Showing 282001 words to 285000 words out of 288345 words

Chapter 95 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

739

Badariya,mu dai tare muka bar su biyu su fahimci juna bayan Engr yace mata ta saki ranta in sha Allahu wannan matsalan angama da ita.
Bai yi wani bayani ba sai chan ba jimawa Badariya tazo tace min yusuf yace tare zasu koma naji Dadi na yi ta mata Fatan alheri ina kara jadaddamata ta yi hakuri ta kuma kara Hakuri.
Badariya tayi mirmishi kafin tace"Nagode Anty Fa'iza ke da Mijin ki kin yi min dukkan gatan da Dangina zasu yi min Allah ya saka da alheri. Yusuf yace an daidaita bayan tafiyata Yayansu ya shiga mganar Hajiyarsu ta amince ya sauyamin gida sannan an yi min iyaka da matarsa kuma ya fadamin megidan ki ya yi masa Fad'a sosai ya kara nuna masa tunda yana sona to yasan Darajata"
Nasan halin Engr daman bazai yi wasa ba muka rumgume juna,muka fita tare har Falo Yusuf nata godiyan Hidima itama Badariya nayi Direban gidan su Papa ya kira shi yazo ya kaisu Filin jirgi Yusuf bakin nan kamar Gonar auduga tsakanin miji da mata sai Allah har ta fad'a masa tana da ciki.
Nima ranar tukwaici na musamman na bama Engr saboda jin dadin yadda ya maida matsalan Badariya kamar tawa muna kwance kaina na saman kirjinsa bayan ya gama shagalinsa yace"Ki daina min godiya duk mai kaunarki nima ina kaunarsa kin fad'amin yadda Badariya ta kaunace ki saboda Allah nima sai naji ina Kaunarta Saboda wanda ta kaunace ki domin sa"
Kuma fa ba wani labari na bashi ba nadai fad'amasa Badariya mai kaunatace shima yace tunda tana kaunarki nima ina kaunarta,Washegari gidan su Papa muka yini ni da shi muna ta Hidimanta ma Hajiya Kudurta da Burinta ya gama cika Tunda Oluwatosin ya yi aure kuma daga gani yana cikin kwanciyar Hankali ita da Maa suna ta godiyar Abinci har Papa sai da ya yi min mganar ina ta Dawaniya da su bana gajiya..?
Kaina na kasa ina mirmishi nace ba wani Dawaniya aciki suna ta min godiya da zamu tafi Maa ta bani Mayafai da Turarukan wuta sai ban ce mata ina hadawa ba na bari sai naje kaduna na hado mai kyau da kanshi na kawo mata.
Da muka dawo gida nayi ma Engr mganar turaruka sai yace na bari akwai tsarin da yake so ya yi min yadda Sana'ata zata tafi tare da zamani daman na fad'amasa ina so maje kaduna ko nayi sako,asiyo min kayan hadin na hada a gida saboda Maa,kuma tunda naji yace haka sai ban kara mgana ba, nasan tunda yace yana da Tsari to ina tabbatar ma kaina Tsarinsa a kaina mai kyau ne.
Ban sani ba ko Badariya ta kira chan Lagos ta fad'ama su Mama komai,?ni dai sai kiranta nagani tana ta min godiya har Anty Binta ma ta Kirani sai gashi da bakinta take fad'amin Halin da Halisa ke ciki da mashayin mijinta kuma an yi an yi yaki sakinta.
Tana kuka tana fad'amin ko zan fad'ama Engr in zai iya wani abu nace mata zan fada masa in sha Allahu.
Ni kuma ganin taimako ne sai nake gayamasa,nima sai alokacin yake fadamin Yaya Ishaq ya kirasa yana ta Godiyan abunda muka yi ma Badariya kamar mun yi mata wani Hidima,mganar Halisa kuma yace sai ya shiga kano zai ga mijin Halisan da kansa ko jari ne bai da shi a bashi ammh sai in har zai daina shan kwaya da saida su.
Nan take ma yace akwai abokinsa dake aiki da Kotun musulunci a kano Lauya ne zai sa ya gayyacesa ya yi masa nasiha da barazana ko za'a dace.
Ta hannun Anty Binta aka samu lambar wayarsa aka turama Lauyan shi kuma yace in sha Allahu zasu zauna da shi.
Kwana Biyu tsakanin Lokacin muna shirin tafiya Edo washegari tunda yace tare zamu koma ya Kira Engr ya fad'amasa ya nemesa sun zauna ya Fahimci rashin sana'a ne da kuma rashin gata yasa ya fad'a wannan harkan sai kuma Tarayya da abokan banza,ammh ya yi masa alkawarin in yau ya samu wanda zai tsaya masa zai bar wannan sana'ar daman sha ba kullim yake afata ba,zai koma makaranta sannan zai zama nagari
Engr na jin haka yace tafiyarmu sai Jibi washegarin jirgi yabi zuwa kano sai Dare ya dawo yace min kamar ya yi ma mijin Halisa kuka ga namiji har namiji ammh zuciya ta mutu,yace ya bashi Miliyan daya zai fara kasuwanci sannan zai koma makaranta Tunda yana da Diploma kuma ya yi masa alkwarin zai zama nagari in dai zai Tsaya masa shi kuma yace zai Tsaya masa har abada, ya bashi lambarsa yace in yana bukatan wani abu,Har kuma gidan yaje yaga Halisa yana Fad'amin ko abinci basu da shi ga gidan Haya an yi yawa. sai ya ce masa ya samu wani gidan da zasu kama su kad'ai zai biya kudin to sun rabu akan sai an samu zai kirasa.
Idanuwana suka ciko da hawaye Allah Sarki rayuwa na rumgumesa ina masa Godiya sai ya rikeni sosai yana Fadin"ko kashi ne indai dan'uwanki ne abun Darajawa na ne Faa'izaa"
Ban ji wani bakinciki domin ya taimaki Halisa ba yar'uwata ce har Abada ban isa in raba wannan jinin ba,ballatana abuda ya faru a baya ya Dade da wucewa ni din ne kuma na rabu da Ishaq na auri wani wanda yasan Darajata da mutumci,ban taba rikonsa araina ba ina yin komai Saboda Zumunci ne.
Sai ga Anty Binta na kuka tana min godiya ita da Mama tsakani na ko da Halisa kamar uwarta haka ta Dauke ni. kira akai akai Anty Fa'iza kaza Anty Fa'iza tun balle da suka samu gida karami Flat,Engr ya biya musu kudin haya na shekara Biyu,sun koma sannan Rayuwa ta fara zama daidai bata iya yin komai sai da shawarana.

