Showing 126001 words to 129000 words out of 157081 words
Tsaki nayi na mike ina mai barin parlourn, ya cigaba da ihu da masifa wai na bala'in rena shi, na mare shi amma naki bashi hakuri." Ban wani damu da abinda yake faɗa ba. Domin idan ka biyewa Aryaan uwaka ubanka zaku rabu kullum, shi na lura magana bata damunshi.
Karar ihun Princess na ji, tare da faduwar abu daga sama kummmm, Nadiyyah ta kara fasa ihu. Shi kansa mai gidan da yake can waje suka shigo da Faruq, Innalillahi wainnalihir rajoun, wai Ijlal ce ta turo wurgo princess daga sama godiyar Allah ma, akan kujeran parlourn ta fado, sai aka yi rashin dace ta kara buga kanta a kasa. Take kan ya kumbura, na ga tashin hankali da ban tab'a gani ba, Domin Yaya tsakaninsa da Allah yake dukar Ijlal kamar zai kashe ta, zan fita Aryaan ya mai dani ma zauna ya fita. "Idan ka kashe ta sai ka bi ba'asi, ai ko bata turo ta ba zata fado, ƙaddara ce a rubuce yau zata fado. Sannan da kake dukarta mace ce fa? Gaskiya na rena maka!" "Waye kai da zaka gaya min magana?"
"Sa'an kakanka na uku!" Ya zauna yana kallonshi. "Lusarin banza lusarin wofi kai baka ji kunya ba? Da kake jin kukan Zaitunah mai yasa baka zo ba? Har yanzu haka zaka cigaba da karkata bangaren guda? Me yasa baka da alkibla? A duk lokacin da wani ya dauko hanyar shiriya taya shi hawa hanya ake, ba kaucewar da shi ake ba, ita bata taɓa yunkurin kashe ka ba ita kuma ta yi yunkurin kashe ka, duk abinda Ijlal tayi akan ka tayi, ko sanadin mutuwar Yaron cikin Nadiyyah bana tunanin ta yafewa kanta domin har yau tana cikin kunci da ciwon abu, ka sani babu wanda baya kuskure,ita nata husuma ta haɗa wacce tayi kisar tana raye tana gefenku, don Allah ka nutsu kafin kayi hukunci zuciyar bai da amfani tayi laifi amma kafin tayi waye ya fara? Kai yanzu a kama wancan tsokar a watsa masa danyen barkono zaka ji dadi!" Zare idanun yayi ya ce mishi. "Ai ho Ashe ba dadi kuskure ne duk sunyi Gara ka sani tun wuri kai ne matsalar gidanka. Kato ba wayo wannan Bargaga yafi ka hankali!"
Ya fada yana mikewa, tare da cewa. "Shashancin banza ka zauna kana ta hauka a tsakiyar mata kana hauka." Yadda yayi mishi tas yasa shi jin kunya a gaban Ijlal ya manta a gaban Yaranta yake hauka da shiririta, wannan abin ya ƙara wutar tsanar Nadiyyah a zuciyarta, itama Nadiyyah shirinta shine ta cutar da Nana A'ishah, domin tunda suka iso asibiti aka rufe yarinyar, sai kuka take tana jin ciwon abinda ya faru da ba kama Ijlal ta yi mata abinda tayiwa Yarta.
Wurina Aryaan ya kawo Ijlal, ya ce min. "Dubi abinda sakaran Mijinki yayi don Allah?" "Bana son haka, ka girmama shi." "Ke ba zan girmama shi ba, shi din wani abu ne da xan girmama shi!" Ya ja tsaki yana zama akan kujeran yana hararana, "yanzu da ka kawo ta mai zan mata?" "Ki duba ta ya dake ta!" "Ni likita ce?" "Ba aikin ki ba ne, amma ki duba goshinta!" "Wai me yasa haka ne?" Na tambaye shi, "saboda tana son ta shiryu ta hau hanya madaidaiciya!" "Kishiya ce fa!" "Ke bana son sanabe, miji ce ba kishiya ba."
