Showing 204001 words to 207000 words out of 288345 words

Chapter 69 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

741

ammh Su Abba ko da suka shigo akace ga abinci yace sai an gama zaman muna Daki ni da Ammi ya kirata yace tazo dani.
Ina jin haka sai na Rude ganin haka yasa Ammi ta mike ta Dafa kafad'ana tana Fadin"Kada kii damu Fa'i ba wanda zai miki Dole. sai dai kada ki yi shuru ki Cutar da kanki ki yi mgana domin nema miki yancinki aure Ibadan Allah ne ba Cutarwa ko bautan Mutum ba ne, kin ji ko?
Sai na gyada mata Kai Lokaci d'aya ina maimaita sunan Allah a raina yadda zan samu natsuwa Hijabi na saka ta riko Hannuna har Falon Goggo kaina na kasa har gaban Abba.
Ina zama na dago kaina karaf ana Yaya Ishaq ya rame yayi baki yana Sanye da shadda navy blue daga bangaran Hagun Abba ni kuma ina Bangaran Dama mun saka shi a Tsakiya, sai na dauke idona ina zagayen mutanen falon da kallo.
Dukkamu muna saman Cafet ne Inno da Baba Ati ne suke kan kujera,Naga Mallam mijin goggo sai Ammi sai Mama sai ni sai Abba, sai Uban gayyar Ina jin Yaya Abdul'Ahad yana waje shi da su Yaya isa.
Kaina na maida kasa ina kokarin Daidaita kaina. domin sai naji kamar bazan iya mgana a yanayin da na samu kaina a gaban Abba ba.







*Janafty*
[7/25, 8:30 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3004*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*


*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY*


Abba ne ya fara bude taron da addu'a sannan ya gyara zama ya yi gyaran murya kafin ya fara da fad'in"Alhamdulillah dukkanmu nan mun san abunda ya taramu Magana ce akan ya'yan mu Fa'iza da Ishaq,"
Ya na gama fad'in haka sai ya karkato ya kalleni kaina na kasa ya kira sunana na amsa bakina na rawa na Dago ina kallonsa,Sai ya karkata kansa zuwa ga Uban gayyar shima ya kira sunansa abun mamaki da kwarin gwiwa ya amsa har yana wani gyara zama.
Abba ya sauke numfashi yana Fadin"Zaman nan naku ne. Tun tuni ya kamata mu yi sa sai bamu yi ba. Saboda Rashin Lafiyan Fa'iza da wasu uzurirrikan da suka sha kan mu, ammh yanzu Alhandulillah ga shi lokaci ya bamu dama mun zauna ke Fa'iza dake zan fara mganata"
Ina jin haka naji na fara rasa karfin gwiwana bai damu ba ya kalleni ya kara kiran sunana Idanuwana cike da kwallah na Dago ina fadin"Na'am Abba"
? Cikin kaushinsa yace"Mijin ki ya rasa aikinsa a baya kin zauna da shi acikin Halin babu kuma da bakinsa ya fad'a min kin Tallafa masa da sana'o'in ki,bamu taba jin kan ku ba,Sannan Daga Baya Allah ya wankesa aka dawo masa da aikinsa da karin girma. kowa yasan Dake aka yi shirin komawa Lagos sai kuma Daga baya zence ya sha bambam,ina so ki bud'e baki ki Fad'amana me ya faru kika bin mijin ki Sabon Muhallinsa? sannan meyasa kike neman Saki a wajensa..?
Yana Dire mganarsa nima na Dire kukana saboda yana mgana zuciyata na bud'ewa da wani kunci sai na kasa mgana gabad'aya suka zubamin ido suna kallona.
