Showing 6001 words to 9000 words out of 157081 words
yi alfahari da kai a matsayin miji? Taya zan gayawa Yarinyar da zan haifa ubanta jarumi ne? Kana sona amma baka san yadda zaka nuna min soyayyar ba idan ganka sex ya kawo ka, ban san ƙaddaran da yasani baka rayuwata ba, amma maganar gaskiya, ba zan iya hada shirgina da kai ba, kuma dole ka hakura da ni ka je can matanka su cigaba da baka abinda kake so, tunda kayi mai da kanka Womanizer!"
Naushin bango yayi da waɗannan kalaman ta hana shi jin dadi da nutsuwa da wannan kalaman tasaka shi jin yan ya gundura da ita, da wannan kalaman tasa shi jin shi kamar ba namiji ba, mace kenan ta saka shi jin ya muzanta ina kuma maza? "Iya abinda ka iya kenan kazo kaci mace ka ji dadi ka kwanta da ita ka ji dadi idan har wannan shine rayuwarka Salmanu Faris gaskiya baka yiwa mai sunanka adalci ba, gani ci yadda kake so idan ka gama ka bar min sauran jin nayi yadda nake so da shi!" Yadda tayi maganar a cikin dakewa yasa shi jin kome ya ishe shi. Mai ya dace yayi? Mai ya kamata yayi? Tabbas ya kamata yayi wani abu ya dace ya yi wani abu, wata bangarena zuciyarshi ta ce mishi. "Namiji zaka zama mai fada a jiki mai tsawa daya wanda matan zasu shiga hankalinsu?" Lumshe idanun yayi ya bude sannan ya gyada kai yana jin kamar yanzu ya samu mafita, ya kuma samu yadda zai yi!
Lokacin da ya fito ya nufi wurin kayanshi, ya bude closet dinsa ya ciro kayan da zai saka ya saka a hankali, yana tuna a da can ita take zuwa ta taya shi saka kaya amma yau shi ɗaya. Tsaki yayi ya cigaba da saka kayan sannan ya nufi waje, babu abin karyawa haka ya nufi cikin gidan, har lokacin Mai babbar daki bata dawo ba, turawa Faruq sako yayi ya ce mishi. *Brandy ya ajiye kome ya dawo bakin aikinsa!*
_Yes sir_ ya mishi reply, fitowa Sailuba tayi ya zube a gabanshi.."Barka da asuba Allah ya baka nasara." D'aga mata hannu yayi, mikewa tayi ta koma kitchen din ta hado abin karyawa ta kawo mishi, dama abinda ya kawo shi kenan, a hankali ya fara ci yana kallon abincin, a gigice na fito parlourn sanye da wata doguwar riga na nufi kitchen, Sailuba ta ce min. "Ranki shi dade mai kike so?" "Bani tukunyar dumame ki zuba man shanu da yaji." Da sauri tayi abinda nace, don tukunyar tana kan.wani karamar gas ce wanke hannuna nayi na dauko tukunyar n a dawo parlourn na zauna na fara ci a hankali, idanuna ne suka fada kanshi, yadda yayi kamar bai san ina parlourn ba, haka nima nayi kamar ban san yana parlourn ba, "Sailuba don Allah hada min da katon kofin kunu idan babu hada min ruwan shayi maza!" Ba musu ta haɗa min kunun tunda na fara cin abinci shi kenan kome ya sauya ga shi saura kwanaki a fara azumi, yana kallon yadda ta cinye abincin tas, ta kuma daura da katon jug na kunu, sannan aka kawo mata goran ruwa ta shanye, abin mamaki ya bashi anya dan adam zai yi irin wannan cin abincin? Share zancen yayi ya mike tare da bari parlourn ydda bai shiga harkata ba nima kuma ban shiga na shi ba.
