Showing 186001 words to 189000 words out of 288345 words

Chapter 63 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

782

tunda akwai Haraba sosai,sai kudi wajen miliyan Ashirin gidan tunda Sabo ne shima mijin Nana Fadilan wani kaninsa ke harkan gidajen shiyasa suka samu da sauki,Ya siya gidan sannan kuma yayi oder din gadaje da kujeru da sauran kayan bukatu da ya Kirani ya fad'amin sai nace"ka san kana da yara a siya musu kananun Gadaje. Ga uku anan ga biyu Farhan da Fadil,Anum kuma ko ita da Badariya sai ka had'asu,Mama kuma tana Dakinta ita kadai sai jamal kada ka manta da shi"
Cikin gamsuwa yace"ban manta da shi ba wajen zai isa ba takura fa. na Dauko muku hoton gidan in na Dawo zan nuna miki"Da haka muka rabu sai da yayi sati sannan ya Dawo da shirin zai tafi damu gabadaya Zainab kuma sai daga baya zata biyomu ita.
Sallama yace duk mu yi da abokan arzuka da yan'uwa da makota,Ranar a karofi muka yi yini,washegari kuma da muka dawo na zaga cikin gari naje nayi ma Sa'adatu da Habiba sallama saboda? sabo har suna kwallah,makaranta yara daman tun kwanaki naje na sanar da su suka ce zasu yi kewar hazikan Dalibai.
Hajiya ma naje mataa sallama,ta bani kyautan kaya da su Turaruka da mayama mai na gyaran jiki muka rabu cikin mutumci,Abba dai shi ya hana naje yi masa sallama duk da ko ba inda suke tunani zan tafi ba, yace shi zasu je har lagos suga muhallina.
Anty Binta da da Mama sai Anty Hure da tazo zasu tafi daga bangarena yace a samu mutum biyu sai Goggo ta wakilta Anty Nasara da matar Yaya Isa tunda Yaya mariya tace bazata samu zuwa ba,Yaya Asiya kuma yaronta bai da lafiya yana fama da kyanda.
Tafiyar jirgi yace zamu yi,zamu je kano daga katsina kenan,Ya siya mana Ticket gabadayanmu zamu tashi karfe uku na ranar talata,damu da kayan sawan mu,ana gobe Tafiyar na had'a komai nawa na kayan zobo na da kunin aya.
Sannan na cire soket din Freezer di'na,duk kulle kullen da Goggo ta aikomin da shi na had'a cikin kayan yaran nasa zai musu amfani.
Na zata ina da Dauriya sai ga shi na fara raunanaa, in naga yadda yaran ke Tsallen Murna ina Tunanin ya ya zasu ji gobe in har na ce musu ba Tafiyar mu d'aya ba..?





*Janafty*
[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2020*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Ko yaran ban bari sun fahimci Halin da nake ciki ba,daki na shige ina kokuwa da yanayina.
Nace kada su dameni da Hayaniya Hafsah bata nan daman tun jiya ta wuce karofi daganan Abba zai turo mota a Dauketa zuwa kaduna.
Yaran ne kad'ai da babansu ke ta Budurin su da murnan gobe zasu hau jirgi,sannan zasu koma Lagos da zama,kayan su dai masu muhimmanci na hada musu saboda tafiyar jirgi ce yace ko shi daga baya zai saka a taho mana da komai gabadaya,Badariya tana kano sun kusa gama Hidimar kasa bata da Lokaci sai dai zata taho daga baya.
Kwana nayi ina kuka Sai dai ban kwanta ba ina sallah hawayena sun kasa tsayawa sai kuma naji kamar abunda nake shirin yi bai kyautu ba.?kamar in nayi haka na karya raunin zukata da dama ciki har da ta yarana. da suka fi kowa shakuwa dani ammh sai wata zuciyar ta tunasar da ni Babban Dalilina da yasa naji na kara samun karfin zuciya.
Sai dai a komai in zan yi ba ma yin gaban kaina Allah nake fara sawa cikin Duka al'umarana,Shi na daga hannu na roka da kyawawan sunayensa sannan na yi masa magiya na yi masa naci ina kuka ina fadim"Ya Allah kasan damuwar dake damuna acikin zuciyata, sannan kasan wahalwahalun da nayi ta fama da su yayin biyayyan auran da kai ka Umarcemu da yin sa.
