Showing 177001 words to 180000 words out of 288345 words

Chapter 60 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

771

baki fad'amin ba Fa'iza..?ai naga dai duk lalacewar aure sunansa aure"
Sai na kasa mgana nasan ban kyauta ba yasa nace"Kayi hakuri.."
Bai ce komai ba illah yaran da ya mika ma wayan muka yi mgana Duk sun damu da in dawo daman mun yi waya da Hafsah ta fad'amin Ahmad nata rigiman bana nan,sai na fara Tunanin komawa gida kwana hudu nayi a Dutse kamar kar in dawo,Nana Fatima macece mai kirki ita da mijinta sun fita dani naga gari sannan zama da fatima yasa na kara sanin ita mace mai Daraja ce sannan yar kwalliya ce.
A na gobe zamu tafi kano da ita ni dagachan zan wuce katsina take kara min mganar Zainab kai Tsaye nace"Ina da abokiyar zama ammh tana Abuja chan take zaune"
Cikin karin mamaki tace"kuma tana da ya'ya..?
Ina dariya nace"Sosai biyu har da cikin na uku ma"
Sai ta rausayar dakai tana fadin"meyasa ita tana Abuja ke kuma kina katsina..?
Ganin Nana Fatima ce akwai yarda Tsakanina da ita yasa na gayamata kadan daga abunda ya shafeni sai dai ban gayamata irin zaman da nayi da Ishaq da jinginar aurena? dashi ba,sai dai na gayamata Dalilin da ya sa zainab ta zauna abuja ni ina katsina.
Cikin mamaki tace"Tab kuma tana zuwa gidan ki na katsina ki sauketa a Dakin ki..?
Ina Dariya nace"A'a dakin dai megidan"
Sai ta bude baki tana mamaki Dariya ta bani na kwashe da dariyan ina fadin"Rufe bakin Mana"
Sai ta rufe lokaci d'aya tana Fadin'"Lalle kina da karfin zuciya wlh bazaki kwanar min a shashe ba..Tabdijam"
Dariyan yadda take jinjina abun nake yi a raina nace don ma bataji ni ke Dawainiya da su ba da sai ta zageni,a kwana Hud'un da nayi da ita na kara sanin wasu abubuwa na kuma kara yarda kwalliya da ado? na duka mata ne,ba na bambamcin Fata ko kyawun Fuska ba.
Na kuma kara sanin ko kana da kyau to ka kara da wanka sai kafi haka kyau gata dai mai kyau da ita ammh kwalliya da gyara bata rabo da shi har mgana nayi mata nace"Nana baki gajiya da kwalliya da gayu..?me zaki gyara ke da komai Allah ya baki mai kyau a jikin ki"
Dariya tamin kafin tace"Ko kana da kyau Fa'i ka kara da wankan sannan ki yi shuru kawai ba komai Allah ya bamu ba. muma duk barazana muke da kwalliya da gayun yana karamana kwarjini"
Kuma na yarda da mganarta,Domin naga gayu in da ake kiran gayu a wajenta tana fadin Ammi yar gayu ce sannan bata shiri da wanda bai son gayu,nace tabbas na shaida haka Sai naji nima ina so na fara gayun nan na shiga Sahun manyan mata Cikkaku.
Washegari Direban mijinta ya kaimu kano har gidan Yaya Asiya tare da ita muka dumguma zuwa gidan su Ammi,sun yi murna sosai sai nuna ni suke yi suna tambayan ita ce Fa'in Azizat mai turaran kamshi sai Nana Fatima ta gyada kai wasu daman mun Hadu Bikin Yaya Abdul'Ahad,Balle kuma daman Yaya Asiya ta zama yar gida,Duk yadda naso na wuce katsina a ranar bai samu ba saboda mun jima muna Hira a gidan su Ammi ita kanta Nana Fatima tayi yammh don dai motar gida ce.
Mun fito gidan su Ammi Nana Fatima ta nuna mana wani katon gidan Bene tana fadin"ina Engr din da zaku ji Abba na yawan mganarsa..?
Sai muka d'aga mata kai Saboda duk wanda yasan Abba yasan Labarin megidansa Engr.
Cikin Nuna mana gidan Nana Fatima tace"Ga gidan kakaninsa ta bangaran Uwa.nan aka haifi mahaifiyarsa dalilin makotansu da gidan su Ammi ma Suka hadu da Abba."
