Showing 261001 words to 264000 words out of 288345 words

Chapter 88 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

720

kuma ina son zuwa,tsaikon ma da na samu Anty nasara ne suka dawo sun yi tafiya zuwa kasar Ghana inda dangin mijinta suke wajen watanta uku duk bata nan ma akayi aurena dayake kuma na tayata gyara gida da sauran su.
itama da taji abunda ya faru tamin murna balle da taga yadda bini bini muna manne da Tosin di'na a waya yana min hira ina Dariya sai ta tsinke da lamarin balle kuma wajen kwana uku nayi a gidanta yana ta magiyan kada nayi aiki duk nagaji so yake kafin ya ganni na zama Tife, din gaske ina jin haka na mika ma Anty nasara wayar suka gaisa kai tsaye yace"Gaskiya Anty ki yi hakuri anemi wacce zatayi aikin zan biya. ke kinga ya kyautu ango na wata duniya yana kuma son in ya dawo yaga amaryansa tayi bulbul tayi kyau sai kuma ya ganta duk a jime..?
A yankwane..?
Anty Nasara na dariya tace"Ina fa mu kanmu bazamu so haka ba. zamu fi son ka ganta shar da ita ai mu a dad'in mu ne"
Yana yar dariya yace"To ina godiya Anty daga gani kina so kanin naki ya zuba shagalin sa"
Haka ya saki jiki suna ta Hira sai da suka yi sallama ta bani wayar kawai sai yace"Gaskiya Anty nasara dagani yar kara'i ce ita"
Dariya na tsintsire masa sai kuma ya rage murya yana fadin"Ke kuma saura ki fad'amata sirri ne dai tsakanin amarya da ango"
Aiko muna gama waya na gayamata ta sha dariya kafin tace''Ya ko fad'i gaskiya yar kara'i ce ni kuma zan mara masa baya ya yi kara'i"
"Masha Allah Fa'iza Wlh nayi miki murna kin samu miji irin wanda kowacce ke fata,ina miki fatan wannan kaunar da yake miki har tsufan ku"
Na amsa mata da Ameen ina bata labarin irin halin Engr da kuma inda yace zan zauna da garin su da zamu je su yi nasu shagalin.
Cikin sanyi na nace"Ni fa ina so na zille wani irin shagali Anty nasara kamar wasu yara..?
Anty nasara ta ballamin harara kafin tace"Ke dallah ja chan daman nasan sai kin taba halin wlh sai mun yi shagali zuwa Benue ba fashi muma mu ci zani da alaku mu saje cikin yarbawa sai kiji akaro na tashi bazaki ganemu ba"
Tana dariya ina Dariya ta cigaba da fadin"Kuma wlh gyara zaki yi malama na jiki da chan kasa gwara dai a gyara mai yaji dadi.ttunda shima yace yana son ya yi shagalinsa"
Ina rufe ido nace"Anty Nasara kada ki lalatani"
Duka ta dakamin tana fadin"Shegiya ki gwale kafa ki haifi ya'ya har hudu kike kiran zan lalataki. ?
Kaji min wani iskanci wajen Fa'iza..?
Ina dariya ban ce komai ba nasan ko na bude baki na shekara ina mgana ba wanda zai yarda cewa ban san komai a harkan auratayya tsakanin miji da mata ba. shiyasa nake mamakin yadda su Anty Mariya suke rawan jikin gyara Saboda maza ina mamakin me suke ji..?domin mganar gaskiyan bansan dadin da suke mganar ana ji ba.
Shiyasa ni wlh ban damu ba. shima Engr sai dai yayi mganar zai yi kara'i ammh wani mganar daya danganci haka bai taba hadamu ba.
Anty Nasara tayi ta bani shawarwari tana ta nanata mganar gyara nace mata Ammi nachan na jira tayi dariya kafin tace"Shikenan ma nasan Ammi bata da wasa mu in kin raina mu ita kaniyarki zata ci"