Ammi dake gefe ta kalleni ta kalli Ishaq taga sai kifta ido yake yi alamun rashin? gaskiya karaf ta taso tazo gabana ta rike min hannu tana Fadin"Yanzu ba Lokacin kuka ba ne Fa'iza. bude baki ki fad'i Abunda ke faruwa dukkan mu nan mun zauna me domin yi ma kowanni bangare adalci"
Wani irin kallo Abba ya watsa mata da ban taba ganin yayi mata irin shi ba. Da Sauri ta sakeni tun kafin yayi mgana ta koma wajen zamanta tana Fadin"Kayi hakuri Baban Nana"
Kai ya jinjina cikin bacin rai yace"Baki da Hurumi a kan wannan mganar ki yi shuru da bakin ki"
Jin haka yasa ta hade rai ta kama bakinta,Abba ya dawo da kalllonsa kaina yana Fadin"Umh muna jin ki Fa'iza ki juya ki ga wad'anda ke zaune gabadaya iyayen ki ne da kakaninki, zaki iya fad'amana duk abunda ke Faruwa Domin neman masalaha"
Hannayena na saka na kare bakina ina kuka,kamar a wani Lokacin kalamansa suke min duka acikin raina Dakyar na iya bude Idanuwana cike Taf da hawaye na sauke kan na Ishaq na wani Lokaci ina kallonsa ina kallo ya sunkuyar da kai yana zufa ni kuma kai tsaye cikin muryata da kuka Ya taimaka wajen Dasashe su nace"Ku tambayesa shi ke da duka amshoshin tambayoyin ku Abba. Ammh ni bazan iya cewa komai ba matukar bai yi mgana ba"
Na fad'a ina kuka na da Sauri ya Dago yana kallona gabansa na fad'i bai Dauka zan iya Dawo da wannan mganar ba Tunda nace na yafe masa cikin rawan baki yace"Haba Fa'iza na dauka mun gama da wannan mganar Tunda na roke ki gafara,kuma kika yafemin"
Ina Sharan hawayena da bayan Hannuna nace"Da gaske nake yi na Yafe maka yaya ishaq duniya da Lahira,sai dai ka sani ba hurumina ba ne Tun a wata Hudun Farko addini ya bani Damar haka. Mganar nan kuma Wlh kamar yadda nayi alkwarin baza'a ji ta daga bakina ba. Ka sahale min auran ka,kamar yadda na Bukata sai mganar nan ta mutu har Gaban Abada ba wanda zai jita"
Sai ya Rude kamar zai ta shi Daga inda yake Abba da suka zama yan kallo yace ya koma ya zauna ammh ya kasa zama Daidai Cikin sigar Lallashi yace"Bazan iya ba. ai na fada miki bazan iya sakin ki ba Fa'iza Baba yana kabarinsa wlh zai yi fushi dani Sannan me zan fad'ama su Anum da suke? jiran na dawo musu da Umman su..?Sannan Zainab na fad'amin bazata zauna ba indai bakya gidan don Allah ki yi Hakuri Fa'iza ki janye wannan mganar ki had'a kayanki mu tafi"
Yadda yake mgana zaki san bai da gaskiya duk ya rasa natsuwa sai kowa ya koma yana kallonsa ni kuma Sai naji duk wani Fargaba na fita daga rainaa.
? Naga kamar yama raina min wayau yana so na koma saboda ya'yansa da Muradin matarsa ba domin muradin kansa ba. sai na samu kaina da yin Wata karamar Dariyar da babu Nishad'i ko kadan acikinta sai zallar bakinciki sannan nace"In dai Saboda kalaman Baba ne kada ka damu Bazai kamaka da Laifi ba ko da yana raye domin ba'a so dole, sannan ba'a aure Dole.
Maganar yara kuma Kai ne Uban su kuma Dolen su. ni kuma nan ne ya Dace dani kayi hakuri ka rike su domin bazan bika ba,mganar matarka kuma ta zauna mana ai daman bani na aurota ba, kai ne mijinta kuma kana Tare da ita daman kuma bamu taba zama waje d'aya da ita ba. ballatana Domin bani ya zama abun damuwa,masu kular muku da yara kuma akwai ma'aikata a gari in kuka nema zaku samu in sha Allahu"
Na fad'a ina kokarin maida kwallan dake neman ziraromin,kowa sai mamaki ya cikasu na mganganun mu daga wannan ya kalleni sai wannan ya kalleshi Inno ta gyara zama ganin Abba ya kasa mgana cikin muryan data kwana Biyu tace"Kai mu duk bamu gane kan mganganin ku ba .Ku Bude baki kuyi mana mgana yadda zamu gano bakin zaren kai Usman ka yi musu mgana mana"
Abba ya sauke Numfashi kafin ya kalleni yana bude baki yace"Fa'iza..".
