Showing 237001 words to 240000 words out of 288345 words

Chapter 80 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

729

cikin taushin murya mamakin kalamansa yasa na dago ina kallonsa kwarjinsa yasa na kasa mai gaddama sanda ya sake nuna min kujera yana fadin"Ga inda ya dace dake nan"
A kunyace na mike na zauna kamar zan yi kashi,saboda yanayin zaman nawa sai ya yi dariya kafin na ankara sai ganinsa nayi a gabana ya zauna har da tankwashe kafa baki na bude ina kallonsa da Sauri yace"To Rufe bakin mana kada ya makale a haka na shiga uku"
Mganarsa ta bani Dariya har sai da na kannen fuskata cikin Hijabi Saboda kunya shima yar Dariyan ya yi kafin kuma yadan ci Serious yace"Da farko dai ni sunana Abdulbasit Abdulghaffar Alowatosin.."
Da sauri na d'ago ina kallonsa in naji dakyau sunan yarbawa naji ya fad'a shi kan shi yasan yanayin kallon nawa kenan yasa yayi dariya kafin yace"Yes ni bayarbe ne mahaifina Haifaffan garin Beneu ne,mahaifiya ce Bahaus???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?hiya haifaffiyar garin kano ni ruwa Biyu ne Hausa_Yoruba"
Yafada kai tsaye bai kuma bani Damar mgana ba ya cigaba da fadin"Ni Engr ne ina aiki da matatan mai na Edo state,ni ba yaro ba ne ba Wasa ko bata Lokaci ko Doguwar mgana yasa nace ayi miki mgana ba. jiya ne da kika zo gaisheni na ganki to mganar gaskiya tun daga jiya zuwa yau baki bari zuciyata ta Huta ba Faa'izaa.."
Ya fad'a yana kallona nima abun mamaki shi nake kallo ina auna daman akwai yarbawa masu kyau haka..?Na san maza masu kyau da gayu tunda na zauna da Ishaq ammh sai naga kamar wannan na gabana ya hada wasu abubuwa masu tarin yawan da Ishaq bai da su.
Sai dai tunanani ya tsinke ne da nganarsa na karshe gabana ya fad'i kada dai shima jiya tunani ne ya kamasa kamar yadda ya kamani..?
Sai dai ganin yadda na bada Hankalina a kansa ne ina jin yadda yake kiran sunana na shiga duka sassan jikina FAA'IZAA..!
Gyara zama ya yi yana fadin"Kai tsaye ba tare da kwana kwana ko zagaye zagayen samarin zamani ba, na ganki kuma naji ina son ki Faa'iza kuma so irin na aure"
Ido na waro a firgice kafin nace"Ni..?
Sai ya gyadamin kai kafin yace"Yes..Ko ban kai ki soni ba ne..?nayi miki tsufa ko..?Shekarata arba"in da Biyar kiyi hakuri ban fara Furfura ba, a kai ne kuma bata wuce guda Biyar? ba? in baki so sai na aske su Faa'iza.."
Dariya ce take neman kamani sai na kanne na juyar da kaina ganin yadda ya marairaicemin a gabana cikin yanayin muryata nace"A'a ko d'aya ai kai ba tsoho ba ne"
Ajiyar rai yayi har ina jin saukanta kafin yace"To mene laifina ne..?ko so na ne kawai ba'ayi..?
Kai na girgiza kafin nace"Ba haka ba ne"
Da Sauri ya katse ni da fadin"To ya ya ne Faa"izaa..?
Yadda ya kiran sunana sai da tsikar jikina ya tashi kai na girgizamai kafin nayi mgana yayi saurin fadin"Bana son mgana da kai. Ina son ko da wani Lokaci na rika jin muryan ki mai Dadi"
Sai na saki hanci kawai ina jin abunda ban taba ji ba,ni daman ashe muryata na da dadi...?muryan da Yaya ishq yace yana jin haushi ina mgana ina rabeta kamar yar koyo.
Sai idanuwana suka ciko kwallah kaina na kasa nace"Ni ba ajinka ba ce kafi karfina bani da dukkan abunda mata masu kyau da wayewa suke da shi..ni bazawara ce"
"Ya'yan ki kuma hud'u ko..?
Yafad'a da sauri bayan katseni cikin mamaki na kallesa shi kuma cikin kwarin gwiwa yace"Nasan ke bazawara ce na kuma san muna da ya'ya yaushe kika shirya kaini na gan su? ko kuma ki bani lambobin su New papa din su zai kira su ya gaishe su"
Sai na kasa mgana kiris ya rage in yi kuka kai tsaye yace"Sai kuma me ma kika ce..?
Yauwa ke ba ajina ba ce sannan baki da abunda da mata masu kyau da wayewa suke da shi ko..?
Yafada cikin sigar tambaya sai na kasa bashi amsa yanayin Fuskarsa sai ta sauya cikin Sautin maza jarumai yace"Kafin na baki amsar ki meyasa kika yi min wannan mganar..?