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 47
Ya fada yana watsa min harara shi nan ya ji haushi, "ko don Yaranta taimaka mata!" " Da ka kyale ta zan je asibiti!" "Ban ciki da gulma?" Ya fada yana mai kallona, shi dai ya cika gundura wallahi. Haka na gyara mata wurin, sannan ta koma bangarenta. Na zo zan kwanta sai ga Yaya ya shigo, kallonshi nayi sai na ji ban ji dadin abinda yayiwa Ijlal ba, zama yayi yana faɗin. "Yanzu fisabiilillahi haka zaki hana ni hakkina!" "Baka warke ba ne!" "Daddy!!" Muka ji muryan Nana A'ishah, fitowa muka yi muka ganta a barandarsu. "Nana A'ishah!" "Mommy tana fitsarin jini ta mutu!" Ta fada tare da yin baya da hannunta alamar uwar ta mutu. Da gudu muka dauka tare da nufar bangaren, tabbas jini yake zuba cikin tashin hankali ya dauki Ijlal ni kuma na dauki Nana A'ishah na kawo ta bangarena, na koma na dauki Amiratul Zaitunah, na dawo bangarena, na nufi dakin Yara na ga Aryaan yana tsaye, su Ayaan suna barci. "Ya mata duka a cikinta ko." Kamar nayi kuka na kai yaran dakin na kwantar da su. "Mijinku bai da hankali Allah Sarki!" Iya abinda ya furta kenan, haka na ji kamar zuciyata zata bar jikina, gaskiya Ijlal tana bukatar wani ya tsaya mata, haka na kwana a zaune har aka yi sallah asuba, sai da nayi sallah, sannan na mike na nufi dakin yaran na tashe su, suka yi fitsari sannan na dawo da su dakin suka kwanta, kamar xan yi kuka ina kallon Yaran har kusan gari y waye jin motsin da a shigo parlourn na mike zan fita ban san yadda aka yi duhu ya mamaye ilahirin ganina ba, kawai zubewa nayi ban kara Sanni inda kaina yake ba, tashin hankali da ya shiga Allah kaɗai ya sani shi kanshi sai yaji kamar zai zauce, haka lamarin ya zo mishi ba dad'i. Zai kai ni asibiti Aryaan ya shiga jikin Ayaan ya ce mishi. "Kyale ta a gida, ka gwada jininta ka gani!" Ya fada yana kallonshi, haka kuwa yayi ya ga jinin yayi mugun hawa kamar zai yi kuka haka ya rubuta magani ya kira Faruq, can kuwa sai gashi nan yazo yana zuwa sai gashi nan ya bashi takardun, bayan kamar minti talatin sai ga Faruq, haka ya daura mata ruwa ya mata allurai sannan ya koma gefe ya zauna. "Kwana tayi bata rintsa ba, wallahi ka ji tsoron Allah domin sam baka da future kome naka a buɗe yake baka iya kome da maza zasu yi su amsa sunan maza fisabiilillahi kashe ta zaka yi ne?"
Ajiye numfashi yayi kafin ya cigaba da cewa. "Baka da lissafi kamar sauran mazan, haba don Allah kalli yadda ta koma kai da matanka zaku kashe ta ne? Ya kake son tayi ne?" Shi kanshi sai yaji bai kyauta ba, tunda abin ya faru bata yi magana ba sai bin shi da take yi da idanun kamar zata yi kuka, har da yazo kafin sumar Ijlal bata mishi magana ba, Zainab ta sauya sosai kamar ba ita ba, mutuwar Mahaifinta har yau bai kyaleta ba, yana bibiyarta.
Karfe shida na yamma na bude idanuna, Maluma na gani a gefen gadon dakin, tana magana a hankali a waya alamar bata son na farka tana faɗin. "Na rasa gane meke damun mijinsu bakiɗaya matan suna kwance babu me lafiya, gaskiya zan dauke ta zuwa gida idan ta ji sauki sai ta dawo amma wannan fitinar tayi yawa. Ita wancan ance Yarta aka sako daga sama, daya kuma dukarta yayi abu sai kace hauka kai ɗaya a cikin gidanka baka da alkibla." Yadda take fadar na juyar da kaina ina jin kamar har da laifina da abubuwan da yake faruwa da Yaya. A hankali na mike tare da sauka a gadon na shiga banɗaki nayi alola sannan na dawo na kwanta na huta kafin nayi sallah, bayan na idar na kwanta, saboda jirin da nake ji.
