni da yara muka kwana Daya muka Dawo sai kuma washegari naje Gidan su sa'adatu nima tazomin ranar Sallah na biyu,Daganan na sauka gidan Hajiya ana ta fentin gida saboda Biki bayan salla da Sati Biyu ne.
Hajiya tace wajenta zan zauna kaduna sai za'a tafi da Raliya sai na bisu mu tafi ina Dariya ina fadin"Hajiya su da suke jiran mu tun ana sauran Sati daya..?
Hajiya tace"Aa su mariya su je ammh ke kina gidan nan ai Raliya kanwarki ce, ke zaki mata gyaran jiki da Hadin Turaruka'"Na dauka Hajiya wasa take yi sai da Ammi ta kirani tana fadin"Fa'i shikenan sai Hajiya ta mana Haka.? Ina uwar d'iya ammh ana min fin karfi akan ya'yana".
Nidai dariya na dinga yi ban yi mgana ba ina jin Abba na gefe na fadin"D'anki zata gyara ma Amarya fa Maman Nana"
Sai tace"Kuma fa hakane to na d'aga kafa. ammh da sharad'in a Turaran Amarya za'a dibarmin nayi ma Baban Nana kwalliya da shi"
Abba yace"Shikenan kuwa na uwar miji da matar d'a ba"
Ni dai sai dariya nake yi in ka Biye ma Abba da Ammi sai cikin ka ya Kulle Tuni muka shiga shirin Biki,Biki ne na manyan mutane,Balle Abba wannan ne na farkon da zai aurar da Namiji,an aiko da katinan Daurin aure kayattu Abba yace duka jama'ar Karofi yan'uwa na kusa kusa yana gayyatarsu,Har Hajiyar Dala Yaya Asiya ta gayyata ita da suke ta shirin su ita da yan gidan su Ammi ga Nana Fatima a kusa da ita, tunda har gidan juna sun je ina Dutse ina kano.
Hajiyar Dala taga bikin na irin nasu ne tace zataje har kaduna,sai mamaki take yi yadda Lokaci da'ya Gata ya Lullube rayuwarmu yanzu babu abunda ya'yan gata zasu nuna mana muna.
Nima a barayina na gayyaci su Anty Binta da su Anty mahma,da mama ni daman ina gidan Hajiya kamar yadda ta fad'a,Hajiya tamin dinkunan ankon Biki,Kala hudu har da na Lonching din da zata hada na mata zallah,achan kaduna ma su Nana Fatima sun ce duka kayana sun zama Ready na fitar Biki achan zasu yi Dinner din su gabad'aya.
A na saura sati daya biki Badariya ta Dawo suka fara shirye shiryen saboda gyaran jiki sai suka tare a gidana nan suke kwana,gefe daya kuma ina hadin Turaruka ga zuwa gidan Hajiya ba na ko zaman gida,Abba ya kirani yace na turo yara suzo tunda ni sai ranar Daurin aure,sannan a kaduna za'a Daura auran Raliya gidan kanin babanta Hajiya tace ayi chan yafi sauki kawai,su Goggo duk zasu tafi kaduna ana gobe biki sai na had'a su da yaran suka fara yi min gaba da su Mama su goggo tabi Anty Binta kuma ita da Anty mahma da Halisa direban Anty Binta zai kai su, su Yaya mariya da su Yaya Asiya tuni suna kaduna ana sha'ani da su sai kirana suke yi naji kamar nima nayi tsuntsuwa na ganni achan.
Tun ana gobe biki na tare gidan Hajiya,gidan ba kowa sai Yaya Ishaq da jamal,zasu Daurin aure gobe domin Abba yace yana son ganinsa,mota guda Hajiyar su Raliya ta basu zasu bi tawagan mazan da zasu tafi daga nan katsina. mu ko muna chan muna ji da Lonching,na hadu da manyan mata sosai kawayen Hajiya,Amarya bazatayi walima ba sai ranar Lahadi da yammah bayan an kaita gidanta,Hajiya da ya'yanta ni suka saka kan abinci akwai ma'aikata ammh ni nake nuna musu yadda za'ayi.
Ranar asabar daya daga cikin asabar din karshen mako aka Daura auran Raliya Kasim Saulawa da angonta Abdul'Ahad Usman karaye a garin kaduna a masallaci sultan bello,Ana gama Daurin aure ango da Tawagansa suka nufo katsina inda akayi pinic party dasu da kawayen Amarya adaran Ranar,Washegari sai shirin kai Amarya tun Safe aka shirya Daman tuni an je an yi mata Jere a gidanta acikin garin kaduna zai zauna anguwan Sarki chan yake da gidansa mai kyau.