Kamar ko ta sani Ammi akwai wasa da Dariya ammh in taci Serious kowa shiga taitayinsa yake yi.
Engr na da saura kwana goma ya Dawo Abba ya turo Direba ya Daukeni zuwa kaduna ina zuwa Ammi Daman na jira na turarukan wuta da Humra da kwallacha tace ni zan yi ma kaina Dilka da Halawa kuma tace na hada ruwan yin sa akwai wacce zata zo tamin har gida.
Abba kuma mun zauna da shi kan mganar kayan daki nace Engr bai min mgana ba sai yace na tuntubesa saboda aje a jeramin komai a muhallinsa da na yi masa mgana sai yace"Matas rabu da Abban naki kawai duka gidajena ba abunda babu ina kuma zai yi tunanin saka wani kaya ban da rigima..?
Alamun dai baya bukata ina fadama Abba yace"A'a kamar kowacce y'a kema haka zan yi miki ya ware cikin gidajensa ya fadi in za'ayi miki jere ni zan ma kirasa da kaina"
Ai ko an sha muharawa kafin yace ayi amfani da gidansa na malali,duk da shima bangare daya akwai Furnutures,Bangare dayan ne ba komai aciki za'a gyaramim.
Shima yana korafin wai Abba ya ki ya Fahimcesa ni dai na samu na lallashesa ya hakura.
Kudin kayan lefe kuma 500k ya fara turomin tun yana chan ni da Ammi mukaje kano muka yo siyayya,kaya ba ni da kaya ba aakwatina biyar ta siyamin,muka siya kayan da zan fita tarewa da shi da duk abunda bukata Gidan su Ammi muka kwana washegari mukaje gidan Yaya Asiya muka gaisheta taga kayan tana ta saka albarka sannan muka dawo kaduna.
Engr an ce yana da kudi ammh har ga Allah ni baya nuna min yana da shi,in zai min abu daidai misali yake yi min.
Domin Ammi ma da nace mata Dubu Dari biyar ya turomin sai da tayi mamaki har tana fadin"Ko dai yace sai ya dawo zai cikamiki..?nace bansani ba,ni kuma ba kudinsa nake so ban damu ba wlh.
Muna ta shirye shiryen mu Tunda su Goggo sun ce sun barma Abba azo nan a Dauke ni,Anty Fadila tace sai tazo itama sai na roketa akan ta yi ma Baban su Anum mgana ko zai barta ta tahomin da ita.
Tace min zata tuntubesa taji a bakinta nake karajin yasha jinya kwanciyarsa asibiti biyu bayan wanda na sani,duk ya rame ya lalace a kaina tace min har ita yasha fad'amata cewa rashina gibi ne babban ne a rayuwarsa.
Ni ko sai dai fatan Allah ya sauwake domin bani da abunda zan yi masa.
Fatana Daya Allah yasa ya bar Anum din tazo domin zan ji dadin zuwanta.
Kayan Furnitures kuma Abba ya ba ma Ammi kudi anan kaduna ta siyamin komai da komai,masu kayan sukaje har gidan suka shirya komai Tare da Raliya da su Nana khadija ni dai ban je ba ina gida an faramin Dilkar matar na zuwa tamin na rana ni na goga ma kaina na Dare.
Kayan mata kuwa musamman Ammi ta saka aka kawomin kayan sokkoto na tsumi na tsugunne ga gumba ga garin aya da ake sha da madara.
Sannan ga saiwar Gudayo ta hannun Surayya marubuciyar Halin yau.
Ina ta sha wani yana da dadi wani kuma daci sai na Daure nake iya shansu.
Sun dawo suna santin gidan mai kyau Falo biyu Bedroom hudu sai Kichen sannan kowani daki da Tiolet,kuma ko'ina yaji kaya Abba ya kashemin kudi domin kayan alfarma ya yi min kayan kitchen kuma Ammi ta siya sauran su zannuwan gado kuma Nana Fatima tayi su cafets kuma da sauran kayan kamshin girki abubuwa Anty Fadila zata yi.
