Showing 210001 words to 213000 words out of 288345 words

Chapter 71 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

748

nima na kallesa da ruwan Hawayena kafin ya gyada,kai yana Fadin"In kina tsammanin zan sake ki ne to gwara ki sake Tunani Fa'iza.."
Aurena dake har Abada babu Saki"
Mama muje.."
Yafada Lokaci daya yana Saurin barin Falon Abba ya bisa da kiran sunansa ammah yaki juyowa Mama ta mike jiki a sanyaye tana Fadin"Kuyi hakuri. Fa'iza Allah ya baki Hakuri"
Daga haka itana tabi bayansa Abba ya kada kai cikkn takaici kafin yace"Wlh ko auren zobe ne sai ka saketa ishaq. mutumin banza da wofi kawai"
Ina kuka Abba ya Durkusa gabana ya Rumgumeni yana Lallashina fad'i yake"Zai sake ki Dolen shi ma,nayi miki wannan alkwarin"
Ki daina kuka Ba raina ki yayi? saboda baki yi boko ba..?makaranta ba'a Nageria ba har kasashen waje duk inda kike so nan zan kai ki samu Ilimi Fa'iza"
Nasan karamci da kauna yasa Abba ya ce min haka ammh ni ba shi ba ne Burina shiyasa na Dago ina kallon Abba kafin nace"Aa Abba bani da sha'awan yin karatun Boko. Har kuma yau bana Nadamar rashin jin Turanci da ba na yi ai nasan Allah kuma ina jin yaransa wato Larabci, sannan ni ba Jahila bace Abba ina da ilimin addini nasan Qur'ani nasan hadisai da Hukunce hukunce Tsarki Abba nasan yadda zan gyara Sallata da Ibadata, Abba ka fad'amin akwai wani Ilimi ne bayan ilimin da Manzon Rahma yazo mana da shi..?
Cikin girgiza kai Abba yace"Babu Fa'iza sai dai zamani ne yazo mana da komai. An ce mu nemu Duniya kamar bazamu barta ba sannan mu nemi Lahira kamar bazamu je ba. kuma ana so kowani Mutum ya Had'a Fukafukai guda biyu saboda zaman Duniya da Lahira"
Duk na aminta da mganar Abba kawai Ra'ayin karatun bokon ne bana so shiyasa nace"Abba ni ba ni da ra'ayi ne kwata kwata ku bar ni kawai"
Da Sauri Abba yace"An barki Fa'iza ki Fada'min abunda kike Bukata ni kuma nan duniya in dai bai fi karfina ba zan yi miki shi"
Cikin jin dadi ganin Abba ya bar mganar Karatu nace"Abba ka karb'omin Shaidar sakina wajen Ishaq"
Da Sauri Abba yace"Nayi miki alkwari"
Sai me kuma..?
Kaina na kasa tace"Ina so na bunkasa kasuwancina Abba shiyasa nake neman alfarman ka barni wajen Goggo kada kace zaka tafi dani Kaduna"
Shuru yayi kafin kuma yace"Na amince zan baki jarin da zaki bunkasa kasuwancin ki Fa'iza. sannan zan barki wajen Goggo har sai ranar ke da kanki kika so dawo wa wajen mu da zama"
Ina Sharan hawaye da bayan Hannuna nace"Zan shiga islamiyan matan aure sannan ina so zan koma Hadda. Ina so na Haddace Qur'ani tunda Sauka nayi a baya ba Hadda ba".
Kai tsaye Abba yace"Nawa zai isheki Hidimar karatun naki..?
Sai hawaye ina sharban su ina zuba ma Abba Godiya sai ya Dafa kaina yana Fadin"Bakomai ki daina kuka Daga yau nayi miki alkwarin Farinciki a rayuwarki har Abada kin ji ko..?.
Na gyada mai kai sai ya Sakeni ya mike yana Duba agogon Rado baki dake Hannunsa Lokaci daya yana Fadin"An yi la'asar ma bari muje mu yi sallah mu yi harama Goggon su da mallam ga amanar Fa'iza nan ban amince Ishaq yazo kusa da ita ba ni da kaina zan karbo mata takardan Sakinta"
