Showing 120001 words to 123000 words out of 157081 words

Chapter 41 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

20

yi sama da shi. "Inna.... Wayyo Allah, Innahuuuuuuuuuu!" Wani irin ihu ya saka lokacin da ya fahimci ya zama abin wasan wasu al'umma da wata duniya ta daban, yadda ake wasan carabke haka suke cilla shi suna fadin.."wan bani, wan baka ba ni ba!" Shi kan ba mamaki zuciyarshi ta jima da bugawa domin tunda ya ga yadda ake wasan carabke da shi a sararin subuhana, tuni ya rintsa idanunsa, sauke shi aka yi kasa tare da cewa.."Zaka gaya min yadda ake miyar kwadi?" "Wannan wacce irin wulakanci ne balbela kirasa miyar da zaki ci sai ta kwadi?"

Juyawa tsuntsuwar tayi tana faɗin.."ina laifin don nace zan ci miyar kwadi, tunda Yallabai Aryan ya shiga tsakaninmu kowa ya kama gabanshi, ka iya gasa burodi mai tana da kwayon kadangaru?"

Fashe da kuka Alhaji Kabiru Hammud Yayari yayi yana faɗin. "Kuyi hakuri!" "Ni kuma shayin dodon kodi zaka min!" "Ni kuma yau ina son na ji da gaske ne ana dafa dutse!"

"Ni zaka fara yiwa!"

""Ni xaka fara yiwa!" Aka fara wasan jaye-jaye da shi, kamar zasu a cire mishi hannu, kai da aka fara wasan kura da shi wata akuya ta ce musu. "Kai ku tsaya mu tura shi can ya tsinko mana ciyawa ina kwadayin danyen ciyawa!"

"Ba wani ciyawa sai ta fara min miyar kwadi!"

"Wallahi ban iya ba!" "Au ashe yana magana?" Ai kuwa suka cigaba da carabke da shi suna cilla shi, ihu yake yana ya tuba.

"Zamu kyale ka! Amma sai ka gaya mana meye shirinku da kuke yi akan Salmanu Faris?" Aryan yazo kanshi tsaya a iska.."Shirinmu shine a shayar da shi guba, da farko mun so d'agawa Zainaba hankali yadda zata amince yayi tarayya da Ikram, sai aka yi rashin dace yaki yi yadda muke so, shine muka saka aka bishi aka buge motarshi, duk shiri ne!"

"Waye da waye a shirin naku?"

"Hajiya Bilqis, Hajiya Nuratu Kanwar Attahiru Shehu Yayari, matar Ajiyar Zanzabira, tana cikin masu son ganin bayan Ikhlas d Mijinta!"

"Waye ya bada shawarar kashe Malam Junaid?"

"Wannan ne Nuru Yayari tare da taimakon Alhaji Nafi'u da Rilwanu Yayari!"

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 44

"Me yasa kuka kashe shi?"

"Saboda ya sayi duk mutanen Fadan, sannan ya gano cewa mune nan muka kashe Attahiru Shehu Yayari, shine ya ce zai gayawa Yarshi a dauki matakin da ya ce."

"Amma yanzu me ya faru kuke son tafiya da Salman daga cikin gidanshi?" "Idan yana tare da zainab ba zamu iya kashe shi ba, shi yasa muka ce a fitar da shi daga cikin gidan." "Wayyo kunga mugayen mutane, ashe mu bamu kai ku bakar zuciya ba." Inji wata bera tana zane shi da bin ta. "Yanzu yan sanda zasu zo domin na tura sakon kun sace Dan gidan Mai Martaba akan a baku kudin fansa bayan kun saka aka kashe Ubansa."

