Showing 240001 words to 243000 words out of 288345 words

Chapter 81 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

767

da naje gaida Inno,bayan mun gaisa ta kalleni tana Fadin"Naji abun alheri wajen Aziza..Bawan Allah ne mai halin kirki ne matuka Baban ku yasan karamcin sa in kika amince masa bazaki yi nadama ba Fa'iza, sai dai bamai yi miki Dole kamar yadda Baban ki ya fada duk abunda kika zabama kanki daidai ne Allah ya sanya Alheri"
Na kasa amsawa a fili sai acikin zuciyata haka na koma daki jikina a sanyaye,ina ko daukan wayata nagama ya kirani har sau uku ina shirin kiransa sai ga shi ya sake kirana ina Dauka yace"Gaskiya ni dai ba'a kyautamin ba gaskiya"
Ina mirmishi nace"Da aka yi me ne..?
Sai ya basar yana fadin"Kin ta shi lafiya?nace lafiya lau muka gaisa nan yake fadamin zai bar kano Jirgi zai bi zuwa chan Edo din ba zato fa tsammani naji yana mgana sama sama sai naji wata yar tsohuwa na kwalamin sallama na amsa na gaisheta cikin girmamawa da ta fara kwarara mana addu'o"i sai da naji kwallah ta zuromin tsohuwar nan akwai addu'a a bakinta.
Sai da ya karbi wayar ne kafin nayi mgana ya rigani da cewa"Hajiya ce kakata ta bangaran uwa. na bata labarin ki ne sai kuma taji muna waya sai tace na bata ku gaisa,sai na bata ai kin ga yawan gaisuwa yafi yawan Fada ko Faa'izaa..?
Sai nayi Dariya kafin nace"Hakane Engr"
Yana kada Harshe yace''Laalaa aiko zamu bata ke ma Engr ne a bakin ki..?
Sai da na rufe bakina kafin nace"To Ko Tosin zan ce...?
Yanayin mganata yasa yadda na fadin Tosin sai da naji kyatatan Dariyan sa kai kawai yake girgizawa yana Fadin"Zan rama ne zan rama Faa'iza"
Da wannan hiran muka yi sallama yace zamu yi mgana bayan ya sauka,ammh yana Filin jirgi sai da ya Kirani daman ina Daki waya a kirjina kamar yasan Tunaninsa nake ina Mirmushi ni kadai.
Da rawan jiki na dauka ko sallama ban gama yace"Sharadin mu gobe ne ko Faa'izaa..?
Cikin mamaki nace'Sharad'in me..?
Sai kawai ya yi mirmishi kafin yace"Ashe zan dawo kaduna yau kuwa..?har kin manta..?
Ina jin haka na fara dariya sai shi kuma ya kanne yana Fadin"Kwana uku zan yi a Edo zan shiga gida Benue dagachan zan je Abuja, wlh bakin nan nawa bai Haila sai na gama yadaki a Dangi gabadaya"
Da Sauri nace"Kai don Allah kamar wata yarinya..'"
Shima kai tsayen yace"Yarinya ce mana shekaran ki nawa..?
Kai tsaye nace"35..ban karisa ba ma sai watan jibi"
Irin Dariyan da ya yi ta nishadi kafin yace"Ashe ma da yarinya nake mgana.? Ni ai ban ga? baban mace ba yarinya danya Sharaf zan dauka nima ta jikani da yarintarta na dawo Dan Saurayi shar dani"
Dariya ta kamani kafin nace"da Furfuran zaka dawo yaro.?ni kuma da ya'yan hudun zan zama yarinya sharaf.?
Yana shafa kansa kamar ina kallonsa yace"Ke bar wannan mganar muma fa Tsiffon nan mun iya romancewan nan ko wasu matasan albarka,bar ganina haka Tsab zan dawo dake yarinya Dayan sharaf dake abun da duk mun san komai"
Ya karishe fad'a yana Dariya kunya ta saka na kashe wayar yana ta kira ban Dauka ba kawai sai ga sakon shi.

"Karya nayi Tosin da Faa'izaa basu san komai ba..?

