Showing 60001 words to 63000 words out of 157081 words

Chapter 21 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

16

Soyayyar kayi diri idan zata lalata mana shirinmu shine abinda zaka min*.

*08130269641*

5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint 500₦

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 22

Kwanciya ya gyara tare da sauke ajiyar zuciya, kiran wayarshi aka yi ganin number Hajjah ya saka shi murmushi. "Ya dai Uwar Sarki?" "Yaya jikina ya bani kaba da lafiya, Yaya gaya min gaskiya ta ji maka ciwo, domin ina jin sharp pain a raina!" Murmushi yayi ya ce min. "Idan na gaya miki gaskiya ba zaki gayawa kowa ba?" Daga can na ce mishi.."Yes na!" "Ok I love you shine abinda zan gaya miki!" "Yaya kada ka mai dani yarinya yaya ina jin ciwo a gefen cikina, wallahi Yaya ta jima ka ciwo! Ka ga Ayaan yaki barci sai kallona yake!" "Shafa min kan shi ki ce mishi Abby dinsa lafiyarshi lau!" "Yaya!" "Kanwata!" "Yaya ta jika maka ciwo kanta kayi barci kuma idan ka dawo sallah asuba ka zo nan ina son ganinka!" "Tow Ummina!" Kuka na saka mishi, ya ce min. "Ok in sha Allah!" Daga haka muna yi sallama, ai kuwa cikin daren nan ban rintsa ba, sai kusan karfe uku lokacin mai babbar daki ta shigo duba mu ta same ni a parlourn ina kuka. "Zainaba!" "Na'am!" Na amsa ina shashekar kuka. "Me ya fito da ke a wannan lokacin?" Ta tambaye ni, "Ummi ta ji mishi ciwo kawai yaki fada ne. Ina jin haka a jikina, yaushe zamu huta ni da shi? Ummi na rasa hanyar da zan bi Yaya ya daina shiga damuwa saboda ni." Rungume ni tayi tana faɗin. "Ba kome fa, haka Allah ya shirya mishi rayuwarsa, kada ki damu kada ki saka damuwa a zuciyarki kin ga kina da lalura a zuciyarki don Allah ki bar kome ya wuce. " Ta fada tana shafa bayana. Ayaan da yake gefen kujeran kwance shi da Isma ta dauka tana mai riko hannuna muka wuce ɗakinta, kwantar da shi tayi ta haɗa min ruwan dumi na shiga nayi tsarki na gyara jikina, na fito bayan ta kawo min kayan da zan saka, sannan ta kunna room heat, dakin ya bada dumi. "Kwanta!" Haka na kwanta tana faɗin. "Mijinki yana ƙoƙari kawai wani lokaci Allah yana jarabtarka don ya ga karfin imaninka ne!" Sannan ta ja min bargo muka cigaba da barci, domin kamar jira ake na kwanta tuni barci yayi gaba da ni. Ita kuma ta shiga ban dakin tayi alola ta zo ta gabatar da sallah, haka tayi ta nafilla har aka kira sallah asuba, tayi sallah ta haɗa da azkar sannan ta ɗan kishimgid'a barci yayi gaba da ita.

Karfe sha ɗaya ina barci, ashe har Yaran an zo an ɗauka an shirya su. Jin ana tsotsar nono ya sani bude idanu, Yaya bai da kunya ture shi nayi ya sake murmushi yana faɗin. "A'a ai naga wurin zama Kambu ashe haka lamarin yaƙe ga daɗi ga lagwada sai abokaina." Ya shi zaune nayi na fara kallonshi tare da duba ta ina ya ji ciwon, amma haka ya hana ni ganin kome.

