Showing 222001 words to 225000 words out of 288345 words

Chapter 75 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

703

sun je ziyara karnukan sun biyo su uwa da y'a sun ware kafa suna gudu"
Na fad'a har ina kara Dukawa ga waya rike a gefen Kunnena na Hagu karamin Tsaki Goggo taja ta sakarmin Labule tana fadin"Shine abun dariya..?Allah ya shirya ki Fa'i"
Ina jinta ammh na kasa daina Dariyan da nake yi ina jin Anum na fadin"Umma bafa abun dariya ba ne Anty Badariya har fad'uwa tayi ta gurje Gwiwa"
Ina so na bar Dariyan na kasa cikin Dariyan nace"Garin ya kika bar uwar taki a baya..?
Cikin sauri tace"Umma ni ban san ta fadi ba ina ta gudu ban juyo ba sai da na kawo kofar gida"
Dariyan na cigaba da yi domin ta kasa tsayawa,Badariya ta karbe wayar cikin muryan Tausayi tace"Kai Anty Fa'iza ina fada miki duk na kurje kafa kina Dariyan mugunta..?
Ina Danne bakina nace"Waya aike ki..?ai sai da mijinki ya hanaki nima kuma da kika fad'amin sai da nace karki je"
Kamar tayi kuka tace"Wlh don Allah naje mata barka ko Anum?
Bansan me Anum tace mata ba ganin yadda take mgana kiris tayi kuka yasa? na danne dariyata ina Fadin"Hakane ammh dai da kin ji mganarmu da haka bata faru ba,ba sani nayi ba ammh nasan da gangan ta saka a sakar muku karnukan nan"
Badariya na ta jinjina kai kafin tace"Tayi ma kanta Anty Fa'iza ni dai Allah yaga niyyata"
Jin haka yasa nace"Allah ya baki lada
Sannu .Anum ta Dafa miki ruwan zafi ki gasa kafar in taki sai kuje ko Chemist a duba miki.
Da haka muka yi sallama ina cin dariyata a raina.

? Wattani biyar baya muka sha bikin Badariya tare da mijinta Alhaji Yusuf mai kudi ne shaharareen dan kasuwa mai harkan Safaran motoci daga kasashen waje zuwa Nageria,asalinsa Haifaffan Azare ne dake Bauchi uba da uba ammh kasuwanci yasa suna zaune a cikin garin Bauchi sai wasu dangin dake azaren.
Ganin Farko soyayyar Badariya ta shige sa mai zafi a Lagos ya ganta yaje ganin motocinsa da suka sauka ta Jirgin ruwa ita kuma ta fito daga kasuwa suka had'u,Yana da mata d'aya ya'yansa Biyar kuma cousin dinsa yake aure,Badariya ta karbi Yusuf ganin yadda yake kaunarta Saboda Allah sai dai kafin auran su an sha Fama Tunda fafur mahaifiyarsa da Danginsa suka ki amincewa da har mganar ta sha ruwa, sai daga baya Babban yayansu da Dangin Mahaifinsa na azare suka zo har Karofi nema ma Yusuf auran Badariya.
Shagalin Bikin da komai a katsina aka yi shi Tunda Ishaq ya siya gida ya gyara shi an zuba komai lokacin Bikin aka fara amfani da shi,na daki kirji na nuna ma Duniya ni yayar Amaryace ko da aure na ya kare tsakani na da Ishaq na shiga sha'anin sosai ba Domin kowa ba sai domin Badariya,ba kuma don taimakon da tayimin ba a'a ta kaunace ni saboda Allah,ni na siya mata Fridge,sai tv da Tv Stand sai cafet d'an Italiyan sannan nayi mata Turaran wuta na itace kwallacha da Humra,na kashe mata kudi ban san iyakaba sannan nayi mana Dinki ranar Bikin muka saka ni da ita Kowa ya ganni a wannan Lokacin da rayuwa ta sauyamin Gababadaya ya san ba waccen Fa'izan daya sani ba ce
Fa'izan yanzu ta kama kudad'e a hannunta sosai ban sauya ba ina nan a Fa'iza ta y'ar gargajiyata ta. su Nana Fatima har sun gaji da magiyan na rika kwalliya sun kyaleni kayan kwalliya kuwa ko an bani sai dai su Hafsah su mora,bayan Shigata makaranta yanzu haka muna matakin Haddan Izifi Hamsin sauran mu izifi goma? mu sauke,Tunda daman nayi sauka haddan ina wani bangaren sai ya kasance kamar tishi nake yi.