Lalle Engr yafi karfina haka na fad'a a cikin raina ina mirmishi in akace zan iya sakin ma wani namiji fuskata da zuciyata sai nace karya ne,yadda Ishaq ya karya duk wani kwanjina ashe ban sanu jarumin maza ba ne sai ga shi kwana Daya da yini Daya Engr na neman Sauya rayuwata daga Duhu zuwa Haske,sai ga shi ni mai ijiye waya sai ayi ta kira ban ji ba? sai ga shi ina yawo da waya a hannuna Saboda kada Engr ya kirani bana kusa ransa ya baci.
A rana ban san adadin sau nawa yake kirana ba,ranar dai har sai da nace masa"Kana kirana kamar kana kiran wata budurwa..?
Kai tsaye yace"Budurwa ce mana ni kuma Saurayin ki ba"
Ina Dariya nace"A ina na zama Budurwa ya'ya hudu fa suka fito daga jikina"
Cikin Shakiyan cinsa yace"Allah..?ni ko kin ga da na ganki ban ga ta inda suka fito ba..?ta ina ne..?
Ko sai nazo zaki nuna min.?
Ai ranar yini muka yi bamu mgana ba ya kira har ya gaji ban Dauka ta bakin sa Tosin bakinsai ai ba Saiti.
Sai dare na dauka muka yi mgana shi bai san ya yi wata mgana ba cikin Hade murya yace"Ni dai bana son wannan Horon Faa'iza.
Ko aure muka yi ko laifi nayi miki kada kice zaki Daukemin zaki sakani cikin wani Hali, da kiyi gaba dani ai gwara ki ce Tosin Saka gwiwoyin ka a kasa ki saka Bulala ki zaneni zai fimin kwanciyar Hankali da ki horani da rashin jin muryan ki na yini d'aya"
Jin yanayinsa yasa na basa Hakuri nan da nan ko ya saki yace an yafe min ammh next time in na kara to basan kuma wani mataki zai Dauka a kaina ba.
Ikon Allah akace sai kallo sai ga shi na saki jiki na da zuciyata na bama Engr duka amanar rayuwata batare da Tunamin komai ba tunda da kwana Biyun da na dibar masa ya cika ya rika Damuna da naci? mganar. kwanan sa Biyu a Edo ya koma Abuja ya kirani a waya ya Hadani da mahaifiyarsa da yake kira Sweetheart.
Ce mata ya yi ga Faa'iza na son su gaisa cikin kunya muka gaisa yana karban wayar tun kafin nayi mgana yace"Ko ki bani amsata ko kuma wlh mu yi miki gayya har da Papa ga shi nan zaune"
Nasan hali fa zai aika sai nace zan fad'ama sa gobe shima bai barni ba sai da na fadi Time nace da Daddare,ai ni nama manta da kowa da komai Tunanina da mafarkina Engr ne ciki da bayana,Ammi daman ta rigani ta fad'ama su Nana Fatima sun kirani Anty Fadila ce ma bamu yi mgana ba,ta kirani ban gani ba sannan nace zan kirata daga baya ni kuma sai na manta tunda na zama bani da wani Tunani sai na Engr.
Nana fatima kuma ta nuna min goyon bayanta sosai kan al'amarin,Abba ne dai bai ce min komai ba har ranar ni kuma naga rashin kyautarwa na yanke ma kaina hukunci batare da saninsa ba har ga Allah na Ture ishaq da komai a gefe yaran ma bamu kara mgana da ba,su ni kuma ban kira su ba.
Ganin Lokaci na ta tafiya ga Engr bazai bar ni nayi sukuni ba yasa Abba na dawowa naje har falon sa na samesa.
Kunya da nauyi suka lullubeni na kasa mgana shi kuma sai ya gane me ya kawo ni cikin mirmishi yace"Fa'iza mganar Engr ne ko..?.
Sai na gyad'amai ammh na kasa hada ido da shi nauyi nake ji yaushe nasan Engr..?Sai nake ganin kamar Abba zai ce nayi gaggawa kuma ni dai bansan me yake fizgata ba nasan dai ina adddu'a ammh duka mafarkaina na Engr ne bana ganin kowa sai shi.
