Showing 39001 words to 42000 words out of 157081 words
ya hango Mai Babbar daki, ta shigo ta kofar cikin gidan da yake fadar.."Faruq ya ce min kana nan a tsaye!" Murmushi yai ya ce mata. "Eh Ummi!" Mika mishi hannu tayi ya tako a hankali, ya kifa kanshi a kafad'arta, duk da ya fita tsawo amma haka tayi ta bugu-buga bayansa. "Ummi ina jin tsoro!" "Kada ka ji tsoro domin shine first enemy dinka, tsoro makiyanka ne idan ka sake tsoronka ta bayyana akan fuskarka duniya zata kiraka da lusari domin an sace maka matarka ka razana ka zubda hawaye, ba a kuka ba a tsoro ba a fargaba duk abinda Allah ya yi mai kyau ne, Zainaba zata dawo da sa hannunka amma maganar gaskiya sai ka cire kawazuci domin kawazuci ba zai mana aiki ba. Bana zargin wasu can amma ina kyautata zaton har da Alhaji Nafi'u a cikin wannan yanayin, sannan kuma ina zargin wasu da bana son bakona ya furta. Ka nutsu da kyau."
"Ummi ta ina zan fara? Taya xan fara nimanta? Ummi duk yadda na kai ga son kai zuciya nesa ba zan iya ba!" Duk wannan maganar da suke yi sun fita daga cikin masarautar ne suna tafiya. Sosai sun ma bar titin masarautar. "Zaka iya mana, wannan yakin naka ne, ita koda zata iya wani ikon Allah ne." A hankali ya kalli Mai Babbar daki, ganin wani dattijo yayi da yalwar gashi fari, a matuƙar razane ya kalli dattijon. "Mai Martaba, lokaci yayi da ya dace ka san sirrin da yake cikin masarautar zanzabira, ya dace ka san waye a tare da kai. Amma b'atar Uwar Sarki dole tasa na fito na zo ga Meramo, kayi hakuri sunana Baba titi, ka tuna tsohon da yake kawo maka mad'i kana Yaro? Sannan idan yazo yana nuna maka abinda yake faruwa a daji, duk ranar juma'a nake zuwa fada wurin Attahiru Shehu Yayari!" Sunkuyar da kai yayi kafin ya ce mata. "Baba mad'i ta yiwu na tunaka amma a yanzu ba shi ne matsalata ba;" ya juya zai bar titin. " Idan ka koma cikin fadar zasu iya samun damar fitar da kudirinsu, ba daya ko biyu ba ko uku ba. Wasa ce da rayuwarka. Idan ka koma ka saka a kama Zailani domin yana cikin waɗanda suka bada labarin fitarta, a lokacin da ka bar daurin auren ka bita ba za a cimmata ba, amma kai ka yi sanadin b'atarta, domin daga kai har Bargaga baku yi kome ba bayan ta gaya maka jiya cewa tana jin tsoro idan bata ji tsoro ba Shago gaya min me zata yi? Yar baiwa ce da ake nuna mata wasu abubuwan a mafarkinta, kasan hujjar aurenka da ita? Saboda karawa naka tauraron karfi idan har na kara lissafi a yau, shekaru dari hudu da goma cibb da mutuwar Aojanah wanda haka yasa ta rasa duk wani damarta na isa gare ta, jinin Zainab Awatif shi take bukata , shaidanun tsakiyar birnin sun bayyana don haka ruwanka ne ka bincika gidanka ko kuma ka zauna ko gawarta ba zaka gani ba har abada, ni da Ismaha zamu tabbatar da mun nimo ta, wannan shine alkawarin da nayiwa Mahaifiyarka! Shawara daya zan baka ko ga matanka kada ka nuna musu b'atar Awatif ya dame ka, domin akwai mugaye a cikinsu" Ya rungume Isma, a hankali wani kofa ya bayyana saka hannu yayi ya tura sannan ya shige kofar ta b'ace bakiɗaya, da gudu kamar mai motsa jiki ya nufi Fada, kai tsaye wurin mai babbar daki ya nufa da take rike da kanta da hannu bibbiyu. Kallonsa tayi yadda ya shigo, yana hakki. "Kin san wanda ya fita dazun?" "Baba titi?" Ta furta a hankali, "Eh shi wai dama na sanshi?" "Ka manta da shi ne? Baba mai mad'i?" Ta kuma tambayar shi, gyad'a kai yayi ya ce mata..".Na manta da shi, sai dai ko!" "Me ya ce maka?" "Yace kada na kara komawa fada!" Ya furta a hankali domin ta gama gajiya da kome. "Kada ka sare, a yanzu zaka fahimci su waye ke tare da kai su waye zasu iya taya ka wannan yaƙin, babu batun guduwa, yanzu zaka yi aiki da ƙwaƙwalwarka sama da zuciyarka."
