Showing 144001 words to 147000 words out of 288345 words

Chapter 49 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

772

da Fa'iza da Zainab naji dadin wannan ziyaran Allah ya hada kawunan ku"
muka amsa da Ameen ta karbi Fadil tana fadin"Wannan ne kama da yan sudan di'n fa..?
Ina dariya nace"Kanin Farhan ne"
Tana dagasa sama tace"Naga kaman su da Amadin ki".
Hajiya ba ruwanta tana da sakewa muna ta Hira da ita tun zainab bata saki jiki ba har ta saki yaran kuma tuni su Raliya sun jasa su cikin gida,duk yadda muka so mu tafi kafin isha'i sai da ta hanamu shi ko Babansu sai kira yake yi Zainab nace mai muna Hanya sai da muka yi sallar isha'i muka yi shirin tafiya ta bamu kyautan atamfofi super guda biyu,yaran kuma kudi sabbin yan Hamsin kowannen Bandir d'aya Badariya kuma tace ta dawo ta karb'i nata Sakon har haraban gidan ta rakomu ita da ya'yanta da sai tambayan Hajiya suke itace Fa'iza me Turare da dilka..?.Sai Hajiya tace itane sai kiga wad'anda basu sanni ba suna gaisheni cikin girmamawaa.
Sai da muka kamo hanyar gida sannan Zainab tace min"Yar'uwan ku ce Hajiyar nan..?
Na girgiza kaina ina fadin"Aa sune shugabannin wata kungiyar taimakon mata da marayu,wad'anda suka koya mana wannan sana'ar da nake yi. sanadin haduwar mu kenan sannan Raliya diyarta kawar Badar ce"
Sai ta rausayar da kai tana fadin"Tana da kirki sosai"
Na jinjina kai ina ba'a mgana,hirar ta muka rika yi har muka isa gida,Badar na fad'in irin kudin su ya'yan Hajiya manya maza duk ma'aikan gwamnati ne,matan ma suna auran manyan manya a garin katsina,itama aiki take sannan suna da manyan kungiyoyin mata na taimakon mutane"
Ko da muka koma Gogan ya cika saura Kiris ya fashe sai hararan mu yake yi,Zainab tace"Honey mun dawo"
Yana kwance kan kujera yace"Na ganku,sannan ku da zuwa sai a tube a sama min abunda zan ci"
Ina kwantar da Fadil da yayi barci akan kujera nace"Yunwa kake ji.?ina abincin da na bar maka a kula..?.
Yana daga kwancen yace"Ban yi ra'ayin ci ba,sabo nake so"
Ni da zainab muka kalli juna sai ta zauna wajen kafafunsa tana fadin"Maman Amir barayin ki ne wannan, ni bari naji da lallashi"
Ban damu ba,na shige dakina na sauke mayafina da kayan hannuna na shige kitchen. yaran kuma suna ta murna da Budirin kudin da aka basu suna nuna mai ya karb'a yana fadin"Tunda kun zama masu kudi kowa sai ya bani goron sallah"
Suka fara Dariya yana taya su bansan ya suka kare da Amaryansa ba, ni dai Shinkafa na sake dafamai sai nayi mai miyar albasa da naman kaza na kawo mai da maltina na iske suna hira da matarsa sai na shige daki nayi wanka na Sauya kaya na gaji ga barci yaran ma da kansu nace suyi shirin kwanciya,Fadil kawai na karb'a mukaje muka kwanta Farhan tare da su Amir zai kwana Anum kuma sai ta gama iyayinta zata shigo ta kwanta.
Mun so washegari mu je karofi ya hana,Sai da aka kara kwana sannan muka tafi gabadaya har da shi da Badariya da Jamal,sai dai su Goggo suka ganmu kamar daga sama mamaki da murna ya hana Goggo sakat sai fad'i take"maraba da bakin alheri. ni kadai da zaratan masu gida haka,Allah yasa kun zo da cefanen ku"
Amir ya zaro mata kudi yana fadin"Nawa kike bukata Tsohuwa..?.