Sai da muka koma Edo sannan na Tura mata 50k nace itama ta fara sana'an cikin gida sai ta nuna min tunda ta iya su Cake,donut bari ta gwada sai nace hakan yayi ta kuma tallata cewa tana aikin su Sai a biyata,bansan irin addu'an da muka sha Daga ita har mijin nata ba,
Ni da Engr ne madubin su yanzu a baya Hajiya Dala suke ganin zata iya musu komai sai ga shi yanzu an ce tsakanin su ba Mutumci Hajiyar Dala da kanta ta Kirani Duniya mai ya yi tunda yanzu ina auren mai kudi nima kuma ina da abun hannuna na wuce reni.
Da bakinta take fad'amin fadan su da Anty Binta daga karshe tace"Chan sanda Halisar ta hadu da shi nama sani ya yi musu barin kudi lokacin ana samun dillar kwayoyi na kai masa,kuma koda suke ganin dan'uwan megida na ne. yace fa Zaman makota ne na iyayensa da kakkanin yaro ammh basu hada komai da shi ba. ammh daga karshe Binta da Saudatu na ganin laifina ai ni kiri kiri na fad'a musu cewa hakkin ki ne ke bibiyan su suke ta ganin haka daga Halisan har Badariyan'"
Mamaki bai barni nayi mgana ba ina Tunanin ita duniya daman haka ta gada tunda har yau Hajiyar Dala ke kirana tana sukan Mama da ya'yanta komai daman ka gina shi da amana,ba ma ita ba kaf ya'yanta suna kirana da masu auren da yanmatan alhalin a baya ba wanda ma yasan da zamana ba..