A ransa yana tunanin meyasa suke da wannan tunanin Baban Nana ma ya fad'a masa
Ni ko kaina na kasa nace"Saboda mazan wannan mazanin basa auran mace in bata da abubuwan kamar kyau,nasaba,gata,karatun boko wayewa,in kuma suka samu akasin haka sai kuke
ganin kamar ba ku auri macen da ta dace da su ba kuma haka naga kuna yi shiyasa"
Katsaneni ya yi da fadin"Kika ga suna yi dai Fa'azza..!
Ni ba haka nake ba ni Abdulbasit kyan mace bai taba Damuna ba"
Wlh tallahi billahil azim in kyau nake nema ba a Nageria zan yi aure ba akwai kasashen larabawa,ina ne bamu shiga ba wasu matane bamu gani ba..?
Ammh ba wacce ta kwantamin arai sai ke Faa'iza ina sonki da zuciya d'aya ba domin wani abu naki ba ke din kawai nake so.."
Yafad'a yana bina da wani kallo kaina na kasa sai hawaye cikin Tagumi yace"Ya illahi ni Tosin saboda rashin so na har da kuka Faa'izaa..?
Sunan da ya fad'a yasa bansan sanda na kwashe da Dariya ba ina Tare bakina kallona yayi yana mirmishi kafin ya cire tagumin yana Fadin"Eh Alowatosin Yoruba name dina ne shine a gida su papa ke kirana Tosin in ba a bangaran aiki ba, achan Benue Da tosin suka sanni ammh yanzu a gabanki Abdulbasit ne"
Ina dariya nace"Ko dai Tosin..?
Sai kawai ya sake tagumi yana kallon bakina kafin yace"Tosin din FAA'IZAA ammh"
Dariya ta shakeni na fara tari da sauri ya mike ya isa frige din Abba ya Daukomin ruwa jiki na rawa ya budemin ya mikamin na karba na sha kadan na mika masa ya karba yana min Sannu sai da yaga tarin ya Tsaya sannan yace"Oh ni Tosin zan ma kaina Tsiya tun kafin na gama na kafa gwamnatina.."
Dariya naji ta kara kamani sai da ya sauke ruwan hannunsa sannan ya zauna yana fadin"Ni dai ki bar Dariyan nan ki fara ji da Tosin bawan Allah"
Ya fad'a kamar ya yi kuka ni yanayin yadda yake fadin Tosin din ne yasa Naji na kasa daina Dariya ai sai ya Hade rai yana Fadin"Kin san Allah? kika kara shakewa ko ruwa bazan miko miki ba"
Sai na natsu ina Sadda kai na kasa mgana sai dai ina ta mirmishi leken Fuskata yake yi yana Fadin"Cute"
Nasan ma'anar cute da Sauri nace"Nasan zagina ka yi"
Ido ya waro kafin yace"Ni tosin yaushe..?
Kai tsaye nace"kace cute ni nasan ba Cute ba ce..Nasan ni mummuna ce sannan ana yawan fad'amin ni mummuna ne"
Rai ya hade kafin yace"su waye..?
Gaskiya ba gaskiya suke fad'a ba..To ni dai koma menene haka naji kuma nagani"
Kai tsaye nace"Baka ce ni. ga shi ban da ilimin boko ban iya turanci ba"
Shima kai tsayen yace"Ni bakin ki ya yi min daidai ma,nima baki ga bakin ba ne, mu taru mu ta haihuwan ya'ya dunaye balakai."
Hausarsa ta saka dariya ta kamani bai damu ba ya cigaba da fadin"Mganar Turanci kuma ina ruwan Tosin. Ni ai ba da Turanci muke mgana ba sannan ni kaina in fad'a miki gaskiya ba Turancin nakeji ba, duk barazana ce wlh asaran kudin tara Papa ya yi gabadaya kaina nan a Duhu yake"
Yafad'a yana Buga kansa Dariyata har tana fitowa cikin dariyan nace"To ya akayi ka samu aiki..?
Kai tsaye yana mirmishi yace"To wannan kuma su Papa ne suka shiga suka fita ammh ban chanchanta ba"
Fuskarsa fa ba wasa ya cigaba da fadin"kinga kenan dukkan mu bamu iya ba an had'u da an dace kenan"
Ina Rufe bakina nace"Kuma ka zama megidan Abba..?
Da Sauri yace"ai na fada miki Papa ne ammh ina Tosin ina zaman Ogan Abban ki..?
Dariya ya yi shikan shi da mganarsa nasan yana yi ne saboda na amince masa ni ko dan barkwancinsa yasa na saki jikina da shi ban sani ba.
Dariya ya rika bani ni ko nama manta inda nake har ina kyakyatawa.
Ganin na shashantar da zencen yasa ya marairaice yana Fadin"Har yanzu dai Fa'iza bata ce tana Tosin ba..?
Fuskata na rufe kafin nace"Sai na fad'ama Abba"
Kai tsaye yace"Da izininsa ma na neni ganinki. Ba ruwan Abba a wannan mganar domin ya fadamin na nemi yarda a wajen ki tunda shari'a ta baki damar zaban miji a karo na biyu.