Goggo tace"ba kwana zaku yi ba..?
Kai Tsaye yace"Inno da Baba Ati suna nan.
Ni da maman Nana da Abdul'ahad kaduna zamu kwana yau in sha Allahu"
Yadda ransa ke bace yasa bama wanda ya basa baki har Inno shi da Mallam suka fita aka bar ni da Ammi nata faman Lallashina da su Inno Yaya mariya na Fadin"Fa'iza fa ta Dade cikin wannan bakincikin, Allah ne ya kawo karshen abun har kuka ga Haka ta faru"
Ni dai ina jinta ban yi mgan ba. Dakyar na daina kuka na koma Daki nayi sallah ina yi ina kuka,kawai ni yanzu abu daya nake so Ishaq ya Sakeni da gaske nake yi nagaji da auransa
Abba kuwa suna Dawowa masallaci sama sama suka yi mgana da yaya Isa kan in ya koma gida ya natsu zasu yi mgana da Ammi kan kayan da za'a zuba a gidan su kansu sun gansa a Zafafe sun sam zaman bai yi Dadi ba Balle daman suna kofar gidan Ishaq ya Fito shi da Mama cikin wani yanayi Yaya isa bai damu ba a Fidi sai da ya Furta ma Yaya Abdul'ahad cewa Baya so Abba ya Daidaita Fa'iza tabi ishaq Lagos da ya nemi sanin Dalilinsa sai ya Fara fadamasa iya abunda ya sani kan zaman Fa'iza da Ishaq Shima nan take yaji ya Tsani Ishaq din haka kamar wani Dabba shiyasa suna zaune ya fito suna kallonsu yana kallonsu suka ki mai mgana shima baya cikin yanayi mai Dadi..
Katsina suka koma Mama tace ita ya barta gidan Binta kamar yaso yaki Saboda yara yasan Zainab bazata iya kula da su ita kadai ba,ammh sai ya Tuna Badariya zata bi Jirgin Jibi da Rana shi ya biya mata ma kudin jirgin sai?Direban da suka yi tasha Daga karofi ya sauketa gidan Anty Binta shi kuma ya karisa dashi kano ya samu jirgin karfe 5pm zuwa Lagos bai yi wata wata ba ya siya Ticket suka tashi sai birnin Ikko.
Anty Binta ita kanta ta tsorata da Lamarin da Mama take maida mata abunda ya faru Rike baki tayi kafin tace"Shi ko Ishaq meyasa yayi haka..?gaskiya bai kyauta ba wannan zalunci ne"
Mama ta ja majina kafin tace"Wlh ban sani ba Binta bai taba Fad'amin ba"
Anty Binta tace"Allah ya kyauta ya bari in Abban Fa'iza ya huce yaje har gida ya kara bashi Hakuri ammh Sakin Fa'iza yanzu ai akwai matsala ni kaina Sai daga baya na Fahimci mganar Baba, da yace Fa'iza ce Matar rufin asiri ga Ishaq?Mama"
Mama na sharan kwallah tace"Ni zan Fada miki haka ni da na zauna tare da ita.Ta ci damu ta sha Damu da Guminta,tayi mana suturra bata Duba abunda ya faru a baya ba Zainab din daya ke so bazata iya wannan Rayuwar tare da shi ba.."
Anty Binta ta sauke Numfaahi kafin tace"Sai muje har ni mu bama Abban Fa'izan hakuri. ko don yaran nan Mama"
Mama tace"Anya?bana jin zai yarda ya Dauki fushi daga shi har su Goggon bana jin zai iya Sauke gudurin sa"
Anty Binta sai ta kasa mgana saboda Lamarin ya fi karfinta kafin tace"Yanzu ina shi Ishaq din..?
Mama tace"Ya wuce kano jirgi yace min zai hawo ya koma lagos"
Anty Binta tace"Allah ya kaisa lafiya"
Daganan suka cigaba Tattauna Lamarin.