Sannan kasan komai da ya faru tunda kai mai ji ne kuma mai gani ne na yanke wani Kuduri a raina ya Allah in har ba alheri acikin Tunanina, Allah ka hanani aikata wannan kudurin nawa in kuma Hakan shine alheri a gareni da Duniyata gabad'aya Allah ya bani Hakuri ka sanyamin juriya kada kuma ka barni ni kad'ai kayi Riko da Hannayena sannan ka yimin Jagoranci a duka al'murana,sannan ya'yana Allah ka tallafe su,? kayi musu albarka, ka kara shiryamin su cikin addininka"
Ina addu'an kukana yaki Tsayawa sai na kife kaina a kan hannayena ina ta rafzan kuka,ni da barci sai wajen hud'u na asuba shiyasa na makara sallar asuba sai da naji sa a kaina yana Tab'a kafafuna na bude idanuwana jajir da suka kumbura saboda kuka,na sauke a kansa cikin mitsike ido na ce"An yi sallah ne..?
Kai Tsaye yace"Har mun dawo masallaci ni da yara kina kwance ashe baki tashi ba..?
Jin haka yasa na yunkura Dakyar na mike ina fadin"Ban yi barci da wuri ba ne"
Kai tsaye na wucewa zuwa Tiolet sai ya bini da kallo yaga idanuwana sun tasa ammh ganina a kan darduma sai yayi tunanin sallar Dare nayi,Ficewa yayi falon wajen yaran har Anum ta kunna gas ta Dora ruwan zafi saboda wanka,Amir kuma ya saka a Heater tunda akwai wuta.
Sai da idar da sallah na fito falon ina ganin an saka ruwan zafi nasan Anum ce uwar zumud'i ban dora abun kari ba sai da duk sukayi wanka har da Baban nasu,sannan na fere dankalin Turawa na soya musu sai ruwan Tea muna da sauran kayan ciki sai nayi mana Ferfesu da yawa saboda Mama da Anty Hure,su Anty Nasara suna Karofi sai yau zasu taho ammh ina Tunanin zan Dakatar dasu.
Saboda tafiyar dake gaban mu yasa suna gama karyawa suka fara shiri ni dayake ban iya saka komai aciki na ba gabad'aya komai baya min dadi.
Yaya Ishaq yana dakin mama shi da yaran zainab ta kirani bayan na Dauka mu gaisa tace"Maman Amir yau sai kwanan Lagos ko?
Sai nayi yake kafin nace"Uhm ke bakin k'i mu je mu gyara gidanmu tare ba.?tana dariya tace"Wlh ba haka ba ne zan tsaya shirye shirye ne Daddy wannan karon bai bani matsala ba,da Full yes din sa zan koma ai ko Sati biyu baza'ayi ba zan same ku achan in sha Allahu"Jin haka yasa nace"To Allah yasa"
Ta amsa da Ameen mun taba Hira sama sama na tambayeta yara tace suna makaranta,mun yi sallama cikin girmama juna kamar yadda muka saba,har ta kashe sai na sake kiranta tana dauka nace"Maman Fadil ga amanan yaran nan. Don Allah ki kula da su sannan kiyi hakuri da su,Amir da Anum sun girma nasan zasu yi miki kokarin kula da sauran kannensu. In sun yi ba daidai ba ki tsawarta musu ki yi musu fad'a ki Tsaya kan tarbiyan su don Allah, in sun fi karfin ki ki had'a su da Babansu shi sai ya yi musu hukumci"
Bata gane kan mganata ba yasa tace"yaran da duka nakin da nawan kike hadawa ki rike Maman Amir..?kinsan bani da juriyan kwarammiya yara fa..?kina ma wata mgana muna komawa ai su Farhan daman ya'yan ki ne"Sai nayi mirmishi kafin nace"Ki rike mganata zaki tuna da abunda na gayamiki watarana"ban tsaya sauraran mganarta ba na katse wayata ina maida numfashi anya zan iya kuwa.?sai wata zuciyar tace min zaki iya in sha Allahu Fa'iza.
Anty Nasara na kira tana Dauka sai tace min gasu nan gidan Goggo yanzu zasu taho kai tsaye nace"Ku yi zaman ku nima ganinan tafe"
Cikin mamaki Anty nasara tace"Ga ki nan zuwa..?ban gane ba.?kun fasa tafiyar ne..?
