Showing 12001 words to 15000 words out of 157081 words

Chapter 5 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

8

nufi wallahi sai ya ji tsoron hada idanu da kai. Mu mutnen da shirya Yaro muke tun yana dan karaminsa. Ba yanzu da ka girma ba aikin zai matuƙar wahala ya kama jikinka. Don ma Uwarka tana tsaye akanka ba dare ba rana!" Haka Hajjah ta haɗa mishi magani. Ya fito dauke da jakar, ya nufi parlourn Abba aka sake bude hira wurin sha daya ya ce. "Zamu tafi!" Ya fada yana kallon yadda nake loda kosai a bakina. "Zaki yi kiba fa!" Ya fada yana murmushi, kallon Umma da Maluma nayi na ce mishi."wacece ka gani da kiba a tare da su, ni ba zan yi kiba ba." Na fada ina tattara kayana, muka fito a lokacin Tauhid ya shigo gidan, ya fara min shirme na bude jaka na ciro kudi na mika mishi dariya yayi yana faɗin. "Sorry bai kai 20k ba;" "sai ka yi hakuri!" Hajjah ta faɗa. "Hajjah ba dai koro ki tayi ba?" "A'a kada ku musu sharri alkazubu karya zagin Allah ne, dariya yayi ya tsaya muka bar gidan, muna saka hancin motar a kan hanya convoy na security dinsa suka saka mu a tsakiya muka dawo har fada, sai da ya kai ni tare da nufar wurin Ummi da sakon hajjah, ya mata bayani. A daren aka dafa mishi shayin ya sha, sannan ya balli tsinken ya wuce gida, koda ya isa gida sai da ya kira ni, na ce mishi lafiya ya ce "da fatan babu wani abu ko?" Na ce babu ya kashe wayar.

**

Hajiya Turai, kamar ta mutu ganin Zainaba da ciki abin yana mata matuƙar ciwo, duk yadda ta so yarinyar ta lalace ta rasa wannan damar. Tayin da aka mata kwanakin baya shi zata amsa don haka ta dauki wayar a hankali ta danna number da ta saka sunan Fadar zanzbira, danna kiran tayi yana shiga aka katse, sannan aka kirata ba zata iya cewa muryan mace ce, ko namiji oho ita dai ta san an amsa mata da wata irin murya, a hankali ta ce. "Na shirya zan duba yarinyar, burina ayi waje da Zainab a kashe ta a lalata mata rayuwa, a daidaitatta yadda ba zata tab'a moruwa ba, ina son kare ya fita daraja a idanun duniya da kowa da mijinta, idan fa hali a saka mata bakin jini ta yadda kowa zai tsane ta!" Can aka yi magana ta ce.." Nagode!" Ta kashe wayar yana ajiyar zuciya domin ko ba kome yanzu zata ruguza Zainab yadda Iram take zaune haka take fatan itama ta zauna ta koma baya a wulakance.

