Showing 135001 words to 138000 words out of 288345 words

Chapter 46 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

734

watarana ruwa ne sai ranar da na samu ciniki sosai har da Lemu ina siyan musu, yau ma nayi niyya ganin shi zai kai su sai na bashi naira Dubu nace ya siya ma kowannen su Lemu da biskit.
Bai yi min gaddama ba ya karba yana fadin"Ni kar na siya ma kaina Umma?
Sabon salon nasa ne ya girmeni sai na wuce kitchen ina fadin"Kaima ka siya"
To fadan da yafi karfinka ai sai ka maida shi wasa,ina cin abinci ya shigo nayi mai sannu da zuwa na bude baki na ce abincin nasa na Dakinsa sai kawai naga ya tankwashe kafa a gabana ya zauna ya tsoma min hannu acikin Farantin da muke ciki ni da Hafsah ta tashi taje ta Dauko mana Ruwa ne.
Baki na saki hade da Hanci ina kallonsa shiko ko ajikinsa Hankalinsa kwance ya fara ci a baya nasan Halin Fafansa,Ko abinci ban taba gani yaci da Hannu ba, sai da cokali ammh yau da Hannu yake ci har yana sude hannu,ganin haka yasa na tsame hannuna zan yi mgana yayi saurin tare ni da fadin"ki ci mana Fa'iza. ko baki son ci da ni ne.?
Kai na girgiza ina fadin"Aa tare da Hafsah muke ci"
Kafin yayi mgana ta fito Dauke da Ruwa itama ina gani ta saki baki taga bakon abu,yana ganinta ya Dago yana fadin"kin ji Hafsah jeki zubo naki kici ki barni na samu Ladan cin abinci da Matata yau"
Kalmar Matata din ne na rika nanatawa kaina ya yi wani dum sai ya kasa Dauka duk da yaso na sake naci abinci da shi,sai na kasa saboda abu ne da ban saba gani ba.
Kai ranar naga abu ni Fa'iza Shigowar Jamal ya ceceni suka zauna afalo suna Hira ammh Fita goma shiga goma in na dago idonsa na kaina mamakinssa ya cikani kamar wamda yayi gamo..?
Ashe wasa farin girki tundaga ranar Yaya Ishaq ya sauya daga Ishaq din da na sani ya koma wani mai sanyi mai kula mai tallali,yanzu ya daina zama in dai yana gidan komai zan yi sai ya taimakamin yara ko da nayi musu wanka shi zai shirya su ya basu abinci ya kuma kai su makaranta,Ko gyaran Daki nake yi sai yazo ya amsa ko ya fara tayani tun yana bani mamaki har yazo ya daina bani.
Sai wani kafa kafa yake yi dani wanda sam wannan Sabon dabi'an nashi bai burgeni ba domin nafi sabawa da wanchan Ishaq din,Ranar kwana Biyu Tsakani na fito da wankin yara kawai shima ya fito yace zai tayani jikina ya fara rawa kada Mama ta fito ta gan shi na shiga uku.na fara Hada sa da Allah ya bari yace bazai bari ba, sai kawai na sakin masa wankin na koma gefe ina kallon sa.
Ganin haka yasa sai jikinsa yayi sanyi ya ciro hannuwansa a ruwa yazo kusa dani yana fadin"To na bari shikenan..?
Ajitar rai na sauke ina fadin"Kana so ka jamin fad'an Mama ne in ta fito ta ganka kana wanki..?
Na fada cikin fargaba har ga Allah yanzu ina gudun abunda zai sa a tozartani.
Sai kawai ya koma ta bayana bakinsa gabda kunnena yana fadin"Ina ruwan Mama don ishaq ya taya Fa'iza wankin kayan ya'yan su"
Jikina ya fara rawa nayi gefe ina Haki,sai ya bini da Dariya kafin ya shige Daki ya juyo yana fadin"Yau ba zobo ne da kunin aya kuma..?