Kai Tsaye nace"Aa.."
Anty nasara tace cikin mamaki"Bangane a'a ba ki bude baki ki yi min mgana Fa'iza"Bana son mgana alokacin sai kawai nace"Sai dai nazo"
Da sauri na katse kiran,ina jin kaina yana saramin ban zauna ba na mike na rika fito da jakunkunan kayana na zuwa falo,Sai ledan kayan da ba cikin kayana zan hada shi ba.
Ina cikin aikin ne sai ga shi ya shigo yana ganin haka sai yace"Yauwa daman mganar da na shigo nayi miki ne,bari naje tasha na yo tashar Ko Sharon ne yadda zasu daukemu da kayanmu duka"
Kai na gyad'a mai kafin nace"ni ma ka yo min tashar Ko karamar Golf ne don Allah"
Cikin mamaki ya juyo yana kallona lokaci d'aya yana fadin"bangane ba..?sharon fa zata ishemu in na yo tashar ta"
Kai tsaye nace"Aa ina so zan aika ma Goggo wannnan Frezer din karofi ne, in na barsa anan ba'a amfani da shi zai lalace. shiyasa nayi mgana da ita zan aika mata da shi"
Kamar zai yi mgana sai ya fasa ganin zai fita yasa nace"Kayi ma su Amir mgana su zo su fitar da kayan su"
Ya amsa min da toh ina ji ya leka Dakin Mama yana musu mgana,sai da suka zo nace su fito da kayan su tsakar gida daman tun jiya nagama duka kaye kaye muka kwashe komai muka adana cikin rawan jiki suka fara fito da kayan suna murna suna jin Dadi kallon su kawai nake yi ina zaune ko wanka ban yi ba Anum ce tace"Umma ke bazaki shirya ba ne..?
Sai na Rausayar da kai ina fadin"Zan yi wanka yanzu Anum"
Nan suka fice suka barni,ina sake sake ganin zaman bazai amfaneni ba yasa na mike na shiga daki,tubewa nayi na shiga wanka,kokarin daidaita kaina nake yi saboda in na rasa kwarin gwiwa bazan iya aiwatar da kudurina ba.
Na fito wankan kenan ina Shafa mai,naji dawowar Yaya Ishaq da maganan su Mama sai hayaniyar yara kamar suna fita da kayan ne waje da Sauri na Zura Doguwar rigar leshi,daman kwalliya ba aikina ba ne,Dankwali kawai na dora na zura Hijabi,na fito da sauri duk suna Tsakar gida har su Mama yana ganina yace"Ga motar chan a waje."
Nasan wanda nayi masa mgana ne kai Tsaye nace"akwai yara a waje ne..?
Juyawa yayi yana fadin"Bari na duba"
Ba jimawa ya Dawo,da wani Saurayi tare suka kama suka fita da Babban Frezer din da Starplezer,Anty Binta da ta shigo kenan ta ci karo da su suna fita da shi shine ta shigo tana fadin"Ina za'a je da wannan frezer din.?ba dai Lagos ba..?
Dayake na gayama su Mama karofi zan kaisa sai itace ta bama Anty Bintan amsa ni dai muna gaisawa na koma daki na shirya a gurguje saboda kada na bata Lokaci,hijabina na saka Dogo har kasa ni na kulle sauran Dakunan gabad'aya na fito da jakar hannuna na,karama na duba duk sun gama fita da kayan suna? jidan sauran zuwa waje ne, har da Baban nasu ina kulle dakin na juyo ina kallon Amir da zai Dauki karamar ledar da na fito da ita da Sauri nace"Kai bani ledan nan"
Ba musu ya mikamin na karba ina fadin"ina kayana.?kun kai waje ne..?
Cikin natsuwarsa yace"Daada ya saka a mota"ina shirin mgana sai ga shi ya shigo yana fadin"Ku hanzarta fa Goma ta wuce mu isa kano akan Lokaci,ke kuma ga mai motar nan yana mganar lambar wanda zai kira in ya isa karofin..?
