Showing 117001 words to 120000 words out of 157081 words
suka nuna basu san kome, daga baya ban yi mamaki da labarin da ya rubuta min ba, ba don kome ba sai don yadda kome Tauhid yayi zai nuna maka shi jini Malam Junaid ne, sannan yanayinsa damu yake kama, shakuwarmu da shi na musamman ne, domin kuwa jini daya yake yawo a jikinmu, zai matuƙar wahala idan da yana raye baka ga yayi wani abu da da Ya Abid ko Nawwas ko Nuraim bai yi ba, haka daga tafiyar Abba maganar Abba, yanayin bayani da hannu duk sun dauka. Idan ka cire maganarshi kudi tow ba abinda ya bar kome namu iri guda ne, haka yasa nake kara imanin jininmu yana da karfi.
Yadda Mommy Turai take nuna nadamarta sai bakiɗaya Umma tace ita dai ba abin yarda ba ce. Ba mamaki da hannunta a cikin abinda ya faru, sai dai yadda Abba bai ki Iram ba haka su Umma da Maluma suka rike Iram, dakyar na dawo gidana sai a lokacin Nadiyyah ta min ta'aziyar rasuwar Abba, amma bata zo gida ta min ba, tattara kowa nayi na ajiye a gefe, Matar Salim tazo wai ta tafi Umara ne sai gashi ya kawo ta, a nan nake jin labarin wai ana niman dan gidan Alhaji Rilwanu Abubakar Yayari ba a ganshi ba, ban wani damu ba domin wanan hanyar kawai zai saka kowa ya ji yadda muke ji, duk yadda nake son na danne zuciyata amma na kan kasa haka xan shiga cikin bawon wanka na cika ruwa har ya shanye ni a cikin na bude idanuna a cikin ruwan im feel like dream. Sai na shaki ruwan nake ji a raina Abba baya raye, haka xan zauna a dakin shiru, Jakadiya tana yawan zuwa tana min wasu abubuwan. Ranar ina zaune a daki wurin ƙarfe biyu na dare na idar da sallah. Na zauna a tsakiyar gadon, a hankali na ji kukan mage, kafin can naji wani irin gurnani a kofar dakina ana ƙoƙarin bude kofar. Turo kofar aka yi ina kallon wata mage wacce girmanta yayi kusan wani katon dan akuya. Ayaan da ya shigo daga kofar ta juya a fusace. Wani kallo yayi da ita sai da ta daku da bango. "Jakadiya manya!" Na fada mata ina murmushi, Take ta koma siffarta, tana zare idanu. "Kin san kwana nawa muka dauka muna jiranki?" Ayaan ya fada saboda Aryan yana jikinsa. "Bata sani ba domin ita kanta a rufe yake," na fada ina gyara zamana da kyauta ina kallonta. "Me yasa kike haka?" Na kara tambayaarta. "Ni ban san kome ba wannan ma nayi ne domin na razana ki, amma yanzu na gano kuskurena, ki yafe min."
"Zan yafe miki, bayan nayi miki tambaya uku, na farko jinin wasu a jikinki d hannunki? Na biyu su waye suke bayanki? Na me yasa kike cutar Mai Babbar daki dA iyalanta!" Dariya ta soma tana kallona tana nuna da yatsa. "Kin yi kuskuren yarinya!" A fusace Ayaan yayi kanta. D'ago masa hannu nayi ya dakata yana huci. "Ni yarinya ce, amma naga yadda jini yake yawo a kanki, ba iya ke daya ba duk wani mugu cikin zanzabira na ganshi sai dai ban san me ya aikata ba, idan kuwa zan samu xan bashi hukuncinsa daidai da laifinsa" wani mahaukacin dariya ta saka. Tana nuna min yatsa tsare da faɗin.."karya kike!" Dukar hannun Ayaan yayi ba sai ga hannun yana lilo ba, ya daki kafarta ta zube akan gwiwarta. Matsowa nayi gaban gadon na zuba mata idanu. "Idan na sake kika fita daga nan ba zaki tab'a fada min kome ba, idan na barki kike haka dai ba zaki fada zaki yi yunkurin cutar da rayuwarki ne. Domin na san zaki yi shiru da bakin ki. Zaki gwammace."
