Showing 174001 words to 177000 words out of 288345 words

Chapter 59 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

745

ina jin tashin muryoyin su daga Falo,Chan sai ga Hafsah da wayarta ta kawo min Abba ke son mgana dani bayan na dauka mun gaisa yacee"Kuna lafiya ina matata da megidan naki..?
Nace"Duk suna lafiya Abba"
Sai yace"To madallah kan mganar Binciken da nace za'ayi kan Case din mijinki ne,Engr ya dawo nayi mgana da shi yace ba matsala sai dai zamu kara jira Tunda mahaifin nasa yana London Mahaifiyarsa ke chan za'ayi mata Dashen koda. hankalinsu duk ba'a kwance yake ba shiyasa har yanzu bai yi masa mgana ba"
Sai nace"Ayya Allah ya bata lafiya Abba"Sai ya amsamin mud'an taba Hira har ya bama Ammi muka gaisa tana min Tsiya"Hajiya Fa'i mai turaran kamshi"
Dariya nayi ina fad'in"Kai Ammi"
sai kawai tace"Abban ki ma yace y'ata ta iya had'a Turaren kamshi"
Kunya suka bani su ko ba ruwan su Abba da Ammi sai su,mun gama wayar kenan naga mutum tsaye a kaina ina dagowa cikin mamaki nace"Sannu da zuwa"
Sai kawai yace"ina son mgana dake. ki sameni a dakina"
Daga haka ya fice mamaki ya kamani na rike haba a fili nace"Topha..!
Ina shirin tashi aka fara kiran sallar Isha'i sai na mike nayi salla na idar kenan na mike ina ninke Darduma Anum ta leko tana fadin"Umma Daada na kira"
Sai na gyada mata kai ban ko cire Hijabin jikina na fita zuwa Dakinsa ina Shiga sai faman safa da marwa yake yi har sai da nace"Lafiya..?
Kai tsaye yace"Ina jin yunwa ina abincina.."
Kai Tsaye nace"Aiki nayi nagaji sai da Hafsah ta shgo nace ta dafa mana ko Taliya"
Sai kawai naga ya karisa ya rufo kofa da Sauri nace"Ya da rufe kofa..?
Yana juyowa yace"Yau zamu yi ta kare Fa'iza hakki na zaki bani nagaji"
Gabana ya fadi na kwalolo ido waje hakkina..? Na maimaita a raina.
na shige su ga shi in nayi wani ihu yara na falo suna jin mu.
bakina yayi nauyi ina ji ya ja har hannuna bakin katifarsa ya cire min Hijabin jikina cikin rawan murya nace"Abincin fa..?
Kai Tsaye yace"Zamu ci in mun gama. Fa'iza bazan iya jira ba"
Bakina naji yayi wani Dif. Jikina kuma Kamar mara Lakka, kamar rakuma da akala haka yafara bi da ni a gaggauce kamar daman ni yake jira.







*Janafty*




[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2017*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Saboda yanayin da zuciyata take ciki yasa kwata kwata gangan jikina bai karb'i sakonnin dayake aika min da shi cikin zafin nama ba,Doguwar riga ce a jikina har ya samu nasaran Rabani da ita,ammh na kasa wani motsi na riga na Sadakar bani da wani Tsumi ballatana Dubara a lokacin.
Bakina ne yayi min wani irin nauyi, ina ji kamar ya kumbura saboda irin yadda Yaya Ishaq ya rika sumbatata a raina sai cewa nake yi daman haka Sumbarta take..?
Sharaf nayi masa ko hannuna ban yarda na motsa ba,kwance nayi masa kamar ruwa ya cinye ni,Ina jinsa yana gwama Numfashi,sama sama sannan Lokaci d'aya yana sauke ajiyar rai chan naji yana kiran sunana fad'i yake yi"Fa'iza ki rikeni. Ki rumgume ni don Allah"Ya fad'a cikin wani irin yanayin da ba kowa zai iya sanin yanayin ba.
Nayi masa banza kamar ban ji ba, kuka ne ya taho min daga karkashin Zuciyata sai hawaye sharr sannan na saki Shesshekan har yana jina.
Sai naji kamar an zare masa lakkar jiki ya koma ya kwanta a gefe yana maida numfashi. ni kuma ina ta kukana sai ya mike zaune cikin yanayin Sarkewar murya yace"Yanzu Saboda zan karbi Hakkina ne yasa kike wannan kukan Fa'iza.?