Anty Binta har ta fice,Mama ce da Anty Hure ban damu ba nayi karfin halin yi masa mgana ganin zai sake fita cikin Dakiya nace"Ina son mgana dakai"
Ba shi kad'ai ba har Mama sai da tayi mamaki gabad'ayan su suka kuramin ido,Sai nayi saurin Kauda kai ina juyawa na koma na bude dakin na shige daidai Lokacin da yake fadin"Fa'iza zamu makara fa kinsan jirgi ba jiranmu zai yi ba"
Ina kokarim daidaita yanayina nace"In sha Allahu bazaku makara ba"
Biyo bayana yayi muka Tsaya a Tsakiyar falon,na juya bayana ina maida hawayena a bayana ya tsaya yana fadin"Kin kuma juya.?wata mgana ce..?
Sai na juyo cikin karfin hali,idona yake son kallo saboda ya Fahimci yanayina ni kuma sai naki basa Dama,jikina ne ya kara yin sanyi Sabida ba jimawa mun yi mgana da Anty Fadila tace ita da mijinta zasu zo Filin jirgi daukan mu sai min je gidanta mun huta sannan su rakamu Sabon muhallin mu,da ita taje jiya ta kara gyara shi bayan kamfani yazo ya saka kayan Furnitures.
Har muka gama waya ban samu abunda na gayamatabba, ina jin kunyar gayamata cikin masu sauka a Lagos ba Fa'iza a ciki.
Ledan hannuna na mika masa sai ya saki baki yana kallona cikin sanyin jiki yace"Meye wannan kuma..?
Kai Tsaye nace"Duba ka gani mana"
Sai ya amsa ya bude yana gani Lokaci d'aya yana kallona da mamaki da alamun karin bayani da sauri nace"Kayan ka ne. Tun daga lokacin da ka jingine aurena da kai na daina amfani da duk wani abu naka,Abinci dai naci sannan ka bani wajen kwana Darajan ya'yana nagode kwarai Ishaq."
Na fad'a ina kallonsa ido cikin ido yadda ya kafeni da ido ne yasa nasan karin bayani yake so sai na yi ta Mazan cewa"Kayi hakuri Ishaq. Bazan iya binka Lagos ba."
Cikin Daga murya yace"What..?wannan wata irin mgana ce Fa'iza don Allah ki bar wannan wasan bana so.."
Ya fad'a har yana d'agamin hannu,sai nayi mirmishin takaici kafin nace"Ba wasa nake yi ba. Da gaske nake yi, daman na fad'a maka ka bani Lokaci naga ko zan iya bama auran mu wata Dama ko ba haka ba..?
Kamar gaula haka ya gyad'amin kai sai ya bani Damar cigaba da mgana ina fadin"To abunda na Dad'e da yankewa kenan,rasa aikin ka da abunda ya faru yasa na dakatar da kudirina,ammh yanzu tunda ka samu aiki komai ya wuce zama na dakai ya kare daman auran ka jingina ne,? shine nake rokom ka ka karisa ballesa daga wannan jinginan ma'ana ka Furta min SAKI da kan ka"
Na gama fad'a ina maida hawayena lokaci daya ina jin karfin gwiwa na shigata shi ko ledan hannunsa ne ta kubce ta fadi kasa cikin Tsananin Firgita kamar kiftawan ido na ji sa ya Damki kafaduna duka Biyu yana fadin"Fa'iza ki daina irin wasaan. Wani irin saki.?ki yi tunani mana kina tunanin zan iya sakin ki ne.?so kike na rabu dake wai Fa'iza..?
Kai Tsaye na gyad'a masa kai cikin idonsa nace"Kwarai haka nake nufi ka Sauwake mun auran ka domin bazan so ka cigaba da zama da matar da baka so ba. Ka auri zab'inka a wanchan Lokacin kace nayi maka adalci in barka ka yi rayuwa mai Dad'i da matarka. ni ma a wannan karon ina neman wannan adalci nima a wajenka kayi hakuri ka sakeni, daman a jingine nake kamar yadda ka fad'a"
Ban ko gama mgana ba kawai naga ya sakeni da karfi yana fadin"Ina. Wasa kike Fa'iza har fa mun shirya jirgi na jiranmu fa ?kowa yasan yau zamu tafi sai yanzu ki sauya mgana..?ga yara chan na murna sai na fita nace musu me..?su Mama na Tsakar gida me zan gaya musu..?to wai kina nufin na tafi ni kad'ai dagani sai yara.?wa zai kula damu Fa'iza rayuwar mu ta fara tare dake kuma Dole mu karisa tare Fa'iza har Abada babu saki ko yaji Tsakanin aurena da ke"
Nima cikin Tsawa da Daga murya na taresa da fadin"Ammh akwai jingina acikin auran namu ko..?sannan akwai Tozarci da wulankanci duk aciki ko.?kayi hakuri na riga na yanke hukunci bazan iya cigaba da zama dakai ba.."