Faa'iza ni ma ba kowa ba ne mahaifina ma'aikacin gwammati ne nima haka muna zaune a garin Abuja tare da mahaifiyata da Sisters d'ina guda Biyu,sai granny kakarmu wacce ta haifi Papa,Shekaru takwas da suka wuce na taba aure sunan matata Tauhidat satin mu hudu da aure wutar gas ya kona ta Allah ya yimata rasuwa ,tun daga Lokacin ban kara mganar aure ba sai yau a kuma kan ki Faa'iza shiyasa na fada miki ni ba yaro ba ne kalleni nan bazawari ne ni ki bani dama bana son na bata Lokaci mu wuce wajen ina sonki nasan Sauran Fahintar junan zamu yi shi idan muka zama mata da miji"
Karfin Halinsa ke bani mamaki in yana mganar aure farawa da iyawa alokacin sam na manta da wani Ishaq,sai kawai nace masa zan yi Tunani kara marairaicewa yayi yana Fadin"Tunanin minti daya Faa'iza..?
Ina zaro ido nace"Aa nan da wata biyu"
Sai kawai ya gyara zama yana Fadin"Abba zai bani Masauki ko..?
Nayi dariya kafin nace"Da gaske nake yi"
Shima kai tsaye yace"Baki isa ba fa. Sai kuma chan yace Allaha sarki Tosin bawan Allah Fa'iza ki Tausayama Abdulbasit mana kin gani kano zani. ammh saboda ke na fasa sanda kika yi tunanin kika fad'amin Abdulbasit na amince ka zama miji na sai na tafi inda zani"
Ganin yadda ya zauna yasa nasan ba wasa a mganarsa da sauri nace"Kayi hakuri ka tafi bazai d'au Lokaci ba.
Shuru yayi kafin yace"To kwana daya Faa'izaa."
Zan yi mgana ya tareni da kallonsa Dskyar nace"Sati daya dai don Allah"
Kamar yana jira yace"Aa kwana Biyu Faa'iza bazan iya jiran Sati ba zaki kashe Tosin da Tunani fa"
Kina so in na mutu ki biya Diyya ne..?
Da Sauri na girgiza kai sai yayi Mirmishi kafin ya zaro wayarsa a Aljihu yana fadamin"Sakamin lamabarki anan Faa'iza"
Yanayin mganarsa yasa ban yi masa musu ba na karba na saka masa ya amsa ya kira da bai ji ringing din ba da Sauri nace"Tana Daki"
Sai ya gyada kai kafin yace"Ki rika barinta kusa dake. bana so na kiraki ban ji ki ba"
Ina kallomsa kafin nayi mgana yace"Abba ya fad'amin an haifeki da Hearing problem ni kuma nace Daidai kenan daman ai ni kadai ya Dace ki rika jin muryata sosai ko..?
Sai ya bani dariya na Lura in muka kai wani Lokaci cikina zai kulle.
Wayar? mikamin yana cemin na sakamai lambar ya'yan shi.
Cikin mamaki nace masa"Basu fa da waya. Yara ne babba ne Amir(Kabir)16yr yana Ss1 sai mai bi masa 14 Anum(Saudatu)tana Jss3 sai Mustapah dake jSs1 Ahmad ne karamin su yana primary 5 ne"cikin gansuwa yace"Masha Allah suna ina yanzu..?
Kai tsaye nace"Suna wajen Baban su a lagos"
Kai tsaye yace"Ana Daura mana aure zamu karbo su damu zasu zauna in sha Allahu"mamakinsa ya kamani kawai sai nace"In babansu ya baka ba..?
Yana kallon cikin idona yace"Zai bani mana nima ai ya'ya na ne"
Kamar wacce ta samu abunda ta jima tana nema haka na saki jiki da Engr muna Hira,na manta da kowa da komai sai da Nana khadija ta kawo abun kari naganta da shirin makaranta sannan na Duba agogo tara saura nayi salati ina sallalami shi kuma yana Dariya fadi yake"Kinsan Tosin akawai hira Abdulbasit ma ba baya ba"
Ina Dariya na fice ina ji yana kiran sunana naki dawowa dakina na koma na kwanta kan gado ina mirmishi ni kadai kamar wacce tayi gamo ina ji Ammi tana kirana nayi saurin Shigewa Tiolet na tube na fara wanka saboda Kamar zai tafi ne,aka kirani ai ko sai da yabar gidan na fito,nako ga tarin missedcall a wayata har da bakuwar lamba kuma nasan shi ne sai da naga na Zainab kusan guda biyar na Tuna da wayar mu ta dazu sai gabana ya amsa gabadaya jikina ya wani mutu kamar bani da Lakka.
Ga Engr ya yi min bake bake a zucci da baki,ko tunasa nayi sai nayi Dariya sai naji mirmishi ya kamani sannan ta wani bangaran ga mganar da na Fad'ama yara na.?
Gefen gado na koma na zauna ina jin Hajijiya ni Fa'iza ya zan yi..?
Engr ko Ishaq..?
Ko da ban ga Abba ba nasan bazai ki ba. sanin Darajan da Engr ke da shi a wajensa, Ammi daman sai tafi kowa murna ammh Ishaq fa..?ba shi kan? shi ba, saboda yara na.."
Tabbas ina cikin Tsaka mai wuya.