Shuru nayi masa ban yi mgana ba sai dai ina cigaba da kukana kamar karamar yarinya sai kawai ya mike Kaina na juya gefe har ya gama Suturtata jikinsa,ina daga kwance kawai naji ya yi wuf ya tadani zaune yana fadin"Tashi ki saka kayan ki"
Sai na bisa da kallo ina Tunanin ko ya fara samun matsala ne ganin yana komai a gaggauce.
Mikar dani Tsaye ya yi ya na kokarin sakamin rigar na rike hannunsa muryata a shake nace"Bari zan saka da kaina"Kamar wacce zan gudu ina gama sakawa ya jawo hijabi ya zuramin Saboda Sauri kamar zai ciremin kai, nayi baya ina kallonsa da Tarin mamakinsa Maikon hawaye sun cikamin ido ban samu damar mgana ba. kawai ya finciki hannuna ya isa ga kofa ya Bude yana jana muka fito Falo yaran duk suna falon suna ganinmu suka bimu da ido ganin yana kokarin Fita daga Dakin yasa na Turje ina fadin"ina zaka kai ni..?.
Bai ko Saurareni ba ya fincikeni zuwa waje sai kawai naga mun shiga Dakin Mama Lokaci d'aya yana fadin"Mama kin kwanta ne..?
Mama na zaune saman kujera da waya a hannunta kamar ta ma gama wayar ne muka fad'o dakin yadda ta ganmu ne yasa ta mike a firgice tana Fadin"Kai lafiyan ku kuwa..?
Gabanta ya zaunar dani yana Fadin"Mama gata nan ta fad'a miki meyasa take hanani Hakkina..?
Ki tambayeta meyasa take guduna bata kaunar na rabeta. Mama Fa'iza na gudu na a Shimfid'a"
Shi yake mganar nan ammh ni kunya da bakinciki sun rufemin ji na da ganina na wani Lokaci,Tsabar yadda na kad'u na girgiza da wannan wulakancin na Ishaq .ashe shi yana da bakin mgana ban sani ba..?ni shekarun da ya kwashe a jingine da aurene wajen wa na taba kai karansa.?sai shi ne yake da bakin mgana."
Kaina na dunkule a kasa ina kuka kamar na mutu haka nake ji Saboda kunya ita kanta da Mama sai da ta kasa zama kunya duk ya Rufeta ta kasa mgana tana mamakin d'an yau.
Kallonta yayi a rikice yana fadin"Baki ce komai ba Mama..?
Sai Mama ta juya baya tana fadin"Fa'iza ki yi hakuri don Allah.Kada ki kara gudun mijinki a shimfid'a. kai kuma ka bita a hankali kada ka matsa mata."
Wannan mganar ku ce Tsakaninku ne, don Allah kada ku kara sakani"
Daga haka ta shige uwar Dakin ta tabar mu nan zaune,shi yana Tsaye ne kamar wani Saraki.
Kafafuwana sun yi min zafin da na kasa tashi sai da na ganshi Durkushe a gabana yana fadin"Kin ji dai abunda Mama tace ko..?kada ki karamin Gaddama in dai na kira ki a Shimfid'ata"
Sai kawai na Dago Rinannun Idanuwana na sauke a kansa cikin wata irin murya mai cike da Takaici nace"Meyasa ka kawo k'ara na wajen Mama..?
Sai hawaye ganin kukana sai kuma ya Rud'eni ya fara kokarin son rikoni yana fadin"To ke ne Fa'iza duk yadda zan yi dake kin ki ganewa shiyasa na kawo kararki wajen Mama"
Ture hannunsa nayi dake kokarin rikeni na mike Dakyar ina fadin"n ban taba kawo kararka ba.
Ban taba fad'ama kowa halin da nake ciki ba,ko da yan'uwana ne. sai kai ne da bakin ka yafi nawa Tsini..?.
Na karishe fad'a a Fusace cikin kuka Sai shima ya mike yana kallon Dakin da Mama ta shige Lokaci daya yana Fadin"haba mana.."
