Showing 156001 words to 159000 words out of 288345 words

Chapter 53 - Kana Naka Book 1 Complete Hausa Novel

Janafty   

01 Nov 2025

768

da gida da motar hawa sannan Ina da Rufin asirin da na Dauko mahaifiyata Gata nan Inno muna zaune tare da ita da. Bikin ma da ba ta tafi tare da su Maman Nanah ba,Tana faman da matsalan ido,jiya ne ranar zuwanta ganin likita yasa nace ta tsaya in na kaita ajiyan yau sai na wuce kano da ita sai kuma muka wayi gari cikin wannan al'amarin nan take na kira Direba nace mu Dauki Hanyar katsina bazan iya sukuni ba sai nazo naga Ahalina"
Ya karishe fad'a yana kallon mu gabadaya su Goggo suka amsa da Masha Allah.
Cikin yanayinsa yace"Ya'yana ku fadamin a inda kuke aure da adadin yaran ku..?ina mazajen ku..?ko dai yake nima ban zo da iyalaina ba. ammh da zarar na dawo daga Tafiyar da zan yi zamu zo gabad'ayan su ku gansu suma su gan ku"
Cikin yake Yaya mariya ta fara fad'in sunanta da adadin ya'yanta sannan ta fad'i yaya Asiya sai ni muryata a shake nace"Fa'iza ya'yana hud'u Kabir Amir,Saudatu Anum,Musty da Ahmad Ina aure a katsina"
Hafsah kuma karamar mu ce tana wajena shekaran nan ta fara karatu a jami'ar katsina"
Cikin gamsuwa ya gyad'a kai yana kallonta kafin yace"Aa Transfer zan yi mata zata koma kasu su yi karatu tare daa yar'uwanta Nana khadija,bazan bari ku yi nesa dani ba bangaran karatu fa baku gayamin inda kuka tsaya a karatun ku ba..?
Sai na kasa mgana Yaya mariya tace tayi Nce cikin gamsuwa yace"Meyasa baki cigaba ba Mariya..?
Sai ta sunkuyar da kanta sai yayi mirmishi kafin yace"Zaki cigaba insha Allahu ilimi shine mace zan dauki Nauyin karatun ki da komai,su Nana Fatima kowacce sai da ta gama Degree tayi aure Nana Fadila Nurse ce tana aiki da aibitin Gwamnati na garin Lagos"
Ni dai na riga na zama mutum mutum ina jin sunayen wasu ahalin namu da bamu taba sani ba,ni ya kallah kafin yace"Ke fa Fa"iza..?a ina kika tsaya a karatun ki..?.
Sai na kasa bashi amsa kaina na maida kasa kafin nace"Ban yi karatu ba ni"
Cikin mamaki yace"Bangane ba..?
Da Sauri Goggo tace"Fa'iza batayi karatun boko ba sai dai na addini,kasan Lokacin rasuwar mahaifin su mun raba su ne a Tsakanimu ta zauna hannun Kabiru ne kafin rasuwarsa D'ansa ma take aure yanzu Haka mai suna Ishaq"
Kai Tsaye yace"Aa wannan ba Hujja ba ne. Da za'a barta batayi karatu ba,Ai ilimi ginshiki ne ga y'a mace Dole Fa'iza zata koma makaranta domin ta sake inganta rayuwarta"
Cikin rauni nace"ko primary fa ban yi ba,sannan ina da raunin ji"
Cikin yar dariya ya Dafa kaina Lokaci d'aya yana fadin"Kada ki damu girma baya hana neman ilimi lesson Teacher za'a sama miki ya koyar dake kafin ki fara shiga makaranta,Mganar raunin ji kada ki damu makafi ma sun yi karatu kuma sun zama wani abu indai ni ina Raye y'ayan yar'uwata bazasu taggayara ba,na ji takaici da ban sameta a raye taji gajiyan dukiyata ba,ammh bakomai tunda ga ku, kamar wani nauyi ne a wuyana kamar yadda Nauyin su Nana khadija ya rataya a wuyana"
kai tsaye yake mganarsa Kuma babu tsoro ko shakka,Nan ya rika mana Tambayoyi kan Rayuwarmu muna bashi amsa ya tambayemu muna sana'a ko kasuwanci ne muka gayamasa ni na fad'amasa ina zobo da kunin aya ina Turarekan kamshi.