Ban bari ya cigaba da mgana ba ina kallon Ishaq nace"Abba shi zaka tambaya in dai bai yi mgana ba nima bazan yi ba. Saboda ina so na cigaba da yimasa adalci da ya rokeni nayi masa Tun a baya"
Ina mgana ina kuka muryata na Sauyawa sai Abba ya maida kallon kansa sai zufa yake yi duk da Fanka sama data kasa dake aiki a Falon da ka gansa kasan ba gaskiya, bai taba zaton zan iya dawo da wannan mganar ba na Shammacesa.
Abba ya kira sunansa ya amsa yana Rawan baki Abba mamaki ya kamasa sai dai bai nuna ba cikin Sanyi yace"Kaji abunda Fa'iza tace..?shin zaka iya yi mana bayani ne yadda zamu gane? Ko kuwa zaku cigaba da wasa da Hankalin mu ne..?
Sai Ishaq ya fara share zufa da Farin Hanky din dake hannunsa ya Juya yana zare ido suka Had'a ido da Mama wacce ta kauda kai da Sauri ta kasa kallonsa ya dawo da kallonsa kaina ya kasa zama kansa na kan kafafunsa Cikin rawan murya yace"Plz Fa'iza ki bar wannan mganar mana"
Nima kai tsaye nace"Zan bar ta kad'ai ne in ka sahalemin auran ka Ishaq"
Marairewa ya kara yi kafin ya kalli Abba yana Fadin"Abba ka bani minti goma kacal mu yi mgana ni da Fa'iza"
Har zai yi mgana Goggo tace"A baya da baku fallasa mana abunda ke Faruwa ba,ba wanda yaso yaji ammh yanzu tunda kuka fallasa a gaban kowa da kowa zaku yi mganar daga yau koma menene muna so mu ji kuma mu sani"
Tafad'a tana kallona ina Kuka haka kurum taji duk abunda yasa Fa'iza mgana abu ne mai taurin da jinsa sai ya Girgiza zukata,kuma ta fi kowa sanin zaman hakurin da Fa'iza tayi a gidan Ishaq mganar ta yasa Inno da Baba Ati suka ce ya yi mganar nan kowa yaji ai Sulhu ake nema
Abba ya kalli Ishaq ganin yadda yake rawan jiki yasa ya Dafa kafad'ansa yana Fadin"Kada ka damu ni ba Uba kad'ai nake ga Fa'iza ba.
Har da kai,in ita ke da Laifi wlh da kaina zan tasata sai Dakinta bazata kara kwana a garin nan ba"
Jin kalaman Abba yasa sai ya fara samun natsuwa yana Hango adalci a mganar Abba Cikin ajiyar rai ya koma ya zauna yana Fadin"Abba ku yafemin kuskure ne na aikata cikin Rashin Sani ammh wlh nayi nadama Tuni kuma naba Fa'iza Hakuri tace ta yafemin ban san me yasa ta kuma Dawo da mganar data wuce ba"
Da sauri nace"Saboda itace mafarin duka al'amura. mganar yafiya kuma na Jima da fad'amaka na yafe maka Duniya da Lahira"
Abba sai ya koma ya kalleni ya kallesa kansa ya Daure,da yasa ya kasa mgana Shuru falon ya Dauka Kafin Inno tace"Muna jin ka Isiyaku"
Ya dago yana kallon Inno ga Tsoro ga Takaicin sunan da ta kirasa da shi ya Tabbata in bai yi mgana ba,ba mafita ammh kuma yana ji ajikinsa Abba zai Fahimcesa Mama ko Jikinta nata rawa,kunya duk ya kamata bata Fatan Fa'iza ta fad'i musgunawanta gareta duk da taga irin kallon da Goggo ke jifanta da shi ji take kamar ta tashi ta Fita sai dai ba Dama.
Kamar Daga sama taji Ishaq na Fadin"Wato Abba..Lokacin da zan kara aure ne..Sai sai na ce ma Fa'iza..Mu mu.."
Ya kasa karisawa Saboda kunya da nauyin mganar Abba ya kuramai ido yana Fadin"Uhm ina jin ka"
Ishaq ya Runtse ido kafin yayi gundinbalan fad'in"Nace ma Fa'iza zamu jingine auran mu ni da ita"
Gabad'aya sai Falon ya Dau shuru kamar Mutuwa ta gifta ni ko kamar a Lokacin yake min mgana Hawaye wasu na korar wani a saman Fuskata.