Rarrashi da ban baki, haka mai babbar tayi ta mishi, har da raka shi gidansa. Sannan Faruq suka dawo da ita. A lokacin da ta dawo sai take jin wani irin yanayi mai tab'a zuciya, amma bata son kowa ya san tana cikin tashin hankali. Iyayen Zainab din suma haka suka kasance shi yasa ta ce su tafi kawai ayi ta addu'a, a ga abinda Allah zai yi. Amma tana shiga dakinta ta fashe da da kuka, wani irin ciwo take ji, kamar lokacin da aka sace Salmanu Faris yana yaro, tsoro da tausayin Zainab din ya cika zuciyarta. Tayi kuka tayi matuqar danasanin aure a cikin wannan bakar masarautar, wannan shine karo na uku da take jin tsoron kada ta sake rasa wani da take ji da shi a cikin rayuwarta, ta rasa Salmanu da fari ya dawo dai-dai lokacin da take rasa Mai Martaba Attahiru Shehu Yayari, sai ta ji zuciyarta tayi wani irin nauyi.
**
Malam Junaid Gobir, kuwa kasa rike zuciyarshi yayi domin haka yayi ta zubar da hawaye yana jin laifinsa ne na daukar kasadar jefa Zainab cikin wannan masifar. idan ka cire Maluma bakiɗaya gidan kowa a cikin yake, idan ka cire Mommy Turai da tasan kome yake faruwa, wani irin dad'i take ji, idan Zainab ta mutu Iram zata shiga cikin gidan Salmanu Faris, kuma dole ya yafe mata dukiyarshi da yake hannunta, ban da ma rashin kunya irin nasa yana aure yar Mijinta, sannan ya zauna yana mata barazana. Dariya ta saka Tauhid ya ce mata. "Kina da hannu a kan b'atar da Ikhlas tayi kenan domin haka kawai ba zaki wannan dariyar da farin ciki ba, Mommy akwai Allah idan babu shi a yanzu Akwai ranar da mai tikewa zai tike kome na shi, Tun ina Yaro na fahimci yadda kike son ganin bayan Ikhlas, amma Allah bai nufa ba, ki duba Iram yadda ta koma kamar wata bola kome nata ya lalace, me yasa Abba ya ki rabuwa da ke? Saboda rayuwar Iram da ni Mommy nasan wata rana zaki fahimci abinda nake nufi amma lokacin da kure yadda zaki yi ta kuka shine nake hango miki, Mommy ki kyale Ikhlas ta rayu da Mijinta lafiya, idan kuma kika ki tow kuwa abubuwa zasu faru marasa dad'i. Na gaya miki." Ya fita a gidan zuciyarshi tana mishi zafi, duk yadda yaso ya dauke kai akan abinda Mommy Turai take yi ba zai iya wannan lokacin ba, domin tana shirin Crossing line din da ba nata ba ne.