Kuma wai yana kokarin rikoni Saboda bai da kunya a fusace na make Hannunsa ina fadin"Tunda kaso a fasa komai za'a fasa kowa yaji"
Ganin ina nufar dakin da Mama ta shige yasa ya rikoni da karfi yana Fadin"Don Allah a'a Fa'iza don Allah"
Daman ba fad'a zan yi ba sai na Turesa na kama Hanya na fita Daga Dakin mama,zan shiga Dakina ya Taremin Hanya yana faman marairaicemin sai kawai na juya da gudu nayi hanyar waje saboda naji hayaniyar yara har lokacin suna falo kamar abinci suke ci bana so su Fahimci abunda ke faruwa.
Shima da gudun yabi bayana yana kiran sunana gaba na ya sha yana Haki yace"Ke ke ina zaki..?
Cikin duhun Korodin dakin Jamal na balla masa Harara ina fadin"Tafiya zan yi..Zan tafi ne wlh bazan zauna dakai ba"
Na fad'a masa cikin Tabbacin mganata sai ya Rude ya fara fadin"Ban gane ba.
Wani irin tafiya kije ina kuma..?.
Kai Tsaye nace"In da baza'a takurani ba sannan inda nima zan kai kararka.Nima ai ka jingine shekaru ina maka gadin ya'yan ja wa na taba kai ma kararka..?sai ni Zaka kai ma Mama karar na hanaka kaina ina ce ba kai ka ce na kyaleka ba..?
Ba kai kace na barka kayi Sabuwar Rayuwa da wacce ka zaba ba .?
Meyasa sai yanzu zaka matsamin na gayamaka aurena dakai ba aure ba ne yanzu,Jingina ne.."
Na karishe fad'a cikin Tsawa lokaci daya ina kuka sai ya kasa mgana Saboda yadda na ke ture hannunsa in yakai min zai rikeni Cikin fitan Hayyaci yace"Ke ba ki Afuwa ne Fa'iza..?wlh na yi nadama na tuba na bi Allah na biki kiyi ma girman Allah ki saurareni"
Da Sauri na daga masa hannu ina Fadin"Bazan saurareka ba. Na fada maka ka daina cewa aure aure, auren mu a jingine yake in ka cigaba da matsamin na rantse da wanda raina ke Hannunsa zan bar gidan nan Daman ya'yan ka ne kuma sun yi girman da zasu kula da kansu. Ahmad ne matarka ta had'a da na Hannunta da wanda zata haifa ta rike maka ammh in dai na tafi to Har abada BAZAN DAWO BA"
Na karishe fad'a ina Tsaida kallona a kansa Cikin Firgici yace"Eh. A'a kije ina.?Fa'iza kina son ki kasheni ne..?
In kika tafi to na zauna da uban wa.?.kai Tsaye nace"Ka zauna da Zainab wacce ka zaba sama da ni"
Kara girgiza kai yayi yana fadin"Aa ba inda zaki.Ba zaki tafi ba Fa'iza in ba so kike na laalace ba"
Cikin kuka nace"To wlh in ka kara matsamin sai na tafi kuma nayi Rantsuwan in na tafi bazan dawo ba. Sannan in ka kara kai karata ba ma wajen Mama ba,wlh ni kuma sai na Fallasa ma duniya komai, tasan Tsakanina Dakai auran jingina ne"
Kamar na watsa mai ruwan zafi haka yaja baya yana fadin"Na shiga uku don Allah kiyi hakuri Fa'iza, eh naji Wlh naji na yarda bazan kara matsa miki ba ammh kimin rai kada ki fad'i wannan mganar wani yaji don Girman Allah.."
Kukana na Tsagaita kafin nace"To naji bazan tafi ba. kuma kamar yadda nayi maka alkwari tun a baya sai dai kai ka fadi mganar da bakinka ammh ni nayi maka wannan alherin kamar yadda ka Rokeni,kada ka kara cewa zaka Takuramin ba wani hakkin ka dake kaina, domin tun kafin auran ka da Zainab ka rokeni da nayi maka adalci na kyaleka kayi rayuwa da wacce ta dace Dakai a lokacin ban yi maka korafi ba.? sannan ban taba maka gaddama ba har Tsawon yau din nan To nima bana son kayi min Korafi abunda ka zaba ne, nake yi maka kada ka kara damuna ni bani da jikin da zan baka ka mora sannan ban chanchanci wannan binbinin daga gareka ka ba. kyaleni don girman Allah.