A tare da Yaya Asiya muka jinjina kai ina kallon gidan daga gani masu gidan suna da kudi sosai,irin kamar fasalin gidan da Abba ke ginawa a karofi sai dai wanchan ba gidan ba Bene ba ne.
Muna tsaye jikin motar da zata maida ta gida muke mganar Yaya Asiya ta ce"To ina masu gidan..?
Nana Fatima tace"Hajiya Tafisu ce mahaifiyar Hajiya Shukra ce kadai a gidan sai ya'yan yan"uwa Datake riko megidan ya rasu da jimawa daga ita sai yan aiki a cikin wannan gidan"
Na? jinjina kai ina kara kallon gidan da akace mace d'aya ce aciki Nana Fatima ta cigaba da fadin"Shi Engr babansa bayarbene mutumin Beneu ne, Hajiya Shukra ce bahaushiya suna Abuja da zama. Sai dai dangin su kaf suna Beneu har kakansu tana chan da ciwo ya kamata ne ma ta koma hannun Hajiya Shukra,Engr kuma shi a Edo yake aiki"
Ni dai har gajiya nayi da labarin Engr Nana Fatima ko ta zage har Yaya Asiya na tambayan"Tab.To ya"yansa nawa..?
Nana Fatima tace"Tab. Bai da ya'ya fa, ya taba aure sau da'ya sati biyu matar ta kone da gas shikenen bai kara aure ba.?kuma fa Abba ya girmesa, matashi ne sai dai yana da kirki sannan ya taka matsayi mai girma da kananun Shekarunsa"
Gani nayi sun bud'e hirarsa da Sauri na katsesu da fadin"Nana kada ki yi Dare"
Sai da nayi mgana ta farga Mukayi sallama Ta shige mota suka tafi,Dole na kara kwana gidan Yaya Asiya washegari motar asuba na hau sai katsina,Ance in mace mai ya'ya ta fi sati bata a gida sai abunda ta gani nima haka na tarar,kudin zobo da kunin aya sun ci ubansu,Hafsah sau Daya take yi a rana watarana ma in bata da Lokaci?batayi,sannan kudin kuma suna tabaawa in zasu siya wani abu ,sannan yara wlh sun yi kewata ranar da na dawo yini Ahmad yayi Tsalle acikin gida,Shi kan shi Gogan bakinsa har kunne har da fadin"Mutanen kano da Dutse maraba"a Tsime na amsa masa nazo musu da Tsaraban Dutse da Nana Fatima ta bada a kawo masu,nafi kwana Biyu,gidana da kasuwancina bai Dawo daidai ba,Na yarda mace itace gida ranar da bata to sai kame kame har Mama tayi murnan Dawowata..
A satin kuma naje Karofi,Matar Yaya isa ta haihu naga ginin Abba an kusa gamawa a raina nace komai in da kudi an yi an gama,ammh duka duka yaushe aka fara ginin nan har an kusa gama shi..?ban kwana ba na dawo gida Hafsah chan na barta zatayi weekend,ina kuma Dawowa na iske wani sabon salo ban sani ba ko Mahaifin zainab ko ita wanda ya kirasa kan zainab zata baro aikinta ta biyo shi katsina ammh sai ta fara neman wani anan sannan zata zauna agidanta ne ita kad'ai in ya amince shi ko yace bai amince ba sai dai tazo mu zauna tare a wannan gidan.
Yana gayamin takaici ya kume ni na kallesa nace"To gidan da zata zauna wazai Dauki nauyin sa..?
Kai Tsaye???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yace"Daddy ne mana"
Nima kai tsayen nace"To meyasa bazaka barta ta zauna inda zata Sake ba.?Mganar gaskiya gidan nan yayi mana kad'an ban ga inda ita da yara zasu zauna ba abun kuma yayi yawa"
Hade rai yayi kafin yace"To wai haukatani zaku yi ne..?
Nace Haukatani zaku yi ne..?
To anan zata zauna nace"
Sai na bude ido kafin nace"Ba damuwa ta zo mu zauna din na d'an Lokaci ne, kowa zai san matasayinsa"
Mgana na gasa masa ammh bai gane ba,Ya gimtse bakinsa nima na kama kaina ina ji har Mama sai da tayi? masa mgana tace gidan yayi mana kad'an ammh bai jita ba.