A bakin Aryaan nake jin ya naushi cikinta ne ya samu mahaifar, sai da ya tsage shine aka mata ɗinkin, shine suka mata ɗinki Yaranta bakiɗaya suna wurina, Mai Babbar daki ta turo min wata yarinya mai suna Madinah ta, taya ni kula da Yaran. Haka Maluma ta kwana uku sannan ta koma gida, na cigaba da kula da harkokin gidan. Washi gari na shirya da Yaran har da Amiratul Zaitunah, na gaishe da Uwarta na bar Yaran kafin na wuce wurin Nadiyyah da yarta kawayen ta yan bariki, sai gulma suke ganina da Yaran sai suka yi shiru. Yaran suka nufi gadon Princess tana ganin Ayaan ta kama murmushi.."Didih ya jikinki?" Ya tambaye ta, yana haurawa gadon. Mikewa Nadiyyah tayi a fusace a raina na ce. "Allah yasa Aryaan ta samu!" Ai kuwa tana nufarshi sai ta kasa kome ta ce mishi.."kada ka tab'a kafar ta karye anan!" Ta nuna mishi kafar. "Allah ya bata lafiya!" Ya fada yana kallon yarinyar. Saka hannu yayi a cikin aljuhunsa ya ciro sweet ya mika mata, "ki sha zai warke!" A hankali ta bare tana kaiwa bakinta. Tana tsotsa ta ce mishi.."Ayaan da dadi Sweet din!" Gyada kai yayi yana faɗin. "Na san da dad'i." Gyara zama yayi ya ce mata."Princess gaya min gaskiya Maamah ce ta wurgo ki daga sama ko Mommynki?" Kallonmu tayi cike da tsoro. " Ayaan!" Hannu ya saka a bakinshi yana faɗin.. "Shiii! Princess gaya min ba zan bari wani yayi hurting dinki ba zan kawo giant lion yayi gadinki, sannan zan kai ki daji ko ga Giraffi da Sumba da Nala!" "Yaya nima zaka kai ni na ga Timo da Pumba?" "Yes Ayaanah, oya gaya min zan kai ki, ki rafi da Sabrina da Zazu!". "Mommy ce ta turo ni bayan ta buge hannun Maamah!" Sauka yayi daga gadon. Ya taka gaban Nadiyyah. "Stop biting around bush, stop show your self like victim, hmm!" Daga haka ya fita daga cikin dakin, ya hanata magana domin rufe bakin kowa yayi, ya koma dakin da Ijlal take tana kallon shi ta kama murmushi. Yadda ya goya hannunsa a bayanshi yasa ta fahimci ba Ayaan ba ne. "Malam magajin malam!" Zama yayi yana wani murmushi irin a yabe shi nan!
"Ya jikinki?" "Da sauki sosai" shiru yayi kafin ya ce mata. "Da nace ki yi hakuri me yasa baki yi ba? Nace ki yi hakuri ba wai don ba wata hanya ba ne, baki da uwa amma mahaifiyarki Mutuniyar kirki ce, bata cutar da wani ba shi yasa da kike haukarki Allah ya baki sa'a, amma ki sani ko yaya kika yi wani kuskure kece zaki sha wahala, domin kuwa Nadiyyah tana kokarin bata rawanta da tsalle. Kada ki sake irin wannan sakarci." "Ba fa ni na turo ta ba wallahi!" "Waye zai yarda? Bayan kin kasa kama zuciyarki inda Zainaba ta fiku kenan, tana iya danne abinda kuke mata tayi kamar bata ganku ba, amma ku dan abu kadan zai ku fusata ku kama ihu da kin kyale yarinyar, Uwarta zata yi sanadin faduwarta gashi ita ta turo ta gashi nan kin ci duka a kyauta." Ya fada yana kallonta yadda take kuka, akwai giɓin da yarinyar ta rasa shine uwa, shi yake damunta domin uwar riko bata mata wani rikon Allah da Annabi ba.
