Showing 75001 words to 78000 words out of 157081 words

Chapter 26 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

31

aikata kuwa? Kin bar kowa cikin zulumi da tashin hankali. Wacce irin mutum ce ke mai matuƙar son zuciyarta."

"Ina da son zuciya! Amma domin yayi farin ciki na danne kishinsa nake bashi goyan bayan yayi duk abinda yake zan kashe kaina ne akan shi? Zuciyata kumbara take idan ya rufe idanunsa yayi abinda yake kasan yadda nake rayuwa a cikin kunci? Na gaji idan ma bai rabu da ni don kanshi ba dole manya su shiga cikin maganar na gaji na ce idan ya so ya mutu don ni shi ya sani!" Na fada ina kuka, ko ba kome yanzu na fara jin kirjina ya daina min zafi. Bude jakata nayi na zazzage mishi maganin da nake sha. "Allah ya daura min ciwo, amma shine sanadi shi da matansa suka samu matsala ni ce abin zargi da tuhuma. Gaya min zaka iya wannan bagahuwar rayuwar? Don Allah idan ba zaka taya ni niman yancin kaina ba gara kawai ka kyale ni na rayu ko babu shi!" Daga haka na tattara na wuce gidan Baba Ya'u, a can na kwana duk inda na shiga ba a son na bar wurin saboda Yarana. Kowa son Yarana yake kamar yayi yaya. Haka yasa naki kula kowa na ko shiga harkan kowa da maganar Salmanu Faris.

Haka na gama hutuna na dawo makaranta, a lokacin yarana suna da wata tara a duniya. Na mai da hankali akansu da karatuna. Ana haka kwatsam Ayaan ya fara zazzabin hakori. Haka nayi ta fama da su daga asibiti zuwa gida, muna cikin haka sai bakiɗaya suka kwanta. Nasan masu yara biyu zasu fahimci yadda nake ciki, sai naji kamar zan yi hauka haka na kira Abba ina kuka na gaya mishi,washi gari sai ga Maluma, nayi kuka ganinta amma na ji dadi ita da Rabi haka muka wuce Asibiti Ayaan yana bayana da ya fara samun sauki. Ayaaz, Ayaat da Ayyanah suna jin jiki. Haka muka dauki kwanaki goma sai ruwa suke sha da allurai, ranar da na aka sallame su cikin dare nima na yanki jiki na fadi. Ba don kome ba sai yadda Maluma take min mita idan a gidan Ubansu ne ai da kome zai zo min da sauki, sannan ita bata ga laifin Salmanu Faris ba sam bata gani ba, kuma idan na ce haka zan cigaba har abada ba zata tab'a ganin laifinsa da kuskurensa ba, domin idan har Salmanu bai da wayo ba zai tab'a yarda ya rabu da Nadiyyah ba, yana da wayo idan ta b'ata mishi rai yasan ina jin zafi sannan yake Amfani da shigar da ni da suke yi ya hukuntasu, daga baya idan wani abu ya haɗa ni da shi sai ya jingina min laifin rabuwa da matansa, gyara zama tayi tana murmushi ta ce min.."Yana da hankali da wayo fes, irin yanayinsa kenan, idan wani abu ya haɗa ki da shi zan jure idan yana kullace da matansa yana niman hanyar da zai kuntatta musu sai ya samu damar su shigar dake rigima, da yake kina da hauka akanki sai ki ga kamar ai shi sonki yake." Dariya yayi tana faɗin. "Yana son zama dake ne, saboda kece wacce mahaifinsa suke so, sannan yadda yake miki da sauki akan na sauran Matan har yau Mijinki da sauran matan bai san meye so ba, domin ko na miskala zarratin baya kaunarku, dukkanku baya kaunarku shi din zuciyarshi baya kanku baya saka ku a cikin duniyarsa da yana da wani abu da ya yi replace dinsa da ku, tow godiyar Allah shine yana zaune da ku ne, domin biyan buƙatarshi idan da yana da hanya da ya watsar da ku ya samu wasu." Batun Maluma yana kan hanya, Tabbas na yarda da haka, abu daya zaka ga yana da shauki akai da fari ciki idan yana kallon ƙwaƙwalwa idan an bashi aiki, wani irin duka zuciyata tayi ba dai ina tare da psychopath ba ne? Wani irin tsoro da tashin hankali ya cika zuciyata, kwana ɗaya nayi a asibitin aka sallame ni, Maluma ta cigaba da cewa.."matukar ba zaki daina shiga harkansa da matansa ba, tow aiki yana tare dake sau dari idan ya ce miki zan sake wancan mike ki ce mishi ai ba ke kika aura mishi ba, idan ya ce zai dawo da mace zamanki take? Ina ruwanki da amsar yarsu? Ke bari na gaya miki ko namar jikinki kike bawa namiji duk ranar da kika samu matsala da shi tow ke ba gwana ba ce, abinda nake so ki fahimta zaman aure kike ba zaman wata yar iska ba, sannan ke kika bashi fuskar ya dinga azabtar da ke akan matansa ke gaki gwana mai miji mai son a nuna matar miji, ke ko mai kike yi matukar yace baki da amfani baki da shi ne, balle kuma har wasu matansa. Yadda Maluma take shiga ba nan take fita ba, sai da ta min tass sannan ya cigaba da mana jinya kusan maluma sai da ta kwashe wata biyu a tare da ni, sannan ta dawo ta bar min Rabi.

