Showing 231001 words to 234000 words out of 288345 words

Chapter 78 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

719

ta shiga Dakina ta iske har nayi barci kuma har ga Allah nayi barci domin ina shiga kaya kawai na sauya na kwanta.
Tana ganin nayi barci sai ta koma Falon Abba tana fadin"Engr ta yi barci Fa'izan"
Kai tsaye yace"Is ok..ma gaisa wani Lokacin"
Har Ammi zata fita ta barsu su yi hira tunda daman sun gaisa da ya shigo sai ya yi gyaran murya ta juyo cikin yanayin mganarsa yace"Ammh yaran ku ba duka sun yi aure ba..?in ban manta ba,Baban Nana ka fad'amin Autan ka kadai ta rage ko..?
Abba na mirmishi yace"Yes mun taba mganar dakai"
Ya fad'a yana kallon Ammi itama Mirmishi tayi kafin tace"Oh Na gane. yan mata biyu da suka zo suka gaisheka Doguwar ciki ita ce Hafsatu diyar kanwar Baban Nana ce mai rasuwa, d'ayar kuma Nana khadija itace Auta mu"
Kai ya jinjina kafin yace"Good. Allah ya raya su"
Suka amsa mai da Ameen Ammi ce ta fara tambayan sa ya gida ya su Hajiya yace duk suna lafiya.
Ammi tace"Ya jikin kakan naka ta warware ko..?
Kafada ya zakuda kafin yace"She is fine now, tana Benue? granny ai akwai rigima taki zaman Abuja"
Ammi na yar dariya tace"Nagani fa haka tsofaffin suke Allah dai ya kara tsawon rai"
Ya amsa da Ameen Hajiya Tafeesu ta tambayeshi yace sai jibi kila zai sauka ta kano kafin ya wuce Abuja ya Dubata ta,sun yi hira da Ammi kan itama Rigiman Hajiya Tafeesu na Tsufa,Abba na taya su da dariya tun da zuwan nasa ma na rigiman nata ne na sai an kawo mata D'anta Bukar. kuma fa ya rasu ammh duk sanda abunta ya tashi sai tayi sati tana kuka tana kiran sunansa.
Ya jima a gidan sai wajen goma ya tafi bayan ya shiga ya gaida Inno dubu ashirin ya zube mata tace ya Dawo ya Dauka yana duke gabanta yace"Haba Hajiya in Baban Nana ya yi miki alheri kina cewa ya dawo ya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? Dauka..?
Sai bakin Inno ya mutu ta bisa da saka albarka Ammi ma kudi ya zube mata ita da yara Sai dai bai ce ga na Fa'iza ba aran Ammi nata tunanin ko ya manta sanin Halinsa mai Hannun Alheri.
Abba har bakin bakar motarsa ya rakasa inda Direbansa ke jiransa wannan karon tafiyar mota ya yi Daga?Abuja yake shiyasa wani aikin gaggawa ne ya dawo da shi ,sun yi sallama ya wuce Abba ya Dawo cikin gida Ammi ta taresa da fadin"Baban Nana nace Engr ya manta da Fa'iza ne..? Naga bai bar mata nata Sakon ba.."
Abba sai ya kalli Ammi kafin yace"Sakon me..?
Sai da ya fad'a ya gane manufarta kai ya girgiza kafin yace"Allah ya shirya ki Maman nana,abun bin bashi ne"
Dariya tayi batace komai ba.
Bansan duk wainar da suka toya ba sai da Safe Ammi ke fad:amin Engr yaso ya ganni yamin godiya na yi barci da wuri cikin mganata nace"Wlh Ammi kaina ne jiya ya yi ta ciwo shiyasa na kwanta da wuri"
Ammi tace"Ayya sannu.in bai yi sauki ba sai muje asibiti"
Da haka muka rufe hiran bayan Ammi ta bani labarin kudin da Engr ya bata na tayata godiya,Ammi macece dake son kayi mata kyauta komai kankantarta tana jin dadin haka Nana Fatima ta fadamin sannan nima zama na da ita yasa na Fahimci wasu hallayan nata.
Panadol na sha sai ciwon kan ya fad'a ranar na yini ina harkokina har kasuwa naje siyo kamshin Turare saboda zan hada ma wata kawar Ammi,tare da na Nana Fatima tace min nata ya kare zan hada mata,za'a saka a mota a kai mata,da na dawo sai na hada Humra na itacen kuma na bari sai zuwa da Safe zan gama hadasa.
