Showing 117001 words to 120000 words out of 288345 words

Chapter 40 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

722

mai mirmishi kawai ban ce komai ba araina ina jinjina yarinta Amir ne kadai yasan halin da ake ciki Anum kuma uwar Shiriritace Dadi suke ji ganin har da Mama ta Dawo gidanmu da zama basu Dakinta basu Shashen da muke basu tsakar gida suna murna,Abu daya yasa gidan ya sakeni Burgeni akwai ruwa sosai domin akwai Famfo a tsakar gida, sannan suna da wuta kamar anguwan da muka taso,sai dai ita wannan anguwan tafi cika da mutane daidai misali ba kamar na masu? hali da dukiya ba.
kwanan mu biyu a gidan sauran kud'aden da suka rage Hannun Yaya Ishaq ya yi mana siyayyan kayan abinci da su, da suka dawo siyo cefanen kayan abincin.Dakin Mama suka sauke komai ina cikin Dakin yaran ina gyara musu kayan da yake duk an hada kayan ne waje da'ya basu raba musu ba, ni kuma da na samu natsuwa sai na zauna ina ware ma kowa nashi ina saka musu a inda ya dace.
Sai ga Anum tazo kirana in ji Daada na kalleta cikin mamaki sanin baya nan tun safe ya fita cikin yanayin mgana nace"Ina Daadan yake..?
Kokarin hawa kan kayan da nake kan gyarawa tayi na hanata ina Hararanta sai ta juya tana Tura baki kafin tace"Yana Dakin Mama"
Jin haka yasa na tsaida abun da nake yi na fita falo na Dauki Hijabina Hafsah na zaune a kasan cafet tana Duba Littafinta Amir na gefenta kamar yana gane me take rubutawa na Fice ina fadin"ina dakin Mama"
Suka bini da toh da sallama na shiga,Na iske Mama zaune kan kujera jamal na gefenta yana danna waya Yaya Ishaq na nesa da ita ga kayan abincin nan a falon ta Badariya bata nan taje gidan Anty Binta da Safanan.
Har kasa na duka na gaida Mama da gida ta amsa a Dake kafin ta kalleni tana fadin"Kayan abinci ne ya rikita da Sauran kudin da suka rage a hannunsa ya siyo.Shine yayi mganan za'a sauke a bangaran ki zaki rika Dafawa kina bamu nace ya kiraki gaki ga shi ga ni,ki fad'a da bakin ki in zaki iya dafa mana abinci kina bamu bana son abunda raina zai rika baci Daga baya"
Kalamanta sai suka bani mamaki na Dago ina kallonta shima na juya muka Hada ido sai ya Dauke kansa nima sai na maida kaina kasa cikin Ladabi nace"Ai mama ko ba na auran Yaya Ishaq kina da hakkin da zan dafa abinci na baki indai muna zaune waje d'aya bakomai bazai gagara ba, da yardan Allah"
Kai ta daga sama kafin ta karkace kai tace"Shikenan a kwasa a kai dakin ki"
Har na mike zan fice tace"Sai a bi a hankali kin dai gani ba irin baya ba ne lokacin da akwai, yanzu babu. sai kiyaye da barna Ahto"
Ban ce komai ba na fice a raina ina mamakin Mama yadda bata kaunar taga na zauna lafiya cikin Aminci sai ta Kirkire wata mgana da zata zama cin Fuska a gareni.
Jamal ya shigo da kayan ina Dakina Hafsah ta leko tamin mgana nace ta gwadamai inda zai saka su,Ita ta nuna mai Store ya shiga ya jera komai ba wani abun sakawa a fridge sai kayan miya,sai kayan lambu da suka siyo ba su da yawa,Tun daga ranar ni nake abinci Safe da rana da yammah har Dakina nake? kai ma su Mama cikin wata Cooler mai girma yadda zai ishe su ita da jamal da Badariya,Ni kuma na ji da Yara sannan da Babansu kamar yadda wahalan komai nasa ya dawo wuyana yanzu tunda yana gida bai fara fita ko'ina neman aiki ba, kamar yadda yace zai fara fita ya gani ko za'a dace.
