Showing 258001 words to 261000 words out of 288345 words

Chapter 87 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

743

babu tursasawa ko takura da lalle sai ka auri yar'uwan ka bayarbiya.
Kuma hakan ya samo asali ne ga ilimin zamani da na addinin da ya lullube su kuma ko a garin Benue gindom din su na malamanta ne. shiyasa kaf zuru'an Abdulfattah a garin Benue ba wanda bai san su ba.
Daga cikin ya'yansa sai aka samu wanda ya yi gadon sa shine kakan Engr wanda ya haifi mahaifinsa Sheik Abdulbasit Abdulfattah Oluwatosin wanda sunan shine Engr ya ci, Ma'anar Oluwatosin da yarbanci shine God is worthy to be Saved,tunda su a al'adan su ko da an saka maka sunan yanka wannan al'adace za'a rika kiran ka da sunan ka da yaren su ko da na ranar da aka haifeka ne.
Mahaifin Engr, Mr AbdulGhaffar Abdulbasir Babatunde,shi kuma ma'anar Babatunde da yaren yarbanci shine The Father return,shi ne kusan manyan ya'yan Sheik Abdulfattah,yana da yayye maza da kanne mata,kusan dukkan su sunyi ilimin zamani da na addini matan suna Gidajen mazajen su suna aiki wasu kuma suna kasuwanci mazan kuma kowanne ya kai mataki mai girma na karatu kuma suna aikin gwammati. suna garuruwan da aiki ya ijiyesu duk da wasu har a yanzu suna garin Benue da zama su da iyalansu.
Hajiya Kudurat Olaminde,itace kad'ai matarsa da tayi masa takaba sauran matan sa guda biyu duk sun rigasa mutuwa kuma Hajiya Kudirat Abdulghaffar kad'ai ta haifa ya tsaya sai da ta binne tara reras a kasa suna rasuwa sannan shi ne na goma Allah ya raya mata shi,shiyasa ya samu dukkan gatan duniya da kowani d'a kan samu a wajen iyayensa.
Mr Abdulghaffar Abdulbasit a london ya hado Degree dinsa na farko kafin ya zo Usman dan fodiyo University Sokoto ya yi mastering Degree dinsa. ya zama Cadet na EFCC Officers tun wanchan Lokacin.
Ya fara aiki da EFCC a matsayin Assistance Detective superintendent(ADS) kafin jajircewan sa a aiki yasa ya samu karin girma zuwa Deputy cheif Detective superindent (DCDS),Mr Abdughaffar ya yi gwargwamaya sosai a aikin sa Saboda yana da ilimin matakin Kwalin Degree hudu garesa a mabambata kwasakwasai,Sannan kuma ya yi anragama da masu cin hanci da rashawa da masu d'iban kudin gwammati kama daga yan siyasa ma'aikatun gwammati dabam Dabam kuma ya yi nasara shiyasa tsawon shekaru Tara yana nan a matsayinsa na Chairman na EFCC gabadaya.
Mr Abdulghaffar da yaransa ke kiransa Papa yana da mata aure guda Daya Hajiya Shukra wacce ta kasance bahaushiya ce gaba da baya mazauniyar kano, kuma haifaffiyar kano din ce sun hadu ne a sokoto inda yaje degree dinsa na biyu itakuma taje hada Degree dinta na farko a kan Economis.
An yi soyayya kamar me,Itana ganin D'an mutan Beneu ta rude shima yana ganin asalin bakanuwa yaji duk duniya ba wata sai ita,kuma da yake yasan Family dinsa basu da matsala Sai ya saki jiki ta bangaranta ne aka so a samu matsala Tunda tun a baya mahaifiyarta Hajiya Tafeesu mafadaciya ce ta dinga fad'an yarta bazata auri yarbawa masu kashi a leda ba, sai da lokacin dangin mahaifinta da suka yi binciken gidan su Mr Abdulbasit suka kuma suka ga cancantan suka bashi auran Hajiya Shukra sai ga shi ko gidan da take ciki yanzu a kano shi ya gyara shi ya zuba mata ma'aikata sannan babu abunda ta nema ta rasa,sai gashi Hajiya Tafeesu tafi kowa jin dadin Yaron yarbawa masu kashi a leda, a cewarta ko banufe ne in dai nagari yazo zata bashi aure ta fahimci a kowani yare akwai na banza kuma akwai na kirki.