Bakiɗaya yake jin kamar kanshi zai fashe, idan yayi shiru kome zai faru. Yana kan babban titin old zanzabira, aka kira shi a waya yana ɗauka Alhaji Nafi'u ne wnada yayiwa lakabi da Devil king, dauka yayi ya ce mishi.."Me kake so?" "Kada ka sake ka ce zaka yi wani shirme Mahaifiyarka ta ce zaka gayawa Mahaifinka, ka sani sai ka zab'a domin ga Abid zai wuce gidansa idan ka sake bakinka ya bude Matarshi da shi kanshi da Yaransa, gobe za a hada dukkansu har da Ikhlas ko? Duk za'a ayi musu jana'iza sai mu ga yadda za a kama Uwarka bayan na saka kai ma an bi ta kanka. Akan muradinmu dole mu hakura da na jikinmu balle kuma irinka da kake jin dadinka, gara ka koma gefe mu yi aikinmu idan ka sake kayi wani motsi hmm!" Kashe wayar yayi ya kifa kanshi a samar motar, yana jin kuka na zuwa mishi, a hankali yake shashekar kuka yana jin kamar zai mutuwa. Buga kofar motar aka yi ya d'ago kai yana kallon Mutumin ya sauke glass din motar, kamar jira mutumin ya janyo wani abu a cikin aljuhunsa, take ya sarke wuyar Tauhid. Gashi babu kowa a titin haka ya ja igiyar tun Tauhid yana ƙoƙarin kwantar kanshi har ya kasa, har Ubangiji ya dauki rayuwarsa, bayan igiyar ta yanke mishi makogaro, jini ya shiga fita ta bakinshi da hancinsa, kunnensa da idanunsa haka jini yake zuba, a hankali mutumin ya janye igiyar sannan ta rufe motar tare da jingina kan Tauhid akan sitiyerin motar. Kafin ya dauki wayarshi ya danna number a hankali ya ce . "Hajiya Layla kome ya kammala, an ajiye mata tambarin da ba zata manta ba, Ya jikin Princess?" Yana tambayarta daga can ta ce masa da sauki sannan ya kashe wayar ya nufi inda machine dinsa ya hau ya fita da gudu, ya bar unguwar.
***
Malam Junaid Gobir.
Yana tsaye amma shi kaɗai yasan yadda yake ji, yadda zuciyarsa take bugawa yasan kawai ya rasa Zainab. "Kiran min Abid, Yunus, Nawwas da Nuraim ku tabbatar da suna gida Ina Tauhid? Na ji karan fitarshi a motarsa!" "Zasu dawo bari na kira su!" Inji Umma, a hankali ta kira su Abid ya ce ya isa gida, Nuraim da Yunus tare da Nawwas suna bangaren Maluma." Shiru tayi kafin ta ce mishi, "Tauhid bai dauki kiran ba!" Gabanshi ne ta fadi, kafin yaron ya bar gidan sai da ya tsaya ya kalli window Malam Junaid, shima yana tsaye yana kallonshi.
"Kira min Turai ina, ina ta tura min Yaro?" Ya faɗa yana jin wani irin tsoro, ya cika shi akwai abinda ya kuma faruwa tsoron ya kara ninka na baya, yana ji kamar ya rasa wasu Abubuwan masu daraja da muhimmanci a rayuwarshi, idanunsa ne suka cika da kwalla ya ce. "Ba zan iya zama ba babu Zainab babu Tauhid a wannan daren Ina Ibrahim ya tafi?" Ya fada hawaye na zuba mishi, haka ya nufi bangaren Mommy Turai ya same ta itama tana ta kiran Layin Tauhid din bai dauka ba. "Ina kika tura min Yaro?" Hankalinta a tashe ta kalle shi kafin ta sunkuyar da kai tana jin wani tashin hankali na cika mata zuciya. Bata iya magana ba haka ta gama surutunsa ya bar parlourn. A cikin daren haka ya kasa zama ya kasa tsaye ya saka kai ya fito daga cikin gidan, yana bin gefen hanya tana leka motar da suke gefen hanya. Cikin gidan kuwa ganin yadda ya fita Umma ta fadawa sauran Yan mazan suka fito aka rufa mishi baya, haka Nuraim ya tafi ya dauko mota suka shiga nimansa, a rana guda ya rasa Yara masu daraja a zuciyarshi.. a babban titi suka hango shi yana tsaye hannunshi a baya, ya hango motar Tauhid