*

Da asuba da mai babbar daki ta, tashi sahoor. Tashi nayi na fito nima na zauna aka cin abincin da ni sai ga Nadiyyah ta fito itama. Muka zauna muna cin abincin har muka gama. Tashi nayi na nufi dakina na zauna ina shafa Isma take barci. Na shafa kanta a hankali ina murmushi a hankali. "Ismah kin yi barci!" Sai da abincin ya fada na kwanta. Ana shiga sallah asuba na tashi na yi wanka da alola nazo nayi sallah na koma na kwanta, ban san me yasa Ismah ta koma bakin kofar dakin ba, ta kwanta. Wani irin ihun Nadiyyah na ji, isma ta kama agararta tana ja da ƙarfi, "Ismah!" Na kira sunanta. Wani irin dawowa gaban Nadiyyah tayi da wani irin tsalle ta shiga kama hannun da yake makale a kafad'arta, ihu take tana ƙara kuka da niman agaji, ni dai na san na bude idanuna, ganin wata Giant cat fara sol kamar isma daga nan na cigaba da barci, ai kuwa Nadiyyah tayi dana sanin shigowa dakina, domin magen nan sai da ta yaga hannun Nadiyyah sai ga kwayoyi nan a zuba a kasa. A daidai zuwan Mai Babbar daki."lafiya?" "Wayyo na kasa gudu?" "Me kika zo yi ɗakinta? Ita tazo.dakinki ne? Wacce irin Fitina ce haka? Ismah bata kula kowa dai ka so cutar da Zainab!" Ita dai kuka take tana rokon mai babbar daki ta shiga lamarin mai babbar daki ta rarrsshin Isma. Kafin ta sauka can tana gurnani. Haka yasa tana sauka ta fita da gudu, Sailuba mai babbar daki ta sa ta kwashe kome zata kai waje Mai Babbar daki ta ce mata. "Kai min dakina!" Haka ya wuce da shi dakinta, bayan ta yi sallah walaha ta kira Amina Zurmi ta ce ta zo, wurin karfe biyu sai gata ta mika mata maganin ta duba da kyau. " Ina kika samo shi?" "Hmmm gaya min hatsarinsa?" "Na zubar da ciki ne." Gyada kai tayi tana faɗin. "Don Allah ya zama sirrinmu ne dake." "Kai haba, a kiyaye shigowar irinsu kawai!" Ta fada tana mai mata sallama, shiru mai babbar daki tayi ta san tana gayawa Salmanun Faris labarin zai datse alakarshi da Nadiyyah dama gashi ana tacewa saboda Zainab ya sake ta, bayan ita ce ta zubar mata da ciki, wannan lamarin aka sake wani labari related to Zainaba ai magana ya ƙare, haka yasa taki gaya musu abinda ya faru ba a yanzu ma ya kara jin haushinta zai yi. Bayan azhar ta kira Baban Nadiyyah ta ce ya zo tana son ganinsa, shi a tunaninsa ko zuwan Nadiya yayi amfani ne, ranar asabar kasancewar ta kira shi ranar Alhamis aka yi juma'a ranar asabar sai gashi, kai tsaye aka mishi iso suka zauna da mai babbar daki suka tattauna kafin ya kawo mishi maganin ta ce mishi. "Ina son ta zauna akan Yarta bamu san ƙarshen rabon ba, amma ita da alamu ita lissafinta daban da namu, Yarinyar nan da take bi da sharri ita ce sanadin da ta rike Halimatu sadiyya,.amma yau Nadiya ke son ganin bayan Ikhlas bayan bata mata kome ba, da za tayi tun farko ya da ce amma ba kome, sai dai ina son ka sani Ikhlas idan iyayenta suka ji labarin ba zai mana dad'i ba. Na rufe maganar a nan domin maganar nan ya fito ban san yadda xan lakwasa shi ba sannan Iyayenta itama ba zasu yafe ba ." Daga haka ta mishi sai an jima, jin wannan bayanin yasa jikin mahaifinta yayi sanyi ya rasa yadda zai yi da zancen domin maganar ta dake shi daga yadda yaji jikinsa ya mutu yasan Nadiyyah ta rasa miji na har abada, godiya yayi mata sannan ya bar gidan.

Kamar yayi tsuntsu ya isa Jos, koda ya isa ya samu Uwar Nadiyyah yayi ta fada kamar zai aro baki ya kara daga karshe ya ce mata.."kinyiwa kanki domin kuwa Uwarsa ba zata tab'a barin ya dauko masshiya irinki ya zauna ki kashe mishi ma, ke taya aka yi kika ci abincin nan har cikinki ya zube?"