Hajiyar su Raliya ma ta aikomin da su Dinner sets masu kyau da kofunan shan Tea sai Kayan adon mata na kwalliya kala kala da kayan gyaran fata da na gashi.
Ina da kudi ammh basu barni nayi amfani da kudina ba komai su suka yi min yan'uwana kuma kudi suka hada suka siyamin katon Showglss na Turare sannan suka siyamin Turaren da kwalaben batare da sun fadamin ba,bayan wanda ni na hada da kaina Har hawaye sai da nayi Goggo kuma kayan dake dake tayi min irin su Kuka,daddawa kubewa kayan kamshi,sai kuma suka yi min kayan gara ita da mallam hatta Yaya Abdul'ahad dake chan sai da ya Turo kudi Ammi ta siyamin Dan kunnayen zinare masu kyau aka yi ci ko da sadaki na aka siyamin masu sarka har da awarwaro.
Badariya ma da mijinta ba'a bar su a baya Tv suka siyamin da Freezer babba,Sai frem masu kyau na kwaliyar Daki,Mama ma ni da kaina na kirata na fad'amata ta rika sakamin albarka da fatan zaman lafiya Anty Binta ma ta kirani tamin Fatan alheri har da Halisa rayuwa kenan.
Jamal kuma har kaduna yazo ya yi min murna ya kuma bani Dubu ashirin gudumuwa yana ta bani hakuri nace masa bakomai nagode da farko kin amsa nayi sai da ya nuna bacin ransa sannan na amsa.
Engr na da wata daya da kwana Biyu ya sauka Nageria ta lagos dagachan ya hayo jirgin Abuja.
Kwana daya yayi yazo kaduna ganina Karo na farko da jikin mu ya hadu waje daya domin ina shigowa falon Abba a bazata ya tashi ya Rumgumeni wata irin Rumgumar da ban taba sanin ana yin ta ba.
Rumgumar da har ya tafi ban daina jinta ajikina ba.
Mun fi minti goma ahaka kafin ya sakeni ya dago kaina yayi min kiss a saman goshi kafin yace"Kin yi kyau'"
Kuma ba kwalliya nayi ba,Nadai sha gyaran fata da jiki nayi walwal ina tahin kamshi.
Bai jima ba daman tsaraban America ya kawomin sai mganar wad'anda zasu bi ni zuwa Benue daganan su rakani Abuja,Sai nace zan musu mgana abincin ma da nayi masa kadan yaci kamar yana sauri ashe kada ya yi kara'i ne tun agidan Abba sai da ya tafi ne ya kirani yana Fadin"Kamshin ki ya yi min Dadi Faa'iza. na kusa na turmusheki a falon babanki wlh"
Kunya duk ta kamani bai damu ba ya cigaba da fadin"Wlh na kosa na ganki gani ga ki, na kosa Tife na"
Ni kaina na kosan duk da bansan yanayin abun ba ammh ina son sani ko ba duka ba sai dai kunya yasa ban furtamai ba.
Ammi na fada'ma yadda muka yi ita kuma ta kira su Goggo suka Tattauna an Tsara tafiya da Yaya mariya da Yaya Asiya tunda yace akwai motoci ba matsala,sai Ammi su Nana khadija na gida suna jarabawa Anty Fadila zata zo sai Nana Fatima,Anty Nasara,Anty Amina matar Yaya isa,Badariya sai Raliya da Hajiyar su itama tace har Benue zata rakani. sannan na kira Sa'adatu na fad'amata tace min zataje itama sai ni mu sha Biyu kenan Goggo tace ta wakilta Ammi itama ai uwace sai Halisa da itama Daga baya tace zataje har ma na fad'amasa yawan Mutanen sai kuma Goggo ta kira tace Hajiyar Dala zata je.
ina ji nace gwara taje taga komai duk da nasan abunda zai kaita kenan.
Kai duniyan nan akwai mutanen da duk Daukakan da zaka samu bazasu ji suna sonka ba.
kuma bazasu bar adawa dakai ba, to irin su Hajiyar Dala ce.



