Showing 168001 words to 171000 words out of 288345 words

Chapter 57 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

789

yi kyau"
Nayi dariya ina shafa kamshi nace"Kai ma haka Amir dina."
Su Anum suna tare dasu Hafsah da Nana Khadija kowa ya kama bangaran da zai zauna muna sai muka kama Tebur d'aya dukkanmu mu Bakwai har da su Hafsah su Laila suna nasu bangaran,Gabadaya ji nake yi a takure saboda shigar jikina ga uban Takalmi Kallon da su Mama suke min ne yayi min yawa na tashi naje na gaishe su Allah ya taimakeni ban Turgud'e ba.
Anty Binta haka take kallo na kamar na Sauya mata har sai da tayi mgana da cewa"Lalle Fa'iza kece haka..?
To kada dai ki manta kina da aure ba Budurwa bace ke'"
Ban ce mata komai ba, sai ga Nana Fatima tazo tajani muka yi gaba tun ina Dari Dari har dai na saki jikina ina ganin zuwan su Yaya Ishaq shi da Jamal sai mijin Anty mariya,da wasu da ban sani ba,kuma a Tebur din bayan mu suka zauna ina da Tabbacin basu gane ni ba.
Ammi tazo ita da tawaganta daga ita sai Tawagan amare da angwaye.
Matuka wajen ya hadu bazaka ma gane Dare ba ne,an ci an sha an sha rawa sannan an yi nishadi,Badariya ta bada Tarihin Amarya wani daga cikin abokan ango shima ya ba da Tarihin ango.
An kira kannen ango mun fita mun yi liki Daman Ammi ta bamu yan Dubu sabbi muka? zubda da su,ana bikin Duniya in da ake yi jama'a haka muke taka kudi,Sannan an bamu fili mun rausaya Nana Fatima in na yi kokarin Sulalewa ta rikoni,ni na samu na yafa mayafin su basu yafa ba a Hannu suka Rike.
Mun koma wajen zaman mu sai igiyan takalmina ya warware na duka in gyara ina Dagowa muka hada ido da Yaya ishaq sai naga ya kauda kai kamar bai gane ni ba,sai na mike na isa gabansa cikin wani irin takun da bansan na iya ba kuma abun mamaki Tsab na saba da tafiya da takalmin kafata ina zuwa gabansa nace"Hy.."
Ina mai kura masa ido na make murya yasa bai yi Saurin Dagoni ba. Jamal baya wajen ya koma chan Teburin gabammu.kauda kai yayi yana wani basarwa zan kara mgana sai ga Amir yazo yana fadin"Umma.."
Yaron nan shi ya Tona min asiri a Firgice ya Dago yana kallona yana kuma kallon Amir kafin yace"Bangane ba..Wata Umman..?
Amir yace"Daada Umma ce fa baka ganeta ba ne..?
Yadda ya saki baki da Hanci yana kallona ne yasa na bushe da Dariya ina Talle ma Amir keya Lokaci daya ina Fadin"ji yaro ya batamin shiri na"
Amir shi kanshi Dariyan yake yi ganin yadda Babansa yayi daga sama har kasa yake kallona,daman shi bai so zuwa ba Abba yace sai sun zo tunda suka zo yake ganin yan mata kenan har su Yaya Asiya bai gane ba, tunda ya Dauka yaran yara mata ne kawai a wajen.
Kirjinsa sai duka yake yi yana kallona Amir da ya ga haka sai ya Sulale ya barmu kujeran gefensa naja na zauna ina fadin"Samari."
Sai kawai ya miko hannu ya kama Hannayena duka Biyun yana Fadin"Fa'iza wai don Allah da gaske ke ce..?
Sai na kara saka Dariya kawai ban tsammani ba sai naji saukan sumba a saman bakina cikin wani yanayi yace"Kin yi kyau Fa'iza ashe ke mai kyau ce ban taba sani ba.."?
Ina shirin bashi amsa naji Tafi a bayana ina juyawa Naga Nana Fatima da Sauri na kwace hannuna ina Hararanta karisowa tayi gabanmu tana Dariya Lokaci d'aya tana fadin"Allah ya kamaki wato kina nan kin zo gwada ma miji kwalliya ammh nan ina fama dake kin ki Tsayawa ayi miki,Ranka ya dade a biya ladan kwalliya domin sai dakyar ta amince akayi mata"
Ba musu ya saka hannu a aljihu ya zaro kudi ya damka mata,suma Abba ne ya basu yace na liki ne,Tako amshe Abunta tana fadin"To yanzu sai ka mora kallon ka..Fa'i."