"Me kika sani? Ai kina da Yara mata biyu, idan har Allah ya jarabce ki da samun wani bakin azzalumi ya lalata miki gadon yarki ya zaki? Sannan don rashin adalci da mutunci ya fito ya gaya miki shi ne ya zaki yi!,yarinyar da babu ruwanta ta taso da nutsuwa da hazaka, yarinyar da bata damu da kowa ba sai mahaifiyarta da Kakarta. Anan idanuna na ga gawar Yata daya tal da Allah ya bani, akan idanuna na ga jinin budurcin Y'ata ko yanzu na mutu ban yi kaico ba domin yau ga sarki a jinin Yayari kwance cikin jini ko iya nan na tsaya zance Alhamdulillahi. Ke ce kadai ban san kome akan ki ba, amma kome da kishiyoyinki suke miki domin daga shigowarki kome na gidan Ya lalace ki kashe ni amma ki sani ba zan daina bibiyar Ahalin Yayari ba....
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 43
Bayan kwana biyu
Na gama sallah ina cin abinci, Aryan ya kalle ni, "Kina nan ga dan uwanki can dakin Malam Junaid zai kashe kanshi da bakin ciki da bakin cikin mace." Ya yi waje yana murmushi. "Ni xan tafi wani aiki ne na kai da kai!" Cikin mamaki nake kallonshi ni fa a sanina da shi bai tab'a cewa zai je wani wurin ba sai gidansu, ko Umminsa tana kiransa. "Hmm!" "Mana ciki da munafunci gaya min abinda yake ranki kada na bar ki ya kashe ki!" "Idan zaka yawonka ban hana ba, amma ka fita a jikin Yaron da babu ruwansa!" Na fada ina watsa mishi harara, murmushi yayi yana faɗin.."Kada ki min gori don kin haifi Ibrahim da nayi aure da wuri da sai dai ko zo a jikar Jikar jikar jikata!" Ya fada yana wani d'aga min baki. Ya saka kai ya fita abinsa.
Da ace nasan inda zai je da zance ya fita yayi tafiyarsa ya bar min Ayaan, sai dai yana fita kamar ana jiranshi aka shaka mishi abu a hanci, suka saka shi a motar. Daga shi har Ayaan suka yi barci.
Ni ban sani ba, asalima kiran Gida nayi na tambaye su halin da Nuraim yake ciki suka gaya min, na ce a karya kofar a fita da shi, kada ya kashe kanshi. Haka kuwa aka nimo Ya Abid da Yunus suka karya kofar yana zaune can inda Abba yake sallah, ai nima suna gaya min na fito daga gidan na kira Faruq ya kai ni gidan sannan na kai Yaran wurin Mai Babbar daki, lokacin da na isa na samu Umma tana sababi. "Akanka aka fara samun haka? Sai ka kashe kanka a iska, Yo ni tunda naga yarinyar nan na san akwai wani abu tunda na fara magana naga Allah ya gafarta mishi Abbanku bai ce kome ba nasan ka dibo masifa da hannunka, ai ba dukka masu kyau suke haka ba, sam dama bata kwanta min a rai ba, ta cika sanabe."