Ranar wata Alhamis ina tsaye a bakin department dinmu ina gyara zaman jakata, kamar an ce na d'ago kai muka yi ido hudu da Salim Attahiru Shehu Yayari, murmushi yayi sannan ya karaso, yana murmushi bakin shi ya ki rufewa, nima kadaran kadahar na tsaya muka gaisa. Ya mika min hannu na juya ina kallon gefena kafin ya ce min. "Jakarki nake nufi!" "A'a barshi kawai!" "Please bani nace!" Yadda yayi maganar ya sani na mika mishi ba tare da na sake magana ba, sannan na cigaba da tafiya a hankali, yana bin sawuna a hankali har muka isa inda motar da aka kawo shi yake. Ya bude min na shiga shima ya shiga wani abin da na fahimta sai na ga kamar yasan garin domin har gida ya kai ni, bakiɗaya sai na rasa bakin magana da kunya na gayyacce shi cikin gidan kamar yasan mai nake tunawa ya ce min. "Anan kuke zaune da Yaran?"gyada kai nayi ya wata karamar murmushi ya ce min. "Zaki iya tafiya, an jima zan zo na ganku!" Kamar na juya na ce mishi a"a sai nayi shiru na wuce. Tun daga ranar ban kara ganinshi ba, amma duk safiyar duniya zaa kawo min sako daga wurinsa, ranar da muka cika sati da haduwa da yamma sai gashi ya zo ya kwashe Yaran har da rabi suka fita da yake ina karatu, Yaran kamar sun san shi ainun sai gashi suna ta murna. Basu dawo ba sai dare lokacin da suka dawo ina parlourn ya shigo dauke da su biyu a kirjinshi Rabi goye da Ayaat Ayyanah kuma tana rungume a kirjinta, na sauri na isa na karbeta ina faɗin. "Sannu!" "Small Daddy sannu da kokari yau kasha hidima!" Ajiye su yayi ya fita ya sake kawo wasu kayan da yazo da shi, kaya fa kamar an aike shi haka ya tula min kayan na d'ago kai zan yi magana idanunsa ya fada cikin nawa, sunkuyar da kai nayi na ce mishi. "Mun gode sosai! Allah ya bada lada!" Daga haka ya fita yana faɗin. "Ina zuwa!" Can kuwa sai gashi da takeaway. Ya baza mana a parlourn, girgiza kai nayi na ce mishi. "Ni na koshi!" Zuba min idanu yayi yana murmushi ya ce min. "Tow shi kenan, bari na ci sai na tafi!" Haka ya ci ya tafi, yana fita na samu nutsuwa ya zo min, washi gari da kanshi ya zo ya kai ni makaranta sannan ya dawo ya kwashe su suka sake fita, a cikin sati biyu da yayi kullum sai ya fita da su, har na fara exam sai a lokacin ya bar Nijar.