Mirmishi yayi cikin jin dadi yace"Good ina son naga mace da ta iya sana'o'iin hannu.Dakyau Fa'iza zamu inganta wannan kasuwan cin naki'
Ban san Lokacin da nayi mirmishi ba,Sai Hira ta tsinke a tsakaninmu shi kuma sai kiransa ake yi a waya ya koma gefe ya sauya harshe zuwa Turanci yana ta mgana mu ko Inno tajamu jikinta tana fadin"Ya'yan nan ban ji kun ce kun yafe min ba..?
Dukkanmu muka ce mun yafe mata tana dariyan jin dadi tace"Nagode. Daga yau kun tashi daga marasa kaka kun koma yan gatan Inno.Daga yau ni kakarku ce Baban Nanah Kuma Uba yake gareku Aziza kuma uwa take gareku su Nana fadila kuma yan'uwan ku ne"
Wani farinciki ya Lullub'eni daman zan ga wannan ranar..?
Ashe mu ma muna da gata bamu sani ba..?Nan Yaya mariya ta kira Yaya Asiya ta fad'amata haka ta dinga Tsallen Murna aka bata Inno suka gaisa Lokacin Abban ya gama wayar aka bashi suka yi mgana mutum ne mai barkwanci da son yan'uwa Yaya Asiya ta kirasa da kawu yace"Sunana Abba.Ya'yana haka suke kira kuma ya'yana ne haka zaku rika kirana.
An ce kina kano ai yan'uwanki da maman ku duk suna kano sun je sha'ani nima daganan ni da Inno kanon zamu je zan sauketa ni kuma zan hau jirgi zuwa Porthercourt,muna da Taro ammh da zarar na dawo zan kawo su dukkansu su gan ku,kuma kuga sauran yan'uwan ku"
Cikin murna Yaya Asiya tace"Na kosa Abba don Allah ku zo da wuri"
Cikin Dariya yace"Kada ki damu ba domin kuna gidan mazajen ku ba, da duka Gidana zan maida ku.ko o a yanzu kowacce da mijinta zata zo da ya'yanta ina son ganin iyalan ku gabad'aya"
D haka suka yi sallama da Yaya Asiya duka duka ko awa uku bamu yi ba tare ba, ammh mun saba da juna ji muke yi kamar in ya tafi bazai dawo ba,kamar bazamu kara ganinsa ba,Sai dai ana ta kiransa jirgin karfe hudu da rabi zai hau a kano shiyasa suka yi shirin Tafiya idanuwan mu ya ciko da kwallah ya rike Hannayen mu yana fadin"Kada ku damu da zarar na Dawo daga tafiyar da nayi zamu zo sai kun gaji da ganinmu kuma zan tafi daku gidana kuje ku yi min sati d'aya na san komai akan ya'yana suma susan komai a kaina"
Bai zo da komai ba Saboda tafiyar Gaggawa ce kud'i ya zube mana da bamu san nawa bane Direba ya kawo su da wata bakar Jeep dankareriya,Su Baba ati ma ya cika su da kudi da Sallaman yana dawowa daga tafiya da shi da iyalansa zai dawo,Inno ma tana ta sallama da alkwarin wannan karon zumunci an fara kenan har Abada,kafin ya tafi ya karb'i lambobin mu har da na Yaya Isa,mune rakiya har bakin mota da zai shiga mota ya dafa kan Hafsah yana fadin"Auta sai na dawo ko.?domin kece auta Nana Khadija zata girme miki,Zamu dawo in sha Allahu bayan Abba har Babban Yaya ma kuna da shi"
Da haka muka yi sallama suna d'aga mana hannu muna daga musu hannu,Cikin gida muka koma ana ta maida zence Goggo ta kallemu tana fadin"Kunga abun Allah ko..?
Allah ya nufa ganawar sai a wannan lokacin ne"
Yaya mariya tace"Naji dadi Goggo naji Dadi yau naga wani ahali daga Ahalin Tamadina murna kamar zata kasheni"
Ta fad'a cikin farinciki Hafsah kuma ta Daka Tsalle tana fadin"Abba yace ni ce auta kuma muna da Big bros muna irin na ya'yan yan gayu"
Ni dai sai faman washe baki nake yi farinciki ya gama cikani Yaya Asiya ta kasa zama sai kira take muna bata labarin abunda ya faru,Murna kamar me tace itama cikin? Satin nan tana Tafe su Baba Ati sun koma gida da Tarin alherin Abba garesa muma kudi ne sun fi dubu dari ya zube mana,Goggo ko kwandala bata Dauka ba sai muka raba a tsakanimu,nan mukayi azahar da la'asar saannan muka tafi ni da Hafsah muna masu Farinciki ko da muka koma gida yara sun dawo makaranta Mama abun mamaki ita ta dafa musu Taliya Jallop muna shigowa Musty da Ahmad suka zo suka makaleni suna kiran Umma Umma daman nayo musu Tsaraban su Chaculate,Dakin Mama na fara shiga na gayamata na dawo ganin yanayi na fara'a yasa ta kalleni kafin tace"Ina fatan su Goggon lafiya..?