Da kaina na shiga makotan mu gidajen da ke kusa damu muka gaisa na gabatar da kaina a matsayin makotan da muka dawo anguwan cikin Satin da ya gabata, na daina barin kaina Cikin Duhu tunda na san shiga mutane nada Dadi ban kara yarda na zauna agida ba.
Duk kuma inda na shiga sai yi musu tallar ina Saida zobo da kunin aya, sannan ina hada Turarukan wuta na Daki da Humra da kwallacha sannan ina Dilkar Amare na gyaran jiki,Sai girke girken suna biki ko walima na kuma ce su min tallah wasu har suna tambayata ko akwai zobon nace ban fara ba tukunnah,sai mun natsa agidan, sannan sun tabbatar min da zasu siya Insha Allahu sai naji dadi kwarin gwiwa ya shigeni Duk daman masu sari ta wajena basu hakura ba sun ce duk inda nake zasu biyo ni su siya Saboda inganci zobo na da kunin Aya na.
Su Anum sun koma makaranta ba nisa da safe ko Yaya ishaq ya rakasu su tsallaka titi ko Jamal,watarana har Amir ko Hafsah,Amir ne kadai ke gida shi da zai fara Junior section ga ba kudi ammh ina iya bakin kokarina ina so ya fara zuwa da wuri kafin wannan zangon karatu na farkon ya kare.
Muna da Sati Biyu da dawowa Sabon Muhallin mu na cigaba da sana'ata Ranar tare da su Hafsah da Badariya suka taimakamin muka hada zobon da kunin Aya,ta waya na kira masu sara,bayan yayi sanyi chan da yammah suka zo suka Dauka Mama sau daya ta leko komai batace ba ta tabe baki ta koma ciki Sannu Sannu sai ga shi an fara ganeni ana zuwa Siya,ballatana anguwan akwai Dandali na matasa sosai tunda suka gane shikenan da yammah haka nake Ciniki sosai,Daga Mama har Uban gayyar basu taba ce min ba nima ban ce musu ba ina kokarin kiyaye abunda zai saka a tozartani.
Jamal zai koma makaranta,ga kudin mota ga pocket money da kudin kayan abinci ga kudin makaranta Haka ma Badariya,Anty Binta tazo ranar sun dade a daki suna tattaunawa dukkansu sai dai har kwana Biyu ba wani mafita,Na lura shi kan shi Hankalinsa duk ya tashi a ranar suma su Anum aka basu takardan tunasarwan Biyan kudin makaranta Saboda damuwa abinci daren sa ma yadda na kai masa haka na koma na dauke sa bai ci ba,Da safe ma ruwan buni kadai ya sha ya fita ashe gidan Anty Binta yaje itama duk bata da wani kudi duk da su ta kwashe aka rufa asiri,Ammh tace ta ma mijinta mgana zai biya ma Badariya nata kudin makaranta sai dai a nemo na jamal ita zatayi kokarin nema mai na abinci kafin Lokacin tafiyarsa.
Haka naji yana Mama bayani da Daddare da ya dawo ni kuma na shiga
kai mata abinci.Mama tayi tagumi duk ta shiga damuwa kawayen nata da take takama da su,Duk sun janye daga gareta daman sai kana da shi ake yi da kai,Sannan itama babu jarin yin kasuwancin komai ya tsaya ita kanta duk ta rame ta Fige alamun ba natsuwa ba kwanciyar Hankali.
Sai da yadawo bangarena na zubo mai abinci naga ya kasa ci yayi Tagumi sai naji ya bani Tausayi Namiji har namiji ammh lokaci kadan ya nemi ya susuce,batare da Tunanin komai ba ko shawara da wani ba,ina da kudi a banki na sun kai dubu dari da Hamsin daman shawaran Yaya Isa nabi da ya ce na tara wani abu ko Fili na siya kaddara ne saboda watarana,Washegari da Safe na bama Hafsah Atm dina zata tafi makaranta nace ta ciro kudin dake ciki Duka ita kanta tayi mamaki sai dai bata tanka ba.