Shigowarmu ya mike muka mata sallama, sannan duk suka biyo ina dauke da Amirah akan keken marasa lafiya. "Me yasa kake son saka kanka abinda bai da dame ka ba, an gayyace ne."
"Tunda bake kika haife ni ba da sauki idan kin ji haushi rufe ni da duka." Ya fada yana mai cigaba da tafiya har wurin motar, shiga muka yi ya cigaba da cewa. "Zaman tare yasa nake tausayinta, sai na fahimci Jinyar Yarta yasa nake hango nadama a cikin idanunta, ta sauko sosai. A yanzu da tasan ciwon yarta ba na warkewa ba ne, shi yasa zaki ga ta saka yarinyar a gaba tana kuka, ko ba a hukunta Allah ya hukuntata da ciwon Yarta, kuma kin ga ƙaddaranta kenan shi yasa nake tausayinta."
"Idan ta shuka maka rashin mutunci ba ruwana, yawwa na gaya maka ka ji." Na fada mishi domin na lura yana da iyayi, ban san me yayiwa Ijlal ta nutsu ba, amma tabbas tayi sanyi kalau. "Ba zata iya ba, domin Allah ya amsa Addu'ar kakanmu ba wanda ya isa ya mana rashin mutunci, ko wanda muke tare da shi ba a wulakanta shi. " Ya fada da wata irin kwarin gwiwa. Ganin takaicinsa zai hana ni magana yasa nayi shiru, haka Yara suka yi ta ihu a saya musu ice cream, haka Faruq ya tsaya ya sayo musu, sannan ya mikawa Aryaan na shi ya ce gana Ayaan. Haka muka iso gida babu wani damuwa a harabar gidan muka same shi an shimfid'a mishi abin zama, ga Jakadiya a gefenshi sai wani karya kai take tana wani magana kamar mai niman wani abu. Yaran suka nufe shi tana ganinsu ta fara musu kirari. Wucewa nayi cikin gidan na zube a parlourn.
Satin daya aka sallamo Ijlal da Nadiyyah, duk zaman da Ijlal tayi a asibiti babu wanda yazo daga gidansu, sai na kara hango maganar Aryaan marainiya ce da take jin abin. Haka nayi ta kula da Yaran sai bayi da aka kara kawowa gidan Ni dai Madinah, take zama da Yaran, Amma bangaren Ijlal akwai bayi biyu. Wani irin firgita tayi da Yaya sau biyu yana gaya min wai idan ya je dakin raxana take tayi ta matsawa kenan. "Allah ya kyauta!" Nake fada ina zan iya bqshi tip ya samu Matarshi daga nan naji labari ya sauya, ai ni kishiya da Yaya sun koya min hankalin. Haka suka yi ta jinya Princess kuwa kamar tayi tsuntsuwa ta zo wurin Yaran tana zuwa kuwa zata fara ihu da hauka da niman fada, Aryaan ya kore ya ce ba ayin wasan da ita, haka yana yiwa Nadiyyah ciwo.