bangaran islamiya kuwa mun yi nisa tuni mun gama wasu littafan mun Dora wasu,Sana'o'i na na rike sune suka zame min kashin takawana bayan Abba ya kasance bango gareni.? Bayan girke girken da nake yi yanzu na suna ko biki ko walima ko wani Taro a biyani ina aikin Dambun nama ko na kaji Dari ne a biyani ladana,ga Dilkar amare da Halawa,ga aikin Turareka na amare da matan aure ga Zobo da kunin aya domin ban daina ba Sai dai bayan ma'aikatana jummala da Laure a kallah yanzu mata masu min aiki ina Biyan su sun yi goma sannan ga almajirai masu Hidimam wanke wanke na manyan tukwanen abinci da kuloli,kaf Karofi ,Dutsemah,katsina kano,kaduna da kewayanta sun san Fa'iza mai Turaren kamshi ko SAFMA,tunda har lokacin ina Buga Sticker kuma ina amfani da ita a Kwallaben Turaruka na.
Ina da karfin jari a hannuna wanda Abba ya bani sannan ga Ribata shiyasa kafin Lokaci na sha kwana na mallaki kudad'en da ban san adadin su ba,Ni mutum ce mai kyauta hannayena suna Bude ne sannan ina yawan Sadaka da kyautata ma mutane ko matan da na Dauka ko da yaushe cikin min godiya suke yi na taimake su wasu mazajen su ba sana'ar sai wahala ni ko ba iya albashin ki ba in aka samu babban aiki aka biya da tsoka nima nakan yi musu ihisani.
Kuma ban bari hakan ya taba karatuna ba in ba na gida aka kawo aiki duk sun iya jummala da Laure suke jagorantan komai, in na Dawo sai dai na Duba kawai na dan gyara wani waje a ajin Haddamu ni kadai ce babba sauran duka matasan yara ne,Ammh kwakwalwata naja tunda na saka abun a raina gwara ma ajin islamiya tunda ta matan aure ne akwai sa'i'o na da ma wad'anda suka girmeni ana ta gungurawa tare,Duk da ban yi karatun boko ba ammh yanzu ina jin kananun kalmomin Turanci sai dai in turancin yayi tsawo sannan na iya Lissafi ba Dole ma na iya ba Tunda na kama kudi a hannuna.
Hatta su Yaya Asiya Abba ya basu manyan jari a hannunsu,sannan mazajen su ma bai barsu haka ba Mijin Yaya Asiya yayi mai hanya yanzu Vice principal aka basa ita kuma mijin Anty mariya aka kara ma kasuwancinsa jari Hafsatu kuwa ta zama yan kaduna wayayyiyar mace mai ilimi da gata sai kace ba ita ba. ita da Karofi sai dai da Hutu ko wani sha'ani.
Ba wani abu tsakanina da Ishaq tun abun da ya faru tsakanin mu lokacin da yazo inaga ya Hakura ne,sai dai ina waya da ya'yana ko da yaushe,tun kuma daga Lokacin bamu kara haduwa ba sai a bikin Badariya bai min mgana ba ni kuma sai na gaishesa Darajan zumunci ammh bai amsani ba araina nace kan ka akeji,a sha'anin nan ko Zainab Mama bata rika sakata cikin lamarin bikin? kamar ni ba, komai sai tace a yi ma Fa'iza mgana,Hatta da Anty Binta rayuwa ta saka tayi sanyi yanzu mijinta yayi Ritire ba wani arzikin yanzu Halisa kuma kannen miji da yayyinsa sun hanata zaman Lafiya. sau biyu tana samun ciki suna barar mata da shi,Duka sau biyu ga na miji ga na Danginsa igiyar aure saura d'aya kuma yaki ya saki duka Halisa ta rame ta Lalace kamar ba ita ba,Duk kushen Hajiyar Dala da Kallon renin ya'yanta yanzu sun san a inda suke yi,Sun kuma gane muma mun sha kwana Fiye da yadda suka sha barin ma ni shigar alfarma da kaya masu Tsada sai dai su nuna min kwalliya da gayu, yar wayewar nan ma ai muna da ita daidai gwargwardo.
