Showing 132001 words to 135000 words out of 288345 words

Chapter 45 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

713

ya jawo ma ka nan, kaje in ya cire hannunsa a kanka sai ka duka ka Dauka."
Anty Binta tayi tsaki kafin tace"To me ma ya kawo mganar ta ijiye aikinta ta dawo nan ta zauna..?in ta Dawo kana da wajen da zaka ijiyeta ne..?
Sakarci kawai achan ya baku gida ya Dauki dawainiyar su Farhan da komai nasu ammh baka gode ba sai ka Tsiro da wata mgana Saboda kada a zauna lafiya.?
Idanuwansa jajir ya dago yana fadin"Don Allah ya isa.Ya isa nace.."
Mama ta saki baki tana kallonsa Anty Binta tace"To dake ni don na fada maka gaskiya Ishaq dake ni nace"
Gefe ya koma yana numfarfashi Kafin yace"Bazan dake ki ba ammh bazan fasa fad'a muku wannan ba gaskiya muka taka ba.Ta yaya wannan abun zai yuyu Mama duk bayan fa Sati Biyu ina naga kudin motar..?
Bude bakin Mama sai cewa tayi"Ba ga matarka nan na sana'a ba. tana da kudi sai ta rika baka Lokacin da kake da shi taci gajiyanka yanzu sai ta rama ma kura aniyarta"
Ina duke ne sai da na dago ina kallon mama tako zabgmin harara tana fadin"Munafuka ta saka shegen kurman kunnuwanta tana ji tana Dariya"
Sai na maida kaina kasa na cigaba da aikin Gabana shiko a fusace yace"Sai kawai saboda ina jani talau saboda zuwa na ganta sai na rika karban kudin mota wajen fa'iza wannan wani irin mutuwar zuciya ce?Haba Mama ki ma bar wannan mganar bazai yuyu ba wlh na jawo ma kaina bansan haka abun yake ba"
Yafada cikin kosawa Mama tace"Da auran Zainab din ka jawo ma kanka..?kada ka manta sun maka komai..?
A fusace ya katse Mama da fadin"Basu min komai ba Mama don Allah ki Daina fad'in haka me suka min.?da girma na ya ganni aikina Bashi ya nemamin ba,Auran yarsa da nayi nawa ya yafe min komai sai nayi Mama Dawainiyarta da yake mgana yaushe ya farayi..?ko da take aiki duk watan duniya 100+ nake tura mata nata da na Hidiman yara in adalci zan yi kudin zasu isheni..?nawa nake turo miki ke da Fa'iza da Dawaniyar yara sai kuma don yanzu Kaddara ta hau ni sai afini nuna iko Kan matata da ya'yana wannan wani irin kaddararran aure ne..?
Ya karishe fad'a kirjinsa na Dagawa alamun bacin rai ganin ya birkice yasa Mama ta fara lallabasa tana fadin"Taho mu shiga ciki"
Kin shiga yayi ya cigaba da fadin"Meyasa kuna ganin gaskiya bazaku bi bayanta ba.?In adalci zai yi bazai min uzuri ba..?ko bai san bani da aiki ba ne yanzu zaune nake nima lalurorina Dauke min su ake yi bai taba Duba Lokacin da nake wata biyu har uku a Abuja ya taba? ko sau d'aya ya yi min fad'a cewa na rika zuwa gida akai akai ina da wata matar da ya'ya..?bai taba ba yana jin dadin haka sai yanzu don kaddara ta fad'amin na rasa aikina sai yace Dole duk bayan sati biyu sai naje na Duba yarsa..?bazan iya ba Mama wlh bazan iya ba gwara na zauna anan ko banza ina ganin gilmawar ya'yana da mahaifiyata tare da Matata,achan kuwa ban ma ganta ba yaran kuma basa yini a gidan ni kad'ai kamar maye ina musu gadin gida.wlh ban taba jin abunda nake ma Fa'iza Laifi ba ne sai yau kuma na Tabbata Hakkinta ne ya fara Bibiyata, na Danne mata tarin hakkokinta daya rataya a wuyana, ko da sau daya ban taba duba hakan ba nasani akwai hakkinta dake Bibiyata na sani har da Hakkin Fa'iza Mama"
Ya karishe fad'a kamar zai yi kuka ban taba ganinsa cikin rauni haka ba inaji ajikina kallona yake yi ni kuma sai naki Dagowa sai ma na mike na Sauke tukunyar zobon na shige Daki Hawaye suna cika kwarmin idona.