*Tosin..#*
*Ishaq..#*
*FAA'IZAA...#*


*Janafty*




[7/30, 7:00 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3012*


*Goron Tula*

*Ingantaccen maganine dake saukarda niimar mace sannan dadin dadawa fruit ne ga dadi abaki zakine dashi chakwai sannan bashi da wata illa yadda kikasan fruit haka yake*
*yana da matukar kyau da tasiri ga ma aurata daga mace harna mijin Kuma munada Syrup nasa da akataceshi sannan aka hada da ingantattun magunguna dasuke temakawa ma aurata kwarai don inganta lafiyarsu dakuma maganin matsalarsu ta auratayya yana saukar da niima sosai yana karawa mace dadi fiye dazatanku sai kingwada zak ibada labari insha Allah*

*Sannan akwai zumar kiba*
*Duk macen dake son ta murmure tayi kyau taciko tatada komad'a sosai shaf dinta yafito sosai da sosai to tasha wannan zumar insha Allah zaki gode min*

*Zumar gyara nono*
*Zasu yi kyau suciko ammanfa bawai su tsaya ba=?? zadai suciko suyi kyau sosai insha Allah*

*Zumar hips*
*Indai kinsha zumar nan to hips dinki zai bude zasu yi kyau suciko sosai zaki godemin nina fadamiki insha Allah*

*Note magungunan mu ingantattune basu da side effects kokad'an anyisu da ingantattun*
*magunguna sosai*
*Location Gombe munaturawa ko ina 08030861857*