Kafin bikin Badariya su Amir sun zo min sun min hutun azumi har salla tare dani suka yi naji dadi matuka,har da su Farhan tunda ko'ina daman tare suke zuwa har yau ban taka kafata Lagos ba har kuma karin girma mijin Anty Fadila ya samu aka had'a walima ban je ba su Ammi sun je tare da su Nana Fatima. har da Hafsah sun kuma Biya sun ga su Amir suka dawo da labarin kyakyawan rayuwar da yaran ke ciki.
Mama na tsaye kan su ita da Ishaq zainab kuma ba'a sakata a lissafi Fa'iza ma da suke kira islam gida take barinta Mama da Shema'u na jigilan wahala da ita.
Yanzu haka Amir he is now 16yr kuma ya gama Jss zai shiga SS section ne ita kuma Anum she is now 14yrs Tana bauchi wajen Badariya ta roki yayan nata yasa an kaimata ita hutu da sun koma zata shiga Jss3 ne Musty kuma he is now 12,da wani abu kuma ya gama primary zai shiga Jss1 Ahmad ne ke matakin aji shidda a primary yana da shekara goma a duniya yara tuni sun biyo tsawon kafan Ubansu, sun zama manya barin ma Amir wlh in mukajera sai ace kanina ne to an fada ma Lokacin da suka zo min Hutu kowa ya shiga ya gan su in Goggo tace ya'yan Fa'iza ne sai an tsaya kallona barin ma Amir da ya fini Tsawo Anum haka ni ko yar karama jikina ba Kiba sai murjewa,Amir yana kara girma Hallayansa na bayyana shuru Shuru marason Hayaniya sai dai baya Daukan Reni yadda yaran ke tsoron sa ko Babansu basa tsoro haka, tsawa kawai zai Daka musu yanzu nan zasu shiga Taitayin su duk rashin jin Farhan da Ahmad kuwa basa rawan kai a gaban Amir hatta ko da Anum da suke sako baya mata da wasa ni ko sai Hakan ya yi min dadi na tabbata watan watarana Amir ne duka Uban ya'yana zai iya karesu a duk inda rayuwa ta kaisu addu'ata kullim Allah ya raya su ya shiryamin su.
Da bikin Badariya ne naga Anum har ta fara kirgen Dangi da na gani sai da gabana ya fadi,araina ina fatan Tsarewar Allah a kan y'ata sai dai Hankalina ya kwanta da Badariya ta tabbrtamin da bata fara? Jini ba.
Sannan karin salama ta weekeed gidan Anty Fadila suke saboda Hadda idonta na? kansu a gida daman basa Fita suna gida,Mama kuma na lura da su ga Amir sannan ga Jamal duk da shima ya koma kano da zama da taimakon Abba ya samu aiki da Hukumar Wutar Lantarki na jahar kano chan yake zaune yanzu har ya siya motar hawa sai dai in ya samu hutu yana chan Lagos din yayi achan.
Tsakanina da Zainab har yau bata sauya ba,Muna zumumci mu ko nace kawancen mu har gobe ko fad'a suka yi da Ishaq sai ta nemi shawarata ni ko da zuciya daya nake bata shawara duk da sai a Hankali tana son mijinta shi kuma ya riga ya gama Sarewa da ita ana dai lallabawa kawai,Ko shi bata Fad'ama ta saka Tsarin iyali ba ammh ni ta fadamin saboda tace bazata iya wahala ba ga fita aiki ga yara sai kace ita ke kula da su yaran da ko cikakken minti goma bata zama da su in ta Dawo aiki d'aki take shigewa ta kwanta, Mama ce kan yaran Don ma Allah yasa ta Dauko Diyar Anty Hure daga yamai tana taimaka mata da girki da gyaran gida shema'u kuma taji da Hidiman yara.