Kamar Abba ya karanta abunda ke raina ya gyara zama yana kiran sunana sai da na amsa sannan ya cigaba da fadin"Fa'aiza kamar yadda na fad'a a farko yanzu zan kara maimatawa bazan yi miki Dole ba. kamar yadda shari'a ta baki Dama nima na baki. Engr mutumin kirki ne mai Halin Dattako in nace zan fada miki Tarin hallayansa sai kice ina yabonsa ne ammh ni nasan kin fara gani Saboda shi mutum ne Free da kowa ya zauna da shi ko na yini Daya ne sai ya tafi da halinsa masu kyau a baki. Bazan ce ki amince masa domin yana Tare dani ba? sai domin zabin ki. Ki natsu kada ki yi gaggawa Fa'iza abunda duk kika yanke ni ina Tare dake har Abada"
Sai naji kalaman Abba sun sakamin natsuwa cikin gyada kai na amsa mai Tare da godiya Abba yace"Allah ya sanya alheri Fa'iza.'
Na kasa amsawa da Ameen sallama nayi masa na fice ya bini da kallo ko da ban fad'a ba labarin zuciya ai a tambayi fuska yasan Engr ya gama Siye zuciyar Fa'iza da Halinsa shifa Dan baiwa ne yana ma siye zukatam maza ba ma mata ba.
Tabbas in Fa'iza ta amince ma Engr sai yafi kowa murna ba saboda komai ba sai saboda Halin nagartansa,ammh kuma yaji matsanancin Tausayin Ishaq ya kamasa ko dazu yana Office ya kirasa sun gaisa suka yi ta Hiran aiki,sannan ya jisa cikin farincikin da har sai da ya tambayesa? ko ya samu karin girma ne sai ya yi dariya yace"Abunda na samu yafi karin girma Abba.wani abu ne mai muhimmanci da ya kubcemin har na Fidda rai yanzu zai dawo gareni"
Kwata kwata tunanin Abba bai basa mganar Fa'iza yake yi ba, sai yayi masa Fatan alheri shi kuma Ishaq bai fara ma Abba mganar ba yana jin kunya da nauyi yana Tunanin da Sanin sa Faa'iza ta yanke komawa gidansa.
Abunda kowa bai sani ba tuni labarin zan koma gidan Ishaq ya Zaga Dangi har Karofi bakin su Goggo,Itama Yaya mariya tazo tana fada musu itama a bakin Anty Binta taji tunda Anty Mahma ta haihu sun je suna sukaji ana ta maida zencen Yaya mariya abun ya bata mamaki tazo ta samu Goggo ita kuma tace anya.?
Bata sani ba ammh bari Mallan ya dawo taji ko Abba ya kirasa sun yi zencen to shima abakin Goggo yace yaji bai sani ba jin haka yasa Goggo sai ta Dauka shirme ne jin ko ni ban gayamata ba ballatana shi Baban namu.
Labari har Bauchi Mama ta fad'ama Badariya ba wanda ya kaita Murna ita da Jamal,Anty Fadila ko har gida Ishaq yaje ya sameta da mganar kan zasu je tare ta zabamin Furnitures din da za"a sakamin a dakina,abun itama ya bata mamakin zan dawo ammh bataji ko a bakin Abba ba,sannan ta kirani bata Sameni ba Abba kuma data kirasa sai yace yana meeting ne zai kirata Daga baya.
Ayyuka suka sha kanta bata ko yi zencen da kowa ba. a tunaninta ai za'a sake Daura aure tasan Dole za'a fadamata sai bata kara neman wani da mganar ba ammh da ita akaje aka siya min komai na kayan Daki masu kyau da yarari har ga Allah taji dadi ganin ma yaran nata Murna har da ita Zainab din da Mama yasan ta san gabadayan su suna maraban da dawowata a ranta tace nayi hankali da zan dawo saboda ya'yana mganar Engr kuma Ammi ta fad'amata ammh jin wannan mganar sai ta Dauka Abba ya basa Hakuri shiyasa ma bata Damu ba.
Bani da masaniyar mganata ta zama zarar buni gabad'aya tunanina da komai nawa yana kan Engr,Sanda na fadamasa na amince masa kai tsaye a inda yake ya duka ya daidaici gabas ya yi sujudul shukur ta godiya ga Allaj sai da ya dago sannan yace min"Alhamdulillah nagode sosai Faa'izaa.ban yi miki alkwarin Farinciki har abada a tare dani ba.
Sai dai nayi miki alkawarin zan yi iya kokarina wajen hana Faruwar bacin rai ko damuwa a kan fuskarki."