"Yan mata tashi ki yi wanka!" Kamar ance na kai hannu gefen damarshi ta wurin harkarkarinsa, "Wash aucchhhh!" Ya fada yana cire hannuna, kallonshi na tsaya ina yi da sauri na cire mishi rawanin kansa tare da wasu abubuwan da ya saka. Zai magana na ce mishi. "Kada ka sake!" Haka ya tsaya na cire rigar ciki sannan na cire singlet din da ya b'aci da jini, hawaye ne ya zubo min. "Yanzu saboda kin Allah ka yi shiru da wannan lamarin?" Janyo ni jikinshi yayi yana faɗin. "Daga ni sai ke muka san da haka, please a bar maganar nan a nan kin ji!" "Yaya zaka kashe kanka ne?" Na tambaye shi, a hankali ya mike ya saka rigarshi yana faɗin.."Idan har Yankan mace zai kwantar da sarki mai duniya irina, gaya min meye amfanina Sarkin mata kadai zaki cigaba da kirana ayi hakuri a yafe mata gaba tayi sai Fulani Babba ta dauki mataki."

"Allah zai saka maka tunda ka hana ayi magana!" "Yawwa ba gashi kin kai kara wurin Allah ba. Kada ki damu wallahi." Ya fada yana kallon yadda na damu, sumbatar bakina yayi na kauce ina mai nufar ban daki, Yaya bai da lafiya amma ya daure yana abu kamar mai lafiya.

Bayan na gama abinda zan yi na fito na samu baya nan. Wata mahaukaciyar kace na samu wanda yayi kakar kayan jikinshi, haka na saka na fito parlourn, na samu mai kwalliya tana jirana, haka na fito na zauna ta fara min har aka gama wurin karfe sha biyu sai ga Ijlal da Ikram sak kayan jikina, da farin ciki na tarbe su, aka mana hoto Ikram ta ce min. "Awatif kina ta murna jiya kin haka Nadiyyah da Shago fada ko?" "Aojanah da na tab'a gani bata daukar reni kuma bata dauki kowa a bakin kome ba, me yasa wannan Aojana zata shiga lamarin kishiyoyin ikram?"

"Idan Awatif da take gaba, cikakkiyar mace ce da tasan ciwon kanta, ta kuma isa da kanta, ta kyale shago ya shiga turakar Aojana!" Murmushi nayi nace mata. "Ki ce rokon yayi tarayya da ita kika zo yi ba suna ba? Ita ba mace ba ce da, ba zata iya shawo kan mijinta ba ne, sai kishiya ta taimaka mata? Ai kuwa idan haka ce tow aiki ja ne a gabanta, wancan mutumin fadar nawa ne, duk wacce zata shigo aro na bata, Nadiyyah kaɗai nake d'agawa kafa domin a tare na same su, don haka kowacce mace nata ya fishe ta." Na yi gaba, ina amsar bakin da suka shigo, wani haushi ya kamani na shiga na cire wannan kayan jikina, na saka wani sannan na fito aka kara gyaran fuskana, ina zaune mai babbar daki ta kawo min Abin karyawa. "Kina jego na lura sam bakya son cin abinci!" Ajiye kwanon tayi ta saka min cokali sailuba ta shigo da kayan abinci a tire ta ajiye haka na shiga ci ba dad'i, amma fa na cinye dumamen tuwon dawa tas miyar kuka domin ta ce ina goyo ba za ayi miyar ganye ko kubewa ba, amma shi kuka natural Herbs ne, gashi ya ji manshanu. Haka na gama na taso zuwa parlourn. Sai gud'a Jakadiya Iyaami take Bilqis ta shiga min kari da zuba min kuɗi. Kai naga hidima wurin karfe uku na yamma yan gidanmu suka iso nan ma wani hidima ce na daban, a can tsohon gidan da muka zauna, anan aka yi walimar da aka bada git fas, Hajjah kuwa da kawayenta an baza Capacity iya capacity.

