Showing 114001 words to 117000 words out of 288345 words

Chapter 39 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

725

da yara ballatana yanzu da na haifa nasan zafin su,Ni nake Dawainiya da yaran manyan da zasu iya cin abinci da kansu suci wadanda baza su iya ba na zaunar da su na basu,Zuwa Dare gidan ya watse sai na jiki jiki bayan sallar isha'i mahaifin Zainab ya iso daga chan inda ya kama yana Hutawa shima a falo aka taru har da ni ina chan gefe? fadil na Hannun kakansa yaran kuma suna jikin Baban su.
Mgana yake akan gobe zai koma Abuja Mama da su Anty Binta suna ta mai godiya ya kada kai yana fadin"Bakomai Ishaq kamar Zeey na Dauke sa shima D'ana ne,Ina so na shaida masa kuma ku zama shaida,Na basu gidana na Abuja su zauna da Zeey Saboda bazata iya zaman wani waje ba in ba Abuja ba,nan ta saba sannan yaran nan sun fara rayuwarsu achan bazau yuyu a sauya musu muhalli ba sannan ta na aiki,Sannan kada ya damu nauyin komai ni zan Dauka kafin ya samu wani aiki zamu iya bakin kokarin mu bazai gagara ba In sha Allahu"
Mama ta hau godiya har da Hawaye shi ko Yaya Ishaq mama ya kallah kafin ya kalli mahaifin zainab yace"Daddy ban ki mganarka ba,ba kuma don na raina kyautatawarka a kaina ba, sai don yanzu ba da ba ne.In a baya aiki ya kaini Abuja yanzu fa..?Ina ganin zamana a Abuja yanzu bamai yuyu ba ne"
Kai tsaye batare da Damuwa ba yace"Why da bazai yuyu ba Ishaq..?ai auran soyayya kuka yi da Zeey, kai ka ganta kace kana sonta itama ta amince dakai na aura mata kai,kuma kai ka zabeta na tabbata zaka bita a duk inda take ballatana ma wannan ba abun damuwa ba ne kada kaji komai aikan ka ya kusa dawowa ko ba wannan ba wani zai samu kaji ko..?
Zai sake mgana Mama ta Dake masa Hannu da kafarta ina lura da su ya Dago yana kallonta yana so yayi mgana ta hanasa har ga Allah sai da naku sa yin Dariya.
Mama ta juya tana fadin'"Kai Alhaji mungode sosai Allah ya bar zumunci shirmen sa kawai yake yi me zai hana ya bita chan in ya zauna anan me zai yi..?mungode sosai Zainab ki tayamu godiya fa"
Tana mirmishi tace"Bakomai Mama"
Niko ina gefe araina nace wai me mata da iyalai ne ake cewa in ya zauna anan me zai yi..?ayi dai mu gani in tusa zata Hura wuta.
Bai wani jima ba yayi ma su mama sallama da cewa gobe zai je kano ya bi jirgi zuwa Abuja.Yaya ishaq da zainab din suka fita rakasa jikokinsa na Hannunsa,ya dade yana Tattaunawa da yarsa kafin ta Dawo cikin gida har ga Allah naso mu koma gida sai naga ko shi kan shi Gogan bai yi mgana ba, kada nazo nayi mgana cibi ya zama kari sai nayi shuru da bakina ammh har ga Allah ina cikin Takura.
Sai da muka shafe kwana Hudu a gidan mama yayi mganar komawar mu Gida Mama tace mutane na zuwa Jaje da murna ya zauna,Zainab kuma aranar Direba yazo ya Dauketa ita da ya'yanta ta koma Abuja saboda aiki a gabana a gaban su Mama tace ma Yaya Ishaq yaushe zai zo..?ina kallonsa ya gimtse fuska kafin yace bai sani ba sai ta wuce tana fadin zasu yo mgana ta waya Mama har bakin mota ta rakata kamar zata goyata saboda kauna.