Ina zama kan kujeran tsugunno nace"akwai sai na gama zan Dafa kunin Aya kuma sai Hafsah ta Dawo"
Ni dai har na gama wankin nan Ina auna wasu abubuwan a fili na furta"kamar wanda akayi ma wahayi'"
Jamal Sati daya yayi mana ya koma makaranta, ni na basa kudin mota,da na kashewa Anty Binta ta hadamai yan kayan abinci,Ya tattara ya koma makaranta yanzu kam ina samun ciniki sosai,Har ta Badariya ni nake bata na mota da na laluran makaranta,Da dawaniyarmu na yau da kullum ba domin sana'ar na ba da Tuni asirin mu ya tonu.
Yanzu in ina aikin Zobo haka Yaya Ishaq zai fito yace sai ya tayani ko nace ya bari bazai bari ba.sai na basa wani aikin zai kyaleni,sannan yanzu ya samu wata banzar Dabi'a ya rika shigemin yana so mu rika hada jiki da juna to banzan dabi'a mana yaushe jikina ya zama abun sha'awa a wajen sa da zai zo ya na rab'ata,da na ga haka sai na rika kauce masa ammh sai naga kamar bai Damu ba sai ya nuna kamar bai gane ba,yanzu ko Hafsah bata nan yana tayani zuba zobon a gorina ko ya wanke min Aya Mama dai bata taba gani ba sai ranar aiko tayi ta fad'a daga karshe ta fashe da kuka tana fadin"Shikenan Fa'iza kin asircemin D'a ya zama bawanki.Allah ya isa tsakanina da Dangin Sidi da tamadina sai mun yi shari'a da su ranar gobe kiyama"
Raina ya baci saboda ta kira iyayena a Kabarin su sai na kallesa Idanuwana sun ciko da kwallah ina fadin"Kagani ko sai da nace ka bari.nasan Halin Mama ga shi yanzu ka janyo ma iyayena Zagi suna kwance a kabarin su"
Ba zato kawai naji ya mike ya rikoni ban tsinci kaina a ko'ina ba,sai akam kirjinsa ya Rumgume ni dukkan mu sai da mukaji wani abu kamar wuta ya jamu Mama daman tana gama fadin mganarta ta shige daki tana cin mutumcina,Tuni naji na gigice na fita Hayyacina,da gaggawa na turesa na fizge jikina ina numfarfashi sai naji abun yazo min kamar daga sama wai Yaya Ishaq ni ya Rumgume..?
Hawaye suka zubo bisa kumatuna sai ya miko hamnu zai share min,na matsa baya ina fadin"Me ye haka..?
Bai damu ba,sai yayi mirmishi yana fadin"Hawayen da na yi sanadiyar fitar su zan goge miki"
Wlh sai mganarsa ta bani dariya,har sai da na dara ganin ina dariya sai shima,ya biyemin yana Dariya ni ko baisan shi nake yi ma Dariya ba Sabon acting din nasa ne naga bai Dace da shi ba.
Acikin Satin sai ga Hajiyar Dala tun da muka yi Hijara bata taba zuwa ba har muna neman wattani shida Mama ta jata Daki ana ta Labarai,duk yadda suke da Mama bata kwana ba,Sai yatsina take yi,Ta shiga har Dakina ta gani duka sai wani yamutsan fuska take yi,ishaq na gida ta kallesa tana fadin"Shikenan Ishaq ka dawo zaman gidan aiki dai shuru..?
Yana zaune kan kujera yace"Wlh Goggo a cigaba da tayamu da addu'a"
Mama na daga gefe ita ta rakota ta tabe baki tana fadin"Ba shiyasa nake masa fad'a bai ji ba,Mahaifin zainab wlh tsab zai sake nema masa aiki ammh ya Tsaya yana shiririta ko da yake an mallakesa ya zama mai Duran zobo da kunin Aya"
Hajiyar Dala tace"ke ko ta ga yana gida sai zaman kashe wando mana. Ya koma chan Abuja ya zauna nan din ai kina nan sai kiga in ana ganin idonsa an fi saurin sama masa aiki"
Mama tace"Gayamai kila yaji ki"
Hajiyar Dala ta wuce tana fadin"Ishaq kayi ma kanka fada dai"
Daga haka ta fice Mama tabi bayanta shine naga ya Damu ammh ni ko agefen gyalena guga daman suka tarar ina yi sai na zama kurma na nuna musu kamar ban ji su ba,shine bayan fitar su ya zabga tagumi.