Sun yi aure lokacin Hajiya Shukra ta gama karatunta a Benue suka fara zama tare da mahaifiyarsa Hajiya Kudurat,dalilin haka yasa ita bata cigaba ba,Saboda aikin mijinta ba na zama waje daya ba ne.
Suna zaune lafiya cikin soyayya da kaunar juna ba su da matsalan komai,matsalan su ma farko shine sai da Hajiya Shukra ta shekara biyar da aure sannan ta haifo d'anta namiji mai kama da mahaifinsa sai dai ya Dauko hasken mahaifiyarsa.
Bayan haihuwan Abdulbasit da yaci sunan kakansa Suna kiransa Oluwatosin sai da hajiya shukra ta shekara ashirin bata yi ko batan wata ba har sun fidda rai da kara haihuwa Allah mai kyauta da kari ya kawo Rabon Cikin yan biyu,cikin da ya wahalar da ita kamar bazatayi rai ba aiki akayi mata a wani asibiti dake India sannan aka ciro mata santalan santalan ya'yanta guda Biyu.
Wadanda suka ci sunan Kafayatu da Sharifatu.
To a yaren su yan biyu ana musu lakabi da Taye da kahinde bayan kuma haka suna da yarouba name din su,Bimpe da Erimipe,koda suka taso sun iske su Abdulbasit ya riga ya girma ammh duk da haka akwai shakuwa mai girma a tsakanin su sannan iyayensu sun yi kokarin basu Tarbiya,in ka gansu bazaka taba cewa sun sirka da wani yare ba sai dai ta Harshen su,kuma sai ma sun juya harshen ake ganewa.
Gwara ma su kayafatu ana gane suna da jini da yarbawa saboda suna yawan zuwa Beneu hutu da kuma sanin kan wasu al'adunsu nasu kamar yanayin Shigar su da sauran su. sabanin Engr da makaranta kwana ya yi sannan shima University of Ibadan ya yi Degree dinsa na farko sannan ya tafi London shima ya hado Degree dinsa na biyu akan Chemical Engineraring, bayan haka ya hallaci manyan manyan kwasa kwasai a kashashe ketare akan abunda ya karanta ya fara da aiki kamfanin Narka karfe a garin Lagos na shekara Hudu kafin wani Uncle dinsa Uncle Tobi ya sama masa aiki a Edo Refinary and petrochemical Limited na karkashin Jahar Edo_Ekiti.
Engr mutum ne na gari mai dattako da sanin ya kamata, duk wanda ya zauna da shi ko na kwana Daya sai ya tafi da Labarin karamcinsa.
Yana da barkwanci da Dad'in zama Mutum ne da yasan abunda yake yi,Ta dalilin Hajiya Shukra da ya ke kira Sweetheart su kuma su kafayatu suna kiranta Mah,ita kuma Hajiya Kudurit Granny ya san Engr Usman karaye saboda suna makota a gidan su dake kano, Dalilin haka har yasan abunda ya karanta ya kuma karbi Takardunsa ya nema masa aiki a NNPC dake kaduna da kuma matsayi mai girma kafin Abba ma ya nema ma mutane aiki da suka zama wani abu sun fi Dubu,haka ma bayan Haka kowa aka kira sunansa sai dai kaji ana fadin nagartansa da irin kyawawan Hallayansa,sannan in ba shi ya fad'i cewa shi ba bahaushe ba ne, yaroba ne,ba mai ganewa ko kuma in anji? karshen sunansa tunda tun yana karami har girmansa bai cire Oluwatosin a sunansa ba,yace a san mutum asan Dabi'arsa da Rayuwarsa da inda ya fito ya fi asan ka batare da an san ko waye kai ba.
Engr ya je kasashen ketaren da baza su kirgu ba,tunda aiki na yawan Fitar da su waje to karshen wayewa yana da shi,sai dai mata basa gabansa ko a cikin Danginsa akwai masu son shi ammh baya maida kai.
A chan family din su kowa da Tosin yake kiransa Papa kuma yace Oluwatosin,Maa tace Babatunde Saboda sunan surukinta ne kannensa kuma suna kiransa Brother Tosin,a wajen aiki da mu'amalansa da mutane kuma Engr Abdulbasit ne,yana da kyakyawan shaida wajen mutane da wad'anda suka san shi daman wad'anda basu san shi ba.