Rana ta farko da Yaya Ishaq ya taba Furta ya zalunceni ashe yana sane da abunda yake aikatawa..?
Maganganun sa ya sanyaya ma su Mama jiki shi dai ina ji ya shuru takalmansa ya fice daga gidan, su mama kuma suka shige Daki jiki ba kwari.
Ranar gidan haka ya yini ba walwala nice ma na dinga zirga zirgan girki da Hada zobo har na gama abincin na zuba ma su mama na sakamai na kai Dakinsa bai shigo ba,yara suka Dawo makaranta kusan Lokaci da'ya suka shigo da Hafsah daman aiki aka basu taje kaiwa sai kuma na fara Damuwa da rashinsa suna ta tambayan ina Daada sun leka baya dakin mama haka ma baya Dakinsa sai nace musu ya fita.
Wasa wasa Yaya Ishaq bai shigo gidan nan ba sai Dare,kafafunsa Futufutu daga gani tafiyar kasa ya sha abunda yasa ya warware da ya dawo Jamal ya iske ya dawo shiyasa ya saki ransa.
Ruwan wanka ma Amir ya aiko yace wai Daada yace don Allah Umma ki saka mai ruwan wanka.
Sai ya bani Tausayi na tashi na saka mai na kai mai har Tiolet din dakinsa na aika Amir ya kirasa,sai da na baro? ya shiga wankan nazo na gyara Dakin da Matarsa ta gama bata sa ammh bata gyara ba,araina in naji kamar tausayinsa zai yi min tasiri a raina,sai nayi Saurin na kauce ma haka sai wata zuciyar tace saboda su Amir bazan bar Babansu a wulakance ba.
Koda ya fito dakin Tsab ya ganshi? ga abincinsa a gefe,sai ya zauna gefen katifarsa yana fadin"Anya ban yi wauta ba..?
Ko dai dai bakin Baba ne ya fara kamani..?.
Ya tuna Baba yasha fad'amai ya rike Fa'iza Amana in ya wulakantata bai yafe masa ba,sannan yana tausayamasa ranar dazai san amfaninta lokacin kuma tayi masa nisa..'
Tuna haka yasa yaji hankalinsa ya tashi bayan fitansa bai san ina ya nufa ba shi dai yasan yayi ta gagari a gari inda yaga masallaci ya tsaya yayi salla yasha a ruwa karon farko da ya tsaya ya fara Tunanin kuskuran da ya tafka a rayuwarsa tun farkon auransa da Fa'iza har zuwa yau..?sai a yau yake jin tabbas zai iya yuyuwa girman hakkin Fa'iza ko Bakin Baba ne sune suka yi Zaren Dabaibayi suka fara taba Rayuwarsa. lalle ko in hakane ya zama Dole ya fara gyara mu'alamansa da Fa'iza ya roketa ta yafe masa kila Furucin Baba zai sake sa.
Yana cin abinci hawaye sun cika kwarmin idanuwansa Ya tuna burinsa na auran Zainab da ra'ayinsa sai gashi Burinsa bai masa komai ba, yau ta kawo Fa'izan da ya raina ya hantara ya wukalanta itace komai nasa ta dauki laluransa har da ta kannensa da ta mama daman Laluran ya'yansa tun yana da aikinsa ya bar ma Fa'iza ragamar komai kaicon sa"
Cokalin hannunsa ya sauke abincin kamar yana cin mgani kansa ya Dafe dake juyamin cikin Fitan Hayyaci yace"Innalillahi yanzu ya zan yi..?ta wata Hanya zan gyara kuskurena..?duk da tarin laifukana a wajen Fa'iza zata iya duba na ta yafe min..?
Tuna haka yasa yaji hawaye masu duni sun zubo masa yayi wauta rud'in duniya da Irin Tarbiyan Mama sun kai shi sun rabo duniya da mutanen cikinta sun saka ya hau keken bera ta kaisa tsakiyar kasuwar nadama ta gungurar da shi me Fa'iza tayi masa da ta chanchanci Tozarcin da ya shafe shekaru yana yi mata..?
Da wani ido zai kalleta sannan da wani yare ko harshe zai fara bata Hakuri ta sauraresa..?Anya Lokaci bai kure masa ba kuwa..?