"Ya isa Haka, ki barshi ya ji da halin da yake ciki idan Ya zalince ta Allah zai saka mata idan ita ta cutar mana da shi Allah zai saka masa. Kayi hakuri in sha Allah akwai mafita!" Inji Maluma. Sannan Umma ta juya gare ni tana faɗin. "Ke me ya fito da ke? Kin manta cewa Mijinki bai da lafiya ne?" "Nazo na ga halin da yake ciki ne, shi yasa na zo haka!" "Ai sai ki juya Allah ya bawa mijiki lafiya!" Haka na bar gidan kamar na korana suke, sun san zan shige dakin Abba na je na kwanta ne, haka yasa suka koro ni, ina fitowa na samu Faruq ya buɗe min kofar, muna tafiya amma kuka nake domin yadda nake kewar Abba. Har muka isa gidan, ina jin wani abu a raina, wurin Mai Babbar daki ya sauke ni na zauna muka yi ta hira, anan take kara tambayata magabata daukar Yaya,na ce mata ai Aryan ya ce na kyale su, "Allah yasa ba wani abu zasu mishi ba." "Amin bana tunanin haka domin Allah yana tare da shi!" Shiru nayi ina kallon gefe guda, na rasa tunanin me nake yi, amma kuma nayi mamakin yadda Aryaan bai kawo Ayaan ba, shiru nayi zuciyata tana rawa, shigowar Aneesah bai saka na kalli inda take ba, na cigaba da nazarin halin da muke ciki. "Zainab!" Kallon mai babbar daki nayi na ce mata. "Na'am!" "Ki yi hakuri!" Murmushi nayi na ce mata. "Ba kome wallahi!" Kasa cewa kome nayi ina kallon kasa. "Kiyi hakuri ki yi hakuri, nasan an yi miki laifi kuma anyi miki ba daidai ba." Murmushi nayi na ce mata. "Ba kome Ummi." Ganin yadda naki na ce kome yasa ta cewa. "Idan babu matsala ko zaki yi magana da Alkali a raba aurenku?" Da wani irin sauri na kalle ta jikina yana rawa. "Akan me? Nayi wani laifi ne? Ko an gaya muku ina wani abu ne?" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Bana son cutarwa ne tayi yawa ne, bana son zuciyata tana kallonki a matsayin wacce na nunawa son kai, duk yadda naso kada na ga kaina a haka wallahi ji nake kamar na so kaina." Ta fada tana kuka, sunkuyar da kai nayi kasa ina jin wani irin ciwo hawaye na zuba min. "Ban gaji da zaman jiranshi ba, ko mutuwa yayi zan zauna haka domin shi din wani kusurwa ne a rayuwata! Na rasa Abba bana son na kara sake rasa wani mai muhimmanci a rayuwata." Daga haka na mike na ce mata. "Zan koma gida!" "Yaran zaki tafi da su ne?" Aneesah ce ta fito, na kalleta a dan hargitse na ce mata. "Zan bar miki su." Daga haka na juya zan fita Aneesah ta ce min. "Kina ta sauri ko? Ai sun tafi daukar shi zuwa Canada jinya!" Tsayawa nayi na sake murmushi na ce mata. "Ayya sun yi kokari." Na fada ina murmushi, haka kawai zan yi na cusa mata b'acin rai ko taji mai babbar daki ta ce zamu rabu ina kuka shi ne zata yi tsammanin ai ba xan iya rayuwa babu dan uwanta ne ko? Lallai ma Yarinyar nan ta tab'a ni yadda ya dace, kuma zan rama.
Koda na koma gida na samu ana ta dambarwan fita da Yaya abu ya ci tura sai sun hadu zasu d'aga shi sai a sake danne shi, tun suna yi a dadin rai abu har ya fara basu tsoro. Ni kuwa ko dakin Ban leka ba, da suka yi suka yi abu ya ci tura ba sai ga dakin ya fara cika da wasu irin kwari, su ba cinnaku ba sai kuma ba kudan zuma ko kuda ba, sai dai duk yadda suka so d'aga shi sai kwarin su rufe su da harbi, da gudu suka fita ita kan Nadiyya abin ya ma fi mata mugu domin sai ta fita da gudu sai ta ji kamar a wuri guda take tun da ta bar dakin take ihu amma ina su kan mutanen da zasu dauke shi ai tuni suka bar gidan motar ma anan suka barta. Sai da suka yi gudu iya gudu wani cikinsu ya tsaya aka ce mishi. "Kambu tsayawa ka yi ina cikin shan iska na!" Juyawa mutumin yayi yana kallon gefe da gefenshi bai ga kowa aka ce mishi. "Shashasha, gani a saman kunnenka yau na samu yanci rabo da na fita shan iska tun ranar zagayowar Yallabai Aryan, yau ya sake mu ne mu sha iska!" Dan Kwaro ya kad'a fuffukenshi a saman fuskar mutumin, wato da ya fasa wani irin ihu, ya karta a guje yana ihu ashe akwai daya daga cikin abokanshi, yadda ya fada kanshi kwaron yace "kai kai kada ka tsinke min gemu!" Ihu da gudu suka shiga yi har suka karo da juna.