Yadda kika amince dani kika bani amanar Ragamar rayuwarki ni kuma ina rokon Allah ya bani ikon rike ki bisa gaskiya da amana kada ya barni na zama silar zubar hawayen ki watarana"
Kalamansa sun saka sai da nayi hawaye na tuna ban fa sauya ba ina nan a Fa'izata baka,mummuna mara gata da galihu,mai raunin ji mara ilimin boko wacce batajin Turanci bazawara mai ya'ya hudu ammh mutum kamar Engr da ya mallaki komai na matakin rayuwa ya ce yaji ya gani sai nima na sallama wata irin Soyayya yake gwadamin kulawa ko kamar tsoka daya a miya,Engr duk yadda zai sakani Dariya ya sani in muna wayar har hawaye ina yi Saboda Dariya ba shi da girman kai kamar sauran maza a baya na Dauka maza ire iren su suna da Dagawa sai da na hadu da Engr na karyata haka sannan na kuma gane me ake kira soyayyah ina jinsa a raina Fiye da yadda nake jin Ishaq a baya acikin Raina. kada ku ga laifina na yi shekaru Cikin bautar aure da Tozarci bansan ace ana sona ko na Burge ba yanzu kuma na samu mai sona wanda yake nuna ma duniya ba kamar ni sai na Zama kamar wata sauna kira mana shashasha zuciyata da gangan jikina ta fara bin Umarnin Engr da duka Bukatansa.
Duk da bai gayamin komai akansa duka ba ammh a Hankali na fara Fahimta,Nayi waya da mahaifiyarsa Hajiya Shukra matar nan tun bata ganni ba ta kaunaceni,cikin muryanta mai sanyi da muka yi waya ta rika min Godiya tana sakamin albarka sannan mun yi mgana da Sisters dinsa duk da Hausan su bata fita sun fi iya Yarbanci da turanci ni kuma ba Turanci sai Hausa kawai ahakan ma nagodema Allah,Mahaifinsa ne bamu taba mgana ba yace sai na zama amarya zamu je ya yi mana Nasiha Benue ko sai nagaji da zama cikin yarbawa akaso ne da kilose sai nagaji da ji,in ya fad'i haka sai dai nayi ta Dariya,ga shi ko da wani Lokaci muka yi waya sai yace ina yara..?
In nace suna lafiya sai yace ina Fatan kin fara basu labarina saboda ina so ranar da zasu fara ganina na bude hannuwana su zo da gudu suna rige rigen kiran sunana da Baba..Baba..!
Ina Dariya nace"Ba Baba Tosin ba..?
Daure fuska ya yi kamar yana gabana kafin yace"Ni ai tosin din Faa'iza ne a wajen Ya'yana sunana Baba Abdulbasit'
Kai Engr abun dariyansa basa karewa.
Dakyar a Daddafe ya yi sati biyu yazo ya ganni ni kawai na kawosa kaduna yazo yayi awa biyu,Abuja ya koma Tunda a daran zai bi jirgi zuwa Lagos,A ranar hirar sa duk ta mganan auren mu ne? yace zai je America next month,yana so kafin ya tafi a Daura mana aure,ni kuma sai nace ya Tuntubi Abba da haka muka rabu,ni in ana fadin Engr nada kyauta bana gani domin bai taba bani ko Biyar ba. sai da yana samun kati yace na kira Yara bayan haka bazan dora komai ba. nima ba wannan ne a gabana ba shiyasa ban damu ba.
Ranar da yazo Ammi har kwalliya tasa nayi nace mata a hakan yace yana sona baya bukatar wani kyale kyale da Katon Hijabina har yana sharan kasa naje masa ko kayan jikina bai gani ba ammh haka ya rika zuzuta nayi kyau Allah sarki Rayuwa ashe akwai ranar da ni Fa'iza zan iya Burge wani..?
Tabbas ko ban auri Engr ba ya yi sanadiyar kafa aya mai girma a Rayuwata.
Kowa ya ganni yasan ina cikin Farinciki da Annushuwa sanadin Tarayyata da Engr,sannan na samu natsuwa tunda su Anum basu karamin mgana ba itama Zainab din sai dai mu gaisa,ashe ban sani ba shi Gogan ya hana su karamin mgana Tunda acewarsa yasan Halina da Taurin kai yanzu sai na iya Sauya ra'ayi.