*12/07/2023*
*8:00pm*
*Janafty*
[7/12, 10:17 PM] +234 906 320 7298: *KNKB2007*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*

Gabad'aya sai yaji abincin da yake ci ya koma masa mad'aci sai ya ture komai kawai ya koma ya kwanta rigingine,idanuwansa na kallon rufin dakin Lokaci d'aya rabin jikinsa da kafafunsa suna kasa ne daga kasan katifar.
tunani ya farayi tunda ga zaman Fa'iza a gidansu har zuwa Had'a auran su da Baba ya yi shi da Hajiyar Karofi abubuwan da suka faru,Zaman auren su da Fa'iza yadda ya tafiyar da ita da kyara hattara tozarci da cin mutumci,sai ya koma yana tambayan kansa me ye illah Fa'iza da ya tsaneta..?ko miye laifinta da yaki karb'anta a matsayin matarsa meyasa bai darajata ya karb'eta ya daidaita sahun ta da matan maza nagari masu takwallali da sanin ya kamata ba.?Sai yaga bata da wani laifi Fa'iza mai Hakuri ce Fa'iza mai biyayya ce Fa'iza mace tagari ce, burin kowani Namijin kwarai zamowarta baka ko mara kyan fuska wani abu ne na bangaran Halitta in da ya jata ajiki ya sota ya tattaleta ya tattali lafiyanta da jikinta sai Fa'iza ta Daukemin Tunanin kowata mace duniya. sai bai yi ba yayi fatali da Umarnin Allah ya toshe kunnensa da furucin Baba a kansa ya zauna da Fa'iza cikin Takura iko,Umarni da Bauta cikin Tozarci da cin mutumci har da wulakanci ya tuna yadda yake barinta da wahala kan cikinsa da kuma ya'yan da shine Silan fitowarsu duniya.
Ya tuna yadda ya kwallafa rai wajen ganin ya samu cikar Burinsa na auran mace mai kyau da gata da ilimi da nasaba, bai taba rokan zabin Allah ba shi dai kawai ya auri mace mai wadanan abubuwan sai Kuma ya basa,Domin ya jarraba imaninsa ya kuma sa ta haifa masa ya'ya daidai da Zabinsa sai kuma ya nuna masa ikonsa tunda ya auri zainab ba ga wani abu na armashi a auran shi da ita ba,sai dai eh! ya cika burinsa na auran mace mai kyau da nasaba ammh ba mutumci aciki ba ganin Darajan juna kamar yadda yake ganin yayi ma Fa'iza alfarma haka Zainab da Ahalinta suke ganin sun masa alfarma ya tuna yadda yake yi ma Fa'iza iko akan komai hatta akan ya'yan data Haifa ya tuna ya rabata da Danginta da yan'uwanta duk bata taba dagaa kai ba ,ya mu'amalanci yan'uwanta ta mummunan siga ba ta taba d'aga kanta ba,sai ya tuna Zainab gabadaya rayuwar auran su Mahaifinta ke jan ragamar shi sai abunda yace da shi Zainab take amfani in kuma yace a'a shi din banza bazata taba yin wani abu batare da cewar mahaifinta ba ko sanin ba,kan ya'yansa ma iko yake nuna mai babu shakuwa ta uba da ya'yansa tsakaninsa da su Fadil suna gidan iyayanta sai an ga dama ake kawosu ya gansu ko da yana garin in yayi mgana sai Zainab tace Daddy yace wajen sa zasu zauna gidan ba kowa Zuzu bata nan,A komai shi ke da ta cewa shi ya zama Hoto,yana Tuna sanda yake da kudi Fa'iza bata dora komai daga samunsa ba,ammh yau gashi ya rasa komai na shi biyar ma sha'awa take basa ta zauna da shi ahaka tana kuma Dauke da Laluransa ita wacce yake ganin ta fita ta kuma yi daidai da shi ta gujesa saboda bai dashi,bazata iya baro aikinta tazo ta zauna da shi ba sai dai shi ya bita,ta nuna mai daman ba sonsa take yi ba. Ta aure sa ne saboda kyansa da wani kyalkyalin duniya kamar yadda shima ya gina nasa auran ashe ba'ayi ma Allah Wayau..?