***
Gidan Alhaji Nuru Yayari.
Nan aka kai Aryaan da yake jikin Ayaan, bude idanunsa yayi tare da sake wata atishawa mai karfi, sai da gidan ya amsa wnada yayi sanadin fashewar window glass na gidan, tashi yayi yana mika tare da kallon Alhaji Nuru Yayari. Waya yake yana fadin. "Idan ta damu da Danta zata nime shi, kuma dole ta saka hannu a kan takardun nan!"
Wayar yana juyi tare da zirga-zirga a parlourn, wani hoton Painting da ake sakalawa a cikin gidan don gayu ko nuna isa da kasaita, ita kanta wannan hoton wani wuri ne aka zana shi mai kyau kamar dausayin Kashmir na kasar Pakistan, ga namun daji an zana su. Gaskiya Painting yayi kyau, kallon zanen Aryaan yayi a hankali yayi ta kallonshi, har sai da ya mai da wurin ya zama da gaske yana wanze, kafin ya ce. "Waye ya kawo ni zan yi ficayi!" Juyawa yayi ya ga Ayaan tsaye. "Kai yaro koma ka zauna!" "Ni Ficiyi zan yi!" "Yaro ka koma ka zauna?" Ya daka mishi tsawa yana kashe wayarshi. Cikin fushi yana zuwa ya make keyar Yaron, wani irin takaici ya cika Aryan, sannan ya ja shi zuwa banɗaki, ya tura shi. Fita yayi a jikin Ayaan ya saka shi yayi fitsari ya ce mishi. "Aboki zaka kalli wasan ko?" Gyada mishi kai Ayaan yayi yA wanke Yaron ya fito da shi waje, sannan ya samu Alhaji Nuru yana zaune yana fada. Komawa Parlourn Ayaan yayi ya zauna a kan kujera. "kunna tv!" "Daga gidan Ubanka aka kawo min Tv!" Bai rufe baki ba Aryaan ya kunna tv, juyawa yayi yana kallon Ayaan ya ce mishi. "Don kaniyarka na ji labarin kana gane gane waye ya kunna tv?" Girgixa kai yayi, can yaji motsi a ta kofar cikin gidan, lekawa yayi ya ga abin mamaki, manya beraye ne guda uku, kafin ya mike har sun iso inda yake, daya ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce mishi.."Alhaji duba min baya da gaske dan tsito ya zuba min kwarkwata?" Wani uban ihu Alhaji Nuru yayi tare da zama kan kujerar parlourn bakiɗaya. "Yawwa Alhaji baka da sabon rena ne, ina son yanke farce na ne?" "Wayyo Allah na." Ya fada da karfi yana niman gudu. Janyo shi aka yi ya zauna da karfin tsiya. Beran nan ya haura jikinshi da gudu yana faɗin. "Sai wani ihu kake dama ina son ayi min gyaran farce ne, taimaka ka gyara min yatsun kafana!" Wani irin ihu mai karfin gaske yayi ya suma, koda ya farka ji yayi ana lashe mishi fuska, bude ido yayi ya ga ƙatuwar tukunya tana lashe mishi fuska. "Yallabai ya tashi. Amma gaskiya ba zan yarda aka fara maka gyaran farce ba, ni gashina nake son a kitse min yau shekaru dari da talatin kenan rabona da kitso Allah yasa ya iya!" Bai san lokacin da ya sake fitsari a jikinshi, ai kuwa aka sake mishi rankwashi a tsakiyar kai. "Dalla tsaya ina maka gyaran kai!" Fashewa da kuka yayi yana faɗin. "Na rantse da Allah ba zan kara ba, ku kyale ni haka!"