Amarya su suka fara yin gaba ita da kawayenta da angwaye,mu kuma sai da muka Tsaya muka shirya wasu kaya muka tafi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? da su,Sai yammah muka isa kaduna,gidan Raliya muka fara sauka chan na iske su yaya mariya da su Nana Fatima sun zo tarban Amarya muka Rumgume juna muna murnan ganin juna, sanye nake da Less din da Hajiya ta dinkamin na yinin ta nayi kyau duk da ban yi kwalliya ba,Da anan za'ayi walima sai aka sauya akace Ndc za'a koma gidan Abba achan za'ayi,gabadaya muka tattara muka koma chan,Hafsah sai wajen walima na ganta ita da Nana khadija sun ji kaya iri daya kamar yan biyu su Anum kuma an saje cikin su Falaq sai dai naji ana fadin Umma haka su Ahmd sun ci gayu suma suna ta wasan su cikin yara sa'aninsu.
Su Yaya ishaq da mazajen su Yaya Asiya Abba ya hanasu tafiya suna nan tare da shi,Sai bayan isha'i aka tashi Daga walima,aka kuma fara shirin Tafiya Dinner ni dai ina ganin in da ake bikin yan gayu,sai ga shi duniya juyi juyi na gaba ya koma baya.
Sai ga shi su Anty Binta da Mama ne a rab'e mu kuma mune amara kirjin biki.




*Janafty*




[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2015*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Kuma daidai gwargwado ba'a wulakantasu ba,an kula da su sosai duk abunda suke so shi suke yi,ba mai hanasu.
Balle kuma ga Badariya da sune manyan kawaye,Raliya ta mata komai na kayan fitan biki,kawancen su ba irin na sauran kawaye ba ne hatta duka ankunan biki duk Hajiya ta siya ma Badariya,Sai dai kunya ce da nauyi yasa suka koma gefe suna kallon abunda ke gudana.
Sanda muka zo naga Abba muka gaisa shima wajen Ammi yazo suna mgana,Baya gidan suna Hotel inda bakin sa suka sauka har da su Yaya Ishaq suna chan suma,Abba sai da yayi min tsiyan ido na kenan..?
Ina dariya nace"Abba kanwata na tsaya nayi ma rakiya"
Ammi tace"kuma matar yayanki ba"
Mukayi dariya gabadaya Ammi bata manta ba sai da tamin mganar Turaranta nace nazo mata da shi sannan tace na fita ko ba soso da Sabulu, abunda na lura da shi Ammi macece wayayyiya mai son kamshi da gayu,domin yar gayu ce ta Bugawa a jarida in ba an fad'a maka ba,baka isa kace itace mahaifiyar Yaya Abdul'Ahad ba,Tana ta shiga tana fita ko a jikinta damu da yaranta duka D'aya ta Daukemu.
Da ita da kawayenta da yan'uwanta suma suna ta shirin zuwa Dinner din Shashen Ammi aka sauke Amarya da Tawaganta,mu kuma shashen Abba gida ne ba ni da gida ba wajen Haduwa da kayan more rayuwa,babban gida mai shashina ba adadi harta Yaya Abdul'Ahad yana da shashensa a gidan.?
Da zai iya zama da matarsa basu takura juna da su Ammi ba,nan su Nana khadija suka zauna da Kawayensu,dasu Hafsah da aka zama yan matan kd,su Goggo kuma suna Shashen Inno ita da su Baba Ati suna nasu sha'anin.