Sun sha sun ci kuma sun gyatse, nama kuwa kyafe shi aka yi. Ana gasawa ga abincin da ake bin tables tables ana rabawa, abincin da aka baka an jima ba shi za a kara baka ba, wani za a baka. Kuma ba za a baka wnada zaka ci kayi kat ba a'a zaa baka wnada zaka ci kana marmarin wani wannan shirin Bilqis da Daulah ne sai Mu'azzaatu da take India da mijinta ta turo musu yadda ake gudanar da biki a can. Suka kuwa dauki yanayin hidimar. Mu'azzaatu ta ce zata zo idan Yaranta suka samu hutu. Ance suna matukar kama da Yaya sosai. Haka aka yi ta nasiha da ɗaukar hotuna, shima Angon karnin ya zo anyi hoto da shi bayan an gama nasiha, haihuwa da tarbiyya a Muslunci, sai sharyawa da reno Muslunci. Bayan an gama muka yi hoto, lokacin da muke hoto da shi kowa ya shiga har da danginsa da nawa, sannan ya bada umarnin a haɗa yaran mu tafi can gidan a babban parlourn shi aka yi ta mana hoto, yadda kuka san pre-wedding pic haka aka muka yi hoton. Kafin muka bar gidan muka wuce fada aka cigaba da hidima, a daren muka bar fada zuwa gidanmu.

Muna zauna wanka muka yi muka kwanta, sai barci daga ni har yaran mun gaji washi gari gidanmu aka tashi da wani gagarumin liyyafa, wanda kowa ya gani yasan an shirya wanna haka, hidima sosai aka yi su Daularh sun zo aka basu nasu kayan hidimar, Hajja cewa take. "Tunda nake ban tab'a jin nama yana min wari ba sai a sunan Yan hudu" ba dole ba taci har ya fita kanta Hajjah Allah ya raba ta da zawo. Wunin ranar shiga ake aka fita a gidanmu, musamman Yan unguwar da suka ji an samu Takwaran Tauhid sai ga kyautattaka daga mutane, ranar nayi kuka sosai ba ni ba hatta yan uwana musamman Iram da ta sauya sosai. Yanayinta ya sauya gashi na ji wai ana shirin kaita asibiti saboda yadda take fama da infection ya kamata sosai domin har ana tunanin ya tab'a mata mararnta zuwa cikin mahaifarta. Na tausaya mata mata domin shegen dabbancin da suka yi ta yi ne ya kamata. Haka muka cigaba da wanka, duk wnada ya ganni sai ya ce na zube saboda yaran basu barci da dare sai rana, ganin haka yasa kowa yake taya ni, ganin bana samun isasshen barci Abba ya ya fara musu rubutu an basu, har ina gaya mishi ya fara nima musu maganin barci Yaran basu barci wani ikon Allah bamu cika wata guda ba sai gashi suna barci, sannan shima zuwan da yayi ya sha mamakin ganinsu yadda suka yi ta kuzari.

Haka muka kwashe wata biyu cif a lokacin duk wanda ya san Yaya ya ga hakurinsa da dauriyarshi, idan aka ce yaushe xamu dawo zai ce musu sai Yaran sun cika wata uku, koda Abba ya mishi magana ma, ya ce a bar Yaran su kara wayo ai basu yi wani wayo ba, kayan da muka samu daga can Bangarena aka wuce min da shi, aka cika min daya exra din da shi, wasu kayan har su shekara biyar suna sakawa musamman wnada shi uban ya saya musu, kayan da ni na samu kusan manyan akwati shida aka cika min wanda kannensa suka da wanda kishiyoyin Mai Babbar daki suka min, sai na yan gidanmu da na Zuriar Yayari, ban da Yeemar da ta min akwati guda, kai ni sai lokacin maganar Hajjah ya dawo min munafuka ina tambayarta, ta kama sosa min kai tana dariya da bani labarin halin Faruq, kafin ta kai aya na ce mata. "Ina farin ciki da haka, idan har kika zaɓi Faruq kaf duniya ba zaki yi danasanin miji ba, wallahi ai lamarin nan namu ne"