Flash back

Kafin ranar da Ilham zata zo, hira da tayi dadi tsakanin Ijlal da Nadiyya, har Nadiyyah take bata labarin ita fa anyi mata scanner an gano namiji ne! Da wani irin tsoro Ijlal take kallon Nadiyyah, amma dai ta wanyece kamar bata damu ba, amma a kasan ranta ji take kamar zata mutu, haka yasa yayi ta fakon Nadiyyah kuma maganar gaskiya ta kasa zaune ta kasa tsaye gashi ita cikinta mace ce, haka hankalin Ijlal ya , tayi ta tunanin babu wani hanya, sai guda daya shine ta zuba mata magani bayan tasan ita Nadiyyah bata cin abincin ta, sai na Zainaba. Don haka ranar da Ilham tazo ta dibi abincin ta fita daga cikin parlour Kai tsaye gidanta ce ta nufa haka yasa ko bayan da ta gama.ta bawa yar aikinta sakon aka kaiwa Nadiya ta yadda zata yi tunanin Ikhlas ce ta turo mata. Wannan shine asalin abinda ya faru. Ita Ijlal ko anan da take zaune da zata samu yadda zasu mutu sai ta kashe kowa hankalinta zai kwanta, haka babban shirinta shine Munirah matuƙar Munirah zata bata hadin kai duk abinda ta mallaka zata bata akan Zainab.

*

Kuka Nadiyyah take tana rantsewa da Allah ita Zainab ce ta zuba bar mata da ciki shi yasa tayi tunanin wannan damar da tasan yadda zai yi hurt kowa da bata yi ba, iyayenta suna matukar tausayinta gani suke tunda ta rasa cikinta ta zama kamar cutar damuwa ya kamata bata da wani abu da ya wuce Yaranta, wani lokaci tayi ta kuka tana jin kamar har da laifinta , kuma ta gane ai an fison Zainab da su, musamman yadda ake kaf-kaf da ita,haka yasa ta kara bin tsanar Zainab din......

(Kambu wallahi barci nake ji ayi maneji🥰)

[8/26, 5:42 PM] Ramlat Manga41: 05

Ita kuma an barta a wulakance, asalin duk abinda yake faruwa Mai Babbar daki ta nuna musu su ba nata ba ne, Zainab ce nata da fari ai ba haka ta so Zainab ba Ijlal ta so amma me yasa ta juyawa Ijlal baya. Da yake mahaukaciya ce ba ta kuma san inda yake mata ciwo ba, a daren ta kira Ijlal tana kuka. Sai dai kash wayar bata shiga kamar zata yi hauka haka take kallon wayarta, tana kuka ita yanzu a duniya ko Iyayenta bata tunanin suna kaunarta kamar yadda Ijlal take kaunarta.

**

Yadda Mai Babbar daki ta tsaya akan abinda Hajjah ta bashi yasa shima kanshi baya wasa da kanshi, da yake ya fara hawa hanya kullum da safe idan zai shiga Fada zai leko sama sama, ya duba ta ya fita bai da ma lokacin da zai mata magana asalima harkan gabanshi yafi ƙarfinsa, na biyu a karan kanshi ya daukawa kansa alkawarin shi yasa yayi watsi da duk wnada zai saka shi ciwon kai, sannan ya barwa Nadiyyah yarta ce don kada a ce ya hanata yarta. Yasa shi bata yana mai ji matukar jinin Yayari ce da kanta zata dawo wurinsa, baya ji zai dawo da Nadiyyah rayuwarsa a karo na biyu. Domin sai yanzu yake hango irin kurakuran da tayi kuma ya kyaleta.

Ranar da aka kai azumi sha bakwai, ranar Ijlal ta tashi da nakuda, ta gayawa Jakadiya Iyaami. Ta isar mishi da sakon halin da take ciki, bai wani jinkirta ba ya sa aka fito da mota aka nufi Asibiti da ita bayan ya kira Munirah ya gaya mata. Lokacin da suka isa, ba karamin jimawa aka yi ba, domin tun asuban fari ake abu daya sai karfe shida na yamma daidai ana shan ruwa, Allah ya sauke ta lafiya. Inda ya samu Yarta mace, lokacin da Nurse Jalilah ta mika mata yar ta gani. "Na ganta je ki da ita!" Ashe fuck heat haihuwar mace, shi yasa tun farko bata yarda an gaya mata gender din ba, babu abinda bata yi ba don ta haifi namiji amma abu ya citura sai ta kare a haihuwar mace for second time? Hawaye ne ya cika mata idanu. Idan ƙaddaranta haihuwar Yaya mata ne, tabbas duk wacce ta sake ta haifi namiji sai ta kashe ta.