*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*


Gabadaya sai naji yar natsuwar da na fara samu kamar an kwace min ita,jikina ya yi sanyi.
Gabbaina sun rusuna,ina kaunar yarana sannan zan iya yin komai saboda naga sun dauwama cikin farinciki sai dai ya zan yi da Engr..?wata zuciyar tace min Sannu Fa'iza riga mallam masallaci Daga had'uwa yau har kin fara tunanin ya zaki yi da shi..?
Sai kaina ya fara wani Dum! eh yau kawai muka na hadu da shi ammh ya yi nasara dawo min da natsuwan da tayi shekaru da kwacemin,sai dai kuma kamar natsuwar ta wucin gadi ce tunda yanzu tana neman ta kwace daga gangan jikina.
Kasa ma fita nayi gabadaya kunya da nauyi tare da sanyin jiki sun haifarmin da kasala ban karya ba ina jin cikina na kukan yunwa ammh Bakina bazai iya karban wani abinci ba.
? Ammi ce ta gaji da jiran fitowata ta Biyoni har dakina ta sameni kunsan dai Ammi ba ruwanta Turkeni take yi sai da na fad'amata yadda muka yi da Engr ai sai ta kama Hanci ta saki Guda kafin tace"Wlh kin yi miji Fa'iza ba domin Engr me kudi ba ne, nake fada miki haka ba,sai domin kyakyawan Hallayansa mutun ne nagari mai kima da sanin Darajan d'an adam ina miki albishir da cewa kin yi miji. mijin da acikin maza Dubu babu kamarsa kada ki tsaya wasa haske ne Allah ya kawo miki ki karbesa hannu Bibbiyu ki yi kuma addu'a muna zamu tayaki. muna nan dake watarana da bakin ki sai kin ce Engr mijin Nuna ma duniya da Tsara ne Fa'i"
Haka ta zauna tana karantomin Hallayar Engr tana kara fito da shi a idanuwana ni ko na kasa ce mata komai har ta fice daga Dakin na shiga wani yanayin da mata ire ire na suke shiga to ni me nake da shi da ya ganni yaji yana sona..?
Amsar da na kasa bama kaina kenan. Ranar ko inno ban je na gaisar ba sai da yammah abinci ma Ammi tayi bata nemeni ba ta barni nayi tunani Abba kuma ban yarda ma mun had'u ba kunyarsa nake ji.
Ammh fa Tunanin Engr bai bar zuciyata ba motsi kadan sai ya fadomin arai sai naji Farinciki ya kamani,ya kirani da rana lambarsa na gani na gane kunya da nauyi suka hanani Dauka sai ga Sakon shi.

"Bamu yi haka da ke ba Fa'iza,a sharadin ki ba bu rowar jin muryan ki mai dadi. Ki taimaka ma Bawan Allah Tosin yaji muryan Matarsa"

Sakon sa ya bani Dariya wai matarsa mutumin nan fa yana da karfin Hali,sai Dare ya kara kirana na Dauka ina Dauka ya sauke ajiyar rai yana Fadin"Har kin sa naji d'adi, zuciya ta tayi Sanyi"
Cikin alamun waka ya fad'a da bansan Lokacin da na kwashe da Dariya ba? Shima sai ya yi Dariyan kafin yace"Tosin din Fa'izaa ne ke mgana ina Fatan kin gane..?
Ina mirmishi nace"Na gane mana ammh ni ba Tosin dina ba ne"
Da Sauri yace"Naki ne mana. Wlh Tosin din nan naki ne Engr Abdulbasit ne na mutane"
Sai naji na kasa musa mai bakinsa ne ya Bude ya cigaba da min Hira yana Fad'amin yana kano gidan Granny din sa tun dazu ta hana shi tafiya zai kwana sai gobe zai wuce Edo yana da Meeting da rana.
Ayyah kawai na iya ce masa kawai sai ya karya wuya yana Fadin"Gaskiya Faa'izaa ba haka ake yi ba. Sai nayi ta kiran waya baki dauka ba. Sannan Dazu kin yi min laifi kika gudu bamu yi sallama ba"
Sai nima naji ban kyauta ba cikin yanayin mganata nace"Kayi hakuri"
Da sauri yace"An yafe miki. ai amarya bata laifi ko ta kashe dan masu gida"
Ni ko nace bata dai kashen ba ne shi kuma sai ya gyara murya yana Fadin"To ki bari ki zo zan jawo miki Taye da kahinde ki kashe su ki gani ai Godiya zan miki ma duk cikin so ne"
Ina mamakin sunayen da ya kira cikin sigar tambaya nace"Taye da kahinde..?
Sai ya yi mirmishi kafin yace"na manta ke baki iya yarenmu ba ko..?kamar kin koya kin gama in dai muna tare.
Taye and Kahinde Twins name ne da Yaroba,Sister na Twins ne ammh asalin sunayen su Kafayatu Abdulghaffar BIMFE,and Sharifatu Abdulghaffar ERIMIPE."
Cikin jinjina kai nace'Tab kowa sai an sakamai sunan yaren naku ne.?
Yana dariya yace"Sosai ke ma ai zan saka miki naki"
Ina rike bakina nace"Fada mu ji"
Sai yayi shuru kamar yana tunani kafin kuma yace"Naki wayan sai nazo,Gani ga ki sai na fad'a miki naki sunan"
Dariya nayi ina hasaso ni da sunan yarbawa wayaga diskindarid'i,hira muka cigaba da yi yawan hiran daman nasane na barkwanci da ban Dariya sai 11pm yace naje na kwanta zamu yi mgana da Safe,ni ina ma na san Dare ya yi haka kai Fa'iza kam na zake da yawa haka na kwana mafarkin Engr da Safe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login