Na zata wani abun arzikin Hajiyar Dalan ta kawo maman,ashe kwalin Taliya da macaroni ne sai kudi da ta bata naji tana fada ma D'anta,Tundaga Lokacin sai na daina Bashi Fuska,da ya fito zai karbeni aiki zan yi tuku tuku da rai sai jikinsa yayi sanyi shi da yaransa dai sai son barka ya maida kansa kamar wani kaninsu, ya Lura sun fi shakuwa dani fiye da shi,sai yake neman shima su fara wannan Shakuwar da shi ni baisan adadin Shekarun da na kwashe ina bama ya'yana Lokaci ba ne.
Alhamdulillah da duka ni'imarsa gareni Domin kasuwar Turarukaa sun bud'emin Sanadin Turaren da Hajiya ta saka na hada ma Diyar kawarta Laila ta Kaduna,sai mutane suka rika gani suna suna yaba kamshi ina ta samun ciniki ba abunda zan ce ma Hajiya sai godiya ta aikomin da kayan sawa ni da yara na dauka Gogan zai yi fada sai naga har da shi ake duba kayan ana murna,na kirata nayi mata Godiyan kayan da kuma Godiyan Yayan mijin Laila da sanadin laila taga Turaruka na,suka burgeta ta aiko na had'a mata na Dubu hamsin kwallacha da Humra,kuma na samu alheri sosai da ita naji dadi ko da yaushe in nayi sallah sai nayi ma Allah Godiya sannan na gode ma Hajiya tare da wadanda suka yi sanadiyar tsayuwana da kafafuwana.
Ishaq ya kafe bazai rika bin Zainab Abuja ba,mama ta kasa tankwasa shi ga shi mahaifin zainab ya kara kiran mama yayi mata gargadi mgana har Yamai sai ga kanin Mama da kanwarta Hure sun zo shi ya yi ta ma Ishaq Fad'a akan meyasa zai bijire ma mganar Mahaifiyarsa Dalilin daya sa ya yarda zai je kenan ammh sai yace bashi da na mota kamar Dole aka Turo mota tundaga Abuja tazo ta Daukesa.
Ina Daki ina gyara kayan Dirowa ya shigo da Jaka a hannunsa daman tunda naga zuwan su kawun yamai nasan za'a rina.
Kusa dani ya zauna ni kuma sai na zame na sauka kasa bai damu ba yace"Zan tafi Abuja fa'iza"
Kai Tsaye yaji nace"Allah ya kiyaye hanya a gaida zainab da yaran"
Sai yayi shuru ya kasa mgana ni kuma bana son muna kebewa a daki mu kadai sai na dakatar da abunda nake yi na mike zan fita karaf ya riko Hannuna.
Sai naji wani iri na ratsani na juyo da Sauri ina kokarin kwace hannuna sai ga shi ya mike gabda ni yana fadin"Ki kula da gida da yara"
Ina kwace Hannuna da ga rikonsa nace"In dai wannan nan ba sai ka bar min Sallahu ba kaima kasan aikina ne"
Ina shirin fita ya kira sunana ina Juyowa,har ga Allah bansan ya taso ba sai ji nayi ya sakar min sumba a kumatuna na gefe????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  n dama Lokaci d'aya yana fadin"Fa'izan Ishaq ki kulan min da kanki"
Har ya fice ina binsa da kallo Gabadaya sai da gabban jikina suka yi sanyi zuciya bata da kashi,sai ga shi na yini ina tuna yanayin da na shiga da ya sumbaceni sai da wata Zuciya ta ankar da ni da fadin"A kul din ki Fa'iza ki tsaya iya matsayin ki"
Sai nayi kokari na yakice wannan Tunanin Lokacin Hafsah taje korafi ta kwana Biyu sai ni kadai sai yara suma sun ji ba Dadi da baya nan Anty Hure kuma ta nan tare damu Badariya yanzu tafi zama gidan Anty Binta.
Azumi ke gabato mu ina ta kokarin na siya kayan zobo da kunin aya masu yawa tunda nasan in Allah ya Budamin zan samu ciniki sosai a raina na guduri niyar ba Jamal ba Har Yaya Ishaq sai nayi ma kayan sallah ko guda D'ai d'ai ne ya'ya na ko sai na gwangwaje su da ikon Allah.