Har Anty Binta sai da mama ta kira ta shaida mata, itama fad'a ta hau yi masa na gidan ya yi mana kad'an,shi kuma yace ba ruwanta shi ya yi alkwarin bazai kara yarda a rika juyasa ba.
Karfin Hali kenan baka da ko asi sai bakin rai da isa,tab zan ko ga yadda wannnan zaman zai kasance.
Sai dai na roki Allah kafin hakan ya faru Allah ya bani mafita.





*Janafty*
[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2018*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Magana fa taki ta kare,Saboda Yaya Ishaq yayi rantsuwan Zainab bazata zauna a ko'ina ba sai gidan nan tare da mu,kuma bazai amince Mahaifinta ya kama mata gida ba.
Kowa yayi mishi mgana ammh bai ji ba,daman yana da Taurin kai wani Lokaci sannan rashin aikin nan nasa yasa zafin zuciyarsa ta karu,Mama gajiya tayi da mai mgana ta kyalesa har da kaninta Dake yamai ta had'a shi ko zai ji mganarsa ammh yace matsayarsa kenan.
Ni tunda nayi mai mgana yace nan din zata zauna ban kara masa mgana ba,na cigaba da Harkokin gabana. Ammh ganin ya dage da gaske yake yi yasa naji kamar nima in kai k'aransa wajen Abba ko Yaya Abdul'Ahad da kan kirani shima duk bayan kwana Biyu yaji lafiyata,Sai kuma na fasa saboda kai kara ba Halina ba ne sannan bayyana sirrin aurena ba Halina ba ne shima,ammh mganar gaskiya Yaya Ishaq zai tauyemin hakkina,Kuma gani yayi ya saba shiyasa yake so ya gwamatsa mu acikin wannan gidan.
Ni ban ma jin kaina nafi jin yarana Saboda komai daman nake yi saboda su ne, an saba tauyemin hakki na Hakura saboda su daman.
Sai nafara tunanin in Zainab ta dawo gidan nan a ina zai sauketa..?
Dakinsa dai falle d'aya ne,Sai bayi rayuwar mace bazai yu yu acikin wannan Dakin ba,bansani ba ko Dakin yara zai sauketa ko kuma ni yake so ya fitar dani daga dakin ya sakata ban yi dai mgana ba na zura ido ina ganin ikon Allah.
Ban sani ba ko sun yi ta ja'in ja da Zainab din ne,kan mganar sai kuma Kwana Hud'u da fara mganar sai ga Mahaifinta Dr.Lawal ya diro gidan Dakin Mama ya sauka sannan,sun jima suna mgana da Mama domin da kan shi yace shi Ishaq din ya basu waje zai yi mgana da Mama, daman wajenta yazo sai ya koma Daki yana cika yana batsewa ina tsakar gida ni dai ina Harkokina ban bi ta kansa ba. sai bayan awa D'aya da wani abu Mama ta leko ta kirasa,ya shiga shima ba jimawa sai ga shi ya fito ya kirani Lokacin kuma na gama Dafa zobo ne, sai na bar ma Anum ta kular min da shi kafin na fita na koma Dak'i na sanya Hijabi nayi sallama Dakin Mama na shiga.
Mama da Dr.Lawal ke zaune kan kujera shi kan shi Uban gayyar yana zaune a kasa nima sai nabi ayarinsa na zauna a kasa dagachan bakin kofar?cikin Ladabi na kara gaisheshi, sai naga ya amsa cikin kulawa ba kamar sauran Lokutan da in na gaisheshi yake amsani a wulakance ba.
Mama ce ta kalleni tana fadin"Kan mganar Dawowar Zainab nan ne. Yazo mun yi mgana yace a kira ki? Saboda mganar ta shafeki"
Tana rufe baki yayi gyaram murya ya cigaba da fadin"Ai itama y'ta ce Hajiya. Engr Usman karaye mutumin kwarai ne mun yi zumunci sosai da shi Lokacin muna masters a Buk bayan mun gama shi sai bai cigaba ba,ni kuma sai na tafi nayi Phd dina,nayi mamaki da ya ce min ke y'a kike a wajensa"
Kaina na kasa ban yi mgana ba sai yanzu nasan wato Dalili kenan da ya fara sakemin Tunda yasan Abba, kai wannan rayuwar sai Allah wa ka sani waya sanka ne. ya manta nan ya taba cewa zai batar dani har da Dangina akan yarsa ammh yanzu ko kunya ya zauna yana fadin nima yarsa ce'
Ina jinsa sama sama yana cigaba da bayaninsa Ishaq yake yi ma fad'a akan ya nemesa yazo ammh yaki zuwa.