Ta ko warce kudin tana fadin"Duka nake so"
Sai ya fara fadin'Ke ko goggo baki san wasa ba"
Gabadayanmu sai da muka yi Dariya Yaya Ishaq dai duk yaji kunya,Kansa na kasa yana gaida Goggo ita ko a Fuska bata nuna masa wani abu ba,Su Anty nasara duk suna gida aka gaisa sai fa alokacin wasu suka san Zainab da su Farhan,mune har gidan su Yaya Isa achan muka sallar la'asar daganan muka isa gidan Yaya mariya tayi mamakin ganin mu sai kallo na take yi cikin gatse tace min"To su Fa'iza dai akwai ki da son a sani yawo da kishiya"
Allah yasa zainab ta shiga ciki tayi waya,da Yaya mariya tamin baramb'arama a gabanta,ban bata amsa ba ta kara kallona tana fadin"Naga kin yi wani d'anye ne ko dai ciki kika kunso ne..?
Dariya na kwashe dashi ina fadin"Ciki? ai mun bar ma masu mazaje a hannu"
Dariya ta yi lokaci d'aya ta daki kafad'ata tana fadin"Oh Allah! ji yadda Fa'iza ta koma shekaru biyar bqya, wazai ce Fa'izan nan ce mai shuru shuru da an yi mgana ta hau kuka tana kuyi hakuri"
Tafad'a tana kwaikwayon mganata ni dai ina ta Dariya Hafsah na gidan daga barci ma ta taso na kalleta ina fadin"Sannu yar hutu gidan Goggon kenan..?tana sosa ido tace"Yau fa nazo chan hayaniyar yara"
Yaya mariya tace"To ai ga hayaniyar nan Fa'iza ta tattaro miki har da gayyar sod'i ba katin gayyata"
Sigina na rika yi ma Yaya mariya ammh ta nuna kamar bata gane ba,Allah ya taimakeni da Zainab din ta fito sai ta gyara bakinta sai dai Taki sakin jiki da ita sai ma had'e rai da tayi shiyasa bamu dade ba muka tafi sai ko ta rakomu har gidan Goggo nan suka had'e Da Yaya Ishaq akayi kallon kallo ta Dauke kai abun mamaki ammh shi sai yace"Mariya ba gaisuwa..?to ni bari na gaisheki tunda ta wani fanni ni kaninki ne an yi salla lafiya ne? ?
Ba ita ba har su Goggo sai da suka yi mamaki sai dai ba wanda ya nuna hakan,Yaya mariya ko da lafiya ta amsa mai kafin ta Dauke kai, daman taji labarin sa a wajen Hafsah kafin ta tafi sai da tajani gefe tana fadin"Ke naga wannan wawan mijin naki na wani rawan kafa akanki saboda yaga yanzu ba shi da komai, kina sana'a kina yi mai wahala to in kika sakar masa ke kika sani,kada dai ki manta da abubuwan da suka faru a baya wlh kada naji kin sakarmai ki bari sai ya samu aiki yi in har chanjin na gaske ne sai ki gani"
Ban ja da nisa ba nace mata toh kawai nasan halinta yanzu ina ta wata mgana sai ajimu daga waje,
Kafin mangariba muka tafi,da Tsaraban su gyada da aya,Sannan na taho da ayan na da ganyen zobon da Goggo tace na bada kudi ayo min Sautin su a kauye anfi samun sauki,To shine na ba ma Hafsah da zata zo ta zo mata da kudin, shine na dauko kayana ita dai Hafsah tace sai ta kara kwana biyu zata dawo.
Tunda muka dawo bamu sake fita ba muna gida muna warware gajiya,Zainab sati daya tayi ta koma Abuja ni kaina sai da naji kewa ballatana yara da suka saba da kannensu,shi ko Yaya ishaq ranar da ta tafi har ce min yayi yaji dadin tafiyarta kila na sauraresa yanzu kai namiji sai a barsa, nan yake shigewa daki da ita fa yana amfana ammh baazai yarda ba sai ya yi dadin baki.
An gama Hutun salla yara sun koma makaranta Mama dai taji dadin yamai bata dawo ba,Hafsat ta dawo saboda makaranta,Badariya kuma na gidan Anty Binta tsakani da sallah ba Dadewa suka yi graduation na gama makaranta,Raliya har walima Hajiya ta shirya mata agida,an yi waliman ko sati ba'ayi ba Hajiya ta aiko min da Kayan saka ranan Raliya,nayi murna sosai Badariya itama tazo tana fadamin har da na Halisa itama an saka,yar wajen Anty Binta zatayi aure a kano dan'uwan mijin Hajiyar Dala ne,ita kuma Raliya chan wajen bikin Laila suka hadu da shi,Yaron yayar wanda Laila ta aura ne.