Maganriba ma Dakin Inno na yi shi su Hafsatu daga makaranta suna gidan Raliya,sun je ganin Walid,na idar da salla kenan bayan na gama azkar na Dauki wayata ina Dubawa,Sai ga kiran Abba mamaki ya kamani sai kuma nayi tunanin kila bai samu wayar Ammi ba ne sai na daga kiran bayan mun gaisa Abba yace"Ya ciwon kan..?ya fada kuwa.?
Kai tsaye nace"Eh Abba na warware yau har kasuwa na shiga"
Dagachan bangaran yace"Masha Allah Allah ya kara sauki..Daman Engr ne ya kirani ya roki alfarman Dinner sai gobe zai wuce kano, na kira maman taku ban sameta ba shiyasa na kiraki"
Da sauri nace"bari na tashi Abba daman Doya da miya muka yi da rana,kuma ta kare bari sai a dora da shi"
Abba yace"Shikenan Allah ya yi miki albarka after isha'i yace zai shigo"
Da haka muka rabu da Abba,na mike da sauri ina fadama Inno sai tace nayi hanzari,sai da na Shiga Bedroom din Ammi na fadamata washe baki tayi tana Fadin"To maza hanzarta"
Kitchen na fad'a kamar na sani daman da rana nayi nikan Ayan zan yi kunin aya sai nayi amfani da shi yanzu,Na fara tunanin abunda zan dafa masa,kawai sai nace bari nayi Cousscouss da Souces din kwai,da yaji albasa,Ban yi fruit salat ba,sai da na yayyaka lemu da abarba da apple sai kankana,Nama kuma daman muna da Soyayyen Nama sai nayi dubara na yi masa pepe yaji kayan kamshi Gabadaya nayi na gidan. Inno Daman bata cika cin wannan cimar ba kunu na Dama mata da rana shi take sha har Dare tayi Farau Farau,dashi ta sha ta kwanta.
Ina gamawa na hada na su Abba na kai falon shi,namu kuma na barsa a kitchen tunda su Hafsah basa gida Ammi kuma sai Dare ya raba take cin abinci ni kuma daman in na sha su kankana ko Fruit salt shikenan ya isheni.
Wanka nayi na saka Riga da wando na barci masu taushi,Sabbi ne Ammi ta siyamin su da muka shiga kasuwa,Na fesa turare na zura Hijabi na tada sallah,bayan na idar ina azkar Zainab ta kirani bayan mun gaisa nace ina Takwarata ta karamin ita tana min gwaranci.
Mun dan taba Hira da ita kan yaran ne nace ina suke tace suna falo tare da Babansu ambaton sa ma da tayi yasa gabana sai da ya fadi,sai nayi shuru jin haka yasa ta samu damar ce min"Maman Amir muna ta biko dai don Allah"
Mirmishi kawai nayi ban yi mgana ba,tacigaba da fadin"Honey na son ki Maman Amir kin sani nima na sani"
Da sauri nace"Yaushe kika sani..?
Daga baya kenan ya fara so na..?
Zainab tace"ko a bayan yana sonki Maman Amir bai bayyana ba ne sai yanzu. Wlh baki ga yadda yaran nan suka koma ba ba sa jin dadi baki nan. shi kan shi duk ya rame damuwa ta masa yawa jininsa ya hau fa wanchan Satin asibiti ya yini ana karamai ruwa"
Kai tsaye nace"Nima ai ya sakamin hawan jini da karancin shekaruna Zainab"
Sai ta marairaice tana fadin"Baki mantuwa..?don Allah ki yi hakuri ki dawo wlh ya yi nadama ki zo mu zauna tare kamar yadda muka saba a farko Har Mama abun na Damunta tace min kunyarki take ji bazata iya miki mgana ba ne"
Sai kawai nayi dariya ban ce komai ba ta cigaba da masa kamfe tana fadamin yadda Ishaq ya sauya duk da tasan an batamin daga farko ammh na yafe don Allah na kara basu wata damar kowa yana so na dawo na duba yaran nan saboda Farincikin su.
Sai naji ta fara jan ra'ayina da mganganunta ga kuma daman mganar Inno sai wata zuciya ta fara rinjayata kan sa. Sai nace mata ta bari zan yi tunani cikin wani yanayi murna tace"da gaske Maman Amir..?zaki dawo..?