Yana gama fadar haka yasa aka daure shi, suka barshi a wurin Alhaji Kabiru Hammud Yayari, yana rike da wuka a kasa kuwa Alhaji Nuru ne a baje. Baya ko motsin kirki. "Zan sako maka danka, amma daga kai har shi zaku kasance kuna jinyar kanku a gidan Yari ne." Yana shiru sai ga motar yan sanda suka shigo cikin gidan, lokacin da suka shigo sun samu Alhaji Kabiru Hammud Yayari zaune ga bindiga ga kuma Alhaji Nuru Yayari kwance cikin jini da alamar harbinsa aka, wanda kana gani kasan yanzu aka yi, ba wata magana suka sanyawa Alhaji Kabiru Hammud Yayari, handcutt suka fita da shi aka kira motar asibiti suka dauki Alhaji Nuru zuwa asibiti, shi kuwa Ayaan da yake barci aka dauke shi zuwa fada.

Kafin wani lokaci labari ya karade Zanzabira, yadda aka samu manyan cikin fadar Zanzabira da yunkurin kisan kai da kuma sace dan wurin Salmanu Faris, a can office din Yan sanda Alhaji Kabiru ya fara lissafo mutanen da suke da hannu a kasar Attahiru Shehu Yayari da Malam Junaid, kafin wani lokaci an turo jami'an tsaron cikin fada suka dauki Hajiya Bilqis, wnada haka ya tilastawa Salim Attahiru Shehu Yayari barin Zanzabira ba tare da ya bar wani trace da za a same shi ba, yasan matuƙar mahaifiyarshi tayi magana zai kasance abin nima, sai dai bai sani ba daga gudun da yayi yasa aka fara zarginsa har mutane na cewa tunda ya gudu yana da hannu a cikin abinda ya faru, kwanaki biyar sai gashi ya dawo ya kai kanshi office din ya sanda da fadin shi ya kashe Mahaifinsu, yan sanda suka ce sun dauki statement na Mahaifiyarshi, ta kuma tabbatar ita ce tayi kisan. Lokacin da aka fito mishi da ita, yana kuka wiwi ya ce mata ."Mama me yasa?" "Idan kai ne anan zan mutu ne a waje da bakin cikin yaushe zaka dawo gare ni, amma ni idan ka kasance a cikin ko ba kome zaku zo duba ni, zaku na tunawa da ni. Ba zan so kayi ruin rayuwarka anan ba domin kana bukatar tsayawa a gefen Zainab Junaid, kayi yaki ka samo ta ita din taka ce bata lusarin can ba." Hawaye ne ya zubo mishi tabbas dole ya kwace Zainaba.

Daga nan ya wuce Fada, har wurin Mai Babbar daki ta shiga ya same ta zaune ta damu sosai. Kuka yake shima yana bata hakuri, tausayi ya bata ta ce mishi. "Kada ka damu nasan itama sakata aka yi amma da kanta ba zata yi sanadin mijinta ba, abinda a can Jamus ya rasu!" Ta fada tana murmushi tana son ya rabu da damuwar da yake ciki.

***

Haka fada ya kasance sai ya zama kowa shakkar kowa yake domin ba asan me yake tafe da dan uwansa ba, haka kusan sati ga aikin Asibitin ya dauki hanya.

Tunda abin ya faru, Nadiyyah take cikin tsoro bata san ko zasu biyo ta kanta ba, tunda aka dawo da Ayaan na lura Aryaan bai kara bayyana a jikinshi ba, abin ya bani mamaki. Yau na shiga dakin da Yaya yaƙe, na ji karar monitor dinsa, a hankali na duba na ga idanunsa biyu kamar mai nazari. "Yaya?" Kallona yayi. Na rufe bakina, na isa tare da rungume shi, ina wani irin kuka.. murmushi yayi yana faɗin. "Zainaba mafarki nake kamar ana ta yaki." "Alhamdulillahi, an zo karshen Yakin ai!" Murmushi yayi yana faɗin. "Na gaji da kwanciya!" Da sauri na fita na kira Faruq, muka dawo tare, d'aga shi zaune muka yi na fashe da kuka, fita Faruq yayi ya kira Nadiyyah da Ijlal, suka tawo, ganin shi suka fara ihu, a hankali na bar dakin naje nayi alola, sannan aka kira likitoci suka shiga duba shi. Sallah nayi ina gayawa Allah kukanmu, tare da gode mishi da wannan dibin alkhairin da yayi mana.yau Yaya ya farfaɗo, haka aka yi ta murna can sai ga Mai babbar daki, Bilqis da take cike da kunya da abinda Mamanta tayi, Salim Kubrah, Daulah da kowa da kowa an hadu, hatta Hisham duk sun ce zasu tawo.