Bansan me ya faru ba sai gani kawai nayi Badariya ta had'o kayanta tazo ta Bude dakin Mama ta share ta dawo,kamar bazan mata mgana ba sai naga tana cikin damuwa ranar bayan fitan yara makaranta na bita har Dakin sai na isketa tana kuka.
Na tsorata na zauna gefenta ina tambayanta me akayi mata take kuka..?
Sai ta mike zaune tana cemim"Don Allah Anty Fa'iza aure na waye..?
Kai tsaye nace"Aure na Allah ne Badar me ya faru ne..?
Sai ta sakamin kuka tana fadin"ba na fada miki an saka ranar auran Halisa ba?
Na daga mata kai sai ta cigaba da fadin"Shine shine fa tunda ta samu ssurayin nan take min gani gani har Anty Binta tana gani Halisa na min wulakanci don ina zaune a gidan su,Gori kala kala take min wai bani da Tsayayyen saurayi sai shirme shine fa a Shekaranjiya Salisun da zata aura yazo daman ya sanni don yace ta kirani mu gaisa muna gaisawa muna hira sai zuwa tayi ta cemin wai don Allah na fita tana so ta gana da saurayinta nayi kane kane kamar ina so nayi mata sinacin"
Ta karishe fada cikin kuka cikin wani yanayi nace"Miye sinacin?
Kai tsaye tace"Wai zan kwace mata shi Haba Anty Fa'iza ko Hali na ne ai bazan yi ma Halisa ba,mamanta uwa daya uba d'aya muke da ita ballatana ba Halina ba ne"
Sai na rike hannunta ina fadin"To miye na kuka tunda kinsan ba haka ba ne..?
Sai ta kalleni tana fadin"Na shiga damuwa ne anty Fa'iza na kai minzali nima kawayena duk da muke tare sun yi aure,ga Raliya itama an saka mata rana,ni kuma gaskiya Halisa ta fada bani da wani Tsayayyan Saurayi, sai ka samu kana murna sai ka nemi mutun ka rasa ga halin da yaya yake ciki akallah dai nima na kauce sai wata Lalurar ta Dauke muku Anty Fa'iza"
Sai kawai ta kara saka kuka ni ko na Dage ina ta lallashinta sai da tayi shuru sannan na kalleta ina fadin"Saurareni Badar.shi aure da kike gani na Allah ne,Sannan mutum bai isa yayi ma kansa aure ba. shi kamar zanen kaddara ne irin na mutuwa da haihuwa ne lokacin da Allah yace kun ya fakum ba wanda ya isa ya hana Faruwarsa,kada kice zaki saka damuwa don wance tayi aure wance batayi ba ki dai ki bar ma Allah zabi ki kama kanki ki Tsarkake mu'amalan ki da Allah da Mutane kina Zaune Allah zai kawo miki miji nagari kiyi auranki. kada Surutun mutane ya Dameki ita kuma Halisa ki kyaleta in dai namiji ne ai d'an Babansa ne kina zaman zaman ki sai nuna mata kalan da zata gane tayi kuskure ki kwantar da Hankali Allah na sane da bayinsa masu takawa da Hakuri"
Sai da na Tabbatar da mganata ta shigeta kuma ta aminta da mganganu sannan na fito daga Dakin ni kad'ai a Tsakar gida ina aiki Tausayin Badariya ya cikani kowaani bawa da nashi kabulen Rayuwar in kana gida baka yi aure ba, ace kaki aure shi kuma mijin ba Tukunya ba ne balle ka tantance na gari,sai ga shiga gidan wani auran kaji gwara zaman ka agidan ku ma,ammh duk lalacewar aure yana da Daraja saboda Ibada ce ta Ubangiji.