*Janafty*



[8/1, 5:16 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3017*


*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Dole akwai wasu kayan da za'a bar su a gidana na kaduna,shiyasa Ammi da rakiyar su Nana khadija suka kara komawa suka kai tunda akwai key din gidan a hannun su Ammi.
Kaya kad'an suka ragemin wad'anda zan sassaka in mukaje chan sai turaruka da kayan kwalliya sai kayan gumbar mata na tsimi da Saiwar kazan da na siya wajen Surayya Halin yau,ta kuma yi min alherin turrukan wutan ta masu kyau da kamshi,Sannan har da garin daka na sha madara ko nono.
Gaskiya Surayya ta na da kirki da iya mu'amala sosai na ji dad'in huld'a da ita,kayan ta kuma masu Inganci ne.
Kazan saiwar nan ina fada muku duniya ce.
Tun zuwan nan da Engr ya yi bai sake dawowa ba. aiki ya yi masa yawa yana Edo sai dai mu yi waya ni da shi duk tsaren tsaren ta waya muke yi.
Ranar alhamis ya kama tafiyarmu Abuja tunda yaso mu fara ta chan Benue din ne ammh sai Sweetheart tace tare zamu tafi saboda haka mu fara sauka ta nan sai a wuce gabadaya.
Ni kuma ranar Talata da Safe naje nayi gyaran kai Steaming akayi min tunda ban saka mai ba.
Mai kitson su Ammi tazo ta yarfamin shi 2step kanana masu kyau,Ranar laraba kuma nayi kunshi Baki da Ja,a baya ina Dauka kunshi bai dace dani ba tunda ina baka ammh sai ga shi an yi min kuma ya fito ras har ya fi ma na Bikin Yaya Abdul'ahad kyau da fitowa ko don yanzu na kara haske ne sannan Fatata ta Murje tayi kyau. kamar bani bace Fa'iza nan ba sannan kuma nayi Dilka da Halawa,sai yanzu na kara yarda da mganar Hausawa da sukace in kana da kyau to ka kara da wanka to in baka da kyau in ka kara da wanka sai kayi kyau din.
Engr sai min santi yake yi,yana jadaddamin ayi min zanen kunshi mai kyau in ya gani zai ba da tukwaici,shi a chan Benue zamu hadu tunda shi yana Edo Bazamu had'u da shi a Abuja ba Motoci kuma daga ma'aikan su Abba aka bamu manyan motocin su mai cin mutane sha takwas guda daya,Tare da Direban su shi zai kaimu har Abuja.
Naso naje karofi nayi ma su Goggo sallama ammh ban samu dama ba, sai dai mun yi mgana ta waya kuma nasan Daga baya in nace Engr ya kaini? bazai ki kaini ba.
Tun ana gobe tafiyar masu harama suka zo,har da Hajiyan Dala tunda ta kwallafa rai sai tazo,Su hafsatu suna ta bakin rai bazasu samu zuwa ba. Yaya Mariya nayi musu dariya har ga Allah na cire rai da zuwan Anum tunda ban ji Anty Fadila tace min komai ba,Sai dare ta iso Lokacin an gamin min lalli har na cire nayi sallah ashe jirgin yammah suka shigo abun mamaki sai gata da Anum,sai D'iyarta Falaq sa'an Anum din sauran suna gida saboda makaranta.
Sai gani ga Anum baki har kunne muka Rumgume juna tana Dariya tace"Umma.."
Irin cikin mamakin nan nima sai na Dago kanta ina kare ma girmanta kallo yarinya ta kusa ma kereni a Tsawo Cikin Dariyan jin dadin ganinta Tsab cikin kamala na ja kumatunta ina fadin"Anum d'in Umma"
Hannayena ta kama ta kallo sai kuma ta kara kallona kafin tace"Umma kin yi kyau kamar ba ke"
Sai na kara Rumgumota ina jin wani farinciki na ratsani ba wamda ya nemi takura mana muka shige daki ina ta faman tambayanta ya sauran yan'uwanta ina su Mama da Antyn su..?
Tace min duk suna Lafiya Anty ma ta bada sako ta kawomin yana cikin akwatin Anty Fadila Allah Sarki daman tace min zan ga sako,bazan mata da alherinta ba taso zuwa ammh awajen aiki ba'a bata dama ba.? har ina mata tsiyan ko megidan ne ya hana cikin Dariya tace"Wlh ya barni maman Amir daga wajen aikin ne. Ai yanzu Honey ya sauya sosai wlh,Karin ma barina da yayi yace in mun had'u na kara roka masa gafaran ki"
Ni ko kai tsaye nace"Bai min komai ba na yafe masa"
To ashe sai da ya kara aiko Anum,Takarda ce karama fara ya bata ta tura cikin sikat dinta rubutun Hausa ne layi biyu yayi aciki.