Ina juyowa ta kashe min ido tayi gaba na bita da dariya,kai tsaye nace"Ina ka samu kudin tukwaici..?
Cikin wata murya yace"Abba ya bamu wai na liki ni ai ga babban liki na nan"yafad'a har yana wani lashe baki yar Dariya nayi cikin yangar da wlh bansan na iya ba,kai wani lokacin bakin mutane na taimakawa wajen Dakushe tasirin da muke da shi a Rayuwa, yanzu da na samu masu yabani da Daidaitani da Sauran mata har na fara tunanin to dame suka fini..?
Kiri kiri Yaya Ishaq yaki barina na matsa ko'ina har yana fadan?na saka karamin mayafi,rai bace ya kalleni yana fadin"Wato kyale kin da nake yi yasa kika maidani sauna ammh bari mu koma gida zaki shiga hannu"
Ina jin haka na shiga Taitayina,Sai da za'ayi Hotuna Anty Fadila Dakyar tazo ta jani shima sai da tasha korafinsa sai bina yake da kallo barin ma takalmin kafana a ransa bai san sanda ya furta"Jar uba.."
Fa'iza fa ta tashi kan sa ,ya so yayi wauta da farko ballatana da kayan suka kamani,gabadaya Shafe dina ya bayyana kamar ban haifi yaran nan ba Tuni kishi ya kamashi muna Hotunan kamar ya fizgoni ya rumgume haka yake ji bamu muka bar wajen ba sai Dayan Dare Shima ba'a tashi ba nan muka bar Amarya da sauran mutane Yaya Ishaq bai sauke ajiyar rai ba sai da muka tafi ba shi kadai ba duk wanda ya ganni sai yace Fa'iza kin yi kyau barin ma Badariya juyi goma sai tace"Kai matar yayana tafi kowa a wannan bikin"
Bamu san yaushe suka dawo ba sai da Safe su Hafsah sukace sai uku na Dare araina nace lalle kaduna bariki.
A ranar? muka raka Raliya dakinta Dangin Hajiya da kawayenta suka wuce bayan sun damka amanarta ga Ammi da su Inno,Mama da Anty Binta a ranar suka tafi bayan Ammi ta hada musu sha tara na arziki tare da Jamal suka Tafi Abba dai ya Tsaida Ishaq yace yana so zai yi mgana da shi. Domin yadda ya samu labarin a bakin Goggo Mijina baya aiki yanzu nice duka hidomomin gida shine yake so ya gansa su Tattauna.
Kuma in dai ba wannan Lokacin ba bai kuma da Sauran hutu in aka gama Bikin.
Hajiyar Dala bata zo ba rasuwa akayi mata, Yayan megidanta ya rasu dole ta Tsaya ammh taso ta zo ta bama idanuwanta abinci,sai dai tagani a waya tunda Badariya nata zuba Hotuna yaran ta na Nuna mata,Hajiyar Dala tayi mutuwar zaune da taga Hotona da Badariya ta saka a kasan Hoton ta saka"Matar yaya na tafi ta kowa. Anty Fa'iza"
An ce har Jamal ya Dauka shima ya saka a Status d'insa, gogan bai da waya bai san wainar da suke toyawa ba,Hajiyar Dala aranta sai da tace kamar an yi min wankin in ji nice na koma wata classis haka a baya tasan ni yarkace yarkace kamar yar Gudun hijira,ammh yanzu kuma taga na zama wata mai aji da Daraja.
Inaga ta wayar Jamal Zainab tagani ta tambaye shi yace ina kaduna muna Biki sai ta kirani tamin Allah ya sanya alheri kai tsaye kuma tace min"Ashe kuna da yan"uwa a kaduna.?ni ko sai nace mata eh na kara da fadin"Kanin Mahaifiyarmu ne mai rasuwa"Sai ta jinjina kai tace"Allah sarki"
ba mu jima muna wayar ba,bayan tambayan yara da gida muka yi sallama.
Zuwa talata kaf gida ya watse hatta Goggo ta koma karofi sai mu har Yaya mariya tanan sai gobe zata tafi Yaya Asiya kuma aranar suka tafi da yammah tabi yan gidan su Ammi daman tare suka iso,Amarya na gidanta suna hutawa ita da ango Badariya na gidan tare dani zamu koma da yara.