Har yau kuma Badariya bata daina Fadin hakkina ne ke bibiyanta ba, Saboda tun auranta itama bata Huta ba Uwar miji ta sakata gaba da Farko gidanta ya gina mata ita kadai ta tare ni kuma har Bauchi sai da na raka Badariya ni da Raliya dake fama da Laulayi Lokacin ammh tace sai taje Badar ce fa,Dayake wanchan cikin fita yayi sai a lokacin Allah ya bata wani haka muka dawo muna santin gidan Badariya sai ga shi ba'a rufe wata ba ta kirani tana kuka tace uwarsa tace zata dawo gidan da zama bazai yuyu a bar ma Badariya katon gida ita kadai ba, ada tana gidan yayan sa a zaune ne ammh Saboda Jaraba ta dawo gidan? Badariya ta shiga takura mata,Ahalin ga uwargidan chan a katon gidan da yafi na Badariya tana watayawa.
Saukin Badariya daya Yusuf na sonta ammh fa basu samun sakewa kuma daman ba mazauni ba ne yana yawan Tafiye tafiye,Badariya na yawan kuka da abunda Mama ta min ne itama ake yi mata na yarda da Haka ni kaina nasan Mama ta zalunceni ta kuntatamin fiye da Tunani sai dai na yafe mata har ga Allah ita kuma Badariya koda yaushe ina gayamata tayi Hakuri jarabawarta kenan
Wannan hutun da Anum taje mata ne Uwargidan ta Haihu zataje barka mijin yace ta bari ya dawo taki jin maganarsa.
Ta Saka Anum a gaba sukaje suna zuwa ta saka aka sakar musu karnuka suka Dawo gida a jigace.
Badariya ta fadi ta Kurje gwiwa shine Anum ta kirani tana bani Labari ina Dariya,Dariya ta yadda Anum ta fi uwarta gudu Naga kuma Badariya bata da wani jiki sai dai in itama aure ya Bud'ata ne.

*****
Yau ina da aikin Dambun kaji guda ashirin,Shiyasa na fito duk da ma'aikatan sun zo har sun tafasa kajin,Da Goggo naci karo a falo tana Faman tsinke zogale sannu nayi mata ta amsa tana Fadin"Kin gama Dariyan kin fito kenan?
Mirmishi nayi ban yi mgana ba Goggo tace"Gwara da kika fito,.Duk da sun iya ammh ki fita ki Duba musu"
Da toh na amsa mata sannan na fita suna Tsakar gida suna cire naman suna rabasa da kashi suna ta Hiran su ina fitowa suka dago suna gaisheni. duk da mun gaisa da wasu daazu Jummala ce ke nuna min abunda suka yi na jinjina kai kafin nace"Indo da Zainabu su yi daka yau,Maman Jamilu da Laure su yi Suya matsewan kuma su Auwalu sai su tayaku ni da jummala Zamu hada kwallacha ne"
Da toh suka amsanin ranar yini muka yi wannan aikin daga karshe sai da nazo na kama musu wajen matsewa yana da wahala ne sai dare na samu kaina nayi wanka nayi sallar Isha'i girki ma Goggo tayi ranar.
Badariya na kira naji ya jikin nata sai take cemin sai da taje chemist yanzu kuma uwar mijin tace sai ta koma gobe karya take makirci ne bata son zuwa ammh karnuka basa komai,ganin tana neman yin kuka yasa nace"To kin gayama Yusuf din..?
Kai tsaye tace"Na fadamai komai shima ya kirata ya ce mata bana jin Dadi ta bari ya dawo, ammh ta kafe sai yace nayi hakuri naje in na isa gidan agoben kada na shiga na kirasa zaisa? azo a shiga dani"
Jin haka yasa na shiga Lallashinta ina nuna mata tayi addu'a Allah zai kawo mata mafita domin naga ranar addu'a Allah na rike shi kuma ya taimakeni.
Kafin mu gama waya na tambayi Anum ban ji karadinta ba tace min tayi barci a raina nace su Anum an ji maza yau dole ayi barcin wuri.
Washegari Aikin abincin biki garemu na Gidan Alhaji Sabo Dutsenmah wani mai kudi ne Tunkunya lamba Talatin talatin hudu muka yi biyu Jalop din shinkafa da kayan lambu Daya Priderice ce.