Gidanmu ma na fada musu, bayan na idar da sallah, na je wurin na ga b wnada yayi tunanin bashi wani abu, fita nayi na dama mishi garin kunun talbiya, sannan na kawo mishi, yana sha yana murmushi domin mai babbar daki ce take bashi, ya kalle ni yana faɗin.."jikina ciwo yaƙe!" "Idan ka gama sai a maka wanka!" Domin ko bakinsa da ya wanke roba aka kawo mishi, yana gamawa aka hada mishi ruwa, Mazan suka kai shi ban daki yayi wanka da kanshi, sannan ya rage gashinsa sannan suka fito da shi, aka gyara gadon da dakin aka fito da shi parlourna, ya zauna ana ta hira, babu wanda yayi yunkurin gaya masa mutuwar Abba domin nayi ƙoƙarin tura musu sako ta text message.

Sun amince kuwa da na fito zan haura sama Nadiyyah da Aneesah da suke gulmar mutane na ji tana faɗin. "Jiki na rawa ya kasa barin motsi za a cigaba da iskanci." Murmushi nayi na tsaya na kalli Nadiyyah na ce mata. "Thank God da ni ba mayya ba ce da take bin majinyaci yana kwance, ita macen da ta isa bata bin miji halin rai kwaikwai mutu kwai kwai." Dariya Ijlal tayi tana faɗin. "Mu da gidanmu wata ta kaso aurenta zata ishe mu!" "Kambu da wa kike?" Hanyar Part ta nufa tana shiga ta ga ta saka key ta ce mata. "Mai kishi da matan yayanta how market?" Ta haura sama da gudu, "tow shegiya yar lesbian kawai!" "Kuma a haka Yayanki ya cusa babba torcinsa a cikin wurin kai har da wani rawa yake, wani kerma yake yaji kayan yar hannu? Ke fa? Uwar miji da danginsa suka koro ki!" Ni dama tunda na basu amsa nayi tafiyata, ban san ya suka kare ba, fada sosai akayi Nadiyyah kuwa kiranta ƙaruwar turawa Ijlal tayi kai abun bai yi dad'i ba, mai babbar daki ta tsawata musu amma Aneesah bata bari ba, daga sama Ijlal ta ce mata. "Anyi asarar uwar da ta haife ka ma baka ga girmanta ba uban waye zaka ga girmansa?" Fitowa nayi zan sauka kasa muka yi ido hudu da ita ba musu ta wuce ɗakinta, na nufi bangarenshi, na samu Mai Babbar daki tana kuka akan abinda Aneesah take mata, kaina a kasa na ajiye mishi kayansa da yake dakina zan fita.."Yanzu ko zaki tafi gida kada ta bi ki ta zauna anan ki huta ko Fulani Babba?" Ya tambaye ni bayan ya gama yanke shawararshi. Ban kula shi ba na wuce abina Ni dai nasan zaman Aneesah babu alkhairi. Budar bakin Salim ya ce mishi. "A'a ba zata zauna ba, daga yau ba zata kara saka ki kuka ba, nayi miki alkawarin haka, sannan ta zauna anan wani abun zai kara faruwa!" Sai a lokacin hankalina ya dawo jikina, na rasa murna xan yi ko takaici har ya tashi zai fara iyayinsa na fama.