Shigowar Wata kura da yaranta, yanayin jikinsu na mutane, kansu na kuraye. "Yallabai Aryan a taimaka a bani shi mu yi kalace da kayan cikinsa, yadda yake katon nan, kasan tumbinsa zai tara kitse!"
"Ni kuwa a bani kanshi domin na samu wurin sake fitsarina!" "Ni zuciyarsa d yake kullum nazarin sharri." "Ni kuma kafarshi zan ajiye kashin kafar ina lasa kullum"
"Kun kwashe kome don Allah taya kuke so karamin alhaki irina ya rayu ko ba kome na samu bakinsan bakin nan zai tara kitse!"
Cizon kunnsa aka yi ya fasa ihu, "wayyo Allah Iyata kunnen da tauri!" Inji wata yar karamar bera tana saukowa, ihu yake, su kuwa dabbobin suka taru tare da yanyame shi, gyaran murya Aryan yayi musu, bakiɗaya suka tsaya. "Kowa ya fadi abinda yake son yi mishi sai yayi amma ban da kisa!"
Kallon wannan Painting wata tinkiya tayi ta juya wurin Aryan ta ce mishi.."kayi min alƙawarin duk ranar da ka samu dama zaka kai ni tsibirin Kashmir na ci sabin ciyawan dusar ƙanƙara. Gashi nan na gani a tura shi."
"Alhaji ka ji abinda aka fada ko?" Ayaan ta fada mishi bayan Aryaan ya shige jikinshi. Kallon Ayaan yayi ya fashe da kuka ya ce mishi. "A tarihin duniya ban tab'a jin wanda yayi wannan katobarar ba, ni taya xan shiga Painting nan?" "Ba kai ne ka ajiye a cikin gidanka ba?"
"Idan ma ni ne sai na shiga?"
"Kai ku sabe shi!" Ai kuwa da gudu suka sabe shi, wata agwagwa a cikinsu ta ce musu. "Allah ba zamu kai shi ba sai mun mishi wasa da ciccillashi sama." "Kai Yar fara kina da abin arziki!" Inji wata akuya da ta shigo yana sake kashinta a cikin parlour can ta fara kukansu na akuyoyi sai ga Yaranta nan sun tawo da gudu, suka daddage aka cilla Alhaji Nuru sama kafin ya dawo ƙasa yana zuba ihu suka dare bakiɗaya suka barshi ya fado kasa ji kake timmmm, haka ya faru daidai Alhaji Kabiru Hammud Yayari ya shigo parlourn yana faɗin. "Wannan wacce irin sakarci ne? Ce maka aka yi kai wani." Shiru yayi yana kallon yadda Alhaji Nuru Yayari ya baje a kasa. Yana nishi bakiɗaya baya jin koda ya rayu jikinshi zai kara moranta. "Kai tashi me ye haka?" Dakyar ya ce mishi.."wancan Yaron shaidani ne, ka fita da shi zuwa gidansu. Yanzu nan!" Cikin fada shima ya ce mishi.."ai ko baka ce dole na mai da su gidansu!" Ya nufi Ayaan ya riko hannunsa, ya zata yaron ya tashi ne, ya ce mishi."muje na kai ka gida ai wannan shiririta ne, da Uwar muke da yar tsama, Don haka taso muje!" Ya kamo hannun Yaron ya cigaba da tafiya, shi nan ya dauko Ayaan bai san hannun wata kaza ya riko ba. "Kai tsohon banza ina zaka kai ni?" Juyawa yayi ya ga hannun da ya dauko, wani irin razana yayi ya sake hannun amma ina ji yayi an dauke shi an