Da wuri muka gama suka zo suka Dauka na saba musu daman girki kudina ta banki suke turomin,Shiyasa ban damu ba da yake ma sunana suka sani da gidan mu ba ni ba,ba fita nake yi ba in nayi nisan fita gidan Yaya Mariya ko gidan Anty Nasara ko gidan su Yaya isa doguwar tafiya sai ko kasuwa katsina dai ina shiganta Tunda Ga sa'adatu ga Habiba,Frezer dina da na siya sabuwa tsohuwar ita na bamawa suna ta godiya ita da Haruna ni ko kaf yanzu ban da wata kawa kamar Sa'adatu kano ma ina shiga siyan kayan hadin turaruka in ban samu wani abun a katsina ba.
Shima bana kwana Saboda karatu da ayyuka na ko Dutse sau daya naje wajen Nana Fatima na kwana Biyu kaduna kuma B'arin Raliya mukaje muka Dubata muka dawo aranar Ammi ce ke korafin bana zuwa ammh Abba ba ruwansa tunda yace ya yi min alfarman na zauna a karofi bai kara tada mganar ba.
Goggo ma tayi ta k'orafin naki zuwa kaduna nayi? ko sati ne,Sai tace in aiki ne ga su jummala ai sun iya komai ga waya ko ba na nan za'ayi komai ni ko sai nace mata"Karatuna fa kin fa san Hadda baya son yawo goggo. Ki bari ai mun kusa gamawa in muka gama zan je sai su Ammi sun gaji da ganina"
Kyaleni Goggo take yi Tunda tasan ni da Kafiya ko kan zawaran dake sintiri a kaina ban taba Fita ba kuma fa da Likaf nake yawo da dogon Hijabi ammh har ake zuwa kirana Mallam ko maza sun fi biyar da suka mai mgana masu tarin mata da yara ni. Har a ga Allah a cikin raina ban dauka bayan mutuwar aure akwai mazan da zasu fito su ce suna sona ba. In ban manta a yadda Ishaq ya sha kusheni ba. ban dauka ina da sauran amfanin da wani namiji zai ganni ya yaba ba,ammh duk da haka ban yarda na ba ma kowa fuska ba.

Goggo tayi ta fad'an ba kyau abunda nake yi. ni dai na kyaleta har k'arata takai wajen Abba wai haka zan zauna nufina bazan kara aure ba Abba ko yace ta kyaleni yanzu Hurumin su tursasamin nayi aure ba na su ba ne,
Su barni na samu natsuwa Daganan ne Goggo ta shafamin Lafiya ammh Har Baba Ati da Inno da suka zo sai da na kosa su tafi Saboda yadda suka Dameni kamar ina kan su ne.
Ni aure yanzu ko sha'awa baya bani mazan ma sun fita raina kuma nasan har da kudin da na ke kamawa a Hannun yasa suke Kara kaina akaina Tsabar ma renin wayau har da mijin Ma'aikaciyata Zainabu da Farko Godiya yace yazomin kan daukan matansa da nayi ashe ba haka bane. sai naga ya zake abun ma sai ya bani Dariya wai me maza suka maida mata ne..?na lura gabad'aya maza Halinsu daya shiyasa nayi musu kullin Goro na tattara su na ijiye na cigaba da kasuwancina.
Anum ta gama Hutunta a Bauchi,Daga chan Badariya da Mijinta Suka sakata a jirgi suka maidata da kansu,da kuma godiya da farko sun so su turata ita kad'ai ne Ishaq yace kada su fara yi mai wannan ganganci su saki kamar Anum ita kadai a jirgi daga Bauchi zuwa Lagos.
Dole suka shirya tafiya suka kaita,kwana Daya suka yi suka dawo duk da yaso su tsaya su huta mahaifiyarsa ta hana dole dai suka Dawo kuma bai jima ba ya sake wata Tafiyar ya bar Badariya cikin Takura da Tsamgwaman uwar miji da yan'uwanta.
Haka dai rayuwar ta cigaba da gangarawa da dadi ba dadi,Koda yaushe muna waya da Badariya tana Fadin Halin da mahaifiyar yusuf ta sakata aciki ni kuma ina bata baki Shudewar wattani biyu mun yi nisa a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login