Haka suka watse, washi gari ake gaya za'a shiga kotu da su Alhaji Nuru Yayari da Alhaji Kabiru Hammud Yayari, ban yi wani murna ba domin nasan ba wani adalci zamu samu ba, haka yasa na share zancen duk da dama Faruq ne yake gaya min, the next day Yayuna suka zo sai raba idanun yake nasan wanda yake nima, Abba yake nima can da yaji babu wanda ya mishi maganar Abba ya ce musu. "Wai ina Abba ne na ji baku ce yana gaishe ni ba?" Zama nayi kusa da shi na rike hannunsa. "Kada ka damu akan Abba zai zo duba ka. Yaushe ka tashi ne baya gari ne." "Ku bani number shi na kira shi!" ", Babu amfanin boye mishi gara ya sani babu Abba!" Rintsa idanuna nayi tare da sunkuyar da kaina, ina damke hannunsa. "Abba ya rasu yanzu ana niman kusan kwanaki arba'in kenan!" Wani irin zabura yayi tare da cewa. "Wacce irin magana ce haka? Ya rasu? Hatsari yayi? Ciwo yayi? Me ya same shi!"

A hankali Umma ta ce bakinta idanunta da suka cika da kwalla ta ce mishi. "Ya fito sallah asuba kenan, wani makocin mu yake gaya mana yaga lokacin da wani Yaro ya zo ya tsaya gabansa suna magana kafin ya ja gidansa ya rufe yaron nan ya sukawa Malam wuka sau uku a cikinsa sai gefen wuyarshi da ya yanke shi da kuma wani abu da ya caka mishi a kirjinsa." Wani irin kuka na sake irin wannan kisar tozarci suka yiwa Abba. Irin wannan cin zarafin suka yiwa Abba, gaskiya idan hukuma bata mana adalci ba waye zai mana adalci, sai aka koma dakin ana bani hakuri..kusan kaina ciwo ya kama.

Salim ya fita daga cikin dakin, can waje ya fita ya kuna wata ƙatuwar sigarinsa ya fara sha..

.......

Yana tsaye ya ga Nadiyyah da Aneesah, d'aga wayarshi yayi ya tura sako, can aka turo mishi da *done* daga haka ya bar gidan, bayan sallah isha Aneesah ta shirya ita ɗaya ta dauko hanya zata dawo gida, wata mota Bus tayi parking a gefen hanya, tana zuwa wurin suka fito tare da kwamushe ta.

Mai Babbar daki bata kawo bat dawo ba, Sailuba ta rufe gidan. Washi gari ma babu alamarta sai tayi tunanin ko tana gidan dan uwanta ne, ta kira Zainab. "Ita Aneesah ba zata dawo gidan ba ne?" Cike da mamaki na ce mata ."tun jiya ta bar gidan nan!" Nan fa hankali ya kara tashi aka fara niman. Mutanen da suka sace ta kuwa, tunda suka shiga da ita wani gida a cikin fadar suka mata tsirara suna mata video. "An gaya miki, ki fita hanyar Fulani Babba,kin ki ance ki daina amma baki ji ba, mu ba a saka mu mu yi miki haka ba kashedi aka ce mu miki, idan kika sake wani abu ya kara shiga a tsakaninku, kika zage ta raba kafarki zamu yi tare da fitsare miki jikinki da namu zamu yi, wallahi ki sake ." Haka suka yi ta razanata da mata barazanar zasu mata fyade, sannan suka mika mata wayarta suna faɗin.."ki shiga wayar zaki ga mun tura miki videonki, ya rage naki, ki fita hanyarta ko kuma mu miki abinda zaki tsani rayuwar bakiɗaya!" Ta razana domin ba a tab'a cin zarafin ta ba, sannan bata tab'a haduwa da irin wannan masifar ba, kasa nufar gida tayi ta koma gidan Dan uwanta wanda tsoro ya gama kamata, da wani irin gudu ya isa gate din taba bugawa tana kuka, aka bude mata ta fada da wani irin razana, har tana faduwa cikin gidan ta shiga da gudu, da faruq ta ci karo, ya rungume ta yana faɗin. "Lafiya? Daga ina kike?" A gigice ta ce mishi.."don Allah ka ni wurin Yayana!" Ta fada tana boye fuskarta, cikin gidan ya kaita tana ganin Salmanu Faris ta nufe shi da gudunta har tana faduwa. Ta kifa kanta a kirjinshi tana kuka. "Yaya Ikhlas ce ikhlas ce ya saka aka kama ni!" "Wani irin zance ne haka?" "Wallahi ita ce!" Bakiɗaya muka shiga rud'ani har dani da nake dakin. "Ni kuma?" Kuka ya cigaba da yi tana fada musu irin azabar da tasha, kuma sun ɗauki hoton tsiraicinta, sun turo min! Mika musu wayata nayi na ce mata. "Idan baki sona ba wani abu ba ne, amma ki min wannan sharrin Allah zai tsayar damu a gabanshi." Zuba min idanu yayi zuciyata tana rawa Nadiyyah kuwa tana taya ta kuka, yadda yake min kallon me dauke da tuhuma da zargi tare da b'acin rai ya sani jin wani irin zafi a raina......(Dan iska ya dawo😏🫤)