Mama ce ta karb'esa ta basa Hakuri da Fadin"Ayi hakuri Alhaji ni kaina bansan meke damunsa ba kwanakin nan"
Mirmishi yayi kafin yace"Rashin aiki ne Hajiya kuma ina nan ina masa kokari. yanzu haka kwamitin Binciken da na kafa ya fara nisa kuma da yakinin insha Allahu za'a samu mafita"
Mama ta amsa da karfin Gwiwan Allah yasa a dace da mafita na Alheri,suka amsa da Ameen nima sai na amsa acikin raina Yaya Ishaq kansa na kasa bai ko Dago ba,Sai da shi da kansa ya kira sunansa sannan ya Dago yana amsawa,Cikin mirmishi Dr.Laawal yace"haka ake yi sai kayi fushi da Baban ka.?ni har Abada a D'a na Dauke ka. Kaunar da nake yi maka yasa na baka auran yata mafi soyuwa gareni. Wlh tallahi ba domin kai ba ne bazan taba yarda Zainab ta baro inda ta saba rayuwa zuwa wani wajen ba,Sai dai tana sonka sannan ta shirya ta zauna dakai,ammh sai nace ga Sharad'ina zan nema mata gida inda zata zauna domin bisa adalci ban ga wajen da zata zauna anan ba,Kuma ga Dawainiyar yara achan duk na Dauke ma kasu gata nayi maka sai kuma naga baka gani ba,kana Tunanin ina maka iko ne da matarka,Sannan nace zan nema mata aiki a nan garin,da aikinta ka sameta baka kuma da ikon da zaka hanata. Ammh sai naji kace baka yarda ba,Sai dai ta zauna anan tare da ku kai kanka kayi ma kanka Adalci,Ta yaya zaku zauna awannan gidan kalli fa gidan ga yara ga ku haba sai kace akuyoyi zaka saka ba Mutane ba..?
Ya fad'a cikin zolaya da yanayin mganarsa zaka san sulhu yake nema Saboda yarsa shi kuma nashi Jarabawar kenan,ammh duk wad'anan mganganun bai shiga kunnen Yaya Ishaq ba. yana dagowa sai cewa yayi"Gaskiya ni Daddy bazan amince kace zaka kama ma Zainab wajen zama ba,?nan din zai ishemu muma aciki muke zaune me ya ci mu..?Fa'iza nan take zaune da su Amir kuma akwai ishasshen wajen da zata zauna bazata Takura ba, idan ma har zan raba musu gida sai dai in ni na kama Hayar da kudina ko na siya gidan. ammh alfarman ne Daddy bana so, ba domin kuma na raina kokarin ka a kaina ba,a'a wlh nagode sosai bisa Dawaniyar ka gareni"
Ya karishe fad'a cikin Ladabi Dukkanmu shuru muka yi ni sai satar kallonsa nake yi ina ganin mamakinsa mutum ka Dage baka da ko asi lalle zan ga yadda za'ayi wannam zaman.
Mama ranta ya baci ta taso mai tana fadin"Kai dai ka cika Taurin kai meyasa baka jin mgana ne..?
Kai tsaye yace"Mama ki bar ni kawai akwai abunda nake dubawa ne. Indai tana so na to zata iya zama dani a duk inda rayuwa ta kaini. kamar yadda Fa'iza ke zaune dani"
Ya fada yana kallona sai na kauda kai nace ji wannan zai jazamin bakinjini Daman sunan Abba ne ya wankeni,To yana ambaton sunana tsakani ga Allah,Shi ko Dr.Laawal jinjina kai yayi kafin yace"To duk naji zencen ka, nuna min in da in Zainab d'in ta Dawo zata? zauna..?