Muna shashen Abba sai shirin Tafiya ake yi Kaya iri d'aya Suka dink'amana Dukkanmu har da Nana khadija da Hafsah,wani uban su material mai ja da baki,yayi kyau matuka dukkammu dinkin Dogayen riguna suka yi mana,Irin na zamani Fitted,sai head ja,da zamu nada da takalmi ja da Karamar pos har da mai yi mana kwalliya na musamman. yaran kuma daga mata har mazan su shadda Fara aka dinka musu sai akayi amfani da zare ja wajen aiki da kwalliya,Ina kallonsu suna ta shiryawa tuni har an fara yi ma su Nana khadija kwalliya,Da farko kayan naga kamar baza su yi min ba, sai da Nana Fatima ta saka nata ta matsamin nima na sake yin wanka na shirya sai ga shi kayan yayi min cif a jikina kamar an gwadani,na juya na kara juyawa na kalli Nana Fatima ina fadin"Wannan ba irin namu ba ne Nana, sun matseni fa dinkin yanmata ne"
Harara na tayi tana fadin"Ni juya na zage miki zif din riga. Ba wanda yace ga dinkin yanmata da matan aure kaji matar nan"Ina dariya na juya ta zage min,na ja head din ina shirin Daurawa ta Fizge tana fadin"Meye haka.?kai tsaye nace"Daurawa zan yi mana"Da karfi tace"Daurawan ta. Mai kwalliya zata daura miki bayan ta gama miki kwalliya"
Sai na Bude ido Lokaci d'aya ina fadin"Ni za'ayi ma wannan fenten fenten haba Nana mana wannan sai su Hafsah"
Dariya tayi Lokaci d'aya tana fadin"Har su fa'i yau sai sun yi kwalliya"na zata wasa take sai gashi tamin Taron dangi Nana Fadila tace"Muma nan kwalliyar zamu yi fa'i banga abun damuwa ba'
Na marairaice ina fadin"Anty Fadila ban fa taba yi ba, na dauka kwalliya na masu kyau ne da yan gayu"
Sai suka kalleni suna Dariya Nana Fatuma tace"Kaji wani Tunani kuma. kwalliya da gayu na macen data san kanta ne Fa'i,kuma yau ko zaki suma ne sai kin yi kwalliya"
Taruwa suka yi suna ta gayamin amfanin kwalliya ni jinsu kawai nake yi, ko kunshi da gyaran kai da nayi Hajiya ta matsamin da na rakata gyaran kai tace sai an yi min, sannan da mai kunshi tazo tace na zauna ayi min gaskiyan mganan hausawa da suke cewa duk wanda ya gyara zai ga dakyau ni kaina nasan nayi kyau a baya ina Tunanin bakin Fatata? bazai saka lalli ya zauna ba sai gashi ya fito ras da shi,Tabbas na yarda ko kana da kyau ka kara da wanka ni kaina da yanzu na samu sauyin rayuwa Fata ta fara gogewa.
Ban gama mamaki ba sai da naga har su Yaya Asiya sun sha kwalliya an buga musu Dauri ita da Yaya mariya na kallesu na kwashe da Dariya ina Fadin"Yaya Asiya wai kema ahaka zaki Dinner din.?
Fari tamin ido tana fadin"Kwarai ma kuwa Fa'i bari ma na kira baban Usaini yace min Abba yace suma sai sunje fa"
Ta wuce tana wani juya jiki gabadayammu muka saka Dariya mamakin yadda ta sauya kawai nake yi Yaya mariya ko sai faman duba madubi take yi na kalleta nace"Yaya mariya mata a gidan Manaja"
Ta juyo tana fadin"fad'i ki kara kuma dagani ba kari"
Kawai sai Nana Fatima ta saki guda suka tafa da Yaya mariya chaa sukamin Dole bayan an gama ma Nana Fadila na zauna nima akayi min kwalliyar zamanin da a baya na Dauka sai a Fuskar mata masu kyau ake yinta,kuma yayi kyau ba irin mu munana kuma bakake ba.
Fuskata naji duk ta Daure,har abun ido aka karamin ina bana so ba na so Nana Fatima tace sai an sakamin,Ina tura baki tayi dariya tana fadin"Sai fa kin zama yar gayu kema Fa'i ga mijin ki na ganshi dan gayu da shi ammh ke baki son gayu"
Yaya Mariya ta tabe baki tana fadin"in dai Fa'iza ne abun haushi yanzu kika fara gani, gabadaya ta maida kanta baya shiyasa har miji ya raina ta ya yi mata kishiya'
Sai Nana Fatima ta Tsaya tana kallona cikin mamaki tace"Fa'i daman kina da abokiyar zama ne shine ban sani ba..?
Sai na kauda zencen da cewa"Kun san fa kari ba kyau a addini"
Yaya mariya tace"Allahu akbar Sayyada"
Da na Dake bana so ne sai Nana Fadila tace kada a sakamin a barmin ido na haka,Sai da aka gama na duba madubi sai naga kamar ba ni ba gabadaya Fasalina ya Sauya na sake kallon kaina na koma na kalle su kafin nace"Wai fuskata ce haka..?
Sai suka kwashemin da Dariya,Nima kaina sai da nayi dariya,ko wajen saka Takalmi an sha Fama dani yayi min Tsini Nana Fadila tace"Ke da ma baki da tsawo fa'i ai na irin ku ne"
Kamar zan yi kuka nace"Ban saba sawa ba. Kuma ban iya tafiya da su ba"Nana Fatima tace"Zaki koya yanzu malama"Haka ta sakamin shi mai igiya,ina tafiya ina neman fad'i Suna min Dariya.