A hanyar dawowarta ta tsaya ta ciro kudin Dubu Dari da ashirin ta bani na adana su sai da Daddare da ya dawo Futu futu daman ya Dauki Takardunsa ya fita,Ko da ya dawo ya gaji salla ma acikin gida yayi ta ya kasa fita tun safe bai ci komai ba,Ruwan Citta da kunfari na Dafamai yasha cikinsa ya warware sannan ya Dora da abinci.
Inda na fahimci damuwa ta masa yawa su Anum tana kiriniya bai bi ta kansu ba sai na saka Hafsah ta tarka su zuwa Dakin su nace su Dauko Littafan su,kafin su kwanta
Sai da suka bar Falon sannan na shiga Daki na fito mai da kudin hannuna na basa da farko kin karb'a ya yi sai da nace ya karba sannan ya karba cikin mamaki yana fadin"Wannan kudin fa Fa'iza.?
Ina zama nesa da shi nace"ka biya ma Jamal kudin makaranta shi da Yaran nan, zaman haka bazai yuyu ba tunda an fara sai a karisa"
Sakin baki yayi yana kallona Lokaci daya yana kuma kallon kud'in bakinsa na rawa yace"Duka wannan kudin Fa'iza na waye..?
Kai tsaye nace"Nawa ne dubu dari da ashirin ne Allah yasa zasu isa"
Kai tsaye ????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
ya maidomin da kudin a gabana yana fadin"Bazan karb'a ba"
Nima sai na turamai ina fadin"Kayi hakuri ka karba dukkanmu bamu da zabi ne"
Sai yayi shuru ya kasa mgana,cikin wannan shurun ne wayarsa dake gefensa ta dau kara ina gani ya Duba yaja tsaki ya kashe haskenta ya mike daga zaune ya koma kan kujera yana fadin"Fa'iza duk ina kika samu? kudad'e haka?
Cikin mamakin Tambayarsa nace"Ina sana'a ai ka sani"
Yana kallona yace"wata sana'a kike yi haka da ta ke kawo miki kudad'e haka..?
Ina yar dariya nace"Kunin Aya da zobon da kake sha kullum,to shine abunda nake saidawa"
Ido ya zaro kamar bai sani ba ahalin nasan ya basar ne ban bari ya kara mgana ba,na tashi da kudin na karisa gabansa na sauke mai saman cinyarsa ina fadin"Don Allah ka karb'a"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya Dauki kudin yana fadin"Zan karba ammh ba kyauta ba,bashi.In na samu aiki na warware zan biya ki kudin ki"
Sai nace mai shikenan na amince nan ya zauna yana lissafin kudaden ya Dago yana cemin"Zai iya isa na biya ma su Anum kudin makaranta ammh Amir fa?
Nazari nayi kafin nace'Shi ka kyalesa gaba sai a saka shi in an samu"sai ya jinjina kai yana fadin"Nagode Fa'iza"
In yayi min godiya har mamakin sa nake yi tun ina mamaki har na daina adaran yaje ya fada'ma Mama kuma har aka bama jamal kudin ya koma makaranta ko mganar batamin ba nima don Allah nayi ban damu ba,daman? bana jiranta.
Bansan cewa zaman Hafsah a gidan nan na damun Mama ba, sai da ta kirani a gaban Yaya Ishaq tace yanzu ba da ba ne nasan ba shi da shi ammh na kara kawo mai Dawainiya ina ganin suma suna fama da kansu,Ni dai har tagama mganar ta ban ce komai ba ina mamakin me zaman Hafsah ya tare ma Mama..?ban da abinci bata cin komai agidan nan,kudin mota da duka Dawainiyarta da Sana'ata nake yi mata Yaya ishaq ne ya tare mganar yasa Mama ta kyaleni sai abun ya dameni a cikin raina kamar Goggo ta sani tace Ko Hafsah zata nemi Dakin makaranta ne ta koma, ni ko naga ina garin kamar bai dace ba da ma ace bana nan ne,shine ammh Tunda ina nan ta zauna a wajena ai nima ina moranta ta bangaran sana'ata.