"Na karishe fad'a cikin Kuka ina Had'a Hannayena jikinsa a Sanyaye yace"Duk naji na yarda mu koma cikin gida kuma ki daina kuka ga yara chan kada su dauka na Dake ki ne"
Ban yi musu ba na daina kukan na Share hawayena na kama hanya na koma yabi bayana muna Zuwa Tsakar sai ga Hafsah ta fito daga Dakin Mama abinci ta kai mata tana ganin mu tace"Fita daman kuka yi..?
Da Sauri yace"Eh eh.."
Dagaji bai da gaskiya ni dai daga shi har ita rabasu nayi na shige ciki Suna cin abinci yaran Anum har ta mike taga nayi Zaraf na shige Daki har da banko kofa,sai suka yi wani shuru Baban nasu na shigowa suka sakamai Ido duk sai ya Daburce Anum ne tace"Daada me ya samu Umma..?
Da sauri yace"Umma.."
Ya kasa mgana Amir ne ya kwace sa da Fadin"Kila bata da lafiya ne" jin haka yasa yace"Eh eh bata jin Dad'i kuci abincin ku"
Daga haka ya wuce Dakinsa yana Zufa yaran suka bisa da kallo harda Hafsah da ta zargi wani abu na faruwa sai dai bata ce komai ba ta kira Amir ya Dauki abincinsa yakai mai,sai gashi ya Dawo dashi yace bazai ci ba. nima kuma sun kawomin nace su Dauke bazan ci ba,da suka shigo ma sun fara min Hayaniya na koresu nace kaina na ciwo,Su kansu sun san an tabani gabad'aya har wayewan gari suma duk sun yi wani iri ban ma fito ba Hafsah ta musu komai Hatta zobo ita ta Dafa ta barmin na hada ta wuce makaranta shara da wanke wanke kuma Anum tayi shi ban fito ba sai da rana Saboda zuwan dangin Mama daga yamai dole ta sani na Dora girki,Yaya Ishaq na dakinsa in ji Anum ammh ban ko duba barayinsa ba,Da yammah Halisa tazo nayi mata Dilka washegari da Safe muka hadu na gaisheshi ya amsa sannnan na gayamai yau zan je gidan Anty Binta akwai Walima ba gaddama yace a dawo lafiya, ni kadai na tafi yara suna makaranta Anum kuma tun safe tabi Anty Hure suka tafi.
Sai Dare muka dawo chan Badariya ta iskemu an yi walima ni nayi zobo da kunin Aya sannan tare da ni akayi cake din Rabo,Da Sassafe kuma na koma Saboda girki duk da ta Dauki ma'aikata ammh ni zan rika nuna musu komai yara basu je makaranta ba Hafsah da ta shiirya ita da Badariya ta taho da su,Hajiyar Dala ta zo ita da Suwaiba,Yaya Asiya ce bata samu zuwa ba Yaya mariya ma tazo abun mamaki har da su Anty Nasara,gida cike da baki na nesa da na kusa, aranar za'a Daura aure,sai washegari Lahadi da safe a wuce da Amarya mun yi waya da Nana Fatima da farko ban fad'a mata zan zo kano ba saboda nayi Tunanin in na tafi wazan bar ma gida? ammh Daga baya sai na fasa nace sai naje shi ya zauna ya kula da gidan da ya'yan sa.
ban yi anko ba saboda bata nuna ma kowa ba,ammh nima na yi shigar alfarma cikin kayan da Hajiya ke dinkamin ne super wax na saka,Da Daddare gida na muka dawo da su Anty Nasara yaya mariya dai chan muka barta daman nasan bazata Biyoni ba.
Amir na aika nace ya gayamasa zan raka Halisa kano,kai Tsaye yace Allah ya kiyaye hanya,Da yake shima da Safen ya shirya ya fita saboda Daurin auran Safe ne Na fad'ama Mama zanje kano sannan zan bar yara Saboda makaranta Ga Hafsah ga babansu tace ai daman ya kamata naje ni ko bata sani ba gidan ne da D'anta suka isheni. zan yi musu yaji na kwana Biyu.
Kaya kala Biyu na dauka da abunda zan Bukata,Anty Nasara ce zataje Goggo gida zata koma Hajiyar Dala Daman yan gida ne suna cikin masu tafiya.
Karfe goma da rabi aka Daura aure zuwa sha biyun rana an fara tafiya Saboda kada ayi dare ni mota D'aya muka hau da Badariya da Anty Nasara,Yaya mariya bata je ba megidanta bai barta ba.