Wasa wasa ina neman yin Sati a kaduna Gida duk ya watse,Nana Fatima ta koma Dutse,hakama Anty Fadila ta koma lagos,Abba ne ya Tsaidamu ni da Yaya Ishaq shiyasa bamu koma ba shima kanshi ya koma Office sannan ga wannan Hayaniyar Biki shiyasa bamu samu zama ba. ammh nasan Ba domin Yaya Ishaq na ganin girman Abba ba,bazai zauna ba,sai korafi yake min shi ya gaji da zaman wuri d'aya da cewa yayi zai tafi ya barni sai na Taho daga baya nace ya dai Tsaya yaji me Abban zai ce masa.
Sai Ranar Alhamis da Daddare suka samu zama da Abba. Tunda bikin ya watse ni nake yin girki,Umarnin Abba ne har kayan hadin zobo da kunin Aya an siyo da sauran lemuka ina ta Shagwabasu da cimata.
To ranar ma daddaran Lemun abarba nayi musu,sannan na soya musu kaji nayi pepe din su sai tashin kamshi yake yi,daman Tuwon shinkafa nayi miyar agusi da naman rago an kai musu sai Ammi tace na bi su da wannan su dora daga baya.
Sanye nake da Hijabi mai ruwan kasa har kasa Nana Khadija ta Dauko min Voul din kazan muka shiga Falon Abba sun ware suna ta Hira da Yaya Ishaaq Abba ne fa da ba ruwansa.
Har kasa na duka ina gaida Abba ya amsa yana fadin"My Dota me muka kara samu ne.?
Ina mirmishi nace"Abba pepe chikchen ne sai lemun abarba"
Abba ya bude kamshi ya Dakesa sai ya lumshe ido yana fadin"Gaskiya Ishaq kayi hakuri ku kara ko Sati d'aya ne nima na Mori yata da girken girken nan nata masu dadin Tsiya"
Yana mirmishi yace"Sai ayi haka Abba?
Abba ya kalleni kafin yace"Fa'i Allah ya kawo kudi Abba ya bude miki katon gidan abinci.."
Ina Dariya na amsa da Ameen khadija na gefe tace"Abba ga Vacany na farko kun fara samu nasan albashin zai yi tsoka"Abba yace"Aa sai mun yarda da kwarewarki bama son masu son jiki"Sai ta fara dira kafan Shagwaba da Sauri yace"Ni fa ba da nake ba"
Yadda yayi ne yasa muka Dara mikewa muka yi muka fice yana sakamana albarka.
Bayan sun taba kazan sun sha Lemun Abba ya koma ya kishingida yana fadin"Fa'iza ta shagwabani da abincinta gaskiya Maman Nana ta kara koya kafin tatafi in baso take na rika barin mata kayanta ba"
Ishaq yace"Baza'ayi haka ba Abba"
Abba yace"To a san yadda za'ayi dani Allah"
Haka dai suka yi ta barkwanci.
Abba baya so ya fara mai mganar kai Tsaye kada Ishaq din ya Dauka da wata manufa sai ya fara sako mai mganar aikin Gwamnati suna hira cikin Hiran ne Abba ke tambayansa ina yake aiki kansa na kasa yace"A baya dai nayi aiki da Hukumar Tattara Haraji ta kasa ammh yanzu bana aiki da su bisa ga wani abu da ya faru"Sai Abba ya gyara zama kamar bai sani ba yace"Subhanallah me ya faru..?kai Tsaye kuma Ishaq din ya warware masa komai, Abba ya jinjina kai ko ni bai yi mganar dani ba.
Yaya isa daya fadamai sai ya Tattauna da Goggo ta kara yi mai bayani ammh yanzu yaji wasu a bakin Ishaq din.
Kai Tsaye Abba yace"A abuja kace kayi aiki da su ko..?
Kai ya gyada yana fadin"Eh Daga katsina chan suka maidani nafi shekara Bakwai ina aiki dasu a wajen"Sai Abba ya muskuta yana Fadin"Nako san chairman din ku na wajen. Dr.Lawal Bako zan kirasa ko zai iya yin wani abu akai,ai bai kamata a bar shi haka ba, sai a tsananta Bincike har a gano gaskiya"
Da Sauri Yaya Ishaq yace"Kasan shi ne Abba?
Abba yace"Yes Tare muka yi Mastering Degree din mu a Buk kano Shekarun baya"
Sai Yaya Ishaq ya murmusa kafin yace"To ai surukina ne. Ina auran yarsa Zainab"
Abba ya ware ido kafin yace"Au daman kana da wata matar ne bayan Fa'i.?sai ya gyad'a mai kai cikin Mamaki Abba yace"Ikon Allah to tana ina ban taba ganinta ba..?