Nayi alkawarin a duka Khamsin Salawatul di'na zan saka Badariya aciki,domin Allah ya sama mata mafita alokacin ma sai da na daga Hannayena sama nace"Ya Allah ga Baiwar ka nan Badariya ka fi ni sanin Damuwarta a cikin zuciyarta Allah ka kawo mata mafita daga cikin kyawawan mafitan da kake bawa bayin ka Salihai,Allah ka turo mata miji nagari wanda zai share mata hawayenta"
Sannan na shafa a raina ina jin Wani iri,rayuwa kenan kowa da irin tasa kaddaran.





*Janafty*



[7/17, 7:32 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2010*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000*
*09069067488*


Har ga Allah na taya Badariya damuwar halin data ke ciki,Saboda ina aiki in abun ya fad'o min a rai sai na tsaya nayi mata addu'a acikin raina ballatana da naga tafi kwana biyu kafin ta warware sai nayi amfani da wannan damar na kara jawota a jiki ina kara nuna mata in dai tayi yakini da Allah ke yi to ta saki ranta mun rokesa kuma shi Allahu Rahimun ne,yana share ma bayinsa hawayensa da haka na samu ta saki jikinta. sai ya kasance in yara sun tafi makaranta Hafsah ta fita zata fito? taimaka min da aikin gida,wani Lokacin har da na sana'ata muna yi muna hira hakan sai ya rika debe mata damuwa.
Ba'a fi sati da dawowarta ba ranar sai Yayan nata ya kirata,ina falon lokacin na shigo da bahon da na jera gorunan zobo zan shiga kitchen na jera a frezer ta ma shigo ta tayani ne ya kirata,Kasa kunne ba Halina ba ne ballatana da nake da raunin ji da nasan ko na kasa kunnen ba lalle bukata ta biya ba,sai ban damu da naji abunda yake tambayanta ba, na shige na cigaba da aikin gabana sai ita ne ta shigo bayan ya sallameta tana cemin"Anty Fa'iza kiji Anty Binta"
Sai na dago ina fadin"Me ya faru da Anty Bintan..?
Cikin yatsina Badariya tace"Wai yaya Ishaq ta kira tana fad'an wai daga mun yi hatsaniya da Halisa ko sani batayi ba na hado kayana na dawo gida"Mirmishi nayi kafin nace"To shi yayan me yace?baki ta tabe bakin tace"Me kuwa.?fad'a ya yi min wai na rika hakuri da rayuwa"
Sai na cigaba da aikina ina fadin"Ya fada miki gaskiya. Ke uwa kike ga Halisa bamai sauya wannan sunan a wajenta har abada"
Daga haka bata kara mgana ba illah hmm!da tace min ta zo ta kama min muna jera gorunan tare ganin haka nima sai na saki mganar muka kama wata,Yadda shi ma bai min mganar ba haka nima nayi kamar ban sani ba ni nasan ina da miskilanci kuma abun nawa ya had'u ne sanadin mijin da nake aure da irin yadda ya tafiyar dani wajen zamantakewarmu,shiyasa na zama ba komai nake mgana a kai ba.ballanta na nuna na sanin din na koya ma kaina ga duk abunda ba'a ce Fa'iza zo kiji ba, ko zo ki gani ba. na fahimci bawa zai fi zama lafiya in ya bar abunda ba ruwansa hadisi ne guda kan haka.
Fargaba na d'aya shekara ta na neman kare mana acikin wannan gidan akwai Karin Dawainiya na kudin Haya,kudin makarantan yara,ga jamal da sai wannan shekaran zai gama ga abinci da Hidimdimun yau da kullum,har takai ga mun fara awon abinci saboda komai namu ya kare sai abunda ba'a rasa ba,da na rasa mafita sai na auno masara aka nika nayi Tsaki da gari yau tuwo gobe fate jibi dambu sannan na kira Goggo nace ta saka ayi min garin Danwake da Taliyan murji ,Hafsah zata zo satin karshe ta taho min da shi ban fito na gayamata muna cikin wani Hali sai dai hikimarsu ta manya yasa sai ta Fahimceni,sai tace ba sai na aiko Hafsah ba,Yaya Isa zai shigo katsina Ranar jumma'a zai taho min da shi
Da haka muka rabu saboda na lura komai in baka Tsara ba sai ka kwana aciki,a kwana a tashi na fara yi ma dan jarin nawa Rugu rugu ga masu siyan zobo da kunin aya sosai ammh kuma ba da yawa nake yin sa sosai yanzu ba,Nafi son ma a bani aikin Had'in Turaruka nafi samu sai dai shi zobo da kunin Aya sana'a ce ta cikin gida da zata tallafi Hidiman da bata gaza dubu goma zuwa kasa ba,duk yadda Yaya Ishaq nake ganin yana cikin Damuwa iya wanda na gani ne acikin Ransa bansan zafin da yake ji ba koda yaushe cikin fad'i yake yi"Kiyi hakuri Fa'iza na barki da wahala.Kiyi hakuri"
Ammh duk da haka ban barsa ya zauna bai je ya duba Zainab da yara ba,tun bayan tafiyarta yafi wata bai je ba ni na matsa mai sai kawai yace min"Kina ta matsamin naje naje..To ina naga ma na motan zuwa ko a kasa kike son na tafin..?