Ammi ta shigo tana fad'an ga motoci chan a waje ana ta Daukan mutane goma ta kusa dare yayi sai taga ina tafiya ina Tangad'i salati ta saka Tana fadin"Me zan gani haka Fa'i..?
Ina matse ido nace"Ammi bazan iya tafiya da shi ba don Allah kicesu kyaleni"Ammi tace"To bari kada ki yi kuka ki bata kwalliyan ki.."
Tafiya kuma da takalmi ya zame miki Dole ana mganar gayu fa'i ko ni kalleni Da wanda ma ya fishi"
Tafada tana d'agamin kafarta mamaki ya kamani nata baki ne mai igiya kalan leshin jikinta a bunka ga farar Mace Less din data saka baki ne sai ya haskakata na zata Ammi zata Sassautamin? ne,itama fad'a ta kama min tana fadin"Saki jikin ki ki yi tafiya ba zaki fadi ba. In baki koya ba sai yaushe Fa'i? yanzu in Tafiya ta kamamu na shiga Villah haka zaki je kina yi mana?
Suka ko kwashe da Dariya Nana Fatima tace"Sai mu tafi mu barta"Ammi tace"Aa fa da ita zamu rika shiga ko'ina bame barinta a baya"
Dole zata koya yadda baki da Tsawon nan ai irin takalman ki kenan yarinya"Ina ji ina gani suka hanani cirewa Yaya mariya tace"'Fa'iza fa sai a hankali komai na gayu bata iya ba"
Ammi tace"
Zamu ko b'ata da ita.Ko ni da nake sauke ku ina gayu na ina Dalili. Shiyasa ban jita tana tashin kamshi ba,kamata yayi yadda kike sana'ar kayan kamshi da jikin ki da Dakin ki sai sun kama kamshin ki, ammh ba ko d'aya"Sai kunya ta kamani na Sadda kaina kasa ammh ita ko ajikinta ta cigaba da min fad'a tana fadin"Mace sai da gyara Fa'iza muma fa duk burga ce,Adon ne ke cetan mu"Tafad'a tana fari gabadaya muka saka Dariya Nana Fatima tace"Ammi to har kishiya fa'i fa gareta..?
Ammi ta saka salati kafin ta mangare ni tana fadin"Ba fad'an yanzu ba ne zama zamu yi,mu yi mata? na musamman wuce muje"
Saboda kada Ammi tayi mgana yasa ban ce komai ba, da naga zamu fita dagamu sai wani karamin mayafi,ance Tuni Yaya Asiya da Nana Fadila sun tasa yara sun yi gaba,Mun fito Falo sai ga ango yasha kamshi sai Nana fatima ta fara kirari yayi Tsaki yana fadin"Ku daman baku tafi ba..?
Tana dariya tace"Tawagan ango zamu bi"Kai tsaye yace"To ku cigaba da jira. Ammi wai ina Abba sai kiran wayarsa nake tana kashe"
Ammi tace"ban san to ina ya tsaya ba. Dazu dai ya kirani yace ga Engr ya sauka daga a kaduna daga Lagos yazo masa murna, bai samu zuwa Daurin aure ba"
Abdul'Ahad yace"Engr din yazo ne Ammi?
Tace"Baka ji me nace ba ne, yazo ammh inaga ya wuce domin Baban Nana yace min Karfe goman daran nan jirgin su zai tashi daga abuja zuwa London zai raka kakarsa ganin Likita"
Kasan tana fama da matsalan koda"Abdul'Ahad sai ya fice yana fadin"Ammi in kin same sa kice ya tabani"
Mu dai waje muka fita motoci sai kad'an tunda duk sun wuce sai Amaryan da tawaganta su kuma angwaye zasu bi,Allah sai ya jeho mana Mijin Anty Laila uncle Junaid yaje ya kaisu Laila ya dawo Nana Fatima ta Dafe mana shi ya kaimu ni da ita da Yaya mariya Ammi agida muka barta tace za'a kawota.
Wani Hadadd'en wajen Event ne mai girma da fad'i goma ta wuce ammh kamar rana chan muka iske su Anty Binta da Mama sun je suma,su Goggo dai na gida sun ce a raba su da zuwa wani shegantaka da Daddare.
Amir na ganina ya taso yazo kusa dani ya kama Hannuna yana fadin"Umma kin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login