Kai Tsaye yace"ko ta zauna ad'aki na akwai Tiolet aciki. ko kuma dakin yara sai su koma Dakin Mama tunda Badar na kano duk inda ta zaba duk D'aya ne"
Baki na bude galala ina kallonsa yako hade rai yasha mur,Mama tace"Wannan wani irin lissafin banza ne..?Kai ya girgiza ma Mama yana fadin"Ba lissafin banza ba ne Mama. Mganar su Fadil kuma Fa'iza zata rika kula da su"
Jar uba bansan haka mutumin nan ya raina ni ba sai yau, wato mganar yara Boyi boyi yar reno zata kula da su kuma bai ji kunya ba,Saboda daman baisan adalci ba kuma bai san yadda ake yi ba,Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa saboda gani nayi ko nayi mgana babu amfani ammh na rantse da Allah in ya fitar min da ya'yana daga bangarena to sai dai mu fita tare da ni da su,domin? bai isa ba.
Dr.Lawal dariya yayi kawai. Tsakani ga Allah uzuri ya yi masa talauci ai bone ne,Yana saka zafin rai da tunani masara kyau Mama zata fara fad'a ya Dakaatar da ita da fadin"kyalesa Hajiya na Fahimce sa. Shikenan zata Dawo ammh sai aikin nata ya samu,Ina kan nema mata ne,kai dai ka gyara mata muhallin da kasan bazata Takura ba tunda a inda ka Daukota ba'a Takure ka ganta ba"
Kai Tsaye yace"Daddy gidan iyayena Dabam gidan aure dabam. Ba lalle sai ta samu abunda ta ke samu a gidan su ba,in ina da shi zan yi mata abunda yafi wanda take samu a gidan su, in kuma bani da shi zan kwantata daidai misali"
Kai ya jinjina yana fadin"Gaskiya ne'"
Ni kaina nayi mamakin yadda yau ya yi laushi,ammh ba'a san yadda ransa ke bace ba ne. Saboda Zeey yake komai ta rokesa tana kuka kada ya yi Fad'a da Ishaq she love her Husband kuma ta shirya zama da shi a ko'ina. da ya nuna bai amimce ba, sai dai a raba auran sai Hajiya Halima tayi masa Bore ta tafi Chan rugar adamawa ta kai karansa wajen iyayensu akan zai kashe ma zainab aure,Kiransa suka yi suka yi masa Fad'a sannan da ikirarim Zainab akan in ya kashe mata aure to zata shiga Duniya sai ya rud'e zai iya juran komai ammh ban da Nesa da ya'yansa sannan zai iya rasa farincikinsa akan na ya'yansa ba haka ya Dauka yaron yake ba ya Dauka yadda ya rika Juyasa a farko yanzu ma haka zai juyasa. Sannan bai taba zaton Reshe zai juye da mujiya ba,ya dauka shi ne zai so zeey kamar ransa ya rika binta a daidai wannan Lokacin basu ne zasu rika lallaba shi bashine zai rika Lallabasu sai ga shi komai yana Faruwa ba yadda ya yi zato ba shiyasa yayi kokarin Daidaita Fushinsa.
Sannan yana mamakin kamar Engr Usman da ya sani mara d'aukan reni da Tsage gaskiya shine Diyarsa ke zaune in da bata Daraja,Tun farkon had'uwarsa da Ishaq? yasan Fa'iza bata da wani Daraja a wajen sa.
balle in akayi duba da abubuwan da suka yi ta faruwa,Sai dai yayi tunanin kila ra'ayinsa ne ammh shi kam bazai iya barin yarsa cikin wannan Wahalan ba Allah na gani.
Bai jima ba,suna gama mganar su ya tafi Daman jirgi ya shigo daga Abuja zuwa kano sai ya Dauko tashar Taxi zuwa katsina kuma yana jiransa zai maidasa,ni dai tun a matsayar farko ya sallameni na fito na cigaba da aikina ammh mamakin bawan Allah nan bai fita kaina ba wai yara su koma Dakin mama..?lalle bai taba ganin Haukana ba ne zai gan shi kwananan kuwa karyan Iskanci ma yake yi wlh raina ranar yini yayi a bace,ko fara'a ban yi ba shima kila hakan ya gani sai bai min mgana ba,Sai washegari yaran sun tafi makaranta Anum na tsakar gida tana shara basu fara daukan yan Jss1 ba ne wannan karon da wuri ba shiyasa. ammh komai nata Abba ya riga ya Turomin kudin Sakata kawai za'ayi.
ina D'akina ina had'a kudaden hannuna Hafsah zan kira akwai wasu kudi a hannunta ta biya kasuwa in ta Dawo ta siyomin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login