Engr mata basa gabansa ya jima bai yi aure ba, sai da ya shekara talatin da Tara har kannen sa su kafayatu sun shiga jami'ar Abuja,Maa ce ta ke damuwa shi Papa ba ruwansa Oluwatosin kamar abokinsa yake haka zasu zauna su yi ta hira ba ruwan shi haka da Uncle's dinsa kamar wani kanninsu haka zasu riga hira suna Dariya shi mutum ne mai Sakewa mai al'amarinsa ba kumbiya kumbiya mutum ne simple,ba kowani Lokaci ake iya ganin Rauninsa ba. yana dakiya da juriya mai naci kan abunda ya sakama gaba mai kyauta da Alheri.
Sister's dinsa kuwa in kaji suna Brorhers Tosin kaza kaza,ya riga ya nuna musi bayan yaya shi din dan'uwan su ne da basu da kamar shi? kamar wani kaninsu haka yake shigewa cikin su ana hira har da Shewa Maa ita bata da Hayaniya sosai ammh fa duk abunta in Tosin na gida sai ta saki jiki an sha hira sai dai bata yin irin yadda Papa ke yi ki ga har suna tafawa da Tosin ko suna mgana ta kunne ko su hada kafada ga shi tsawon su d'aya sai dai shi Tosin har yafi Papa budewa na jaruman maza.
Abdulbasit Abdulghaffar Oluwatosin Dogon namiji ne ingarma kalarsa kalan Chaculate ne kalan yan maroco ne,sannan yana da karan hancin Paapa,kuma ya Dauko Doguwar Fuskar Maa,sai idanuwansa masu girma kamar na mace,yana da bakinsa mai Fadi kadan sai ya tsuke yayi Tudu kamar na mata,hakoransa masu haske da walwali yana da cikar gashin ido da na gira ba ma'abocin tara suma ba ne shiyasa duk sati sai ya yi aski,Mutum mai Fara'a da mirmishi cikin kowani Hali wannan mirmishin baya Bacewa daga Fuskar Engr.
Matarsa Tauhidat da ya aura ta rasu Diyar yayan Papa ne Abdulwasiyu,Hajiya Kudirat ta matsa sai da akayi auran asali ita ke son shi Tana zuwa Hutun gidan su na Abuja kawar su Kafayace,shi kuma baya sonta ammh Yanayin yadda granny ta rikice ne kuna ga shi Lokacin an gano tana da matslan koda,saboda ya faranta mata yasa ya amince ashe auran ba mai dadewa ba ne,A chan Benue duka aka yi shagalin bikin su daganan suka wuce Edo gidansa dake chan duka duka Sati uku ne yana wajen aiki ta kunna gas ya tashi da ita duka gidan ya kone ko Tsinke ba'a Fitar ba gawarta ma duk ta kone sai k'ashii.
Bazai ce bai shiga damuwa ba. tunda Tauhida na son shi,shi kuma mutum ne daya san Darajan dan adam barin ma mace,sai yake biye mata kuma dai bai yi wasa ba ya haikemusu yar yarinya yana ma tsaka da moran auren ne ta rasu to shiyasa ya shiga Damuwa kuma dalilin haka ne aure ya fita ransa,Lokacin da za'a cire ma hajiya Kudirat koda a yi mata dashen na siya da akayi har rigima ta tada akan sai Tosin yayi aure yako ce gaskiya sai dai in yanzu zata karisa mutuwa ammh matukar ko aurensa take jira ba yanzu ba,Dole ta shafamai Lafiya.
Lokacin da yaje ma da Maa da papa da mganar Fa'iza duka fatan alheri suka yi masa suna jin dadin Tosin zai kara wani auren,basu zata abun zai zama cikin gaggawa ba shiyasa achan Benue ba wanda yaji sai labarin auran sukaji Daga sama Dayake mutane ne masu Fahinta paapa na musu bayani suka gane sukace in za'a tare nan benue zai kawota ayi shagalin al'ada.
Farinciki ya cika su kayafatu Shiyasa suka amshi lambar Fa'iza suna kiranta Domin duk abunda Brother Tosin yake so suma a wajen su abun so ne da Girmamashi.