Kai Tsaye yace"Tana chan Abujan Abba.."
Abba sai ya kasa mgana ya Dauko wayarsa yana fadin"Ammh kuma duk da wannan dangantarka bai saka an tsananta bincike ba? domin daga gani kamar Trap ne aka had'a maka acikin kuma ma'aikatan naku ne"
Yaya Ishaq yace"Gaskiya ba'ayi ba. Lokacin dai an ta fad'i tashi Saboda Shigar EFCC kan mganar"
Abba yace"Suma EFCC din ina da wanda zan kira kan mganar ammh bari na fara kiran Dr.Lawal din ina da lambarsa mukan taba juna Lokaci bayan Lokaci"
Kai tsaye ko ya lalubo lambarsa ya Doka masa kira ya kuma sakata a amsa kuwwa kira uku ana hud'u ya Dauka cikin Dariya Dr.Lawal yace"Kaga Matatar mai da kanta ba Sako ba. Allah ya taimaki Engr"
Abba yayi mirmishi yana Fadin"Dr bako kana lafiya..?ya iyalai..?
Shi Dr.Lawal yaje ya karo karatu ne har yazama Dr,shi kuma Abba bai yi ba,aammh dukkansu Chemical Engerniaring suka karanta a makaranta.
Bayan sun gaisa Abba yace"Kai ashe mun hada suruki d'aya bamu sani ba..?Dagachan Bangaran Dr.Lawal yace"Suruki wani surukin nawa kenan..?
Abba yace"Suruki nawa gareka..?
Dr.Lawal yace"D'aya mijin Zeey ne, Ishaq dan katsina ne"
Abba ya yi dariya kafin yace"Shi fa. Nima ai yana auran y'ata"
Sai Dr.Lawal ya mike daga kishingid'en dayake yana fadin"Wata y'ar taka Kuma Engr.?
Abba yace"Sunanta Fa'iza abokiyar zaman ita yar taka kenan"
Sai ya mike tsaye a razane yana fadin"Dama yar ka ce ita..?
Abba yace"Diyar kanwata ce mai Rasuwa. Ga ni ga Ishaq din sun zo Daurin auran Abdul'Ahad ne muna Hira sai muka tabo bangaran aiki, To yana gayamin a office din ku na Abuja ya taba aiki nace na sanka shi kuma yace ai surukin sa ne kai"
Dr.lawal ya share zufa yana fadin"Ikon Allah.."
Abba yace"Kaji fa."
Dr.Lawal yace"To ai baka gayyace ni bikin yaron namu ba".?
Abba yace"Kaina yayi zafi ne kuma kasan mun jima bamu yi mgana ko ta waya ba"
Daganan suka cigaba da Hira Abba ya Sako mganar Ishaq da Tunanin a saka Kwamitin Bincike a gano bakin zaren mana Dr.Lawal yace"Ai hukumar EFCC ke cikin mganar Engr shiyasa"
Kai Tsaye Abba yace"Kada ka damu ni dai ka nad'a kwatimin bincike ta bangaran ka, ni kuma zan yi mgana da megidana Engr mahaifinsa Shine Chairman na EFCC a yanzu haka so nasan zai taimaka mana insha Allahu"
Dr.Lawal a ransa yace aiki ga mai kare ka,Sun dad'e suna mgana yace zai nada masu binciken tunda zai shiga mganar nan take ya kira Megidan nasa bai same shi ba sai ya kalli Ishaq yana fadin"Zan kirasa kuma ina gayamai Cikin Satinan za'a dauko Fayel dinka a Sabunta bincike da ikon Allah za'a wanke ka"
Yaya Ishaq nata godiya,ni bansan me suka Tattauna ba. washegari Direban da Abba ya bamu aka maidamu gida a jeep dinsa ni da yara da Badariya da Hafsa da zata koma makaranta booth din mu cike da kayan Biki.
Bai fad'amin yadda suka yi da Abba ba, sai bayan kwana Biyu da muka natsa sannan yake gayamin nayi murna sannan nasan tabbas tunda Abba yace zai shiga mganar an yi an gama.
Har Mama ya fad'amawa sai addu'an Allah yasa adace take yi,da fatan a gano gaskiya.