Ina gamawa na mike na hada kayansa da nawa na kai kitchen, ina mamakin dadewar Mai Babbar daki, daki na wuce na kwanta barci yayi gaba da ni. Kamar wasa tunda na kwanta nake jin kamar ana warware min gajiyar da ya zuba min. Karfe sha daya na ji hayaniyar mutane a parlourn, a hankali na tashi zaune sannan na sauko da kafana yunwa nake ji, amma sai nayi wanka. Haka na shiga nayi wanka na fito na shirya a hankali. Ina shiryawan naji cikina yana wani irin juyi. Da sauri na saka pant na fito parlourn na ga Yaran gidan ne matansu, sai Hajjah da take zuba surutu. "Sannunku!" Na fada ina nufar kitchen, "Sailuba me aka gama?" Nuna min taliya da miya, sai masa da miyar ganye. Sai shinkafa da take yi. Ban tsaya bata umarni ba na zuba iya abinda nake so nace mata. "Kunun ya kare ko?" "Eh a sake miki ne?" "A'a xan shan tea!" Na fitar da shi waje, na ajiye a tsakiyar parlourn sannan na koma na hado tea na dawo, ganin plat din da na hada abincin sai suka tsayar da hiransu, na saka hannu na fara ci kamar zan cinye da yatsuna. Haka nayi ta ci har na tashi plat din Mai Babbar daki ta ce min.."a karo miki ne?" "Masar ba yayi min dad'i!" Mikewa Bilqis tai tana faɗin. "Tow bari na karo miki!" Ta shiga ta karo min guda uku domin manya ne masar, aka saka min miyar ita wai taga ban ci nama na, haka ta sa aka zuba min a wani bowl. Tana kawowa na zuba mata idanun kafin na ce mata.." ai ni bana son nama!" "Kunga irin ba, ke dai ba a iya miki a kawo miki abin arziki ki ce bakya so?" Inji Hajjah kallo daya nayi mata,sannan na cigaba da cin masar na cinye, Sailuba aka kira da abin wanke hannu na wanke sannan na shanye sauran ruwan na sauke ajiyar zuciya ina jin cikin na wani irin juyawa, lumshe idanuna nayi ina murmushi yadda cikin yake juyawa. "Sannun kin ji!" Mai Babbar daki ta ce min, murmushi nayi na ce mata. "Yawwa Ummi ya kika samu su Abba Umma da Maluma ta?" Na tambaye ta. Murmushi tayi tana faɗin. "Suna lafiya amma baki tambayi Hajjah ba!" Juyawa nayi na kalleta yadda tayi wani irin da idanunta fici-fici da su, na ce mata. "Ummi tunda na ganku tare na san lafiya take." Ns juya kaina ga su Bilqis da Daulah nace musu. "Shine baku tashe ni ba?" Yadda nayi maganar a shagwab'e, suka ce min. "Ina zamu iya tashinki, tunda muka shigo muka isa zauren al'umma muka gaida Mai Martaba ya ce kada mu tashe ki, kina barci sai dai kawai leka ki muka yi muka dawo nan, bamu jima ba sai ga Ummi da Hajjah namu!" Ta wani rausayar da kai tana faɗin. "Fad'i da ihu ki kara da wayo, ai ni ta mutane ce, duk wnada ya ga ba zai iya ganina ba, sai dai yasan yadda zai yi da ni!" Daga haka ta cigaba da hira da su, kallon Mai Babbar daki nayi ina mata magana da idanu me yasa ta zo da Hajjah? Murmushi tayi ta cigaba da cewa. "Hajjah zata mana kwana biyu anan in sha Allah! Zata zauna a wancan dakin da naso hada ku ne saboda sha'anin dare!" "Ni jikar Gobirawa, a yanzu ma ba ayi maraba da ni ba, nima kan na ga karshen kiyayya, ina ga gara na koma inda na fito."
"Haba mai gadon zinari, kiri-kiri yarinyar nan da iyayenta suke guduna ni dai Mariama mai da ni gidan Tarasulu, ni takwara tayiwa diban karen mahaukaciya, ai nasan tunda basu so zamana da ita ba kaf duniya babu me min maraba na godewa Allah da yana sona." "Hajjah don Allah kada ki tara min jama'a, ni ban ce bana son zamanki ba, ba zan tab'a kin zama da ke ba, haba Hajjah ta abar kaunata." Na shiga mata kirari. "Matar Malam Gobir Haba uwar gidan Malam Gobir soyayyar da aka jikata tun daga duniya har lahira a dangwala da kauna!" Na fada ina murmushi wani washe hakori tayi tana faɗin. "Yar nan kin san yadda kike rarrashina shi yasa nake kaunarki ba don haka ba ai da na fita a harkanki, Mariama kin gani ba takwara tafi iyayenta mutunci, yarinyar da zuciyarta kamar ta zinari. Shi yasa kaf dangina bayan Abidi bani wata gwana sai ita."
A hankali aka yi ta hira, tura min matashi Daularh tayi, na kwanta murmushi nayi mata na ce mata.."kin ga ina jin barci ko?" Na kwanta dariya tayi ta ce min. "Eh mana." "Me zaki ci idan kika tashi?" "Ummi duk abinda aka yi zanci fa!" Na gyara kwanciyana, sai nayi ban ji dadin kwanciyar ba, tashi nayi na nufi saman doguwar kujerar parlourn, tun ina jin su sama sama har barci yayi gaba da ni.