Sati Uku muka yi muna jarabawa, a ranar na huɗu mun gama na dawo gidan a matuƙar gajiye ga garin Damina, daga yadda muka kwana da Ayaat jiya na fahimci bata jin dadi, haka yasa ko da zan fita sai da na bata magani. Ina shigowa harabar gidan da nake na ga motar zanzabira. Gabana ne ya fadi haka na shiga cikin parlourn da sallama. Faruq ya amsa min na shiga ina cire takalmin kafana. A parlourn na same shi zaune da Yaransa sun zagaye shi har ismaha. Kallo daya nayi masa sannan na wuce ina gaida faruq. Amsawa yayi na wuce dakina ko me yake cin ransa ina cire kaya sai gashi ya shigo. "Zaman uban wa kike yi a kasar nan?" Banza nayi da shi na cigaba da cire kayan jikina. "Ina magana kin mai da ni dan iska?" Nan ma ban kula shi ba, juyar da ni yayi da karfi yana faɗin. "Waye ne kike tarayya da shi?" Anan ne na ajiye rigar jikina na ce mishi. " Da ka fara saduwar aure da ni ka ji al'amarin budurcina fake ne? Ko an gaya maka yadda ka saba aurar karuwai ni ina cikin class din da suka zauna ne? Look na fi karfin namiji irinka da kowacce mai kayan dad'i sai ya ci, don haka ka bar tambayar waye shi domin ko baka aurena ba zan iya kazamta ba, balle da aurena kuma aurenka. Ka bar shirme kalli Yaranka ka koma wurin masu masu kaya me dad'i!" Cak ya dauke ni da zumar zai warware min abinda ya saba na ce mishi. "Idan akan mace ce da abinda dad'inta nan ake ganin mazantakanka, kada ka sake ka ce zaka min halin da ake yiwa matanka, ai tun daga ranar da ka iya hada shimfid'a da nadiya na gama set up na gama zama da kai, wallahi ba zan zauna da kai ba kuma ka sake ka tab'a min jikina sai na shirga da kai karar ka yi min fyade, da karfi domin ba zan tsaya ka ji wani nutswa da ni ba." Ina fadar haka na ji ya sauke ni a hankali yana kallon yadda nake magana kai tsaye. "Ban da toshewar tunani kazo kana zargina, haka bai ishe ka da yake ja mai da ni karuwa kazo zaka kwanta da ni an gaya maka ni karuwarka ce da zaka ci ni yadda kake so? Tow ka ji da kyau kan mage ya waye ja fita a rayuwata kafin na mai da mana rayuwarmu abin kwantace!" Daga haka na wuce ban daki nayi wanka na yi alola na fito na gabatar da sallah, Isma na samu a gadona kwance a, bayan na idar ba fito parlourn na ci abinci, ban gansu ba sai karfe goma duk nonuwata ya cika tam, ina zaune sai gashi sun shigo da Yaran dauke da kaya niki-niki, ban wani damu ba haka dai suka ya shigo da kaya. A gidan ya kwana a daya dakin Faruq kuma a parlourn. Washi gari da safe su suka yi abin karyawa, ban ci ba domin nima na tashi da zazzaɓi ne sun ki shan nonon alamar basu da lafiya, Rabi take gayawa Faruq, suka zo aka fitar da mu zuwa asibiti a can na wuni aka min allurai da magani, domin wtaansu goma sha daya ne yanzu..wani hakorin suke yi.

Duk yadda yaso na sake jiki mu shirya na gaya mishi gaskiya na gaji ya sawwake min, ya zata wasa ne sai da aka muka dawo gida na shigar da Yran ina fitowa na ce mishi.."Ka ga ina da mutunci a cikin Unguwar nan, don Allah ka bar ni, wai ma waye ya gaya maka inda.? Wani Tsinannen ne ya gaya maka inda nake? Ka fita kafin na kira maka hukuma, bana son ganinka na tsane ka idan na cigaba da zama da kai mutuwa ce zata ziyarci rayuwata ka tafi na tsani ganinka a gabana bana sonka ban tab"a jin kaunarka ba ka tafi na ce idan.kuma zaka hada da Yaran ne Bismillah!" Na.shiga na dauko mishi kayan yaran da Yaran, saboda na san waye Salmanu Faris yanzu sai ya iya amfani da Yaran ya sauya min rayuwta ya san perfect point din matanshi, ni ce ya sani sonshi ne to yanzu ido cikin ido na ce bana sonshi....

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 28

Ganin yadda na ce ya tattara Yaransa sai jikinshi yayi mugun sanyi dama sune weakpoint dinta, shiru yayi na juya cikin can na fito da kayan da suka dawo da shi na ajiye mishi. "Fitar min da su a gidana bana son ganinka da su, kai Malam Na tsane ka bana son aurenka idan aurenka dole ne tow tabbas ni ba dole ba ce a rayuwarka kuma dole ka sawwake min fitar min a gida!" Na fada da wani irin hauka, ina haki. "Bana sonka i repeat it again bana kaunarka ka fita min a gida kada ka kara zuwa inda nake idan na gama abinda nake zan shigo zanzabiran zaka san dalilin sunana Zainabu abu mai tagwayen suna kafin ya iso ka sake ni ko kuma na kunyata ka mafi girman kunyatawana cikin al'ummarka, na shirya tsaf domin tozarka idan nayi karya Allah ya tsine min albarka sai na saka ka tunanin anya nice kuwa!" Ina fadar haka na juya na bar parlourn, ban san lokacin da suka bar gidan ba, sai naji zuciyata tayi sauki tayi sanyi ta kuma rage min nauyin da take min, na kara da hade rai na kafe akan ra'ayina.

Tun daga ranar ban kara ganin ko inuwarsu ba, bayan mun kammala jarabawa aka sallame mu, na hada kayan na baro Nijar na dawo zanzabira, tun da na iso Yeemar ta zo itama muka ci muka rufe babu wanda ya san me yake tafiya a tsakanin ba, sai da na kwana biyu sai ga Daularh da Bilqis tare da Kubrah. Suka zo suka same ni lafiya lau babu wani abu. "Kin jefa mu cikin tashin hankali, fisabiilillahi sai ki kafta balaguronki babu labari! Ina kika shiga ne?"