Cikin yar dariya nace"Kila ina saka ran haka"
ihun data min yasa nayi saurin kashe wayata ina Dariya sai ga hawaye ina tuna mganarta da tace wai Abba ya sauko yan'uwa kuma sun ce matsalan daga wajena ne in na amince kowa bai da matsala.
Ji nayi araina zan iya bama Ishaq dama ko saboda ya'yana na Tabbata ya Hori sannan daga shi har Mama da Anty Binta baza su kara yi min abunda suka min daga farko ba domin Dan zaki ya riga ya girma.
Kiran sallar isha'i yasa na watsar da wannan Tunanin nayi salla ko azkar ban yi ba nace nayi in na tashi kwanciya sai dai a raina ina ta addu''a na kudurta nan da kwana uku zan yi istikara in Allah ya nuna min komawata ga Ishaq alheri ne zan basa wani Dama,in kuma ba Alheri bane Allah ya zabamin mafi alheri a rayuwata ba domin aure na raina ba har abada sai dai darajan ya'ya kawai.
Ban son tunani ya addabeni sai na Kira Nana Fatima muna mgana da ita,ban ma san Bakon Abba da shi kan shi Abba sun shigo gidan ba, sai da Nana Khadija ta leko tana fadin naje Abba na kirana afalo.
Sai na kashe wayar nace mata zan kara kiranta in na dawo.
Hijabin sallah na saka Kato,har kasa Fuskata kadahan kadaran ko kwalli ban saka ba,baki duk ya bushe haka na fita zuwa falon Abba sam na manta da Abba na da bako kai na Tsaye na zurma ciki da sallama cikin yanayin muryata.
Abba baya Falon sai wani mutum Dake zaune a kasan cafet ga kololin abincin nan alamun anci an gama da su,ya tamkwashe kafa ne kafarsa sanye da bakar safa,Sanye da wani yadi mai ruwan kasa shara shara domin har Farar vest dinsa ana gani kansa na sunkuye yana Danna wayarsa,kansa cikin hula mai ruwan kasa na zanna bukar hannunsa Sanye da bakin agogon rado na fata baki,ban ga fuskarsa ba sosai,tunda ya duke kuma kamar da alamu bai ji sallamata ba waige na farayi ganin Abba baya falon,har zan juya sai na ga bai kamata ba sai na kara yin sallama da Sanyin muryata.
Hankalinsa na kan abunda Engr Bala ya turo masa yaji wata murya cikin sanyi da gardi tayi sallama,bai san sanda ya Dago da sauri ba
Daidai Lokacin da nima na dago Sai ga shi mun Hada ido Hudu da shi.
Dam!
Ras!
Gabana ya fadi ashe tare da nashi ya amsa,ni kunya ce ta kamani ganin wani Kamilalliyar fuska mai cike da Haiba da kwarjini,kuma kallon namiji baya cikin Dabi'ata sai na Sadda kai na kasa shi ko tunda ga sama har kasa yake kallona acikin ransa yana mamakin wacece wannan.?
Yana Shirin mgana Abba ya fito Daga Bedroom dinsa yana Fadin"Engr na bar..!
Bai karisa ba ya ganni Tsaye sai ya saki mganar yana Fadin"A'ah Fa'i yaushe kika shigo..?
Ni ko a raina nace au wannan ne Engr..?
Sai na kara satan kallonsa a raina ina fadin ashe ma ba tsoho ba ne.
Kasa na duka daga inda nake tsaye ina Fadin"Abba ina yini..?
Ina yini..?
Na fada ina kallon kasa Abba kadai ya amsa yana zama gefen bakonsa kafin yace"Engr ne yace a kiraki ku gaisa jiya yazo kin kwanta.
Engr meet my Fav.Dota Fa'iza itace mai wad'anan Girke girken masu dadi da kake ci kana yabawa.."
Kyar idonsa da kallonsa a kaina daman ya yi tunanin haka ya yi Tunanin FA'IZAA ce!
Ni ko kaina na kasa ina kallon kwalliyar Cafet din falon Abba.
Abba da bai ji na gaishesa ba sai ya kalleni yana Fadin"Fa'i ga Engr da kike jin Labarinsa ki gaishesa"
Sai alokacin na Dago karaf ko muka kara Had:a ido cikin yanayin mgana ta nace"Ina yini..?
Ya aiki..?
Cikin Muryansa mai laushi yace"Lafiya lau Faa'izaaa.."