Kuma har alokacin bai nemeni ba ammh yana ta shirin dawowata Alhalin ni da shi bamu yi wata mgana ba.

******

Watan mu daya da Haduwa da Engr,Makarantar Haddanmu ta kiramu akan Karban shahada, mu goma Cif zamu karbi shahadar Haddan Qur'ani izifi Sitti,Dole zan koma karofi,Har ga Allah har zuwa Lokacin Abba baisan Halin da ake ciki ba ta bangaran Ishaq ba,ammh sun yi mgana da Engr sosai ta waya akan aurena yace masa ba shi kadai ke da ni ba ina da yan'uwa da iyaye achan karofi zai je ya same su,abunda suka yanke zai Fada masa da haka ma suka rabu.
Sai dai kuma bayan ya samu Inno sun Tattauna itama ta goyo bayan yaje ya samu Goggo da Mallam su tattauna,Ya shirya tafiya ma karofi sai kuma Ishaq ya kirasa da wata mganar data sa ya kasa gane ina aka nufa.
Abunda ya faru shine Mama ta yi ma Ishaq maganar yaushe za'a maida auran..?
Har ga Allah ya ma manta da sai an kara Daura mana aure,ya dauka kawai zan dawo ne ita ta ankar da shi,Sai alokacin ya tuna da sai fa an kara daura wani auran shine Dalilinsa na kiran Abba bayan sun gaisa da Tambayan aiki Ishaq cikin jin nauyi ya yi kasa da Murya cikin Ladabi kafin yace"Abba nace ba..yaushe kuka saka ranar Daurin auran..?
Sai abun ya bama Abba mamaki cikin mamakin yace"Daurin aure kuma..?
Auran wa..?
Ishaq na jin kunya yace"Ko bata fad'a maka ba ne Abba..?
Abba da ya fara hasaso abunda ke faruwa yace da sauri'"Ita wace ce? bata fad'amin ba? kuma me zata fad'amin"
Sai ishaq ya yi tunanin kila Fa'iza bata fad'ama Abba ba tana jin nauyi sai yace"Fa'iza mana Abba.
kan mganar maida auran mu ni da ita"
Sai Abba yaji zufa na ketomai cikin mamaki yace"Topaha..Fa'iza bata fad'amin ba ban ma san da wannan mganar ba"
Ishaq yace"To ban san meyasa bata fada maka ba,ammh ta sanar da yara da Zeey cewa zata dawo har ma ina mata shirin dawowa Abba"
Sai Abba ya jinjina kai kafin yace"Ba shakka. to ka bani Lokaci zan yi mgana da ita abunda muka yanke zan nemeka a waya"
Da haka suka rabu da Abba da ransa ya baci a fili ya furta"Meyasa Fa'iza zata min haka..?domin na bata dama bai kamata tayi wasa da Hankalin mutane haka ba"
Shi kunyarsa Daya Engr ya zai yi da shi..?da tasan tun farko ga inda zata koma meyasa ta amsa masa ai da ta basa Hakuri gabadaya ya shiga Tunani Saboda wlh tallahi yana ganin girman Engr baya so ya yi abunda kuma rai zai zo ya baci ta turo sa sannan kuma ga Ishaq da wata mgana a gefe.
Da bacin ran ya koma gida sai kuma Ammi ta tare shi da mganar Fa'iza zata koma karofi Saboda walimar Saukar su,Da farko ya so ya kirata ne ya tambayeta ammh sai kuma ya Sauya shawara yana so yagani ko zan nemesa da mganar ammh har akayi kwana Biyu bai ji komai daga bangarena ba, sannan Engr ma ya kirasa akan ko yaje karofin yace bai je ba sai weekend sai ya Fahimci shi kan shi bai san abunda ke faruwa ba in ma ni na sani to ban Fad'a masa ba.
Ranar alhamis da Daddare bayan ya Dawo gida yana shirin kirana sai ga shi na shigo Falon,da rana ya Kira Nana Fadila sun yi mgana itama yaji mganar komen a bakinta sai bai nuna mata yaji wani batu ba,Abunda kuma ya kara Dauremai kai da suka yi mgana da Mallam mijin Goggo yace masa zai zo akwai mganar da zasu yi Bude bakin Mallam sai cewa ya yi"Masha Allah Allah ya kaddara da Sauran zama Tsakanin Fa'iza da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login