Cikin Tsananin Farinciki nace"Lafiya lau Mama. Daman Abba ne yayan Tamadina ya zo yau shine goggo ta saka aka daukomu"
Mama sai ta kasa gane kan mganar Cikin Mamaki tace"Bangane ba Wani Yayan tamadinan..?
Cikin zakwad'i na fara bata labari Cikin karin mamaki Mama tace"Ikon Allah ashe tana da dan'uwa kuma shima yana da iyalansa..?.
Kai tsaye nace"Sosai ma don ma tafiya ta kamasa yanzu, iyalan nasa kuma suna kano biki ammh yace da zarar ya Dawo zasu zo gabad'ayan su ganmu mu?gansu muma..,"
Sai Mama ta kasa mgana mamaki duk ya cikata Dakina na shiga Anum ta tare ni tana fadin"Umma nayi miki wanke wanke."
Amir kuma ya amsa min da cewa"Umma nayi miki shara"
Ina dariya nace"Allah yayi muku albarka ya'yan Umma"
Ahmad ke dane kafata yana neman kadani na murde kunnensa ina fadin"Umman zaka kada ko..?
Sai ya fara Dariya Musty na tayashi,Kan kujera ta na fada ina Sauke Hijabin Jikina Hafsah ta shige Daki Amir har ya shiga kitchen ya zubomin abincin Ya kawo min kenan yana fadin"Umma ga abinci na kawo miki ruwa..?
Kafin nayi mgana Anum ta Ruga taje ta Daukomin ruwan na karba ina fadin"Amun di'na ta zama yan mata fa"
Sai ta rufe fuska wai kunya ina ruwan Anum,Mama ce ta kwalama Amir ya kira ya fita sai ga shi ya Dawo da kudi wai cinikin zobon da akayi bayan ba na nan mamakin Mama ya kamani itace har da siyar min da zobo..?ban dai ce komai ba sai da na Huta naci abinci na leka nayi mata Godiya bata amsani ba,Ranar cikin Farinciki muka karishe yini,Yaran har sun Fahimci ina cikin farinciki sai da Amir yace"Umma kina ta dariya ko kin samu kudi ne..?
Dariya na saka ina mamakin wayon Amir yasan dariyata yasan Bacin raina,Kansa na shafa ina fadin"Sosai Amir, ammh ba kudi na samu ba abunda yafi kudi Daraja da Tsada na samu"Amir na mirmishi yace"Umma menene shi..?
Cikin bayyana Murnata nace"Zan gayamaka kaji"
Daganan sai ya bar mganar,Bamu yi mgana da Yaya Ishaq ba,sai washegari ban gayamasa ba ammh yanayin murna na sai da ta bayyana a waya sai da yayi min mgana yace"Fa'iza hala yau an kwashi cinikin zobo da kunin Aya ne kwasha kwasha naji jiki cikin Fara'a.?
Dariya ya bani har sun Fahimci in na samu kud'i ina murna sosai ban gayamasa ba na bari sai ya Dawo kwana Biyu Tsakani sai ga shi ya Dawo,ban kai ga ma gayamasa ba Har Mama ta rigani sai da daddare yake min mganar na kallesa ina da'gama masa kai alamun hakane cikin kallona yace"Na tayaku murna.."
Cikin farinciki nace"Mungode..Yace ai in suka zo har kai yana son gani"
Cikin mamaki yace"Ni kuma..?
Lafiya kuwa..?
Sai na girgiza kai ina fadin"Ban sani ba ya dai ce dukkan mu yake son ganin mazajen mu"
Daganan sai bai kara mgana ba,nima ban kara cemai komai ba kudin hannuna Jarin zobo na da kunin Aya na kara,Sannan nayi Humra makotan mu wata Amarya ta bani na yi mata,har da kwallacha.
Kwana Takwas da zuwan Abba Ya kira Hafsah yace gobe shi da duka iyalansa,Daman su Nana Fadila Daga biki basu koma ba ya Tsaida su yace sai sun zo anyi zumunci Yaya Asiya daman ta kwana Biyu a karofi,Murnan kamar zan zuba ruwa a kasa nasha,Har chan karofi ya kira Goggo ta saka aka gyara bangaran Hajiya na gidan Yaya isa inda za'a sauke su,sai kuma mganar abinci Matan Yaya isa da Yaya Salisu zasu ji da komai,Ga Yaya mariya da itama mun yi waya tace zata shirya musu abinci mai da rai da lafiya ni kuma nace zan yi zobo da kunin aya na Taho dashi a goben dani da yara da Yaya Ishaq da sai da Daddare na fadamai.