*****

Kamar yadda Abba ya fada basu kwana a karofi ba Inno dai da Baba Ati suna nan zasu kwana Biyu,Sai Dare suka isa gida,Ranar Abba barci ma rabi da rabi yayi washegari da yaje Office idanuwansa yayi ja matuka alamun baya cikin natsuwarsa,Kansa sai ya fara ciwo shiyasa ya Dawo gida ya kwanta Ammi tasan Baban Nana bai iya Fushi ba ballatana abunda ya shafi yaransa,Dakyar ta Lallashesa yaci abinci ya sha mgani ya kwanta sai bayan La'asar ya tashi ya yi wanka ya Sauya kaya Ammi sun yi waya da su Nana Fatima ammh bata fada musu yadda zaman ya kaya ba.
Nana Fatima sai taji Hankalinta ya kwanta da Ammi tace Fa'i na Karofi har alokacin.
Abba ko Dariya ya Daina yi yana Sakawa da warwaran yadda zai karb'an ma Fa'iza Takardan Sakinta ko Hiran Daran da sukan taba da Hafsah da Nana khadija ranar bai samu ba,Daman kuma Ammi tace bai jin Dadi daga gaisuwa da Tambayan ya jiki ya koma ya kwanta ya Lumshe ido shiyasa suka fice suka koma Shashen Ammi suna Tunanin kila ciwon kan ne ya matsa ma Abba.
Yayi nisa cikin tunanin sa har baisan sanda Maman Nana ta shigo ba itama gajiya tayi da kiran sunansa ta matso kusa da shi tana Taba kafarsa Lokaci daya da kiran sunansa"Baban Nana"
Firgigit yayi kamar wanda ya farka Daga barci sai yaci karo da sanyin Idaniyarsa,Azizat.
Ajiyar rai ya sauke cikin wani yanayi ya kasa mgana Maman Nana ta zauna gefensa,Sai ya matsa ya bata wajen zama ya mike dakyau ya gyara zama kafadunsu na dukan juna.
Cikin wani yanayi Ammi ta kallesa tana Fadin"Haba Baban Nana meyasa..?wannan tunanin da kake yi fa ba mafita ba ne"
Numfashi ya sauke kafin yace"Alkwarin da nayi ma Fa'iza ke damuna Maman Nana na rasa ta hanyar da zan karban mata takardan Sakinta Ishaq bazai yi sakin nan cikin Sauki ba"
Ko na kai shi kara kotu ne..?
Da Sauri ta girgiza kai kafin tace"A'a duk bata kai haka ba Baban Nana. akwai ya'ya tsakani sannan ga zumunci a bi dai komai a sannu. Kowa ya shaida zalunci da Kuntatawa a zaman auren Fa'iza da shi mganar ma yaki sakinta bai taso ba".
Abba yayi shuru ya kasa mgana Ammi ta cigaba da bashi mgana cikin kwantar da Hankali har ya samu natsuwa cikin Sauke ajiyar rai yace"Bakomai nasan ta inda zan Bullo masa"
Ammi tace"kabi a sannu Baban Nana nasan ka sarai"
Mirmishi yayi mata kafin yace"In sha Allahu"
Daganan shi da kanshi ya Rufe mganar bayan ya bude mganar kayan Funitures din da yake so a saka a sabon gininsa na karofi Ammi tace"Ga inda muke siyan kaya kano.
Har gida zasu kai komai su kuma gyara wajen"
Kai tsaye yace"Ki yi lissafin kudin zan Tura miki ta asusun ki"
Da kai ta gyada masa kafin su cigaba da Hiran su sama sama na mata da Miji masu kaunar juna da Fahimtar juna.
A cikin Hiran ne Ammi ta kallesa tana Fadin"Wai ina labarin Engr ne Baban Nana..?kwana Biyu ban ji kuna waya ba hala bai shigo kaduna ba ne..?
Abba yayi hamma kafin yace"Gaskiya satin nan kaf bamu yi waya. Mgana ta dashi ta karshe yace zai je London ina kyautata zaton ya tafi ayyuka ne suka masa yawa kinsan Engr da Sabgogi da yawa fa"
Ammi tace"Sosai fa,ya jikin Hajiya Kudirat kwanaki na kira Hajiya Shukran bata Dauka ba,Azima ta fadamin kwanaki ta shigo ta gaida Hajiya Jikin Hajiya tafisu ne ya matsa tazo Dubata"
Abba yace"Haba tuni ta warware kamar ma Engr yace min ta saka rigima sai ta koma Benue ,Lokacin muna Warri tare da shi naji an kirasa ana fadin ya Lallasheta yace rigimmiyar Tsohuwa a barta tatafi mana"
Ammi tayi Dariya kafin tace"Kai a wannan matar akwai rigima wlh,ka tuna da mukaje dubata sai Yarbanci take tana masifa saboda za'a bata mgani sai da D'anta yazo ya lallasheta ta yarda fa"
Abba na mirmishi yace"Engr na yawan Fadin rigimarta tana matukar son mahaifinsa da su kansu tunda shi kadai take da shi ance Haihuwanta Goma tara duk sun yi wabi ne shi kadai ya tsaya"
Ammi tace"Allah sarki.."
Nan ya cigaba da bata wasu labaran itama tana bashi wanda ta sani Dalilin Hajiya Tafisu,Suna ta yabon kirkin Engr da iyayensa.
Abba yace"Muna da Seminar a Abuja sai dai ban sani ba ko zai samu zuwa"
Ammi tace"To kila in yana gari"
Abba yace"Ba lalle ba gaskiya"
Da haka suka rufe wannan Hiran suka Fara shirin kwanciyaa