"Ina Nijar!" "Fisabiilillahi sai ki zauna a can ba zaki gayawa gida ba!" "Ai iyayena sun san ina can!" Ware idanu suka yi Bilqis ta ce mana. "A cire son zuciya da son rai abinda kika yi, haka kowacce mace mai aji ake so tayi, ba ta zama ana koranta kamar kare nata likewa namiji ba. And a rufa mana asiri kada a ce ba za a koma ba!" Dariya nayi na girgiza kai nace mata. "Wannan hurumi ne na Allah! Idan yaso mu dai-daita sai ku ga an wuce wurin idan kuma bai so ba, sai ku ga kome ya tsaya cak." Basu ji dadi ba amma na basu tsaraba gari guda, sannan na raka su har waje. A hankali abubuwa dayawa suke ta fara ruwa. mai Babbar daki ta zo ta min magana ya bani hakuri amma yadda na fashe da kuka nace mata wallahi ba zan iya komawa ba, kawai na gaji ne idan na cigaba da zama da shi zuciyata zata buga, sai ta kyale ni haka ta roka yaushe zan tura mata jikokinta, dama Ayaan ta fara kin nono sai ya wuni bai sha ba, sai dare. Gashi Allah da ikonsa duk ya rigasu tashi tsaye har tafiya yana yi ya tsaya sai Ayyanah ta biyunsa Ayaaz da Ayaat kan halin Ubansu suka dauka na tsoro. Haka ta turo Faruq ya zo ya dauke su, na hada har da Kayansu domin da alamu yaye nayi biyun da basu tafiya suna kama abu su tsaya, babu amfanin ajiye su a wurina. Wayyo Allah na, ashe abinda aka yiwa mace akanka zai dawo kanka? Yes ranar da aka kai su fada washi gari naji labarin Nadiyyah ta zo gaida mai babbar daki, sai Ayaat ta ga Princess da murna ta rarrafa tana nufar wurinta, kawai Nadiya ta saka kafa tayi kwallon da yarinayr sai akan idanun mai babbar daki, "laailaha a lillahu Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Innalillahi wainnalihir rajoun!" Ta iso da sauri ta dauki yarinayr, yadda ta saka kafar ta naushi yarinyar haka kafar ya tsaya cak, Ayaan yana kallonta itama mai babbar daki kallon Yaron take yana kallon Nadiyyah ta kasa motsa kafar yana tsaye, kafin Mai Babbar daki tayi magana ayi wurgi da ita a. Bugata da bango, haka ta fadi kanta ya fashe, a hankali ya koma ya kwanta yana tsotsar hannunsa a baki, ita mai babbar daki sai abin ya bata tsoro da al'ajabi domin bata tab'a kawowa haka zai iya faruwa ba, ita tashin hankalin da ta shiga sai ta ga yarinyar ta kama dariya ganin irin kwallon da aka yi da ita tana ihu amma zai gashi ikon Allah sauran yaran sun koma jikin Ayaan din sun kwanta suna mishi wasa, yadda Sailuba ta fito haka ta cigaba da kallon abin al'ajabi ta cewa mai babbar daki. "Wallahi ko kashe ni za a yi ba zan yarda ba. Amma yau da na ga ni da idanuna nasan akwai mutanen da Allah yake tsayawa bayansu da gabansu. Mai Babbar daki tsarki ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, yar uwarsa aka tab'a itama ya tab'ata." Ta wuce kitchen ta dauko ruwan sanyi ta sheka mata ihu ta saka tare da rike kafarta, dole aka nimo mijinta, yana zuwa ya tambaya Princess da take kallon abin ta ce mishi. "Daddy kwallo tayi da Ayaat shine kafanta ya rike aka bugata da bango itama!" Murmushi yayi ya ce mata. "Good girl. " Ya juya ga Mai babbar daki tana kallon yaran da suka zagaye Ayaan ɗin yana zuwa ya dauke shi ya na shafa kanshi bude idanu yayi yana kallon Uban, sauran suka haura kansa suna kallonshi. Kwalla cike da idanun Ayyanah sai mita take tana tab'a dan uwan. "Bani shi na bashi ruwa!" Haka ya mikawa mai babbar daki shi ta bashi ruwa ya sha sosai sannan ya sauke ajiyar zuciya. Haka aka wuce da Nadiyyah asibiti. Hmm shima Uban gayyar kin kulata yayi akan Yaransa bai da mutunci, a can kuwa daure kafar aka yi suka dawo gida. Cikin dare kuwa aka ce ba ita ba barci domin dukar tsiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login