Haka muka cigaba da zama, anan haka Birthday din Amiraah ya zagayowa, shi yasa Yaya yayi sadaka aka raba abinci da pure water, kun san yadda sadakar pure water yake? Kamar a bude maka kofar taskar Ubangiji ne a ce debi abinda kake so, haka sadaka yake sadaka maganin masifa, haka ranar Birthday din aka yi abincin sadaka, da la'asar muka tara Yaran yan uwa, muka cigaba da hidima hankalina baya tare da ni, haka kawai nake jin zazzaɓi yana rufe ni, lokaci zuwa lokaci ina jin abin, sai ga Ikram tazo da presentations dinta, kallona tayi cikin wata doguwar riga mai dogon hannu tana murmushi ta ce min. "Wannan kayan zaman makoki ne ko na taya murna!" Yadda tayi maganar sai da naji gabana ya fadi, haka na dake ina murmushi na ce mata. "Kin ga nayi kama da wacce take Mai Sara ya boya? Ni bana tsoron mutuwa tunda ban dauki nauyin kowa bana jin akwai abinda zai saka na ji tsoron mutuwa." Murmushi tayi ta ce min.."Baki ji kome akan mutuwar Abbanki bane?" Dariya nayi na ce mata. "Ta yaro kyau take bata karko,kafin Abba kin manta waye ya rasu min? Kin ga kuwa ai ni ba bakuwar mutuwa ba ce, kin ga nayi kama da wacce mutuwa zata razana? Kece dai kike gudunta domin kuwa boya kike, na san Yanzu ma wata sharri ne ya fito dake, tunda kin kasance Tauraruwa mai wutsiya ganinki babu alkhairi sai sharri!" "Tabbas baka bayyana sai da sharri zan bar nan amma sharrin zai biyo baya, ni din I'm like grim ce idan na ratsa sai na dauka ko na nakasa." Murmushi nayi na taka har gabanta. "Kina wasa da wuta, idan kika tab'a ni kuma xan tabbatar gudunki ya tsaya, domin xan wulakanta ki sama da yadda baki zata ba."
Murmushi tayi tana faɗin. "Ki saka idanun yadda kika hana shi dawowa da ni a matsayin Aojana sai na saka ki kuka Awatif kin manta yadda na saka a ka binne ki!" "Allah ya baki sa'a! Aojanah......
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 48
Ban san yadda aka yi Ijlal ta zo ba, sai dai tana zuwa tayiwa Ikram diban karena mahaukaciya ba, jikinta har rawa yake ta juya tare da dauko drink ta watsa mata. "Uban waye ya gayyace ki? Fita kafin na wulakanta ki!" Yadda take fisga yasa bakiɗaya muka zuba mata idanun, haka Ikram ta fita cike da kunya, ita kuma Ijlal ɗin ta ce min . "Kiyi hakuri matsiyaciya tayi gaba!" Ta fada tana kallon kofar, haka aka gama taron lafiya Amrah tazo da Yaranta biyu. Daga ita babu wanda ya zo a cikin danginta, haka yasa bakiɗaya aka yi hidimar cikin farin ciki da walwala. Wannan abin da mamaki yake, domin kuwa bamu san yadda aka yi Nadiyyah ta fita ba sai ga tare da Ikram, anan ne kuma na tsaya a bakin kofar na ce mata. "Lallai kina son fitina da rai. Wallahi ta shiga sai dai a fitar da gawarta dama can gawa tafe ce, ta shiga mu gani!" Wannan maganar yasa Ikram ta ja da baya na kara bin ta, ina faɗin. "Kin so ki yi amfani da ni domin biyan buƙatarki da haka bai yi ba shine kika biyo ta baya? Ikram kada ki shigo gidana ko nace Aojanah kin yi kuskure!" A hankali ta juya tana dariya har ta bar wurin, idanun na cike da takaici ina kallon Nadiyyah wacce sam bata da hankali.
Ban san yadda aka yi Aneesah ta kara komawa jikin Nadiyyah ba, amma yadda suka makalewa juna abin ya bamu mamaki, yadda Allah ya daura ni akan Yaya duk abinda za ayi baya tab'a min fada ko ya tsare ni sai dai ya ce muje zai yi bincike, saboda yasan iya haka ne zai zama adalci, idan kuma ya dawo kan maganar da kanshi yake kiranmu ya bawa kowacce rashin gaskiyarta, tun da Aryan ya shiga kunyata shi sai abubuwa suka yi sauki har yakan yi fada da masifa. Akan kowa itama Nadiyyah da yake dan ganin kada ya mata abu ta ga don tana bin shi ne itama rashin mutunci yake haɗawa ya mata, sai dai idan ya gama zai ta bin ta yana rarrashinta. Haka kuma zai bi ta ya turmushe ta shi kenan an shirya.
Wani abu da na fahimta, shine yadda yanzu ya daina karban korafin kowa, ya koma namiji, sai dai