Yayi shuru kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Allah ya kaimu goben"
Mun yi zencen da Badariya da yake ta dawo shekaranjiya tace itama zata je kawai da Safe sai Yaya Ishaq ke fadamin Mama ma tace zataje ban yi mamaki ba araina nasan zataje ganin komai ne,kenan duka gidan zamu tafi,Itama Yaya Asiya mijinta aranar zai kamo Hanya da sauran yaran ni ma dani da iyalaina,Har girki sai da nayi jallop din shinkafa mai rai da lafiya da taji kayan lambu da nama nayi zobo da kunin Aya mai yawa,Na daukan mana kaya tunda dawowa badai ranar ba Kulle gidan mukayi,Tashar Mota Ishaq ya samo mana har kofar gida,Karfe d'aya da wani abu muka tashi Hafsah suna ta mgana da Yaya mariya har da Abban sun yi mgana yace Tafiyar ta su ta Motace,suna hanya sun Tsaya su yi sallah ne ammh sun kusa karisowa
Mun isa karofi Biyu da wani abu na rana, gida cike su Anum nata murna sun zo Karofi,har alokacin basu iso ba ammh sun ce sun shigo katsina suna gabda karisowa.
Yaya Asiya ta fimu murna saboda ita basu taba Haduwa ba ammh mu kanmu murnan ya cikamu,Yaya Isa da su Yaya ishaq da mazajen su Yaya mariya suna kofar gida,mu kuma muna cikin gida muna Dakon zuwan su.




*Janafty"*
[7/17, 7:33 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2013*

*Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.*
*09069067488*

Wajen misalin karfe uku na rana mukaji diran motoci da Hayaniya daga kofar gida,mu muna cikin gida sai muka kasa zama muka mimmike kan kafafun mu,muna masu kurama kofar falon Goggo ido domin ganin masu shigowa.
Yara ne almajirai daga waje suka fara shigowa da jakunkuna da akwatina, sai kuma bayan su wasu fararan yara kyawawa mace da namiji suka shigo mace iyakar ta sa'ar Anum namijin kuma kamar Musty ne,Da gudun su suka shigo daidai Lokacin suma su Anum sun kwasa aguje zasu fita waje sai suka had'e da yarinyar nan,Tsayawa suka yi suna kallon juna kamar susan juna sai kuma dukkansu suka washe baki suna Dariya Anum tace"Laa..Ke.."
Itama yar yarinya sai tayi dariya sai da Kumatunta suka loba kafin tace"Kema kinsan Gidan nan ne..?
Sai gabad'aya mamakin su ya kamamu kafin mu samu mu fita daga mamakin Ina Anum ta san wannan yarinyar mai kyau da ita,sai ga wasu mata Farare yan gayu sun biyo bayansu,da yi sallama sun shigo d'ayar Babar itace ke dauke da karamin yaro a Hannunta sai d'ayan da bata kai ta Tsawo ba tana rike da jakunkunansu na Hannu da wayoyinsu dukkansu Bakin less ne mai adon pink ajiki da mayafansu, a kallo farko in kayi musu zakasan yan gayu ne sannan masu ilimi ne da Nasaba mu dai muna ta bin su da maraba ji kawai ka ke yi ana"Maraban ku."
Sannunku da zuwa"
Goggo kuma ita ke faman fadin"Maraba da baki maraba da bakin mu"
Suna amsawa cikin sakewa lokaci daya suna kallon mutanen dake falon bayan su kuma wata matashiyar yarinya ce tsawon Hafsah inaga itace Nana Khadija itama kayanta iri Daya da na yan'uwanta,tana tafe da wata karamar jaka ta mata a bayanta,Daga ita sai ga wata Farar Mata ta bayyana Tare da Inno dukkansu cikin Fara'a mu dai bakin mu bai daina kiran musu sannun su da zuwa ba.
Gabadaya waje suka samu suka zazzauna,Yaya Asiya tayi ma Inno barka da zuwa data zauna a kasan Cafet ta mike kafa Saboda gajiyan zaman mota.ta kalleta lokaci d'aya tana fadin"Mariya ce ko.?