A haka suka gyara Uwar da yar aka dawo da ita daki, tana hutawa. Da yake ya koma gida bai wani zauna ba, wurin karfe goma na dare suka dawo aka sallame ta domin lafiyarta lau, sannan Munirah zata zo har gida tana dubata. Daukar yar yayi ya mata huduba da Nana Aisha, duk a tunaninta zai ce mata sunan Yar Maryam Yayari ce wato mai babbar daki, sai ta ji ya ce mata ."Allah ya raya Nana A'ishah!" Daga haka ya ajiye mata yar suka fita aka gama kome ya shigo Dogarai suka shiga fita da kayan ita kuma tana bin bayansu, a hankali ta shiga mota bayan ta zauna ya ajiye mata yar akan cinyarta shima ya shiga gaba ya zauna.."congratulations Sir!" "Thank you!" Ya fada yana cikin farin ciki sosai domin yana son Yara. Kuma ba ruwansa mace ko namiji. Haka suka isa gidan ya kira Jakadiya Iyaami ta nimo wacce zata musu wanka. A daren aka wanke Yar tass, sannan ta koma ta juyawa uwar itama tayi wankar ta gasa jikinta. Bayan ta gama ta koma ɗakinta ta wanka aka hado mata tea da gasashen nama ta zauna ta cu sosai, sannan ta zubawa kofar dakin idanu. Kafin ta mike ta rufe kofar ta kwanta drower din gadonta ta janyo ta tare da ciro wata wayar Sumgsung S³ ta kunna wayar a hankali tana kallon Yar da take ta barci. A hankali ta lullube number Nadiyyah. Tana dauka ta ce mata. "Ni ce Ijlal!" "Kin san sau nawa na nime ki?" Murmushi tayi ya ce mata. "Ai ba zaki tab'a samuna ba." "Akan me?" Nadiyyah ta tambaye ta. "Saboda ya kwace wayata, yanzu ma na kira na gaya miki ne na haihu!" "Me kika samu?" Murmushi mai ciwo tayi ta ce mata.."me kike tsammani?" "Baby boy?" Lumshe idanun tayi ta bude tana fatan ace haka ne mana, amma ta ce mata. "A'a Princess da Amirah sun yi kanwa." "Baby girl?" "Eh!!" "Allah sarki, dama ina son na gaya miki na shigo amma ba koma, na zata zai yi hakuri ne amma yaki don har yaso ya kwace min Yarinyata." Dariya Ijlal tayi tana faɗin.."Ai gara da yaki hakuri kina tsammanin zaki dawo ne? Tsaya Nadiyyah idan har Zainaba da ta iya miki halaccin kika ci amanarta gaya min waye zai iya yarda dake baki ci amanarsa ba? Nayi using opportunity din da na samu akanki ne amma ai gara Zainab sau dubu akanki, ke da baki da banbanci da tunkiya. Ai ki saka a ranki itama Princess Halima idan da hali da an kashe ta kamar yadda aka zubar da cikinki. Tunda na fahimci jaka ce ke an gaya miki zaman kishi da jahilci ake yinsa? Mahaukaciyar banza ita Zainab saboda ta haihu aka rike ta a fada ke kuma na saka kafa na shure mutuncinki a idanun Mijinki gaya min taya zai dawo dake? Ke fa ba Yarinya ba ce amma haka kika yi tawa Zainab iskanci, idan nice Zainab ta so haka ba zan tab'a yarda na kyale ta ba sai na dauki yar na bata har abada yadda zata samu kulawa amma da yake tunkiya ce ke ina gaya miki bana kishi da ke ai nafi kowa jin haushinki domin yadda kike fuck sex da shi yasa Ni karar tsanarki. Ita Zainab da yake munafuka ce ai bata yarda a ji me take da shi.sau biyu ina afka musu amma taki yarda na san meye suke yi. Ke dalla kashe wayar kin bar gidan Salmanu Faris hrs abada kenan!" Idan da wani ne zai gaya mata wannan ranar sai ta tsine mishi albarka, me ya faru da ita?