Autan ta ma Futuha,ta kirani tazo Abuja bikin kawarta ko ina nan nace mata ina Edo ammh sai na had'a ta da su Kafaya ta kwana Biyu a gidan su Paapa kuma suka karammata da zata koma Ta jirgi paapa ya siya mata Tiket bayan abun arzikin data koma da shi sai ga shi ta koma tana labarin iyayen mijin Anty fa'iza suna da kirki kadan kadan sai na zama abun so a family kowa yana nema na, har da wanda ban taba zato ba in na zauna ina Tuna matakin Rayuwata tun daga farko har zuwa yanzu hannuwana kadai nake Dagawa sama na godema Allah Tunda Duka Ni'imarsa da ta mamaye rayuwata sanadinsa ne yau ga shi Fa'izar da ake gudunta sai ga shi na zama abun son kowa da kowa Allah kenan.
Muna Edo kafin mu koma Abuja,Zainab ta kirani tace yara sun samu Hutu ammh bata ji Yaya Ishaq na mganar zuwan su wajena ba,ina jin haka sai naji na kosa suzo sai na gayama Engr shi kuma ya Kira Ishaq ya kara rokonsa sai ya cika masa ido yace zasu zo yana jiran jamal ne tunda bazai sako su su kadai ba.
Jin haka yasa Engr ya karbi Lambar Jamal din suka yi mgana shi kuma ya Siyama duka yaran ticket yace su biyo Jirgi in zasu taho mu hadu a Abuja.
Duk yadda naso na boye murnata na kasa sai da na bayyana Engr nata min Tsiyan nace na bar masa ashe zence ne namu na mata kunya naji ganin har Zalamata ta fito Sarari.
In da ta ni za'a bi har Islam azo min da ita Zainab tace bata yayeta ba in bari sai in ta isa yaye zata kawomin na yayeta da kaina,ammh duka yaran su Shidda zasu mana Hutu suma Zainab tace suna ta murna zasu wajen Umma.
A satin muka dawo Abuja mukaje muka yi shooping saboda Engr yace bayaso su nemi wani abu su rasa,kamar Yadda Babansu yace Jamal ya taho da su ni da Engr mukaje Filin jirgi muka Daukosu haka yara nan suka kamkameni suna Ihun kiran sunana Umma Umma har da Anum babban banza Amir dai yana gefe shi Babba bai cika harkan yara ba.
Sai ga Jamal a gidana bai kuma san haka saukin kan Engr yake ba, sai da suka zauna suna ta hira ni kuma ni da yaran muna cikin gida,Amir daki guda na sauke shida Musty ,Dayan dakin kuma su Ahmad,Anum kuma nace ta zauna adakina.
Duk inda na saka kafa nan suke sakawa komai suka gani sai sun yi mgana Labarai ko haka nake shan su gidan sai ya karade da hayaniyar yara daman nayi abinci kafin su iso ai sai kowa yace ga abunda zai ci wannan yace Shayi wannan indomie ammh ban damu ba haka na shiga kitchen ina yi musu ra'ayinsu zuciyata Fes kamar an yi min albishir da gidan Aljannah.