Mu kuwa sai da mukayi kwana Biyar naga zaman dai yaki ya kare na Tattara yara na nace zan koma gida,Sai yace mu tafi shi sai anjuma da Daddare jamal zai rakosa zasu karisawa Tattauna mganar da suka fara da Mama,naji dadi da bai hanani ba sannan itama Maman yan mutumcin na kusa batace komai ba ko da yake mai zugatan bata kusa Anty Binta kenan.
Ina komawa gida duk yayi kura na zage na gyara ko'ina Amir na tayani shida Anum saboda na koya ma yara na aiyukan da basu da wahala saboda gaba,bayan mun gama muka yi sallar la'asar sannan na Dora girki Sa'adatu da Habiba sun shigomin daman sun je har chan gidan Maman sun min barka da arziki da su mukayi ta Hira sai yammah suka tafi,girki daman farar shinkafa ne Amir ke dubamin ya iya hae dafa indomie da, taliya kadan bamai yawa ba,Da miya nayi mana ina da komai na kayan cefane na saboda tunda na fara samun gumina na daina jiran ayi min komai,tsaye nake? a kaina kuma na tsaya akan ya'yana, ko yanzu din ma nace su kimtsa gobe sai makaranta fashin ya isa haka duk da sun koma karatun zango na farko akwai Laluran biyan kudin makaranta ga kuma abubuwa duk sun Chude ni dai na gama lissafina ko zan yini ina aikin sana'ata ne bazan gaji ba,Saboda ina so yarana su samu Ilimi bana fatan su rasa damar su kamar yadda na sara.
Ina da Aiki da yawa na Hada Turaran wuta da Humra,sannan akwai masu Dilka wasu har kudin su sun turomin rashin natsuwa ne yasa ban ce musu komai ba sannan ga yan sarin Zobo da kunin Aya suna jirana,So nake sai hankula sun kwanta na Dawo da sana'ata kafin komai ya daidaita naga kuma inda Rayuwata zata kara Cillamu tunda sun bamu Notice nan da wasu kwanaki zamu tashi ashe da gaske zan tashi daga wannan Muhallin sai dai ba irin wanda na Kudiri niyya ba.
Yaya Ishaq bai dawo ba sai washegari da Daddare muna zaune da yaran suna duba aikin da aka basu a makaranta,Ni kuma ina ta lissafin kudaden mutanen dake kaina acikin wani Littafi inda ban gane ba na Kira Amir ya dubamun suka shigo shi da Jamal,ya rakosa yaran suka mike suna Ihun ga Daada nima mikewa nayi ina musu maraba dukkansu nan falon suka yada Zango na shiga kitchen na kawo musu ruwa muka gaisa da Jamal shima na gaishesa ya amsa hankalinsa na wajen yaran.
Jamal nayi ma mganar abinci yace sun ci abinci a gidan Mama sai dai ko In Yaya ishaq zai ci shi kuma sai yace sai dai zuwa anjuma, jamal bai Dade ba yayi mana sallama shi kuma ya nufi bangaransa yaran suka bisa yanzu har Ahmad ya Daina barci da wuri.
Ni yaran suka bari da tattara musu littafan da suka watsar na kai musu Dakin su na adana musu nima na shige dakina, ina cigaba da lissafin abubuwa bani da wasu kayan Hadin sai na siyo sannan Kudina na Hannun Hafsah nake bama ajiya basa Hannuna.
Ina so na kirata sai na Duburce na rasa ta inda zan latsa na nemo lambarta,Daman sun koyamin ba duka na iya komai a wayar ba,Sai na mike na leka shashen shi na gansu a falo suna da Budirin su na kira Amir sai dai ban ga baban nasu ba,Anum tace ya shiga wanka Amir na ba ma wayar shi ya nemo min Lambar Hafsah ya kiramin nayi mgana da ita tace min tunda na dawo gida gobe zata dawo nace yauwa gwara ta dawo din.