Goggo cikin mamaki tace"Wani irin jingina kuma..?
Inno ta karb'e da Fadin"Ni kaina na kasa ganewa fa"
Mallam mijin goggo da sai a lokacin yayi mgana cikin kallon Ishaq yace"jinginar aure kala kala ne Ishaq, kayi mana bayanin wata irin jingina ce ka nemi ku yi ma auran ku kai da Fa'iza?
Ishaq kansa na kasa ya Dago yana kallon Mama itama shi take kallo Cikin mamakin kalamansa kafin ya Sadda kansa domin ya kasa kallon Abba cikin rawam murya yace"na nemi alfarman Fa'iza kan mu jingine auran mu, ba mu'amalan miji da mata a tsakanin mu ,ba wani hulda ta ma'aurata Tsakanina da ita,sai dai kawai ta zauna ta cigaba da kularmin da ya'yana"
Yana Dire mganarsa sai gabad'aya su Inno suka Dauki Salati suka Dire Baba Ati tace"Lalle lamarin Babba ne"
Ni ko hawaye kawai na bari suna zobomin da mirmishin da ke saman Fuska sai dai a alokacin in za'a tona Zuciyata kamar zata fashe saboda bakinciki da kunci.
Abba ya kasa mgana Saboda Takaici Goggo tace"Wannan mganar sharia"a ce ta ila'i dole muna bukatar malaman da zasu yi mana fashin baki kan wannan al'amarin"
Da Sauri Mallam ya jefomasa tambaya da cewa"Har na tsawon wata nawa ka di'bar ma wannan jinginar?
Ba zato kawai sukaji Muryata a Kausashe ina Fadin"Har na Tsawon Shekaru bakwai. Shekaru bakwai da Doriya Mallam"
Gabad'aya sai suka had'a bakin wajen Fadin"Shekaru bakwai fa kika ce Fa'iza..?
Ina kuka na jinjina kai kafin nace"Iya shekarun da nagaji ne na nemi mafita ammh Jinginarsa gareni ta har Abada
Ne.
Saboda baya kaunar kara Had'a zuru'a dani bana haifa masa ya'ya Daidai da Burinsa,tunda bazai iya sakina Saboda kalaman Baba akansa ba,sai ya Zabi ya jingine ni tunda zai auro wacce tayi daidai da Ra'ayin sa kuma wacce zata Haifa masa ya'ya farare kyawawa daidai da ra'ayin sa Shekaru sama da bakwai na kwashe Cikin kunci da bakinciki bayan wad'anda na kwashe a baya Abba ka gayamin nayi Laifi domin na nemi da ya Sauwakemin..?ba aikin da ya fara na nemi ya karishe ba..?
Na fad'a ina kallon Abba Hawaye kamar ana tunkudo su haka suke zubomin Abba yaji jijiyoyin kansa na tashi,Saboda bacin rai ya kalli Ishaq yafi sau uku shi kuma kansa na kasa su Inno jikinsu duk yayi sanyi Ammi ko har tana tayani kuka.
Abba ya kalleni ina kuka Tsausayina ya kamashi,ya rikoni gefen kafadarsa yana Lallashina jina acikin jikinsa yasa na barke da kukan da shekaru sama da goma ina neman Kafad'an da zan kwanta nayi wannan kukan ban samu ba sai yau sai kawai suka ji muryanta na saki kukana da Dukkan Karfin zuciyata sai Ran Abba ya kara baci ya Dago Cikin Fushi yana kallon Mama cikin Tsawa yace"Da Sanin ki D'anki ya jingine auran yata shine baki yi komai a kai ba..?
Jikin Mama na rawa zatayi mgana da Sauri nayi Wuf na tashi daga kafad'an Abba cikin kuka nace"Bata sani ba Abba. Dagani sai shi ne muka sani.."
Abba ya dakamin Tsawa nima kafin yace"Meyasa baki fad'ama kowa ba..?
Tunda Lokacin bana nan meyasa baki zo kin Fad'ama Goggon ku ba..?