Murmushi Ijlal tayi tana faɗin. "Zainab Ikhlas saura ke!" Haka ta kwana cikin farin ciki, washi gari da safe kuwa kafin ta farka an yiwa yarinyar wanka, an gyara mata jikinta. Tana tashi itama an ajiye mata nata ruwan wanka tayi wanka ta fito tayi breakfast, sannan ta fito parlourn. Wurin karfe tara ta koma ta kwanta bayan ta bawa yarinyar nono, tana barci ya shigo ya ga yarinyar shafa kanta yayi sannan ya fita, lokacin da ta farka danginta sun zo. Anan ake ta hira da shewa take gaya musu ai ta kori Nadiyyah, Ikhlas kuma tana wurin Mai Babbar daki. Shiru wata cikin yan uwan Maman Ijlal tayi ta ce mata. "Tow ko kin kori Nadiyyah basarake ne zai cika ta uku da ta hudu na gaya miki, tunda duk abinda yake yi kin tab'a jin ya sake Zainab? A yanzu ma da yace zai nime ta ba a gaban Uwarsa take ba ne? Hmmm lallai baki san rayuwa ba tabbas zai yi aure ki ajiye a ranki!" "Kai Umma yahanasu wani aure kuma ? Ba auren da zai yi fa itama Ikhlas din tana haihuwa ya ga mace ce zai sake ta ne ya zauna da Ijlal ita ɗaya!" Inji yar Aunty Fa'iza, parlourn ya dauki shewa kamar zasu tashi gidan.

Da yamma bayan la'asar Mai Babbar taki tazo ita da sauran matan aka barmu a gida, sannan suka yi barka da abinda suka zo da shi domin tun ranar haihuwar ya ce ba suna ya soke suna a gidanshi tunda masifa ce suna ba zaman lafiya ake yi ba, kuma ba za ayi shi lafiya ba tare da an tashi gurmi ba, ana saura kwanaki kuwa ya shiga bangaren tana zaune da Aunty Fa'iza, mikewa tayi ta bi bayansa zuwa wani dakin da yake yawan shiga a bangarenta, tana dauke da yar ya mika mata hannu ta bashi yar, yana kallon yar tana kama da sauran Yaran amma Amiratul Zaitunah tafi sauran yaran kyau bakiɗaya. Kallon Uwar yayi ya ce mata. "Babu suna!" "Me?" Ta kara tambayarshi, kallon cikin idanunta yayi ya ce mata. "Kin ji ai!" "Kamar ya ba suna?" Ta kuma tambayarshi, yadda ya kalleta sai kuma tayi kasa da kai ta ce mishi. "Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi!" Hawaye na cika idanunta, daga haka ya mike tare da cewa."Faruq zai kawo kome da ake bukata amma na soke taron suna!" Haka ya fita bayan ya ajiye mata yar, fitowa tayi tana kuka, "lafiya?" "Ya soke taron suna!" Wannan abin da ya dake ya, hakan yasa tayi ta kuka ita kuwa Aunty Fa'iza sai zugata take tana gaya mata tayi duk abinda xa'a iya suna ba fashe ai irin wannan sai a rena ta.

Yadda take zugata har Hajiya Mardiya tazo, tana jin zance ta hau masifa tana kumfar baki, kamar zata cire bakinta don jidali, amma dukkansu aka rasa wanda zai sake tunkarar shi da magana, haka suka yi ta zuga tayi bori, shi fa tunda ya fada babu suna ya fita batunsu. Washi gari ta nufi bangarenshi tana isa ta samu wai ya tafi Umara, Innalillahi wainnalihir rajoun, wuni tai tana kuka kamar zata mutu. Haka bayan la'asar sai gata ta wani kwanjame, ban shiga harkanta ba, ita a tunaninta dani ya tafi umara. Sai dai kuma ganina yasa ta jin nutsuwa. Bana iya fadar abinda yake damuna amma ni nasan bani da lafiya kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login