din. Yadda suka karasa wurinsa, tare da bude mishi motar suna faɗin. "Abba shigo mu karasa inda yake!" Suma sun hango motar. Haka ya shiga gaban motar suka bi hanya daya suka isa inda yake da fari Yunus a fusace ya fito yana faɗin. "Ban da iskanci idan kasan zaka yi shirmenka ai sai ka yi a gida kazo titi ka d'aga mana hankali, fisabiilillahi Yaron nan baya jin magana kwana biyu na zata ya shiryu ne ashe iskancinsa bai sauya ba." Ya nufi inda motar yake yana masifa, koda ya isa ya buga kofar. Tauhid bai bude ba, haka yasa shi jan hannun motar amma a rufe. A matukar tsorace da yanayin dan uwansa da ya gani ya saka shi jin wani abu ya lullube shi kamar an lullube shi da danyen nama, ya kara kai hannunsa zai ja kofar jinin da ya dangwala a hannunsa yasa shi yin baya, haka da sauran suka gani suka fito daga motar a guje, sun san waye Yunus ba kome yake firgita shi har haka ba, amma ganin yadda yake kallon hannunsa da kuma yadda hasken fitilar kan hanya ya nuna fuskarsa yasa suka fito, Nuraim ya rigasu isowa yana zuwa ya naushi glass din motar sau biyu sai da ta fashe tayi dagga-dagga, suka zube a jikin Tauhid din, da sauri ya tab'a Tauhid din, zubewa yayi can jiki har lokacin yana zuba. "Innalillahi wainnalihir rajoun! Bude kofar Nuraim!" Haka suka bude kofar motar da kyar, suka.janyo shi amma ina, yadda ya suka janyo shi ya zube a jikin Yunus, jini ya wanke mishi jiki irin da zafin nan bai yi sanyi ba ma balle a ce ya fara dandarewa. Wani irin ihu Nawwas ya fasa tare da cewa. " Yunus tafiyar minti goma ne zuwa babban asibiti, kawo shi na kai shi bai mutu!" Ya amshi Tauhid din ya saka gudu kamar zai tashi sama, Malam Junaid yana tsaye a wurin motar, hawaye na zuba mishi yau ya ga abinda wasu gani yau ya ga gawar Ibrahim me yayi suka kashe shi? Yana kallon Yara maza ukun rike da dan uwansu na hudu suna gudu.....
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 15
Duk da zafin da yake ji na lalacewar Yaran Turai, amma yau daya yaji kaf duniya babu yaran da yake so da tausayi sama da Tauhidi da Zainaba, sun kashe mishi Tauhid yanzu mai ya rage mishi? Rayuwar sauran Yaran zai kare ko jiran gawar Zainaba? Yayi kanshi wannan tambayar da bai da amsarta, haka ya shiga kira CP ya gaya mishi abinda ya faru a wannan daren, CP ya tambaye shi yana ina? Ya ce mishi. "Gani a wurin motarshi!" Ya furta a sanyayye, "ok ka jira ga mutanenmu nan zuwa!" "Allah ya kawo ku!" Ya furta a hankali, lumshe idanun yayi yana tuna dabi'a da rashin jin Tauhid din, ba a tab'a kawo mishi karar shi ba, duk rashin jinsa baya wuce wurin yan uwansa da shi kanshi. "Abba dubu ashirin kawai idan na fara aiki zan biya ka." Idan yaki bashi yayi ta fitinar shi kenan ko kuma ya samu Maluma ya ce mata. "Ina ta bin Abba ya bani dubu ashirin sai ya ga an biyo ni na runto abin fada a unguwa." Haka zata dauko dubu ashirin ta bashi ya fita idan ya gama na kwana biyu ya bi yan uwansa, su yi ta fada da Yunus yana cewa ba zai bashi ba, shi kuma yana faɗin wallahi sai ya bashi dole ya taimaka mishi kuma hakkinsa ne ya bashi tunda shi ɗan uwansa ne, ashe duk abinda yake duk na lokaci ne zai tafi ya barsu. "Malam Junaid!" Taimakin Kwamishinan yan sanda ya kira shi sunan shi. D'ago kai yayi yana kallon yan sanda. "Na'am kun zo?" "Eh Malam motar ce wancan?" Gyada mishi kai yayi, yan sanda suka nufi wurin motar.