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 45

Murmushi nayi tare da cewa. "Idan ni ce sai me? Kashe ni zaku yi kamar yadda Ahalinku suka kashe min mahaifinsa? Ko tsire ni zaku yi da raina?" Yadda nayi maganar ina ciwon bakina yasa duk suka zuba min idanu na kara da cewa. "Yanzu duk lalacewata ban kashe wannan na gabana ba sai ke? Banxaata amfani wacce ko na kashe ki ba zan iya daukar nauyin zunubinki da yake zagaye da ke ba, ke ni fa bana iya kashe kazami irinki, sannan na saka an kama ki idan kin so kotun duniya ta bi miki hakkinki. Sai me?" Na juya kanshi ina mishi wani irin kallo na ce masa."Tunda ta b'ata ban je ko ina ba ina tare da kai " haushi ya maka ni na zabga mata harara na ce mata. "Ke na saka an sace ki, kiyi uwar d Uban da zaki yi da ni so what?" Yadda nayi maganar yasa duk suka shiga hankalinsu musamman shi da yake kwance a cikin kwanakin bana zuwa ko ina ya cewa Faruq. "Ka bincike me ya faru!" Juyawa nayi na bar ɗakin, a wannan takin sai na ga kamar don Abba baya raye ne zasu min haka, sai na fita daga sabgarsu.

Wani ikon Allah maganar sai bata wani yawo ba, a karshe yadda tso cutar dani da kalmanta sai Allah ya bani kariya yadda reshe ya juya da mujiya domin labari ne mabanbanta suka yi ta fitowa wai ta tafi yawon iskanci, har ya janyo aka yi ta cewa dama ana zargin ta da wasu abubuwan, wayata kuwa tana hannun Faruq da ya gama binciken a cikin kwanaki uku ya dawo mishi da wayar, ya ajiye cikin nutsuwa yayi shiru. "Ina jinka Faruq?" "Da farko ina mai baka hakuri akan abinda zan fada wanda nasan ba mamaki ka iya tsanata, na biyu Allah madaukakin sarki ya sauka da Aya a cikin suratul hujara inda ya ce idan aka zo muku da labari kafin ku yanke hukunci ku fara bincike, amma Yallabai a koda yaushe lamarinta yana bani mamaki, a kwanakin da kayi a kwance Fulani Babba tayi wasu aikin kasada wanda sai da tayi bincike da nazari yadda ko kai baka isa yi ba, na uku ka nuna mata son kai da son zuciya ita ba naka ba ce Aneesah ce naka. Ga wayar nan a cikin kwanakin da nayi har da bin didigin layin da nayi ban samu wani zance na wani ya hada kai da ita ba, a koda yaushe ina son ka sani Zainab ba zata cutar da kai ko waninka ba, kai kake kwance amma ita take jinyar halin da kake ciki, zuwa yanzu na yanke shawarar ajiye maka biyayya zan kasance a bayan Zainab koda kuwa zata ce min Faruq ka mutu." Ya ajiye mishi kome na shi da duk wani Abinda ya haɗa shi da Salmanu Faris. Ya tsaya da kyau. "Idan ka sake tayi kuka ko ranta ya b'aci, zan bibiye kuma zan kashe ka!" Faruq ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login