Ishaq yana da taurin zuciyar da ko abu ya damesa ba dai kaga kukan sa ba.ko mutuwa akayi sai dai yayi kukansa a boye ammh sai ga shi kwance Hawaye suna sauka ta gefen kunnuwansa duka biyu,suna jika zanin gadon dake jikin katifarsa zuciyarsa ta yi wani irin nauyi kamar ana yi mai wahayi haka abubuwan daya aikata suka rika dawomai Daki daki acikin kasan ransa fad'i yake yi"Allah na tuba. Allah na tuba ka yafemin"
Kansa yake girgizawa yana ji a ransa in ma Fa'iza bata yafe masa ba, bazai ga laifinta ba ammh baya raba d'ayan Biyu duk bala'in dake bibiyansa akwai Hakkinta,ya tuna sanda ya wulakan ta Mariya da kalaman data furta masa alokacin, ya tuna ta fadamai ko ba Hakkin Fa'iza ba,sai hakkin Zumunci ya tambayesa watarana. Ga shi tun ba'aje ko'ina ba ya fara gani rana tsaka aka samu saka Hannun Fidda makudan kudad'e bai san hawa ba bai san sauka ba,ya shiga matsala karshe bayan ya rasa aikinsa sai da ya rasa duk abunda ya mallaka Allah ya barsa da ransa ne saboda ya gane kuskusransa in da yaso gidan yari za'a kaisa ya kare rayuwarsa a banza.
Sai hankalinsa ya dawo jikinsa ya tuna ko abokansa yanzu da suka san ba shi da aiki sun gujesa tunda bai da shi bazai iya ma kansa komai ba ballatana su.hatta abokan aikinsa nachan Abuja bamai kiransa sun ma fara mantawa da shi, daman haka Duniya ta gada in yau mune to gobe fa wasun mu ne.
Bai taba daukan furucin Baba a matsayin wani bakar sarka mai wuyar warwaruwa a garesa ba,ya dauka tunda bai saki Fa'iza ba ya fita daga Furucin sa abunda bai sani ba Shi Furucin iyaye kan ya'yan su yana tasiri har mutuwar su Baba ya bashi Amanar Fa'iza sannan ya kakkausa mgana kan in ya wulakantata bai yafe masa ba shi ko adadin sau nawa ya wulakanta Fa'iza bazai iya sani ba..?
Zumbur ya mike kamar an tsikare shi da ya Tuna da shirmen da ya tafka na Jingine auran sa da Fa'iza tun kafin ya auri Zainab bazai manta ba tun a wannan Lokaci wani abu na auratayya bai kara shiga tsakanin su ba,Shekaru Biyar kenan Innalillahi ina zai kai girman hakkin Fa'iza daya Dauka..?bai taba Tunanin ita ma Mutum bace mai lafiya..?bai taba Tunanin zata shiga masifa da bala'i saboda jinginarsa ba..? Ya tuna Zainab macece mai yawan bukata har tama fisa shi wani lokacin,yana da Hakuri wani Lokaci ammh ita bata da Hakuri ta wannan Fanni shiyasa bazata yarda ya yi wata D'aya bai je ya ganta ba. Mahaifinta yasan zata cutu shiyasa ya Tsaya mata Ita Fa'iza wa take da shi da zata kai masa kukan ta ya tsaya mata..?
Sai kamar ana gayamasa da kansa yace"Allah.."
Shi ya tsaya mata"
Hannayensa duka biyu ya saka ya Tallafe fuskarsa yana jin kamar ya fashe da kuka,Sai dai duk abunda ya faru da gudummuwar Mama yasan ita din uwa ce garesa da bai da kamarta ammh ta bada gudummuwa wajen kara karkatar da Rayuwarsa zuwa hawa kan keken bera in da tana ankar da shi ko in yayi ba daidai ba ta yi masa Fad'a da bai kai haka Lalacewa ba.Sai ya tuna Baba lokacin yana gabda rasuwa yake mai fad'an ya zama adali sannan magidanci mai kyautata ma iyalansa,Kada ya biye ma Mahaifiyarsa wajen kuntata ma Fa'iza kada ya manta marainiya ce bata da kowa kada ya wulakantata domin mace ce tagari ce in ya rasata ba lalle ya samu mace kamarta ba.