Jamal jirgin yammah ya sake bi zuwa kano,ya yi ta godiya karramansa da Engr ya yi har yace ma ya kawo C.V Dinsa tunda acikin Hiran su ya fadamasa Software Engering ya karanta,Zuwan yaran yasa walwalata ya karu ranar dai tare da su Engr ya barni na kwana Amir ne kadai ya kwana shi kadai da Musty ammh har Ahmad a dakina suka kwana Engr mutum ne mai kawaici da kauda kai ya kyaleni naci Lokacina ni da ya'yana ba Takura ba shiga Hakki.
Ni da kaina da na gano zakewata sai na rage rawan kafa shima cikin su yake shigewa ayi ta wasa har da Chinness yake biyo musu suna yi shi da su Ahmad Amir kuma in kaga suna mgana kace Amir wani babba ne,Ballatana Anum iyayin karanbana fadi kuma ba'a tambayeta.
Yadda muka saba tun a baya zuwan su ma haka muke yi karatu tare da cin abinci tare,Sannan Anum na zage mata da koya mata girke girke zamani Tunda chan bayi suke ba ita kanta Zainab din tana neman mai koyamata.
Mun fiffita yawo da su na kaisu gidan su Papa suka yi musu ma kwana uku,Maa ke son yara kamar kada su dawo,sannan mun je parks da su Engr ya kaimu suka yi wasa suka sha Hotuna,yaso ya koma ammh yace sai ya maida su har Lagos yadda gobe za'a ji dadin barin su Sati uku daman akace su yi saboda makaranta.
Naso su kara Engr yace a'a gwara su koma akan Lokaci,Farhan da Fadil na kai su gidan kakkanin su ni da Engr muka je sai ga Dr.Laawal kamar ya kwantamin Hajiya Halima daman ban taba samun matsala da ita ba. naga kanwar Zainab zuzu ta dawo daga kasar waje ita kanta da ta ganni tayi mamaki sai ga shi itace da sakin jiki muna mgana har tana karban lambar wayata nan na barsu suka kwana Biyu Zuzu ta kirani tace suna ta kiran yan'uwan su, sun ki zama ita ta dawo da su,To ranar ma bana jin dadi kasala ga zazzabi ga dacin abinci ga shi mun Tsara tare zamu maida su lagos.
Ciwo fa rigis ya kwantar dani Tsaraban yaran ma su Kafaya Engr ya bamawa suka je suka yi musu shopping ni kuma ya kwasheni muka je asibiti gwajin Farko aka gani ina da Shigar ciki wata uku,Murna gurin Engr kamar zai shid'e nasha Rumguma tun a gaban likita tun kuma muna asibitin ya labartama su paapa ina da ciki suma kamar shi haka suke ta murnan.
Dole Saboda Laulayi wajen Maa na koma shi kuma yaje ya kai yaran aranar suna da sati uku da kwana Hudu ne,achan ya kwana da Safe ya Biyo Jirgi zuwa Edo suna da Meeting dalilinsa da yasa ma bai dawo Abuja ba sai dai waya fa akai akai muke yi ko su Abba shi ya fasa mganar cikin a wajensu ni kunya ma nake ji in naga yadda ake rawan jiki a kaina Motsi kadan Maa tace menene..!
Motsi kadan granny tace ina lafiya..?
Haka su kafaya ashe haka ake renon ciki ni na saba nawa cikin har nayi sa na haifesa ba wanda yasan zafina sai ga shi na zo inda kamar a lasheni tun kafin abun cikin ya fito duniya.
Bansan ya akayi ba kowa sai da yaji Labarin cikin na ba Dangina ba ga nasa Danginsa ba.
kunya nake ji wlh gani nayi mu ba yara ba miye na yamad'di.
Zainab ma tace Badariya ta fad'amata ta kirani tana min tsiya ina Dariya.
Ranar da Ishaq yaji ina da ciki sannan ga yara sun dawo da labaran mu ni da Engr sai kishinsa ya kasa boyuwa har ya bayyana ma zainab tunda kamar fada ba gaira ba dalili ya rufeta.
Sai da Mama ta shiga mganar tace ya rika addu'a Allah ya yaye masa jarabawa ce da sakamako
Oho ni bansan yana yi ba ina nan cikin jin dadi da kwanciyar Hankali.
Sai da cikina ya yi wata biyar na bi Engr zuwa Edo muka shimfid'a wata Sabuwar rayuwa komai kuma na shirin haihuwa tun muna Edo muka gama shi chan na fara awo na kafin cikina ya kai wata Takwas na koma Abuja yace anan zan haihu kusa da iyayensa.
Na sauka lafiya haihuwar asibiti ce Ammh ban jima ba na haifi ya' mace mai kama da Engr har gashin idon su tun a ranar ya yi mata Huduba da Hafsat zamu rika kiranta Tamadina sunan mahaifiyata nayi kuka nayi Dariya na karan da Engr ya yi min,Abba ma ya taka rawan gani Tunda sunan yar'uwansa ne,an yi suna na gani na fad'a na masu kuma da shi duka Ahalina sun zo har da Zainab da Mama da yara,Anty Binta da Ahalimta tare da Halisa da komai da ya Daidaita,Badariya ma tazo da jegonta tunda itama ta haifi diyarta mace taci sunan Hajiyar Yusuf itama suna zaune lafiya tunda sun daina shiga harkanta.
Hajiyar Dala ma da ya'yanta sun min kara sun zo,na shiga na fita sannan na samu kyattuka Papa mota ya bani Kirar Honda karama mai kyau na mata Maa kuma ta siyamin Zinare mai Tsada Dangin su ma na Benue kuwa naga karan yarbawa zannuwa ashebe babu abunda basu taramin ba,ba ni kadai ba hatta dangina da abun arziki aka salleme su kowacce da Turmi da kudi a hannunta.
Sai bayan suna ne Goggo karofi tazo ta zauma dani har nayi arba'in Allah Sarki goggo na,Ita ce uwa ta tun Tamadina na raye har kuma gobe ita ce. itama haka Direba ya maidata gida da kayan arziki daga gareni da mijina da Danginsa, na zama Topic of Diccussion a family din mu kowa sai dai kaji yana Fadin Faa'iza haka Faa'iza kaza.
Bayan tafiyar Goggo na cigaba da renon Tamadina a gida bayan Engr ya bani Direba ya kaini garuruwan yan'uwana na yi musu barkan arba'in sannan na sauka a kaduna agidan mu nan na kwana Biyu sai da Engr yazo muka koma Edo tare da shi da D'iyarmu.