Haka na gayawa, hmm ashe har shi da kanshi Ya samu Abba da maganar har sun isa gidansu Yeemar, ai ya bani haushi na fara mita, ya ce min. "Idan baki yi mita ba waye zai ce ke ba jikar Hajjah ba ce!" Tura baki nayi ina faɗin.."don kana sayanta da kudi!" "Eh wallhi wani ma yayi rawa balle ɗan makadi!" Share shi nayi,.kawai haka muka yi sallama, gyaran jiki kuwa ban san iya adadin da Maluma ta bani ba, yadda take kula da cima da abinda xan sha, kuma sai Allah ya taimaka yaran da yake ina shan hulba a akai akai, basu da matsalar ruwan nono, wani bin har jin shi nake a jikina, kafin na koma Maluma ta saka ni gaba na fara biyan azumin da ake bina, abinda na fahimta Yaran kowa da kalar yanayinsa. Ayaan yana da hakuri ko nono zan bashi yaji sauran sun fara kuka zaki amsa, yayi ta wasa haka xan ajiye shi na bawa sauran su sha. Idan na gama ina bashi sai na ga ya amsa yana sha kuma sai naji nonon yana cika da ruwa sosai, haka zai sha har ya cire bakinsa ruwan nonon yana fitowa, idan suka kaure da kuka kuwa zaka same shi ya saka hannu a bakinshi yana tsotso, musamman idan Isma tana tare da shi baya kuka. Idan yayi kuka kuwa tow bakiɗaya sauran shiru suke yi.

Umma cewa take ai Ibrahim bawan Allah ne, hakuri da juriya sannan ga shi da son Yan uwansa tun yana yanzu yana iya hakuri da abinda suke sha ya bar musu.

***

Wani gida can da Alhaji Nafi'u ya ajiye Turai, ana kula da ita cikin tsananin tsana take kallonshi, don ma an daure ta ya ce mata.."Ki daina min kallon tsana, na gayawa Junaidu ban kashe miki Yaronki ba, ban ga dalilin da zai saka ki yi ta jin haushina har haka ba, ana niman wata biyu amma zuciyarki har yau bata daina ci da wuta ba, idan ni na kashe Ibrahim me zaki iya min? Na gaya miki gaskiya amma baki yarda da ni ba, tow me kike so nayi miki? Kin ga ki ajiye tsanar da kike min ki koma wurin Mijinki akwai abinda ya dace mu karasa Yar Mijinki ta haihuwa kuma ta yiwa Ibrahim takwara, wannan saboda nasara ne,ki yi amfani da wannan dutsen ki shiga dakin da Yran suke ki zaga wanda dutsen yayi haske kanshi, tow tabbas shine wnada ya gaji uwar da uban aikinmu y tashi akan Yarinyar akan abinda ta haifa ne, zamu cigaba da hada mishi zafin kai yadda zamu shiga jikin Yaran har mu mishi illar da basu sani ba."

Ajiyar zuciya ta sauke tana nazarin maganar shi, kafin tace mishi. "Yaya Junaidu ba zai tab'a yarda na koma mishi gida ba, domin naga yadda ya tsane ni!"

"Ina Iram ki bata tare da mata barazanar idan bata nimo miki Yaron ba, zaki kashe Yaran har da Ubanta, zata so tayi abinda zai saka su tsira da rayuwarsu." Ai kuwa haka suka kira Iram bayan Alhaji Nafi'u ya yi yar tsafe-tsafensa can kuwa sai gashi ta amsa, ya mikawa Hajiya Turai ta gaya mata abinda zata yi shiru tayi ta ce mata.."ba zan iya ba, domin kuwa ba zan yi abinda zai dame ni ba!" "Idan baki yi ba, sunan Yaran da Ubanki da Uwarsu matattu!" "Shi kenan zan zo na amsa!" Ta fada tana jin kuka, haka suka yi sallama.