Kan Yaya Asiya na kasa tace"Aa Asiya ce"
Sai Inno ta rike baki tana fadin"Asiya..Sannu Asiya kece bamu had'u wanchan zuwan ba,ba shakka Allah ya jikan Hafsatu da rahma"
A ka amsa da Ameen Nana khadija tace"Don Allah ina so zan shiga toilet"ina kusa sai na kalli Hafsah ina fadin"Hafsah rakata"
Sai Hafsah ta mike tace tazo ta rakata ta mike suka shige bedroom kowa ya bisu da kallo gwanin sha'awa.
Yar farar matar nan tace"Inno lalle Jini d'aya ba wasa ba, kinga Nana khadija kamar ta da wannan yar sa'arta ta ta, hala tana cikin ya'yan da marigayiyar ta bari ne..?
Inno tace"Itace Auta Hafsatu kenan. Ga Asiya nan itace Babban su sai Mariya sai Fa'iza gasu nan kun gansu ku bari Shi Baban Nana ya shigo shi da Abdul'ahad zaku ji sauran bayanin"
Daganan Goggo tace ko zasu yi sallah sukace sun tsaya a bisa hanya sun yi sallah,Sai dai aka fara kokarin gabatar musu da abinci Farar matar nan da daga ganinta itace mamansu tace"mu fa ba baki ba ne mun tsaya a inda muka yi sallah mun ci abinci zamu ci anjuma mu da mun zo kenan sai mun gama Zaga dangi gabad'aya ai abinci sai kun gaji da Dorawa kuna saukewa ko Inno..?
Tafad'a cikin barkwanci Inno tace"Kwarai kuwa"
Goggo tayi Dariya kafin tace"Ina shi Alhajin bai shigo ba..?
Inno tace"Ya tsaya da mazan dake waje"
Bata ma gama rufe baki ba sai ga su sun shigo,Yaya Isa ne yayi musu jagoranci,Abun mamaki da zugan yaran nan su Amir kamar sun san shi Bayan shi kuma wani zankaded'en Saurayi ne kamar shi, sai dai shi Saurayin fari ne sannan ya fishi jikin Murjewa,suna shigowa yaran na biye da su zuga guda Maman Nana tayi dariya tana fadin"Baban Nana baban yara kenan"
Baya ya juya yana fadin"Ina ya'yan nawa..?ku shigo mana ku ai ba surukanta zamu yi ba,Duk ya'yana ne ku ku shigo nan ai duk mun zama Daya"
Sai ga su Yaya ishaq sun shigo da mijin Yaya mariya da na Yaya Asiya sai Yaya Salisu waje aka basu suka zazzauna aka shiga gaisawa da tambayan Hanya,sannan muka tashi dukkammu muka durkushe a gabansa muna gaisheshi ya amsa bakinsa har kunne ya saka hannuwansa Biyu ya Dagomu yana fadin"Ku tashi ku zauna ya'yan Abba"
Gabadayamu muka zauna a gabansa yabi mu da kallo kafin ya yi mgana Yaya Asiya ganin yana kallonta yasa tayi Saurin cewa"Asiya ce Abba'
Gabadaya sai da akayi dariya shima Dariyan yayi yana fadin"Zan kama sunan sai kika rigani Ase ase ya gida da yaran..?kanta na kasa ta amsa mai sai ya fara waige yana fadin"To ni jikokin nawa yawa ne dasu kai yara maza kowa yaazo wajen mamansa mu gani"Kamar suna jira kowannen yazo ya rabe jikin uwarsa Anum har da kwantomin saman wuya rad'a take so tamin a kunne ban jita ba.
Abba ya kallemu ya kara kallonmu sai ya juya yana kallon Inno Lokaci d'aya yana fadin"Alhandulillah yar'uwata ta bar min zuru'a inno"
Inno ta gyad'a kai tana fadin"Ba shakka nima ai duk ta kara min yawan magidanta da kishiyoyi"
Abba na Dariya yace"Inno Maman Nana sai dai tayi hakuri Kishiyoyo gareta Rututu ba adadi"
Maman Nana ta washe bakinta fararan Hakoranta suka bayyana Lokaci daya tana fadin"Bakomai ban damu ba dad'in abun ma duk na Roba ce nice dai uwar Nana ta karfen"
Gabadaya dariya akayi daga ganinta itama akwai barkwanci su Mama na gefe suna Dariya Saurayin ya dago ya kallah yana fadin"Babban yaya ta kanka zan fara fa"
Mirmishi yayi mai kayatarwa kafin yace"Girman ka ne Abba"
Badariya ta kara kallonsa ita tun shigowarsa taga kamar ta san shi, sai dai ta kasa tuna a ina shi kuma bai ma Lura da ita ba D'aya bayan d'aya ya fara Gabatar da mu kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login