Yaya Ishaq sai da yafi sati uku sannan ya Dawo,Namiji kenanbyana baya son zuwa sai gashi ya shantake har da kiba yayi,Sai da ya dawo yana min dadin bakin cewa mganar neman aikinsa ce ta taso shi shiyasa ya tsaya,ni ko bi ta kansa ban yi ba,tunda ba sabon abu ba ne, Ba laifi wannan karon yazo da kudi har ya siya mana kayan abinci,ya rage rabin kudin makarantan yara daman na biya musu rabi sai ya cikasa.
Watan azumin Ramadana yazo,ba laifi albarcin watan alfarma mun samu tallafi Goggo ta aiko mana da Buhun shinkafa da taliya da su garin Danwake garin kuni,taliya yar murji,Ni kuma da abun da nake da shi na shiga kasuwa nayi mana kananun Cefane Mijin Anty Binta ma ya bamu gero da shinkafa da siga,Bamu da matsalan abinci a lokacin sai godiyar Allah, Anty Asiya ta aiko min da yaji da kori da Shadda na Ahmad kala biyu,Ganin mun samu rufin asiri bangaran abinci sai na maida hankali ga sana'ata da azumi na chab'a ciniki sosai Hafsah ke taimakamin tare da yara saboda basa makaranta da azumi.
Da kudin ciniki da na tara na azumi. na siyan mana kayan sallah da ni da yara nayi ma Hafsah kala da'ya da ita da Badariya na yi ma Jamal shadda shi da yara sai kuma Yaya Ishaq na siya masa nasa shi kad:ai daga gidan Hajiya aka aiko mana da Naman sa mai yawa ana gobe salla da Sakon kudi dubu Hamsin muyi Hidiman Salla kamar nayi kuka ni da ya'yana mun zama abun son mutane ban tsinke ba sai da Raliya ta kawo kaya masu kyau na mata na Anum in ji Laila Daga kaduna.
Sai ga Mama bakinta Gum ba karofi Tunda taga an rufa asiri har da ita ake cin arzikin,Anty Hure ma tana nan a wajen mu tayi azumi har ta zobo da kunin aya suna sha har suyi kyauta dashi, daga karshe ce min tayi zan koya mata,tana so ta siya komai anan in taje chan ta gwada nace mata toh.
Ana gobe sallah na ba ma Mama kayan sallarta da Jamal har Anty Hure nayi ma Turmi,Mama ta karba a reni ko saka albarka bata yi ba,Jamal har daki ya biyoni yana godiya Yaya ishaq bayan ya gama ganin nasu Mama da yara bayan ya shiga daki na Dauko nasa na bashi duka an dinka,Hafsah ta ba wani dan ajin su yana dinkin maza ya dinka musu,suna mutumci da mai dinkin ne.
Sai kawai Ya rumgumeni yana fadin"Nagode Fa'iza Nagode kwarai. Madallah da Fa"iza..Fa'iza matar Ishaq"
Da wayau na zame jikina daman ina so nayi mai mgana kan Zainab Saboda ina jinsu tana ta kiransa baya son daukan wayarta, kan mganar zuwansa da azumi bai je ba Mama kuma tamai mgana bazai saurareta ba.
Sai nayi amfani da wannan damar na sako mai mganar shuru yayi yana kallona kafin yace"kina so naje da sallah ne ke kuma fa da ya'yana..?
Sai na jinjina kai ina fadin"itama ai matarkace tana da hakki akan ka, sannan itama tana da ya'ya suma kuma suna da hakki a kan ka"
Kawai sai ya kuramin ido yana kallona kafin ya kama hannayena duka biyu ya rike lokaci daya yana fadin"Wata irin zuciya Allah ya yi ma Fa'iza..?
Sai nayi mirmishi kai tsaye nace"Zuciyar hakuri da Takwali ne"
Sai ya girgiza kai yana fadin"Da kuma zuciyar? Diomod wanda samun mai macen aure irinta acikin maza dubu sai mai sa'a Fa'iza"
Sunkuyar da kaina nayi ina jin jikina na yam yam! saboda yadda yake murza yan yatsuna,sai kawai naji Tattausan muryansa gabda kunnina yana fadin"Zuciyar Fa'iza me hakuri ce zuciyar Fa'iza mai biyayya ce da yafiya Allah yasa zata iya yafe ma Ishaq gigimemen laifin sa a gareta?