Sai kuma korafi na biyu ne,mama ta fito da Tsirfan Masu zuwa a bani kunin Aya da zobo sun fara damunta ballatana da taga ina samun ciniki da yake akwai makarantar secondaryn Gwamnati ta mata dake kusa damu, tunda suka gane ni, shikenan arana sai na Dafa zobo fin sau biyu kunin Aya da yawa nake yi,Masu sari in basu zo da wuri ba sai dai su samu kad'an sai ta fara fadan ana damunta da Hayaniya sai na Fahimci bakincinta?da na d'anta? take so na zauna ya kasheni ni ko nace araina, bazan miki Rashin kunya ba ammh kuma baki isa ki hanani sana'ata ba.
Amir ne ke taimakamin tunda yana gida sai Hafsah in tana gida Badariya ma ba'a barta a baya ba, Kuma Maman tana sha kuma in tayi baki ina basu,ammh bata gani ba tamin mgana ban ce mata komai ba shima ta same shi ta mai mgana inaga shi ya kashe mgana bata kara tara ta da mganar ba.
Ni dai na toshe kunnuwana na cigaba da sana'ata ganin wannan abun da tayi bai sa na dakata ba ko kuma shi Wanda take gani bai taka min Burki ba, sai ta fara fadin ina barinta da yunwa ina chan ina sana'ata sai rana ta take nake dafa abinci har da kwanciya ciwo sai da aka kai ta Chemist,ulcer ta kamata saboda zama da yunwa Anty Binta ta zo ta kirani dakin Mama ta na ta masifa Yaya Ishaq na jinta bai ce komai ba nima har ga Allah ban yi niyar mgana ba Saboda ni dai nasan ina dafa abinci akan Lokaci tunda na safe kafin tafiyar yara makaranta ne na rana kuma shi nake fara dorawa in na Dafa Zobon Farko na Dare kuma duk latti na bayan isha'i na gama abinci na kai mata ammh ban tsira ba.
Sai da naji Anty Binta tace zan daina sana'ar da nake yi tunda Saboda ita zan kashe musu uwa da yunwa sai alokacin na dago na kalleta ban ji tsoro ba nace"Gaskiya Anty Binta ki yi hakuri ammh bazan daina sana'a ta ba.Domin banga ta inda hakan ya zama Takura ba"
Sai ta saki baki tana kallona kafin ta kallesa tana fadin"Kana jinta dai ko..?
Rashin kunya zata min a gabanka baka ce komai ba..?
Sai ya muskuta kafin yace"Anty Binta mu bi komai a sannu in zaki ce mata ta gyara sai ki yi mata fada ammh babu Adalci mu hanata sana'arta"
Mama na kwance ta daga kai tana fadin'"Ki yi shuru Binta ta siye shi da kud'i tunda yaga ta fara nuna tausayawa garesa shikenan bai iya tsawarta mata"
Cikin mamaki ya kalli Mama kafin yace"Mama wannan wata irin mgana ce..?
Mama ta zabura ta mike kamar daman chan lafiyarta kalau tana fadin"ai gaskiya na fad'a kada dai ta manta kafin tayi maka uban ka ya fara yi mata gata, sannan ya rufa mata asiri, kaima kazo ka rufa mata,ka zama gatan ta, in adalci kuma zatayi ai jarin? ba Ita ta ginama kanta ba kai ka gina ma ta shi"
Da sauri yace"Aa wlh bani da hannun akan sana'arta ban san komai akai ba"
Anty Binta ta koma ta zauna tana fadin"Shiyasa naso na dauke Mama ka hana ashe zaka bari matarka ta gana mata azaba ne ban sani ba..?
Yaya Ishaq yace"Anty Binta ki bar wannan mganar matukar ina raye Hakkin kula da mama da su Jamal yana wuya na ne sai dai in ciwo ko mutuwa sun kwantar dani"
Ina zaune ina jinsu so nayi na tashi na fita ammh kada suce na raina su,yasa na zauna kaina na kasa ina tsintar wasu mganganun su.