Ina cikin Gyaran gado na Anum ta shigo da gudu tana fadin"Umma Daada yace ki hado masa Tea"
Sai na amsa mata da Toh sai da na gama gyara gado sannan na fita na Dora ruwan zafi na saka mai citta da kanunfari,da Top tea suka Dahu tare na tace sannan na juye mai cikin karamin Fulas din da na siya,Tunda na siya sabbin kayan aikin Kitchen,su dai da suke nawa Tsoffin na Sadakar ne ammh na falo kam suna cikin wani Daki dake haraba kwashewa kawai nayi na sauya sabbi,nasan Halin sa tsab in yaji tijaransa zai ce ina kayansa Tunda shi ya saka komai na gidan kafin mu dawo.
Da kaina na shiga na kai mai yaran dai ke ta duduma afalon shi bai fito ba na sauke mai saman Karamin Center table din dake falon na kalle su ina fadin"Dare yayi aje a kwanta gobe akwai makaranta"
Anum sai ta dira baki tana fadin"Umma mu wajen Daada zamu kwana."sai na rike baki kafin nace"Da wajen Daadan kika saba kwana..?zaki wuce ko sai na mangareki"
Nayi kamar zan kai mata Hannu sai ta goce ba zato kawai naji tace"To Umma Anty in tazo tana kwana anan ke ko baki taba kwana a dakin Daada ba.."
Ta fada daidai Lokacin da ya fito daga cikin Daki yana sanye da jallabiya yaji kuma abunda tace ni ma mamakinta ya sandar dani na shiga tafa hannu Cikin mamaki ya kalleni nima na kallesa sai kawai na kauda kai na sukunci Ahmad da ya barci ina Fadin"Sai da safe..Amir riko Musty kuje ku kwanta"
Daga haka na fice sum sum suka bi bayana Mazan na fara kula har suka kwanta sannan na dawo Daki mamakin Anum ya gama kamani na tashe ta tayi fitsari sannan ta koma ta kwanta araina nace yara ma kada a raina su,su na ankare da motsin kowa Allah mai iko har nayi barci da Tunanin Anum a raina.
Haka muka cigaba da gungura rayuwar mu,Yaya Ishaq sai zaman gida ba inda yake zuwa sai ya bani tausayi magidanci ne fa da ya saba fita aiki da Zirga zirga yanzu ya Dawo sai dai ya kwanta in ya gaji ya zauna,Mutane na zuwa masa jaje cikin mutanen Mama,ko jamal yazo su wuni yana tayasa Hira,Hafsat ta dawo ita na Tura ta shiga kasuwa ta siyo min kayan da bani da shi na kunin Aya da zobo sai na Hada Turaruka ina da nayin Dilka na Halawa ne ta siyomin.
Yaya Ishaq na da sati biyu da Dawowa na Fara sana'ata,yana shashensa bai fito ba sai dai komai ina yi masa,fita ko sai dai yaje gidan mama da daddare ya Dawo,tun Safe da na tashi ban koma ba ranar sau biyu nayi zobo Safe da Yammah Saboda yan sari ko da ya fito da yammah ya ganni ina ta Jera Robobin a katon Frezer na bai min mgana ba,nima ban yi masa ba yadai ce zai shiga gidan mama nace a dawo lafiya.
Ina matukar Tausayamai Saboda akwai Tausayi ga wanda ya samu karayan arziki da kuma rasa aiki,Tunanin inda zamu koma nake yi, saboda ina lissafin saura Kwana goma Wa'adin da suka bamu ya cika yadda bai min mgana ba nima na zura masa ido ranar da yadawo yake fadamin abokan aikinsa daga Abuja zasu zo su yi mai Jaje akawai abincin da zan iya Dafa musu? nace muna da Cefane sai ya kalleni cikin mamaki kafin yace"Wa yayi muku cefanan..?
Kai tsaye nace"ni mana"
Cikin karin mamaki yace"ina kika samu kudi..?
Ina Yar dariya nace"Baka ga ina sana'a ba ne..?
Sai kuma yayi shuru bai kara mgana ba,washegari suka zo sun kai su goma
Hafsah bata shiga makaranta ba ranar ita ta tayani muka yi musu abinci mai rai da lafiya na hada musu da Kunin Aya da zobo na da ke saidawa.