Gidan Papa dankarare ne yana nan a Gwarinpa,Shi ma kuma Engr yana da Dankareren gidan a Apo dake garin Abuja sannan yana da wani Edo bayan gobara ya bata wanchan sai ya Saida ya siya wani a anguwan Benin City,a garin Benue ma suna da gida inda suke sauka inda sun zo kato mai bangarori da dama. kaf ahalin su ba alfahari ba,babu talaka suna da kudi suna da ilimi sannan suna kasuwanci.
Suna kuma da kowani yare acikin su ba kyama da tamgwama,har balarabiya Kanin papa ya auro daga sudan,wani kawun su ma na auran baturiya,acikin yaran su matasa irin su Tosin akwai wanda ya auro Bafullatana acikin Ruggar jigawa. shiyasa nace suna da hausawan suna kuma da turawa da larabawa da kuma Yarbawan, shiyasa basa ka ma da ya'yan su sun fita daman kamar ba su hada jini da yarbawa ba.
Ammh ba su bar gida ba,yara da manya sun yi kokarin koya musu yaren su saboda duk inda suka shiga a gane su ko ba ta kammani ba.

*******
Na dauka yara na za su yi rigima ko kuma zasu raunana kamar yadda na zata a farko sai dai kuma Alhamdulillah da sukaji bazan dawo ba basu yi rigima ba,Ahmad ne kadai yayi kuka shima din Amir da Anum sun lallashe sa,Hatta Anum bata yi kuka ba inaga Amir me ya yi mata mgana da suka kirani ta wayar Jamal Anum kamar Babba sai ce min tayi"Umma Yaya Amir yace sabon Babanmu shima mai kirki ne yace zai rika kawo ki kina ganin mu, muma zamu rika zuwa muna ganin ki"
Mirmishi kawai nayi cikin jin dadi kafin nace"In sha Allahu. Anum ki kula da kanki sannan ki kula da sauran kannen ki Karatun Qur'ani da azkar salla akan Lokaci Anum ban da rashin,jin mgana komai Antyn ku ta sakaki kiyi kin ji ko..?
Ta amsa min da Toh Umma sannan muka rabu sai hankalina ya kwanta,da jin yarana suna lafiya,Sai dai ance shi Ishaq din bashi da lafiya har da su kwanciya a gadon asibiti,
Abakin yaran na fara ji sannan da muka yi waya da Badariya take kara fada'min jiki yaki dadi.
Likitoci sun ce jininsa ne ya hau da kuma Damuwa a raina nace"Dakyau! Shi sai yanzu ya samu nashi hawan jini..?kafin shi ni ya fara sakama hawan jinin"

Ban fad'a a fili ba saboda ina jin nauyin Badariya har ga Allah ban ji tausayin shi ba,Itama matsaloli duk sun sha mata kai uwar mijin ta kara matsa lamba tunda bata samu ciki ba,tana mganar sai Yusuf ya kara aure,Kullum Badariya ta kirani ko tana kuka ko tana cikin damuwa,Ni ce ma ke tausanta da Hakuri tunda mijinta na sonta kuma yana kaunarta kawai matsalan uwarsa ne da matarsa.
Ni dai ba ni da matsalan komai a rayuwata ko da yaushe muna makale? a waya ni da Engr mun kara wata irin shakuwa kamar mun shekara da Haduwa,tunda yace kada na sake yin wani abu ban kara ba iyaka dai ina Taya Goggo dafa zobo tunda ita na barma sana'an tun tafiyata Kaduna,Aikin Dambun nama su jummala na barmawa ko an kawo sai dai nace akai musu hatta da Hadin Turaruka sai dai in An matsamin ni zan yi tuni na samu Hutu nayi kiba nayi haske kamar bani ba.
Ina cin mai kyau ina shan mai kyau,kuma ina shafa mai kyau tunda ni da kaina nayi ma kaina fada ina Shafa mayuka masu tsada saboda gyaran jiki.
mun yi mgana da shi na kayan lefe yace in ya dawo kudin kawai zai bani na siya abunda nake so mganar gida kuma a Abuja zamu zauna bayan mun Dawo daga benue sannan yana Tashi komawa wajen aiki Edo state kafarsa kafata ln nace to tosin ranka ya Dade sai shi kuma yace yauwa yar matata Bolawatifenisola(Tife) sunan da ya samu kenan da yarbanci ni sai dai nayi ta dariya na ma saba har amsawa ma nake domin daya kirani ina Dauka zai ce"yar matata Tife kina lafiya..?