Mama da ranta ya gama baci tayi Kyafci kafin tace"Ta gama da shi ne Binta shiyasa kiri kiri yaje ya Duba Zainab yaki zuwa itama ai tana da Hakki akansa wajen wata daya da rabi bai je ya ganta ba,wannan ai sai mahaifinta ya yi fushi da shi Tsakani ga Allah wannan bawan Allah babu abunda bai yi mana ba ammh nasara uban me ishaq ke yi acikin gidan nan da bai tafi ba"
Mamaki ya kasheni wato Zainab ce matar so ni sanda yake tafiya sai yaga Dama yazo ai bata taba cewa ina da Hakki akansa ba takaici yasa nayi mirmishi mganar ma ta gundureni sai ya kashe zaman nawa da cewa"Je ki abun ki Fa'iza"
Mikewa nayi na fice a raina ina fadin daman ya koma chan wajen zainab din domin da zamansa da akasinsa duk daya ne a wajen fa'iza ba abunda suke Tunani ba ne.
Bansan ya suka kare ba ammh sun kai ruwa rana domin ina jin tashin muryoyin su shi da Anty Binta ina Dakina bansan tafiyar ta ba,mama bata so ta gansa yana zaune agida gani take yi kamar wani abu yake min ko zamansa wani Dadi yake yi min,Abunda bata sani ba ni mantawa nake yi ma yana gidan tun safe in yara suka tafi makaranta zan kama sana'ata Amir na tayani in Hafsah bata gidan ita a tunaninta na tsare shi a Dakina ne yana bani wani abu tunda ta Furtamin da na shiga gaisheta washegari ta kalleni sama da kasa kafin tace"Ki sakar min d'a Fa"iza na rasa me kike son ya baki bayan wanda ya baki a baya ke ko gajiya da nanikan namiji bakya yi ciki ko goyo ne baki gaji da yin sa ba ko me..?
Mganarta sai ta bani Dariya sai da na Murmusa kai tsaye nace mata"Ko d'aya Mama haihuwa ai Fa'iza ta gama shi in dai a nan gidan ne na bar ma Zainab ita ya dace ta cigaba da tara miki Jokoki"
Tasan mgana na gayamata ammh sai bata kara mgana ba,ai kunyan marasa kunya a sara sannan tsohon da bai ji kunyar hawa jaki ba shima jakin bazai nauyin yarfa sa da kasa ba.
Hajiyar su Raliya bata san mun sauya gida ba,taje camoron kanwarta zata aurar da Diya su Raliya kuma sun je lagos hutu gidan Yayan mahaifin su,suna dawowa suka hadu a makaranta Badariya ta fadamata ranar tare suka suka zo,a shashena suka zauna tare da Hafsah,suka ci abinci suna Hira Raliya tace Hajiya bata sani ba ammh zata dawo kwanan nan zata gayamata.
Mama taji Haushin shigar su Dakina da Raliya ta shiga mata sallama har da ni sai harara ta takeyi har tana fadin''Haka ake yi sai ki shigar da yarinyar daki ai ba wajen ki tazo ba sai ki bar ta da Badariya kawar tata"
Daganan na Fahimci Kishi Tsagwararon shu Mama ke yi da ni a baya don bamu zauna waje d'aya ba ne yanzu kuma Abun nata na fitowa ,Cigaba na ne bata so tafi kaunar ganin na wulakanta ko na Tozarta to ai ba ita ke da Rayuwata ba,in ita tana nata ne shi Allah kankat ne ya riga ya gama nasa tsarin mutum bai isa ya hana faruwar kaddara da ya Riga ya zana ba.
Ba'a rufe sati ba sai ga Hajiya Tazo Raliya ta rakota tayi ta min fadan meyasan ban kirata ba ni dai hakuri na bata,Tana ta kallon gidan cikin wani yanayi,da zata tafi ta bani Dubu Hamsi sannan taji dadin yadda sana'ata bai tsaya ba tace na cigaba da yi in sha Allahu watarana sai na bama kaina mamaki sai da zata tafi ta shiga Dakin Mama suka gaisa,Ta bata dubu goma mama nata godiya.
Har waje na rakata tace min Direba zai kawo min sako ba yawa,Sannan tace akwai Bikin diyar kawarta da zasu yi a kaduna tana tunanin kwangilan Hada turaruka ni zatace a bamawa sannan tana tunanin Amaryan zata zo gidan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login