Dagowa nayi ina kallonsa muka yi ma juna kir,kallo ne yake min cikin wani yanayi dake kassara zuciyar ko wata lafiyayyar diya macen da aka zaunar da ita, ana yi mata irin wannan kallon da Ishaq Kabir karofi ke bi na dashi"







*Janafty*


*KNKB2008*

*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*

Ba iya kallon dake narkar da zuciya ba,Sai da ya had'a da langon Matso da jikinsa yana gogan jikina lokaci d'aya da Numfashinsa yana sauka a dokin wuyana,sai suka taimaka wajen fitar dani daga Hayyacina har ina shirin manta matsayina?ballatana da naji yadda hannayensa ke kara kaina acikin Hannayena.
Ban dawo Hayyacina ba sai naji mganarsa a dokin wuyana gabda da bakina yana fadin"Fa'iza zaki iya yafe ma Ishaq.?zaki iya basa rayuwarki a karo na biyu..?
Kamar an dawo dani cikin Hayyacina haka na zabura na mike jikina na rawa,yana shirin riko ni na fizge hannuna na fice daga Dakin da Sauri zuwa Dakina,bai biyo ni ba ina tunanin Saboda ganin yara ne,ni ko gado na na fada ina kokarin daidaita kaina Sai kuma daga baya naga wautata na manta matsayina ne da zai rudeni na saki jiki..?
Meyasa sai yanzu yake tunanin yayi min laifi yake neman gafarata..?
Ko ya manta nice dai Fa'izan da ya sani yar gargajiya kurma mara ilimi da gata baka mummuna ko ya manta wad'anan nakasun a tare da ni ne..?
Sai naji bana son na fita mu kara haduwa,Na shige daki duk hayaniyar yara da buruntun su naki fitowa ina jin su afalo yana ta sha'aninsa da yara da Hafsah sai washegari Ranar idi muka had'u shima gaishe shi kawai nayi sai ya amsa yana wani kafe ni da ido nayi saurin kauce ma kallonsa.
Da shi da yaran suka shirya gabadaya har da Jamal,sai a ranar naga ya Dawo da gayunsa sai dai ba kamar da ba,da zasu tafi masallaci muna tsakar gida muna tuwon Shinkafa miyar agushi ni da Hafsah ban sani ba naji ya karkato wajen kunnena yana fadin"Ishaq na jiran wankan sallar Fa'iza domin ya tanadar mata babban Tukwaici"
Sai na tsorata garin juyowa saura kad'an na fada tukunyar miya ya saka Hannu ya tareni yana fadin"Ki kula da kada ki yi min asara"
Sai na sunkuyar da kai ganin Hafsah na Dariya sai ya bi bayan su jamal yama Fadin"Hafsty ki kular min da matata kada ta fada cikin miya ta ragemin kara'in da na shirya mana da sallar nan"
Har ya fice ina kara jinjina mamakinsa,Hafsah ma ta kalleni tana fadin"Naji dadi Yaya fa'iza yaya Ishaq ya sauya kamar ba shi ba"
Saboda bana cikin yanayin mgana yasa ko tankata ban yi ba.
Ba su jima da fita ba muka gama komai ni na wanke tsarkar gida Hafsah tayi wanke wanke,Ni nace taje tayi wanka na fara gyaran Dakin data gama ta shirya sai tazo ta karbeni itama Goggo ta aiko mata da kayan salla na kala Biyu.
Ba domin ya roka ba sai domin daman nayi ra'ayin cin kwalliyata da gumina sai na saka wata karamar super waz din da na siya ta Dubu Goma sha biyu,mai kalan ja da fari dinkin riga da zani ne ammh rigar fited ce ta kama jikina Dam na saka Sabbin Dan kunne da sakarna da abun Hamnu,Ban yi kitso ba sai dai na wanke kaina na tufke Hafsah ce zata min kitso kuma bata samu damar min ba, saboda layin yan lalli taje karofi tayi gabda sallah ta dawo wajena Anum kad'ai tayi ma kitso,ni kuma aiki yayi min yawa ballatana daman ni ba yar kwalliya bace.
Ko kafin su dawo na aika ma da Mama nata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login