Yadda yaja sunan sai da na kallesa sai kawai ya kasheni da wani mirmishi mai Tsada da ya tsayamin arai,kafafuwana naji sun fara sanyi ban san ma'anar wannan kallon ba. ammh Tabbas kallon ya shiga jikina ya fara kassarani domin ya kasa Dauke idonsa a kaina
Cikin mganarsa d'aya bayan Daya yace"Sannu da kokari Fa'izaa. Mungode sosai Allah ya biya ki da aljannah"
Kasa kasa na amsa da Ameen,Ina shirin mikewa naji Abba na ce masa"Ai Fa'i yar baiwa ce ga girke girke sannan tana sana'ar saida kunin aya da zobo,Turaren kamshin nan duk aikin ta ne ba abunda bata iya ba"
Naji dai yana mgana banji me yace ba Saboda nayi musu sallama na fice kuma har alokacin naji idanuwam Engr a kaina.
Jikina da Dumi na kai Dakina haka kurum nake ji kamar zafin zazzabi ya Rufeni. sai na samu gefen gado na zauna ina maida numfashi kamar wace tayi wasan tsere,wlh a cikin jikina nake jin mirmishim Engr nayi min yawo yam!
Yam!kamar wacce aka yi ma asiri. Haka nake ganin Fuskarsa acikin Idanuwana kai na Dafe da Sauri ina Fadin"Wai meke shirin faruwa da ni ne ni Fa'iza?

? Kiran wayata da Nana Fatima ta yi shi ya fitar dani acikin Halin da na fad'a,ammh ita kanta da muka fara mgana taga bana cikin natsuwata sai da tace"Lafiya Fa'i?
Sai naji daman ta kira sunana Fa'izaa naji ko ta iya fad'in irin na Engr bakon Abba.?
To wai me ke damuna ne..?
Murya shake nace mata bakomai

******

Achan falon Abba kuwa tun fitan Fa'iza Engr ya rasa natsuwarsa. Abunda yake dubawa a wayarsa ma sai yaji ya daina gane komai da komai Abba na masa hiran aiki shima kwata kwata bai gane me yake fad'a ba. in da Fa'iza ta tashi ya kurama ido cikin yanayin da bai gane ma kansa ba yanzu yanzu nan.
Shi Abba duk bai gane ba,ya cigaba da Hira da Engr,shi kuma ganin ya daina Fahimta yasa ya yi ma Abba sallama da godiya yace zai wuce yana Sauri ne gobe tun safe Kano zai wuce abun ya bama Abba mamaki ko zuwa gaida Inno bai yi ba yace a kyalesa da yace bari ya Kira Ammi su yi sallama sai yace itama ya rabu da ita.
Har ya rakasa bakin mota ya dawo cikin gida hankalinsa ya kasu na abunda ya sauya fara'ar Engr yanzu yanzu Ammi ko da ta shigo ta iske ya tafi cikin mamaki tace"kiran sa akayi hala..?
Abba yace"Ko daya muna hira kawai naga ya sauya, sai kuma yace min zai wuce ban san abunda ya faru ba."
Ammi ta zauna gefensa tana fadin"Topha Allah yasa dai lafiya"
Ya amsa da Ameen.
Abunda basu sani ba shi kanshi bai san meke damunsa ba sai da ya isa inda yayi masauki bayan ya yi wanka ya kwanta barci ya gagara yana da gida a kaduna ammh in dai ba tare da su Sweetheart suka zo ba, baya zama a wannan gidan shi kadai kowa ya san shi mai jama'a ne mai harkokin Rayuwa da yawa ammh yau wayoyin sa ma duka kashe su ya yi baya so a Damesa. abun kamar almara bai Taba jin wata mace ta tsaya masa arai ba tun bayan rasuwar Tauhidat,yasani ba auran soyayya ya yi da ita ba rigiman Granny ce ta hada shi da ita,ya ga mata kala kala yare yare dabam dabam na'i dabam dabam tsayin shekaru ashirin da wani abu bai taba ganin macen da ta hanashi Sukuni irin Faa'izaa ba..!
Da ya runtse ido domin yayi barci ita yake gani,Dakyar a Daddafe ya kai asuba ko da ya tashi ya tabbatar ma kansa Fa'iza ce ta hana shi sukuni abunda bai faru da shi da kananun shekarunsa ba ne yanzu da girma ya kamasa zai faru da shi. bai son So ba amnh ko kaffara bazai yi ba SON Faa'iza ya kamasa daga kallon Farko da ya yi mata.?