Suka ci suna ta santi,Daganan gidan Mama ya kaisu sai dare ya Dawo,kwana uku tsakani yace min Mama ta kirasa kan mganar gida zai je yaji,da zai tafi na basa dubu daya nace yayi na adaidata sai yaki karba wai yana dashi ni nasan bashi da shi,bazai karba ba ne sai na kyalesa na cigaba da Harkan gabana.
Daya dawo daddare karo na farko Tun aure na da shi ya taba zama ya yi shawara dani,sai ranar wai mama nata saida kayan gidanta na wuta da kayan katako tana so ta had'a kudin gida ne muma tace abunda zamu Dauka mu fara hade su waje daya Sauran sai a saida su.
Ni ko sai naga kamar tsarin bai yi ba na kallesa nace"Ni ko da zaka bada shawaran da kudin da za'a siya gidan da zamu zauna me zai hana mu kama Haya na shekara daya..?kada ka manta akwai Hidima fa gata abinci gata yau da kullum ga na Makaranta da Dawaniyar yara ga Jamal yanzu yake aji Hudu Badariya wannan Shekaran zata gama ga Laluran Mama duka suna kanka ne shine naga sauran kudin in aka kama Haya sai a toshe wasu ramukan da su ko ya kagani..?
Sai yayi shuru yana kallona kafin yace"Kuma fa Hakane Fa'iza ni sam ban yi wannan tunanin ba"
Har acikin raina ni na fadi ra'ayina ne ban dauka zai ji mgana ba ta sai ga shi har su Maman da ya kawo mganar sai suka aminta,Mun fara shiryen shiryen tashi,na hada kayan da zamu Dauka wadanda kuma za'a saida aka fitar har da Tsoffin wad'anda na fitar duk aka saida su gabad'aya.
kayan bangaransa yace a saida su duka,Katifa kadai yace za'a bar masa ta ishesa ni dai na ware gadona da na yara sai kujeruna sai kayan sana'ata da kayan amfanina na Kitchen, sauran kuma aka kira Dilallai suka yi musu kudi hakama gidan Mama kusan rabin kayan duk sai da su akayi abun akwai tausayi sosai
Yan'uwa ma sun mana kokari Goggo ashe bata zauna ba ta saka ya'yanta suka hada kudi Dubu dari ta kawo tace a kara ita Hajiyar Dalan ma ba wanda ya kara jinta Ina gani Yaya Ishaq nata sunne kai kunya duk ta kamasa.
Da kudin da Anty Binta ta hada da wanda mijinta ya taimaka harta Dangin mama suma sun taimaka aka Hada Miliyan Daya da rabi da su,aka samu gida acikin gari sai kuma Allah ya saukaka mana abun kusa da makarantan yara ne, ko ba abun hawa zasu taka da Kafarsu,Gida ne flat na daidai misali,Shashen Farko falo da Bedroom guda uku sai Kichen sannan kowani Daki akwai tiolet sai dayan Shashen Bedroom biyu da falo ba kitchen sai tsakar gida sai daga wajen Koridon kofar waje akwai wani Daki sai akace Jamal zai zauna anan.
Tun kwana Biyu kafin Wa'adin ya cika kayan mu suka fara yin gaba mu zamu zauna a mai Dakuna uku, mama kuma da Badariya zasu zauna a dayan Shashen,Allah sarki Rayuwa Daman KANA NAKA ne shima Allah ya riga ya gamasa nasa,ranar da zamu tashi yara nata murna zamu tashi,har gwara Amir shi ya fi so wayau.
Ni kaina sai da nayi hawaye inda ka saba da kewar yanayin rayuwa su Sa'adatu duk da su muka kwashe sauran kayana sannan nace don Allah ta gwada sana'ar zobo saboda mutanen dake barayin kada ciniki ya Gudu bayan na tashi,tace in sha Allahu zata jaraba.
Su Mama su ma a ranar sukayi parking din komai,Goggo bata zo ba ammh Anty Nasara tazo ita da Yaya Asiya muna tare da su da Hafsat da makota na bangaran su mama kuma yan'uwanta da su Anty Binta.