*******

Tunda ga ranar da Abba ya bar Karofi, Rana bazata tab'a fitowa ta fad'i Abba bai kirani mun gaisa yaji Lafiyata ba.
sannan ya turamin 100k na bunkasa kasuwancina mganar makaranta kuma Mallam yace a jira sakin ya tabbata nayi iddata in nagama ina da Damar fita duk inda naga Dama,Da haka sai na Dakata ammh na samu natsuwa da kwanciyar Hankali,sannan na fara maida jikina,Goggo na da almajirai masu Dibo ruwa da sharan Tsakar gida gyaran Daki kawai nake yi sai Girki,Yarana kuma muna mgana da su ta wayar Zainab ammh ba ko da yaushe ba,Goggo da kanta ta shiga kasuwa ta min siyayyan kayan zobo da Kunin Aya,aka sauke a dayan Dakin inda na saka Freezer dina sana'ata zata dawo gadan gadan tunda zaman bazai min Dadi ba.
Goggo ta aikamin makota yaya mariya ma haka tunda nan kusa da su suna siya Lokacin da ta kan sara a wajena shiyasa da na fara Zobo ba laifi ana samun ciniki matsala D'aya na samu Rashin wuta in nayi kunin aya sai ya fara Lalacewa kafin ya kare Tunda ba ciniki ba kamar Lokacin ina katsina ba.
? Da na fad'ama Abba ana matsalan wuta batare da sanina ba Sai ga Yaya Isa da katon Generator in ji Abba sai dai na kira nayi Godiya Baba Ati na nan bata koma ba,Inno dai Abba ya Turo Direba ya Dauketa zataje ganin Likitan ido.
Gida kuma Tuni ma'aikata sun zo sun kawata gidan da kayan Furnitures masu kyau muma mun je mun gani mun kara gyara gidan nan Su Abba zasu rika sauka Tunda Baba Ati tace bazata iya zama ita kadai ba.
Muna waya da Anty Fadila kuma tana zuwa duk weekend tana Duba su Amir suma Baban nasu na kawo su Tunda yaga sun shaku da yaranta.
Mama bata koma Lagos ba tana katsina wajen Anty Binta sai dai Badariya da Jamal suna chan Zainab ga Tsohon ciki ammh haka ta fara zuwa aikin da Mahaifinta ya samar mata sannan kuma ya siya mata Motar da zata rika zirga zirga aciki ta Riga ta sadakar maman Amir bazata Dawo ba.
Shi kan shi Uban gayyar tun bayan Tafiyarsa sai kirana yake yi ban taba Dauka ba,in dai naga shine ammh ina Daukan kiran Zainab Saboda nasan ko ita ko yara ko kuma Badariya,Har Jamal ma yana kirana duk korafin su Daya na dawo sai dai na bisu da toh ammh su kan su sun tabbatar da bazan Dawo ba.
Dad'ina Daya da su Amir suka fadamin sai la'asar suke tashi daga makarantar Boko,gidan Anty Fadila suke zama saboda yaranta suna da Malamin islamiya in suka yi karatun Tare babansu in ya tashi aiki sai ya Biya ya Dauke su,Zaman su sai asabar da Lahadi shima gidan Anty Fadila suke yin shi Zainab fama take da kanta Ko nata ya'yan su Amir ke kula da su sai mai renon da ta zo da'ita.
Ashe bani kadai Ishaq ke kira ba Harda Abba shima bai kara Saurarensa ba domin yace in yana son mgana da shi ya rubutamin Takardan Sakina,Tun bayan Lokacin Abba bai zo Karofi ba sai dai Hafsah da Nana Khadija sun zo sun yi Sati Daya suka koma Hafsah ta zama katuwa tayi jajir da ita ta samu Waddatccen hutu da jin Dadi.
Ba Laifi sana'ata ta Dawo kuma Tunda aka ganeni ana ciniki sannan Goggo tasan almajiranta na Dauka su tafin da shi wata makarantar maza ta secondary sai kudina suma da suka gane har gida suke zuwa siya in ba Wuta sai na Tada in ji na,Ganin aikin namin yawa yasa Goggo ta ce na Dauki wacce zata rika taimakamin nan makotan su Goggo na samu wata Jummala Mijinta ya rasu tana da marayin ya'ya ita mukayi ciniki da ita zan rika bata 5k duk wata ta amince da Murnan ita ke Dafamin zobo ta kuma wanke aya ta kai nika nawa kawai Dubawa da zaman Had'awa sai aikin ya Ragemin Kuma Alhamudulillah sai Hankalina ya Dauke Damuwa ta rage samun Muhalli a zuciyata,Saboda ayyukan dake gabana.
Yaya Asiya duk abunda ya Faru Labari taji mun yi mgana ta waya abu daya tace min"Fa'iza ki zauna ki yi Tunanin makomar rayuwarki in rabuwa da Ishaq mafita ce gareki zamu baki Goyon baya,in kuma komawarki itace Mafita Fa'iza ki koma Dakin ki ki Rumgumi ya'yan ki''
Da toh kawai na amsa mata Saboda bani da abun ce mata komai zan Fad'a bazata gane ba Makotana ma muna waya da su barin ma Sa'adatu sai dai ban taba Fada musu ina Karofi ba na barsu a ina Lagos ne Haka ma Hajiya sai dai ita nasan Kila Raliya zata Fadamata ammh har Lokacin batamin mgana ba,Sai nima na share ban mata ba,na maida jikina duk da ramar kasusuwan wuyana basu shige ba,Sai dai sun fara shigewa din
Koda yaushe Nasiha ne tsakanina da yan'uwa suna Lallab'ani Saboda na samu kwanciyar Hankali kuma na samu matuka.
Anty Binta ta kirani sau biyu tana min Daidaiciyar mgana na bita da Toh,ta kuma saka har Anty Mahma da Halisa suka kirani duka mganan su kan ya'ya ne na koma Saboda su,ni ko bana cewa komai sai dai toh, sai yanzu suka san da yaran..? Bazan kara bari Saboda ya'yana a cutar dani ba.
Suna ta so na koma ne na cigaba da Bautar da na saba ina bakin Alkalami ya Riga ya bushe ba Ishaq ba gabad'aya maza ne da aure ya fita kaina kwata kwata.