***

Iram kuwa rasa abinda yake mata dad'i take, tana kuka ta kira Salmanu Faris bai dauka ba. Haka ta kira Faruq shima bai dauka ba, sai ta yanke shawarar kiran Walid Mamman yayari, bayan ta kira shi ta ce mishi.."Don Allah ina son ka isar min da sakona wurin Mai Martaba ne, Mommy na da Alhaji Nafi'u sun ce na zo na amshi wani abu da zasu cutar da Yaran Ikhlas, don Allah ka taimaka min na ga Sarki Salmanun Faris."

"Shi kenan ki je ki amso!" Ai kuwa tayi ta godiya, sannan ta bar gidan sai da ta tsaya a gaban gadon tana kallon Yaran, na fito ban daki na ga tana murmushi.."Yau ma kin zo musu tatsuniyar ne?" "Eh ina son na basu labarin yadda Nannyn dinsu take mita!" Wani tsalle Isma tayi tana lashe fuskartar, haka Ayaan kallonta yake ta shafa bayan Isma tana faɗin. "Don Allah ki bani aronta mana! Wallahi ina sonta!" "A'a wallahi ba zan baki ita ba, nima sonta nake." Wani juyawa Ismaha tayi tana min wani kallon renin wayo. "Isma ba dai saboda abincin gwangwanin da take baki bane zai janyo ki ci amanata!" "Ai fa taci ina zata iya tatalarki da Hajjah, bari na dawo!" Ta sauke isma sannan ta juya zata fita. Na isa bayanta "duk da abinda kika yi Isma ta nuna min wani abu da ban san da shi ba shine ta yarda da ke ba zaki iya cutar da mu ba, a duk lokacin da kika shiga damuwa ko tashin hankali, ki ambaci Allah sannan ki nemi yardanshi da kariyansa, sannan ki kira sunan Isma in sha Allah matukar kina numfashi Allah zai kawo miki dauki sannan zata zo gare ki, kada ki yi kukan baya ki yi farin ciki a gaba shi Ubangiji ba ruwansa da abinda yake bayanmu, idan muka gyara gabanmu sai lamarin yazo mana da sauki. Allah ya tsare ki Uwar Ibrahim Yayar Ibrahim Tauhid;" juyo min tayi tana faɗin.."na gode sosai, na gode sosai, Tauhid ya gaya min ke ba zaki tab'a guduna ba." "Saboda ina kaunarki!" Haka na fada mata tare da juya mata baya, bana son ganin tana kuka, tsalle Isma tayi tana lashe hawayenta, sannan ta mai da ita wurin Ayaan ta shafa kanshi tana faɗin. "My lovely bro ina zuwa kaji, ka min addu'a zan dawo gare ka!" Ta juya ta fita.

* Bayan fitar Iram Yaya ya kira ni, ina dauka ya ce min. "Lafiya na ga kiran Iram har goma?" Goma like how? Ta kiraka? Something wrong;" na fada ina fitowa Parlour, "ta kira Faruq shima kusan goma!" "Don Allah ka bi min bayan layinta bana son na kara rasa wani a rayuwata;" na fada ina shiga tashin hankali, ai kuwa muna sallama ya shiga niman layin amma bata shiga, hankalin kowa ya tashi wani ikon Allah ba a samu layinta ba sai a kan babban titin Shehu Yayari road inda aka kashe Tauhid, kamar mahaukaciya haka nake kuka da ihu, na kira shi ya kai sau goma kafin ya iso. "Iram zasu kashe ta, an samu a wayarta da motarta a babban titi Shehu Yayari, Mai suke bukata don Allah kada su kashe min ita!"

Rungume ni yayi yana faɗin. "In sha Allah zata tsira!" Abba da kanshi ya kira Alhaji Nafi'u ya tambaye shi ya ce mishi. "Tabbas tazo ta ga mahaifiyarta amma ban san lokacin fitarta ba ai ba zan maka karya ba." Daga haka suka kashe wayar.

***

Iram kuwa lokacin da ta amshi sakon, wuce wurin Walid Mamman yayari, lokacin da ta isa bata samu Walid ba, Mahfouz Nuru Yayari ta samu, ai dama shi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login