Ko da aikinsa bazai dawo ba,ammh yana da kyau kada sunanka ya zauna a matsayin barawon Gwamnati.




*Janafty*
[7/19, 2:47 PM] Hauwa Galadima: *KNKB2016*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Wannan shekaran data zagayo. bamu sha wahalan rayuwa ba,saboda Abba ya tsaya mana,shi ya biya kudin makarantan yara da sauran bukatumu na yau da kullum.? hatta da kayan abinci ya cike mana wannan bangaran,Yace komai muke bukata mu kirasa bamu da damuwa Ishaq kuma daman ya fad'a masa shi a D'a ya dauke sa ba suruki ba, shima uba yake garesa kamar yadda yake uba gareni
Shikenan shima sai ya saduda yana karban komai da girmamawa,Mama ma haka tana ta min godiya,ni ko nace mata bakomai,Badariya ta koma kano wajen Hidimar kasarta Jamal ma ya koma makaranta sun shiga Semister karshe a makaranta.
Gefe daya ina cigaba da sana'ata ban Dakata ba,Sannan ayyuka sun karu min yanzu saboda akai akai nake hada Turaruka yanzu daga chan kaduna da kano ko'ina akayi mganar Turare sai Ammi tace Fa'in mu tana Had'asu masu kamshin Dadi,in nayi sai dai na bama Hafsah ta kai tasha a saka a mota kuma kudin aikina cas a Hannuna,Allah yasa ma Anum na gida ta gama primary zata shiga JSS Section.
Muna waya da su Nana Fatima kusan kullum muna sanin Halin da juna ke ciki,Yaya Ishaq yaki ya gyara wayarsa sannan yaki ya siya wata. Matarsa sai kirana take yi ni na zama alkali a Tsakaninsu wani Lokacin sai ta kira baya gida sai ya barni da gayamata ya fita,gajiya nayi ranar muna zaune da Daddare shi ya gama yi ma yara karatu sun kwashi Littafan su zuwa Daki,Hafsah na kitchen tana Dafamin zobo wanda zan yi na safe da shi,ni kuma ina gefe zaune a kasan cafet,shi ko har ya koma ya kwanta a saman kujera.
Dagowa nayi ina kallonsa kafin Nace'"Na manta. matarka ta kira d'azu baka nan"
Yana ji na bai yi mgana ba sai na tura masa wayar gabansa ina fadin"Gaskiya ka siya waya. ko ka gyara taka, nagaji da Damuna da matarka take yi, kana kuma barina da bayani in baka gida"
Sai alokacin ya bud'e ido yana kallona cikin shakewar murya yace"Ba zan siya ba sannan ban yi ra'ayin gyarawan ba"
Ban yi mamaki ba daman nagansa yau sai a hankali yana jin yan tsiyan nasa, sai na rabu da shi aiko ko tashi bamu yi a wajen ba sai ga kiranta na leka naga itace na mike na fice daga Falon zuwa tsakar gida ina faman kaye kaye ban sanin masa ba ko sun yi mgana.? ni dai da nadawo naga wayata nan saman kujera na Dauki kayana na wuce Daki.
Abunda na lura Zainab da mahaifinta sun sauko suna neman sulhu da Ishaq shi kuma yaki basu wannan damar Saboda bayan kwana Biyu ta sake kirana baya nan domin yakan d'an fita ya mike kafa ina ji a gefenta tana mgana tana fadin Daddy wai baya nan ya fita sai naji an yi mata mgana kafin tace min in ya dawo nace ya Kirata Daddy zai yi mgana dashi.
Da ko ya dawo na bi shi har Daki na Fad'amasa sannan na bar masa wayan a wajensa sai gashi ya biyoni nima har Daki ya mikomin wayata yana Fadin"Ki daina kawo min wayar nan Fa'iza wai sau nawa zan fad'a miki ne.?
Sai na bude baki ina kallonsa cikin mamaki nace"To in ta kira sai nace mata me..?kai tsaye yace"ki fad'a mata gaskiya bana son mgana da ita"
Nima kai Tsayen nace"Tace ka kirata Daddy na son mgana dakai"
Yadda ya wurgamin wayar ya fice a Fusace ne yasa sai da nayi Dariya Allah yasa wayar kan gado ta fad'a,Na dauki wayata ina fadin"Bani na kar zomon ba"
Zainab bata barni ba, ta rika addabata da kira kunya sai na rasa me zan ce mata sai taga kamar ni ne bana son had'asu,Gajiya nayi nace gwara na fito


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login