Sai nayi mirmishi in ce"Ina lafiya mijina Tosin"
Rayuwa muke gudanwar cikin aminta da juna ba gundura ba kosawa,Sannan in nayi abu baya so kai tsaye zai ce min"Gaskiya Faa'izaa ba na son abu kaza..kaza nake so"
Shi dan Afadi mgana ce ko yaya zaka Dauka shikenan shidai ya fad'amaka iya gaskiyansa,Mutum ne free da bai da kwana kwana acikin lamarinsa kuma in ya fad'i mgana hakan take daga karkashin zuciyarsa.
Labarin aure na da Engr har ya kai kunnen Hajiyar Dala ba kira tayi ba har Karofi tazo,ta same mu ni da Goggo tana ta kananun mganganu tun suna daki ita da goggo da ta fito zata tafi ina falo ina yanken kumba ta kalleni sama da kasa kafin tace"Yanzu ke Faa'iza ki ka k'i dan'uwanki. saboda Bayarbe ko..?
Mganarta tamin ciwo sai dai ban tanka ba kuma kaina na kasa ban dago ba sai ta tabe baki kafin tace"Ko da yake an ce yana da kudi masu gidan rana baza'a damu da Yarensa ba. Ammh wannan abun kam ba tsari ki ki' bahaushe dan'uwan ki ki auri bayarbe asalin yarbawan ma na garin Benue"
Na kasa juran wannan cin zarafin nata Goggo ce ke fadin"Fatan alheri zaki yi mata kuma kada ki manta wani baya auran matar wani"
Kamar an goggo ta watsa mata ruwan zafi haka ta yarfa hannu tana fadin"Wannan karatun ki ne .Ammh ni ba kudi ba ko duniya ya tara in dai bayarbe ne bazan bashi auran y'ta ba.? ai gwara banufe da bayarbe."
Dagowa nayi ina kallon Hajiyar Dala kafin nace"Shi Bayarben ba musulmi ba ne..?
Na fada idanuwana suna kallon nata kawai sai tace"Musuluncin su bai cika cika Daidai ba.
sunan dai suna musulmai ne"
Nima yadda bataji kunyar gayamin mgana ba nima ban ji ba sai kawai na mike ina fad'in"Kamar yadda a muma Hausawan ana samun b'ata garin addinin musulunci da wad'anda basu cika daidai ba da kuma wadanda suka cika shi daidai suma kamar hakane,Daya muke da su bamu da bambamci musulmai ne su kamar yadda muke musulmai masu imani kuma shi Addinin Ubangiji ba ruwansa da bambamcin yare duk Daya muke a wajensa bai bambamta ba sai wanda yafi jin tsoronsa, ya fi so kuma ban ga Nafsin ko aya da Hadisin da yace kada mu auri wani yare sai namu ba.
In kuma da Aya ko hadisin da ya Haramta aurena da Engr ki fada'min Goggo kila su Abba sun samu makuwa ammh yanzu in kika Tunasar damu sai kila mu gyara kuskuran mu?
Daga ita har Goggon sun yi mamakin kalamai na ita ko kasa mgana tayi saboda bata da abun cewar ganin haka yasa na kakkabe jikina na wuce daki ai sai ta fara tafa hannu tana fadin"Kina gani ko..?ni yarinyar nan zata yi ma rashin kunyar don na fadi gaskiyata.?
Ni dai naji Goggo da ke biye mata tana bata hakuri ko kara sauraran su ban yi ba araina nace ai na bar kara???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yin shuru a rika raina min wayau ana Dannen min hakki shi bahaushen da na aura dan'uwan nawa me ya tsinanimin..?ban da bakin ciki da takaici, Allah na tuba da wani Bahaushen ai gwara wasu yaren sun fi sanin Darajan mata da sanin amfanin su.
Ba irin wasu mazan mu na Hausawa ba. da suka maida mata jakuna ababen biyan bukata masu cikin haihuwa,da wahalhalun duniya Allah dai ya sa mu dace a kowani yare akwai nagari akwai na banza sai fatan mu dace da had'uwa da na garin.

*****

Ba iya ni kadai ba hatta Abba,Engr ya fad'amasa da zarar ya dawo zan tare sai Abba ya kirani a waya akan nazo yana son mgana dani,daman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login