Ko wanka bai tsaya ya yi ba, ya taso Direbansa daga shi sai farar Jallabiya da Dogon bakin wando ya nufi gidan Abba karfe shidda da yan mintina na safe.
Abba ya dawo masallaci kenan sun gama waya da Abdul'ahad sai ga kiran Engr,domin jiyan ma yayi ta kiransa bayan ya tafi wayarsa a kashe.
Ya dauka da kwarin gwiwarsa sai yaji ya Rude jin yace masa yana haraban gidan shi Abba ya mike yana Fadin"Cikin gidana dai..?
Yafada cikin mamaki Ammi da ta fito daga cikin bedroom Da hijabinta na sallah taga Abba ya Sauke waya cikin mamaki da sauri tace"Baban Nana lafiya..?
Kai tsaye yace"Wai yanzu Engr ya kirani yace yana Haraban gidan nan yana son ganina"
Ammi ta zaro ido kafin tace"Yanzu..?
Kawai sai Abba ya wuce bai mata mgana Ammi kuma sai ta fara Tunanin anya lafiya..?
Abba dai bai kara shiga Rudani ba sai da ya fita yaga Engr da Jallabiya da takalmin wanka. ya firgita yana mika masa hannu ma su yi musabaha Engr bai karbesa ba, cikin wani yanayi da bai taba ganinsa aciki ba. ga idanuwansa sun yi ja alamun bai samu barci ba.
Cikin dishewar murya Engr yace"FA'IZAA tana da aure ne..?
Kai tsaye mganar tazo masa domin bayan ya Fahimci abunda ke faruwa da shi, zullumin ko matar aure ne yasa jininsa ke barazanan hayewa sama bai sani ba gwara ya farajin Tabbaci sannan.
Abba ya kallesa yana mamakin kalamansa shi fa har mantawa yake yi da Engr ya hada jini da yarbawa Saboda komai na sa na Hausawa ne hatta Dabi'unsa,ammh yau sai yaga kamar ya juyo masa yau ya fito a bayarben nasa shiyasa ma cikin mamaki yace"Wata Fa'izan kuma Ranka ya Dade?
Engr ya sauke lumsassun idanuwansa kafin yace"Fa'izaa dai..Ur Daughter."
Sai Abba ya ware ido kafin yace"A'a bata da aure wani abu ne ya faru..?
Yana jin sanda Engr ya sauke karfaffan ajiyan zuciya mai karfin da sai da ya kara kallon sa daga sama har kasa cikin Dafe kirjinsa saitin zuciyarsa yace"Alhamdulillah..!
Mu shiga ciki mu karisa mganar"
Abba kamar gaula haka ya bisa ammh yana tunanin to lafiya..?Me ya hada Engr da tambayan Fa'iza nada aure ko a'a..?
Wata zuciyar ta hasaso masa Dalili a razane ya kallesa lokacin sun shiga Falonsa yana shirin mgana kawai yaga ya zube a kasa yana fadin"Ina kwana Abba"
Abba ga mamaki ga Dariya cikin Dauriya yace"Ranka ya Dad'e..Ni ne fa Baban Nana sai na koma kuma Abba.."
Engr na shafa kansa yace"Ka zama Abba daga yau tunda zaka bani auran y'arka"
Abba ya zaro ido cikin mamaki kafin yace"Y'ata wata y'ar tawa..?
Kai Tsaye Engr yace"FAA'IZAA.."
FAaa'izaa zaka bani Abba. I love her ganin Farko da nayi mata jiya, daga dare zuwa Safe na Fahimci ina sonta kuma auran ta zan yi, ni ba yaro ba ne kai ma haka bazan zo na zauna ina maka wasa ko karamar mgana ba, duk abunda nace maka i mean it form my Heart.
Ya fada yana Dafe saitin zuciyarsa,Abba kamar ya kwashe da Dariya mutane suna kallonsa yana da barkwanci ammh yasan in da sun zauna da Engr sai sun san shi a barkwanci bai iya komai ba.
Mutum ne free ba ruwansa mgana fadinta yake daya bayan d'aya a muhallinta.
Ganin Abba ya tsaya yana kallonsa yasa ya gyara zama yana Fadin"Abba da gaske nake ina son Fa'iza.
Zaka iya bama tsoho kamata auranta..?
Abba ya bude baki ya rufe yafi a kirga,Zama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login