*BAYAN SHEKARA BIYAR..*

Bayan shekaru Biyar da suka gabata,Duk inda ake neman cigaban Rayuwa ni kam na gama samu ni Fa'iza sidi karofi ashekarun biyar din baya.
Mun rasa Hajiya Kudirat,Shekaru biyu baya,Inno da Baba Ati suna nan a raye cikin koshin lafiya da kwanciyar Hankali.
A bangaran rashi kenan bangaran Karuwa kuma bayan Tamadina na kara haihuwan ya'ya biyu Namiji da mace,mai sunan Papa muna kiransa Paa da mai sunan Maa Shukra muna kiranta Tauhidat,Bangaran ya'yana kuma Amir ya gama secondary school dinsa Da taimakon Engr ya samu gurbin karatu a Universty of Washington yana karantar Medicine,shekara uku da suka gabata,sai Anum dake karatu a Lagos States University lasu,tana karanta harkan mganguna phamacry.
tan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a shekara ta Biyu sai Mutsy dake University of Lagos yana shekarar farko ya na kuma karanta harkan zane zane,Ahmed sune bana zasu zana jarabawar Fita Su farhan na matakin SS1,Jamal ya yi aure
zuwa Lokacin na riga na zama Babban Mace na taka duka matakin nasara a rayuwata Dalilin Engr yasa na zama wata macen da ban taba mafarki ba,Jamal ya yi aure anan kano kuma Engr ya yi masa hanya ya samu aiki da NITDA information Tecnology Development agency.
Dake reshen jahar kano yana nan zaune a gidan kansa da Matarsa Abida.
Engr kuma ya zama Chairman a ma'aikansu sannan ya zama d'an kwangila Papa ya gama Lokacinsa a EFFCC yanzu haka ya yi Ritaya yana gida yana Hutawa,Su kafaya sun yi aure kuma dukkansu auren gida suka yi ya'yan kannen papa suka aura Kafaya na Abuja Sharifatu na Oyo inda Mijinta ke aiki Hafsatu ma da Khadija sun yi aure rana daya ita Khadija V.c din Kasu take aure ita kuma Hafsah tana aure a zaria tana auren wani likita dake aiki a ABU chika.
Shekara biyu da suka gabata gida ya Rage daga Ammi sai Abba,sai ta Dauko ya'yan kannenta guda biyu tana rike da su saboda zaman kadaici,yanzu zamana ya fi yawa a Abuja tunda ga yara bazamu ta tsallake tsallake ba Sai dai ina bin mijina Edo ina dawowa kaduna kuma muna zuwa sai muke sauka a gidan mu bamu da matsala.
Engr ya yi min Tsari mai kyau game da kasuwancina ya Budemin katon shago mai kama da plaza inda aka sama wajen sunan SAFMA TURAREN WUTA AND

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login