Kamar karamin yaro haka ya dinga rera kuka yana fadin"Ka yafe min Baba..Ka yafe min Baba na Tafka kuskure ka yafe min"
Shi kad'ai haka ya dinga sambatu? Daran nan barcin sa rabi da Rabi ne da asuba Dakyar ya iya tashi fuska da Idanuwansa sun kumbura saboda Damuwa da suka dawo masallaci sai da Jamal ya tambayesa ko zazzabin ne.? yace ya warware saboda Mama ta sanar da shi lokacin da yayi rashin lafiya.
Daki ya sake komawa ya kwanta yana Sake saken yadda zai fara gyara mu'amalan sa da Fa'iza sai dai ba shi da wannan kwarin gwiwa yana tunanin bama ita ba ko waye yaji abunda ya faru zai yi tunanin Saboda yanzu ba shi da shi ne yaga amfani Fa'iza ammh har ga Allah daga daran jiya zuwa wayewar gari zuciyarsa ta cika da Fa'iza sunanta alherinta,Sanyin ta,Ladabinta da Hakurinta kaunar ta Kunyar ta,had'e da nauyinta sun hade masa waje d'aya sun ki barinsa yayi wani sukuni tunda ya dawo masallaci bai bari sun hadu ba ya shigo Daki,Wajen Mama kadai ya leka suka gaisa.
Gani yayi har bakwai ta gota kuma yaji hayaniyar yara afalo suna ta shirin Tafiya Makaranta,Sai ya mike Dakyar yana rawan jiki ya kwashi kular abincin jiya da ta kawo mai da Kofin ruwa,ya fito falo ya iskeni ina Ta fama da Musty wajen saka masa Rigar makaranta Hafsah? Lahadi ne tana gida ita ke Kitchen ta na yi musu abun kari Amir ya shirya tuni shi yake taimaka wajen shirya Ahmad Anum kuma ta shiga Daki neman Hijabinta bata gani ba ,Dagani har yaran Hankalin mu yayi gaba bamu san fitowarsa ba sai da Anum ta fito daga Dakin su tana ganinsa ta bude murya tana fadin"Daada ina kwana"
Muryanta yasa duk muka Dago muna kallonsa Amir ma ya saki Ahmad yana gaida shi ya amsa yana ta sakin fuska kamar an saka shi Dole sau daya na kallesa na kauda kai na,Musty na saki ina fadin"kullum kai ne rigimamme ko Ahmad ya daina rigima ammh kai babban kwabo baka daina ba"
Ina shirin nace Amir ya karbi kayan hannunsa sai naga yaje ya karba ya wuce kitchen shi kuma ya kariso falon yana fadin"Musty na ne Umma ke ce ma Babban kwabo..?
Ya fada yana daukan sa,Ahmad na ganin haka shima ya fara zillo sai ya koma ya zauna yana fadin"To karfin Daada kuma ya kare"
Duka suka hayesa ya dauke su yana Nishi suna Dariya ni kuma sai na Duka ina kwashe kayan da suka cire ina shirin gaishe shi Saboda na Dauka zan gansa cikin wani yanayi sai naga ya ware kamar jiya baya cikin Damuwa ba zato kawai naji muryansa yana fadin"Ina kwana Fa'iza.."
Dankari makari mamaki ya cikani sai naji kamar ban ji daidai ba,na juyo ina kallonsa kai tsaye ya sake fadin"mun tashi lafiya ya kwanan yara..?
Yadda ya kafeni da ido ne yasa bakina na rawa nace"la.lafiya ina kwana"
Da Sauri na wuce dakin yaran har ina cin Tuntube wajen waigensu to Allah na Tuba abun ne naji sa wani bambaramkwai namiji da suna Hajara ban gama mamaki ba sai da naga Hafsah ta zubo musu taliyar data dafa musu ya zauna kasa a cikin su yana bama Ahmad da Musty a baki in Anum ta bude sai ya saka mata Amir kuma sai yace"Daada kai ma bude baki na baka"
Sai ko ya bude baki ya basa,mamaki ya sandar dani wani abu ne da ban taba gani ba ko a baya,zai dai dauke su yayi musu wasa ammh wahalar su kan bai sani ai abun mamaki na gaba sai da suka gama,Shi ya tarkata su yace zai kai su har makaranta,Saboda Halin Rayuwa yaran ma sun koyi hakuri ba kullum suke tafiya da abinci ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login