***
Tunda ya tura faruq asibiti ya mishi hoton Amiratul Zaitunah, ya ga yarinayr tana dan wasanta, sai Uwar da take can gefe tana amfani da wayar hannunta. Ya cewa Faruq. "Idan an sallame su ka dawo da su." "Tow Sir!" Daga nan ya fita can suka dawo da Doctor Mubarak, ya gama dubata sannan ya sallame su, kallon Faruq tayi ta ce mishi. "Ina shi yake?" Murmushi yayi mata, bayan ya dauki Amiratul Zaitunah, itama da nata cikin kamar zai dirko. Cikin Nadiyyah yafi nata girma amma haka ta haifi Yaron nan babu rai. Murmushi tayi tana jin wani irin dad'i a ranta babu Nadiyyah babu Zainab lokaci guda ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, haka Faruq ya ajiye Amiraah din a baya sannan ya koma ya kwaso sauran kayan, abu daya take son sani, meye a cikin Zainab din? Mace ko namiji? Idan namiji ne ta kashe shi kafin ya zama Magaji ai ko Nadiyyah abin da yasa ta rasa cikinta, gaya mata tayi namiji zata haifa, da mace ce ba ruwanta amma jin namiji ne yasa ta kashe shi, wannan abin kawai zai kafata a cikin gidan Yayari. Don ma kada ya gano ta da ta haɗa da Amirah ta kashe amma tasan zai iya gano ta, sau dayawa tana yawan hango wani irin rashin yarda da yake nuna mata, duk da bai fito ya ce bai yarda da ita ba, amma ita tana hango wasu abubuwan da ita daya ta sani ta kuma san dalilin haka.
A motar wata number ta kirata, bata dauki kiran ba. *Sorry akwai Bodyguard dinsa a tare da ni idan na koma zan yi bayani!* Daga haka suka isa har zuwa fada ta ce mishi. "Ka kai ni cikin gidan, zan gaida mai babbar daki na kai mata Amiratul Zaitunah ta ganta." "Yallabai ya ce na kai ki gida ne, idan kin isa sai ki zo da kanki!" Daga haka ya wuce da ita gida, ya ajiye ta ya sauke mata kayan ya ajiye a wurin ya juya ya bar kofar gidan, shi babu wacce zata samu kyautatawarsa sama da Ikhlas. Lokacin da ya koma fada ya samu ana tattaunawa da wasu wakilan gwamnati, komawa gefe yayi ya dauki takarda da biro yayi rubutu, sannan ya nufi inda ruwan gora suke ya jera a saman tire, sannan ya saka takardan a kasar goran yana zuwa ya mikawa Salmanu Faris. Kallon juna suka yi ya dauki goran da takardan, sannan ya nufi sauran wakilan gwamnati ya rabawa mutanen parlourn ruwan ya koma gefe.
_Alhaji Kabiru Hammud Yayari da wancan mutumin mai farar shaddar suna da connection, sannan shi din yana cikin tafiyar siyasar Alhaji Nuru Yayari_ amma yadda yake nunawa kamar babu wani kyakkyawan alaka a tsakaninsu. "Na ji amma maganar batun ayi siyasa na jari hujja ya kare, talakawa suna tare da mu, sannan a cikin shekarun da yayi yana mulki me yasa bai gina kanshi ba? Wanda ya ke son cigaba da mulki gina kanshi yake tare da bawa al'ummar da yake mulkan damar fadar ra'ayinsu." "Wato mai Martaba, wasu abubuwan ne dole a kyale talakawa cikin wahala domin ko wannensu yana da bala'in son kai, idan aka gina makaranta su zasu fara shiga suna kwashe kayan gwamnati suna sayarwa, idan aka kawo tallafi zuwa asibititoci talaka nan da ka tausayawa shi zai fara kwashe kayan al'umma da gwamnati yana sayarwa, Mai Martaba shifa talakan Nijeriya bai san waye ke sonshi ba, waye yake son rayuwarshi ba, wannan yasa nake kara tunatar da kai mun kawo sako mai yawan gaske, kai da al'ummar fadar zanzabira, a taya mu isar da sako ga talakawa yadda zasu fito kwansu da kwarkwantasu!" Inji Mutumin, shiru yayi yana wasa da yatsunsa. "Ka koma ka gaya miki mishi gaskiya ya nime al'umma da kanshi, ni ba zan iya saka hannu akan cutar alumma, abinda ka kawo min ka ga wannan jekariyana? Yana da gomanshi, maza ka mai da mishi kayansa."