Yaya Ishaq da jamal su suka samo motocin da suka kwashe kayan suma sai da suka Chaji kudad'e masu yawa.










*Janafty*


[7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2003*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karon a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*

Kafin mu karisa chan gidan sai ga Matar Yaya isa tare da kanwarta,Yaya mariyasa nasan bazata zo ba.duk da ta bada uzurin bata jin dadin jikinta,ammh ni nasan dalilin ta.
tare da su da makotana su Sa'adatu muka tare a daidaita zuwa anguwar Ajiwa,koda mukaje mun iske su Mama achan,Gidan mai kyau ne saboda sabon gida ne sannan wanda ya zauna agidan bai dade ba ya tashi. kuma basu lalata gidan ba,ammh dai yaya Ishaq ya sake fenti ya gyara bayika sannan an gyara glop din wuta in da suka samu matsala shi kan shi da'n wannan gyaran sai da ya ci kudad:e sosai.
Mun iske su Anty Mahma har sun gyara barayin da mama zata zauna,bata dawo da wasu kaya ba Falon kujeru biyu aka saka sai cafet. sai Dakin Badariya katifa da Wardrope sai kayanta, Dakin mama ne aka jera mata gadonta da wadrope dinta,Da muka zo sai da muka shiga Shashen Mama muka ga waje muka saka albarka yara daman tuni Jamal ya taho da su nan muka iske su sun warware suna ta murna abun ka ga yaro Amir ne kadai muka zo tare da shi.
Da taimakon Anty Mahma da su Yaya Asiya suka share bangaren da zan zauna suka gyaramin, sun maidamin kujeruna a falo da Cafet sai tibi. wanda naso a had'a a saida Yaya ishaq yace a barta tunda an saida na bangaransa,Duka kayan kitchen dina sun koma Saboda yana da girma har babban Freezerna,na kasuwanci ya samu waje da Buhu buhun robobina da sauran aya da ta ragemin sai Ganyen zobo da sauran kayan abincin da muka dawo da su, suka jeramin a Store din kitchen sannan suka gyara Dakin Yaya ishaq kusa da Dakin yaran ne da aka jerama gadajen su da wadrope din su,Shima katifa ce kadai sai akwatin kayansa sai Cafet karami na tsakar daki ni kuma suka maidamin gado na da sauran kayyakina kafin yammah waje ya fito ya yi kyau suka wanke tsakar gidan tas ya bushe gwanin ban sha'awa abun da yafi burgeni ta bangaran shashena akwai Daga gefe wani karamin Rumfa kamar na shan iska inda a raina nace zan rika hada hadar da sana'ata a wajen.
Hafsatu ta yi abinci na saka aka dibar ma su mama,aka akai musu da shi,Saboda Dare dukkan nan suka kwana Anty Mahma ce ta koma gidanta har Anty Binta nan ta kwana Yaya ishaq kuma suka kwana Dakin korido shi da Jamal, sai da safe bayan an karya suka fara shirin tafiya.
Yaya Asiya da Anty Nasara suna min fada da nasihan kan sai na ninka Hakura na wajen iya zama da mama, in a baya zama bai had'amu ba yanzu kuma ya had'amu sai na zama mai Taka tsantsan da kiyayewa.
Ban ce musu komai ba. ammh ina ji a raina zan iya zama da mama a kowani Hali ai ni ba bakuwar cin mutumcinta ba ne? na riga na saba da Hallayarta na zauna da ita tsawon shekaru fin biyar naci wahalarta bayan kuma na auri Dan'ta ban tsira ba, to ban ga abunda zai bani tsoro akan hallayar Mama ba.
Kafin azahar suka koma karofi narakasu har bangaran Mama suka mata sallama bamu fahimci yanayinta ba,sama sama ta amsa tare da yi musu godiya,sai da suka tafi naji wajen yayi min bambarakwai irin baka Saba ba Hafsah dai tana ta kara gyara dakunan,su Anum kuma suna ta Murna Musty har ce min yayi"Umma ina son sabon gidanmu'
Nayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login