Suka fara bincike tare da tambayoyi, irin wanda aikinsu ya tanadar. Kawai Malam Junaid yana amsawa ne amma zuciyarsa tana asibitin, yadda ya ga Tauhid yana son yayi mishi kallon ƙarshe, yana son ya mishi kallon daga wannan ba zan kara ganinka ba. Amma ina haka aka yi ta bincike har zuwa wani lokaci. Kafin suka nufi asibiti.
A lokacin da Yunus suka isa asibitin, Tare su aka yi Nawwas yana ihun kiran "Doctor ina kuke? Ina kuke ku zo don Allah!" Haka suna nufe su. A yadda likitocin suka yi jingun-jingun zaka fahimci lamarin ya wuce saninsu, babu wnada ya iya daura hannunsa akan gawar domin baya bukatar wani abu tunda ya rigada ya mutu, janyo hannun Likitan Nawwas yayi yana faɗin. "Ce mai ya tashi, zan bashi dubu ashirin," "Likita ka gaya mishi kankara mishi ashirin!" Inji Nuraim, a hankali. "Zan bashi duk abinda nake da shi a cikin account don Allah ku tashe shi." Yunus dai yana durkushe gaban gawan da aka daura akan gadon marasa lafiya, yana rungume da hannunshi, hawaye ne yake zuba mishi kamar mace, yau yake jin wani irin ciwo da tsanar kome na duniya, Duk abinda Tauhid yake bai taɓa wayewar gari bai ce mishi. "Yaya Yunus ban san me ya sa ka tsane ni ba, bayan ni dai ban maka kome ba, sannan idan don tambayarka da nake yi ne, Ya Yunus kayi hakuri waye ya sani ko iya rabona nake ciki, waye ya sani wata rana sai dai ku bada da sunana sadaka, amma wallahi ko kashe ni zaka yi sai ka bani dubu ashirin din nan, ni haka Allah ya yi da son dubu ashirin!" Hawaye ne yake zuba mishi shar-shar yana kuka kamar Yaro karami. "Tashi don Allah, tashi mu tafi gida zamu baka duk abinda kake bukata! Tashi kada ka saka zuciyar mu tsoro da karaya!" Drama da tashin hankali yan uwa uku suka yi ta yi asibitin, a lokacin labarin mutuwar Tauhid, a lokacin Abid ya iso, yana zuwa ya ce musu. "Wannan wani irin hauka ne?" Domin dukkansu uku kuka suke a emergency, a hankali suka taso suka rufe shi tare da kuka, a wannan lokacin yan sanda suka iso, tare da Mai Martaba Salmanu Faris wanda kana ganinshi a gigice yake, mutuwar Tauhid ya tab'a shi ko kwana biyu da suka wuce ya shigo akan sabuwar machine dinsa wanda ya ji labarin saya mishi aka yi, duk da yaki fada mishi amma ya ce mishi Abba ne, koda ya zo nunawa Ikhlas bayan ta gama mishi Allah ya sanya alkhairi, ya ce mata. "Ba fa xan bar gidan nan sai kin ban kudin mai dubu ashirin, na gaya miki, domin kuwa ba zan yi zuwan banza ba!" Ya fada yana wani harde hannu a kirjinsa, murmushi tayi tana faɗin. "Kai dai Matsalarka sai anyi maka asiri a jikin dubu ashirin kowa ya huta!" "Kafin wannan lokacin idan Allah ya dauki rayuwata, kin huta da ganina sai kin tunani kina son ki bani dubu ashirin ma bana nan gara ki bani rabona kafin wata rana kina ji kina gani zaki ji kewar ina ma da ina nan."
Yaron nan ya zo ya musu bankwana kenan, idanunsa ne ya cika da kwalla. Tausayin yaron yaji ya cika mishi rai, sai zainab ne ta dawo ranshi, ya zai