*******

Ranar litini da Safe mukayi mgana da Abba zai je Abuja suna da Seminar,kwata kwata Abba bai Fad'amin niyyarsa ta zuwa Lagos ba ashe haka ya kudurta a ransa,sun je sun yi seminar na kwana Hudu ma'aikatansu uku kaduna,Edo,da Warri suka hadu a wajen,Tattaunawa ta musamman kan bunkasa mai a Nageria,Engr bai zo ba yana London shiyasa ranar da suka gama Seminar din Washegari jirgin Safe yabi zuwa Lagos yana sauka a Tashar Saukan Jirage na Murtala muhammad ya samu Taxi har Headquater tattara Haraji na reshen jahar Lagos.
Yana zuwa sunan Ishaq kadai ya Fad'a aka masa jagora har Office dinsa misalin karfe 11am na Safiyar Ranar jumma'a. Ishaq sai dai kawai yaga Abba cikin Shigar Suit bakake ya shigo office dinsa.
Cikin Rawan jiki ya mike yana rawan bakin Fadin"Abba.."
Abba bai damu ba shi da kansa ya samar ma kansa wajen zama Ishaq ya kasa zama Jikinsa ya fara rawa sai zufa Duk da sanyi A.c din dake Office d'in ya san mganar data kawo Abba. shi kuma Rabuwa da Fa'iza daidai yake da Lalacewar rayuwarsa gashi nan yanzu ko cikakken abinci baya ci,Badariya ta gama Hutunta ta koma kano,Zainab bata zaman gidan koma tana nan ba iya girki tayi ba Sai dai fa ya rika siya,me renon ne ma kan yi ma yara abinci da daddare in sun dawo makaranta shi kuma bazai iya cin abincinta ba,Kudinsu duk a Restaurant yake karewa wajen siyan abinci.
Sanda ya dawo din nan dakyar ya Lallashi su Anum da karyan Umman su zata dawo in ta gama karatun data fara,rigima suka yi masa sosai sai da yakai su gidan Anty Fadila suka yi weekend yace ta lallashesu sannan suka Daina rigima Allah ya taimakesa makaranta ya Dauke musu Hankali da kiran Umma,ammh Tabbas yasan Fa'iza ce ginshikinsa yau in da ta nan da da shi da yaransa basu taggyara ba.
Abba ya gaji da ganin Ishaq a tsaye sai ya karkace ya dauko karamar Jakar Briefcase dinsa ya zaro wata Farar Takarda, da Biro ya Sauke a gaban Ishaq Lokaci daya yana Fadin"Ka zauna mana"
Ya fada yana nuna masa wajen zama Jiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login