Anum har da kukanta sai taje sai da nayi mata Jan ido Amir daman bai da damuwa sauran kuma suna wajen Babansu.
Ban taba zaton zan iya tafiya na bar ya'yana ko da na yini d'aya ba sai ranar, na gwada ne daman naga ko zan iya sai dai muna tafiya ne ina jin kamar na bar baya da kura.?wazai kula da su..?Hafsah tana zuwa makaranta shi kuma bai iya komai ba ballatana ya Kula da su, sai dai hankalina ya kwanta da na Tuna na Horar da ya'yana Musamman Amir da Anum zasu kula da Sauran kannensu.
Dama already an yi ma amaryan jerenta gidanta mai kyau ita kad'ai,da muka isa abinci muka ci sai sallah sai kuma dan Saura gyare gyare kawayen Anty Binta sun kama komai yasa mukayi musu sallama sai gidan Yaya Asiya. chan muka kwana muna Hira harda Badariya,washegari Litini muka shiga kasuwa na raka Anty Nasara nima har na siya ma Anum takalmi mai kyau na mata, da muka dawo har da Yaya Asiyan muka leka gidan Amarya chan muka hadu da ya'yan Hajiyar dala sai dare Direban da zai maida su gida ya Saukemu gidan Yaya Asiya ranar Talata Anty Nasara tace mu tafi sai nace ta tafi zan taho bata Damu ba ta wuce karofi a ranar,ni kuma bansan Dalilina nakin komawar ba Yaya Asiya kuma tasha Ishaq ne ya barni Har tana jin dad'i.
Tun da muka zo bai kirani ba sai ranar Laraba da Daddare ina Dakin Yaya Asiya ita kuma tana wajen mijinta naga kiransa sai nayi mamakin sanin bai da waya bayan na Dauka mun gaisa sai yace"yaushe zaki dawo.? Yara sun damu fa"
Sai na basar da tambayar sa,ina ya samu waya na tambaye sa,kai Tsaye yace"Zainab ta aikomin daga chan"
Sai na yi shuru ban yi mgana ba ganin haka yasa sai ya mika ma yara wayar duk dai korafin Umma yaushe zaki dawo ne? nace zan dawo kada su damu ina Tunanin har da shi ya Dinga matsa musu su ji yaushe zan dawo ni ko a raina nace ba yanzu ba,ko zan dawo .har ga Allah ba da niyyar zuwa Dutse nazo ba sai da Yaya Asiya ke min Tadi'n ba nisa fa daga kano to Dutse gidan Nana Fatima kamar almara sai? ko nace zani na kirata na Fad'amata ta daka Tsalle da Ihu tace in na hau mota da nazo tashar Dutse na Kirata zata zo ta Daukeni nan da nan naji Kwadayin zuwa na yi ma Yaya Asiya karya da ta tsareni da tambayan shin an bar ni..?
Nace mata eh mana ya barni sai ta kyaleni mijinta yarakani na hau Mota ranar jumma'a gabana na fad'i hakan nan na Daure bayan na roki Allah ya yafe min na yi doguwar tafiya mijina bai sani ba, Sai ko gani a Dutse ina kiranta sai gata tazo ta Daukeni har tasha muka Rumgume juna.
Sai gani a kayattacen gidan Nana Fatima mijinta babba ne Aikinsa D'an sanda farin kaya ne,Ita da mijinta kamar zasu goyani yana Dawowa a gaba na suka rumgume juna yana da fara'a kamar ita yana ganina Tun kafin na gaishe shi yace"Sannu da zuwa Fa'in mu maraba da zuwa Dutse"
Ina mirmishi na amsa masa duk yadda zan baku labarin gidan Fatima da Ahalinta sun wuce haka,Ya'yanta Jalil da jidda tun saba dani kamar sun sanni daman gani da son yara, Daki guda Nana Fatima ta ware min kuma har ta Kira chan gida ta fesama su Abba zuwana. Ammi tace kafin na koma Nana Fatima ta rakani har kano na gaida Hajiyar su tace in sha Allahu zata kaini,gani nayi dai ban kyauta ba, ranar da na kwana na yini na kirasa na fad'amasa ina Dutse gidan Nana Fatima. kai tsaye yace"Kika tafi har Dutse

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login