"Ki yafemin Fa'iza. Daga karshe ina yi miki fatan Alheri da rayuwa mai inganci. fiye da yadda kika samu a zama na tare dake"

"Ishaq sidi karofi"

Sai naji? Tausayinsa kad'an ya kamani yaga Takardan nayi ban ce komai ba Anum tace"Umma ya ki ka ga yaga..?
Sai na kalleta kafin nace"Bata da amfani Anum. na yafe ma Daadan ku ko Saboda ku! Allah ya yafe mana Gabadaya"
Sai ta rumgumeni tana fadin"Yauwa Umma daman ai Allah na son mai yafiya ko..?
Sai na daga mata kai ranar dai uwa da y'a tare suka kwana har abinci tare mukaci bini bini tace Umma kaza tana kuma nane dani ranar ma ko waya bamu yi sosai da Engr ba jin Anum tazo kai tsaye yace"Ah'a muna da babban bakuwa to bari Baba ya daga ma yarsa kafa. na ara miki kanki ki kularmin da Diyata Sosai"
Bai kuma hakura ba sai da na bashi Anum suka gaisa cikin sakewarsa kamar yadda ya Saba Radam ya rike sunayen su Amir yana ta tambayanta su Daya bayan Daya sannan ya tambayeta karatu tana bashi amsa daga karshe yace sai sun hadu a Benue.
Bayan sun yi sallama ta bani wayar nima bamu jima ba muka yi sallamar ina sauke wayar Anum tace"Umma Sabon Baban mu yana da kirki"
Kai na daga mata ban yi mgana ba,Sai da Safe ne Anty Fadila ta kawo min Sakon Zainab a wani kwali ne ashe Sleeping dress ne kala uku masu kyau da Tsada sexy na rike baki ina mamaki da na kirata in yi mata godiya sai tace"A sa ayi ma Yallabai kwalliya da shi. Don Allah white din nan ranar First nigt zaki saka shi"
Kunya ma ta bani ina yar Dariya nace"First Night sai kace wasu yara"
Shewa ta saki kafin tacr"ke kika san wannan, namiji baya tsufa ko shekara Dari yayi zai yi shagalinsa ni dai don Allah ki saka maman Amir ni fa a yar'uwa na Daukeki kin sani"
Sanin Halin nacinta yasa nace mata zan saka mun jima muna taba hira kafin tayi mana fatan isa Abuja Lafiya sannan muka yi sallama.
Duka shiri ake ta yi,su Ya Mariya da Anty Nasara sun fi kowa zumud'i tun asuba suka shirya karyawa ma sama sama suka yi nima nayi wanka cikin kayan lefena na saka Abaya doguwar Riga sukayi suka yi na yana mayafinsa naki na zuba Hijabina fari har kasa,sannan na fesa turare duk inda na Gifta ina tashin kamshi.
Anum ma da Falaq sun yi wanka sun saka kaya iri d'aya na wani leshi sun saka mayafai sun kyau kamar yan Biyu.
Mota bata zo ba sai karfe sha daya na Safe tun safe da muka yi waya da Engr ban sake jinsa ba. nima da zamu tashi na kirasa bata shiga sai nayi Tunanin network ne.
Motar nan gabadaya ta Daukemu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login