Sai ya juyo yana kallona cikin Fitan hayyaci yana fadin"In sake ki na Lalace Fa'iza?kin manta abunda Baba ya fad'amin?yace in na rabu dake na rasa mata tagari sannan bazai taba yafemin ba in na barki,don girman Allah ki bar wannan mganar ki bari in muka isa chan na yarda mu zauna da Mama ki fad'a mata komai tayi mana Sulhu, ammh zuciyata bazata iya Daukan wannan mganar ba. plz ki bari don Allah"
Ya fad'a har yana hada hannayensa alamun roko gabadaya tsoro da firgici sun bayyana a saman fuskarsa gabadaya,jikinsa kuma sai rawa yake yi,ina kallonsa kamar zan yi rauni sai? kawai na tuna da irin zaman Tozarcin da nayi da shi na Tsawon shekarun auran mu,kuka ya kwace min na juya baya na ina fad'in"Kayi hakuri ba zan iya ba.."
Sai kuka shabe shabe,Ban sani ba ashe duk'amin yayi sai ji nayi yana jan Hijabina Lokaci d'aya yana fadin"Ki yi ma girman Allah Fa'iza ki yi hakiri ki bar mganar nan. Hankalina tashi yake yi in naji kina fadin saki da kuma cewa bazaki bimu ba.?Ta yaya kike so na fara rayuwa a in da baki..?
Bansan Lokacin da na juyo,har ina bangajesa cikin daga muryan da bansan ina da shi ba nace"Zaka iya. Nace Ishaq zaka iya.."
A baya ka zauna da wata macen inda bani kuma baka mutu ba. Na fuskanci Kaskantattaciyar rayuwa a gidan auranka,na fuskanci tozarci a wajen ka da wajen dangin ka a karkashin auran ka,ka rabani da kowa nawa ciki har da mahaifiyata ka rabani da yan'uwana duk wani mai so na baka kaunarsa,baka son ganin Dariyata sai kuka na Ba a macen aure ka Daukeni ba,ka Daukeni a baiwa,mara gata,jahila wacce bata da ilimin zamani,sannan mummuna baka wacce ka ke zaune da ita Saboda alfarma,wacce tayi ma rayuwarka karan Tsaye Fa'izar dai da tayi ma mafarkin ka kutse, Fa'izar da ka zaunar da ita kana rokonta da ta taimaka tayi maka adalci ka zama na mace Daya,Matar da ka fifita a kan Amaryan ka,Fa'izar da baka san ciwon ta ba,baka san cikin ta ba,baka san zafin nagudar haihuwar ya'yanka da ta dinga yi ba, itace dai wacce ahaka ake kiranta kamar akuya ta cika Haihuwa Fa'izar da ka nemi datse mata Haihuwa saboda baka kara kaunar Zuru'a da ita,Ni ce dai Fa'izan da kasa nuna ma duniya ni matsayin matarka kana jin kunya,Nice Fa'izan da ka ke barina wata da wattani Saboda wata mace ni ce Fa'izan da na dauki dukkan Tozarcin yan'uwan ka har da na Dangin matarka saboda Fa'iza bata da gata,Fa'iza ba kyakyawa bace. Sannan bata da ilimin zamani ba wayayyiya bace ba kuma yar gayu ba ce,sannan ita ba fara bace bata kuma iya haihuwan Fararan ya'ya ba,ni ce Fa'izan da kake kirana mara amfani Fa'izan da auran ta bai amfana maka komai ba ni ce dai Fa'iza nan wannan mai raunin jin,wacce ka ce ka tsani mgana da ita saboda tana saka ka ihu ko ka manta ne..?
nice fa nice fa kake kiran bazaka iya Rayuwa a inda bani ba..?karya ka ke yi..Wlh karya ka ke yi.."
Na karishe fad'a cikin Tsawa Lokaci daya da kuka sai kawai na zube saman Cafet din ina wani irin kuka mai cin rai ban sani ba ihu na da mganata yasa su Mama rugowa Dakin,duk a gabansu na rika amayar da abunda ke cikina.
Su kansu jikinsu yayi sanyi sannan sun kasa gane wasu abubuwan
Shi bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login