Sai na kallesa kafin nace" A bun bai kai haka ba,Ko ita ka fad'ama baka da na mota ai zata turo maka ka tafi din"
Wani kallo yayi min kafin yace"Sai na gayamata bata fiki sanin bani da shi ba ne..?
Ina jin ya harzuka sai na kama bakina ni kadai nayi kulla kulla na, na had'a cinikina na kwana Biyu, dubi biyar nabasa nace yayi na zuwa na dawowa bazai gagara ba,Ranar naga fad'a kamar zai dageni ya watsar da kudin yace na kwashe su bazai je ba, naki jin mganarsa na barsa masa su a tsakar daki na fice. ina jinsa yana fadin"Fa'iza ki dawo ki kwashe kudin ki nace,Haba matar nan so kike hakkin ki ya kamani.?gabad'aya kin Lullube rayuwata da alherin ki,so kike na mutu Allah ya sakani a wuta ko Fa'iza ai shikenan kin kyauta"
Ina jinsa sai da nayi dariya wai ina so ya mutu ne ya shiga wuta Allah na Tuba daga taimako ni bana so auran su ya samu matsala ne sannan na dandana rashin miji a kusa bana fatan itama ta dan'dana duk da rayuwata ba irin nata rayuwar ba ne, ita tana da gata gaba da baya ba irina bace da gatan kalilan ne.
Bansan ya akayi ba bayan kwana Biyu ya shirya yace zai tafin duk da bani da Tabbas nasan Mama ce zata matsa mai tana chan ne ammh na tabbata hankalinta na nan gani take yi yanzu tunda bata nan to sai a hankali,da ya tafi kwana goma yayi ya dawo. Sai dai yazo da kudad'e sun kai dubu hamsin yace Mahaifin zainab ya basa sannan ana ta dai kokarin neman aiki a ma'aikatu Dabam Dabam a bangaran da ya karanta wato na'ura mai kwakwalwa, ni ko a raina da fili sallata da zama na ina rokar masa Allah ya kawo masa aikin da zai amfanesa da kasa bakid'aya.
Da kudin da ya samo ya siya mana kayan abinci,duk da Goggo ta aiko mana har da shinkafa da Yaya Isa ya kawomin sakon nan kuma na bashi kudin yaki karba yace tace kada ya karbo na kirata ina ta godiya sai tace"Babu godiya tsakanin mu Fa'iza da ina da shi abunda yafi haka ma zan miki shi"na aminta da mganarta yanzu Goggo ba irin da ba ne mijinta Tuni yayi Ritire yana gida sai kudin Fashion yaran ne ke kula da komai harta kudin makaranta Hafsa sune ba abunda zamu ce da goggo sai godiya,Sauran kudin kuma ya ijiye amfaninsu zai iya zuwa kwanan nan sai yabi shawarana ya bar min kudin a hannuna na adana.
Tunda ya dawo na lura ya dawo da Dama daman da yake yi dani,Sai na fara shan jinin jikina,wani abun ma Saboda Badariya na gidan ne yasa yake ragamin,daya fara shigemin nake zaraf na shige dakin Mama ko na fito Tsakar gida na kirkiri aiki,haka kurum bana so mu kadaice saboda gudun kada ya ruguzamin shirina.
Da daddare kuma baya samun dama Saboda yara ina yi musu karatun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login