Kuka na kara sawa ina Fadin"Ya zan yi Abba..?yace nayi masa adalci da ya shekara takwas yana min na aurena a yadda nake ya zauna dani. to nima ya Roki da nayi masa adalci na barsa yayi Rayuwarsa da amaryansa Abba ina son na zauna da ya'yana Wlh Sabo da su ne. Sannan alokacin bana so na Dorama kowa nauyina Abba Shiyasa ban taba Fad'ama kowa ba"
Na karishe Fad'a ina kuka gaban Hijabina ya jike da kuka.
Abba sai sakin Huci yake yi yana kallon Ishaq da ya gama Tsurewa Mallam ya yi gyaram murya kafin yayi mgana Goggo ta rigasa da Fadin"Tabbas nasan Fa'iza bata ji dadin zama da Ishaq? ba .bata da mutumci a idon sa da shi da Mahaifiyarsa da yayarsa, ni shaida ce ba irin cin kashin da basa mata Har ni kaina da ya'yana bamu Tsira ba Saboda ina kaunar Fa'iza"
Abba kamar zai dagi Goggo yace"Kuma kuka kasa Raba auran dake cike da Zalunci Goggon su.?
Sai Goggo ta saka kuka tana Fadin"Ya zamu yi Alhaji..?ina tausaya ma Fa'iza ina Tausaya yaran nan nata
Sannan ita bata mgana ko yan'uwanta su yi tambayan duniyan nan bata Fad'a musu komai, sai dai tayi shuru bakincikin na cinta,sai dai muga tana ta rama da kamjamewa"
Ta karishe fad'a cikin kuka,Abba ransa ya kara baci ya mike a fusace cikin Fusata yace"To ana aure Dole ne..?meyasa aka bashi auranta tunda baya sonta..?
Mallam ne yayi mgana cikin lallashi yana fadin"Alhaji koma ka zauna ayi mganar nan a tsanake"
Sai da inno ta kara mgana sannan ya zauna yana Huci,Kukan Fa'iza na soya masa rai Mama ma kukan datake yi ya sa kowa ya maida Hankalin kanta.
Cikin kuka tace"Alhaji ku yi hakuri wlh ban san da wannan mganar ba,Ishaq bai gayamin ba sannan ita kanta Fa'iza bata gayamin ba. abu daya na sani a baya na musguna ma Fa'iza ina kuma neman afuwarta data yafemin"
Ta fad'a tana share kwallah da Haban zaninta Abba kyafci yayi kawai ransa na Cigaba da kuna sai kiran wayarsa ake yi yana Kashewa baya son mgana ma alokacin Saboda yadda ransa ke kuna Ishaq ko motsi ya kasa Saboda Fargaba da yadda yaji muryan Abba cikin zafi da kaushi.
Mallam ya gyara zama yana Fadin"Duk ba wannan ba ne Alhaji. A kokacrin Alhaji kabiru shine namiji babba ga su Fatima da Aisha shi kuma ya rike Fa'iza a hannunsa har ga Allah bai had'a auran nan da wata manufa ba. ya hada shi ne Saboda yana Tunanin Ishaq zai iya Rike Fa'iza da maraicinta har bayan Ransa bai taba sanin zai yi haka ba,In da ya sani Alhaji kabiru yana kabarinsa Allah yaji kansa bazai aura mata shi ba sannan inda yana Raye wlh shi da kansa zai raba auran nan indai ya ga Fa'iza na cutuwa"
Falon sai ya yi shuru kowa na Sauke Numfashi Inno ta gyara zama tace"Duk mun ji,Daman yaran yanzu ai ka haife su ne,baka Haifi Halin su ba mu yanzu matsayin wannan auran zamu fara nema domin a shari'a ina jin Tuni auran nan ba shi"
Baba Ati tace"Gaskiya shekaru bakwai ba kwana bakwai ba ne. Inno wannan Cutarwan ya yi yawa gaskiya"
Abba ya yi saurin taransu da Fadin"Ban damu da wannan ba ko da aure ko ba aure sai ya sakar min y'ata tunda ba'a aure dole"
Ya fad'a a kausashe Ishaq ya Dago Fuskarsa ta jike da zufa saboda Fargaba,cikin rawam murya yace"Don Allah Abba..!
Hannu ya daga masa kafin yace"Ai baka sonta ko.?to ka saketa bazan yi maka Dole ka zauna da wacce baka so"
Yafad'a cikin bacin rai sai kuma kowa ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login