"Kai Yaro!!" Yadda yayi kiran shi da yaro fusata shi ainun dukar table din Salmanu Faris yayi take ta tsage gida biyu kowa ya tashi, amma shi yana zaune ya ce mishi. "Zauna!" Ba musu ya zauna ya daura daya akan ɗaya. "Waye Yaro?" Take elder na Palace din suka dawo bayanshi. Faruq ya isa gaban mutumin ya saka mishi wannan sandar hannunsa a wuyarshi. "Sauka ka nime Afwa ko na sare kanka!" Yadda kowa ba fadar ya koma bayan Salmanu Faris yasa shi zubewa a ƙasa yana faɗin. "Tuba nake ranka ya dade, a yafe ni bisa kuskurena." Murmushi yayi ya ce mishi. "Kuskurenka?" D'agowa yayi da sauri ya kalli Mai Martaba, "kasa da kai!" Faruq ya fada da karfi kamar zai buga mishi sandar. "Waye kai fa zaka d'aga min murya? Kana nufin bamu san waye kai bane? Ka koma ka gayawa Musharraf ba za a bashi goyan baya, sannan idan yayi wani kuskuren abinda zai nima ba zai samu ba, kuma ka gaya mishi ya nime al'ummar da kanshi." Daga haka ya mike sannan ya ce mishi. "Hukuncinka zai biyo bayan isar da sakonka ne!" Daga haka ya mike tare da barin zauren al'umma. Yana fita Faruq ya rufa mishi baya, a hankali yake tafiya yana jin kamar wani abu mai karfi ya shiga kanshi, amma yana fitowa yaji kamar abin ya fita a kanshi. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon cikin gidan. "Allah ya baka nasara na kaisu gida!" "Na gode sosai Faruq!" Ya nufi cikin gidan, ba kome yasa shi zuwa cikin gidan ba, sai yadda yake matuƙar son ganinta da ciki, murmushi yayi yasan duk abinda zai yi Mai Babbar daki ba zata tab'a bashi ita ba. Sannan shima a yadda yake so ya zama namiji da ita da kanta ya sauya. Don haka ya juya tare da nufar gidansa, gara ya koma gidansa zai fi mishi sauki ace yau yarinyar nan ya je gani ita kanta zata yi ta kin a kanta kamar bai da wata mafita ce shi yasa yake yawan damunta, banda haka ai da ya shiga amma baya son reni a tsakaninsu yanzu yayi alƙawarin babu macen da zata sake ganin damarshi. Daga yau yayi wannan alƙawarin in sha Allah....
[8/26, 5:40 PM] Ramlat Manga41: 03
Tun daga lokacin ya yanke kafarshi da zuwa cikin gidan. Mai Babbar daki ta ji dadin haka domin ta haka zai tabbatar mata da shi namijin duniya ne, kuma nima a raina naji dadi domin ta haka zai saka kowa ya gane bafa baya yake bi ba. Nima idan yaso kulla min tijara zai yi a gaban kowa ma, wannan yasa ni samun nutsuwa. Hajja da ta tare kuwa kullum ne da duniya sai ta yi maganar salamunu faransa bai shigo ba, anya yana nan kuwa. Ranar wata juma'a na sha kwalliya da wata bubu gown, na fito parlourn na zauna ta kalli Mai Babbar daki ta ce mata. "Mariama anya yarinyar nan bata gaji mugun hali ba? Ace yau kwana uku da zuwana amma Salamunu faransa bai shigo ya gaishe ni ba, dole na je fada na mishi gaisuwa naji dalilin kin zuwan shi cikin gidan." Tana dire aya na ce mata. "Waye ya aike ki? Waye ya saka ki? Ni bana son haka, wallahi zan kira Abba yazo ya dauke ki!" Wani ware idanun tai tare da kankance shi ta ce min. "Idan kin so ba Junaidu ba Azara'ilu zaki kira yar banza wacce bata san gata ba, idan na fasa zuwa wurin Salamanun faransa kafira nake!" Haushin cikin da zuciya ta sani fashewa da kuka, kuka nake bilhakki da gaskiya. Domin na tsani abin haushi tunda Hajjah ta zo take cusa min bakin ciki ina hakuri amma na yanzu ta kai ni karshe cikin shashekar kuka na ce mata. "Ni dai kika je wurinsa wallahi sai na bar gidan nan!" Na wuce daki fuuu don yanzu yakan ganinta zai dauka ni ce na turo ta, tab'e baki tayi, mai babbar daki ta ce mata. "Hajjah kada ki je wurinshi kin ji, idan ya matsu zai zo ni da kaina zan kira shi na gaya mishi kina nan, mantawa nayi ban gaya mishi ba don ko daren jiya ya shigo ya samu kun yi barci." Cikin karya murya ya ce mata. "Ai da kin tashe ni na gaishe shi, bawan Allah jarumin maza, ya zauna sai juya shi wancan ja'iran take, shi kenan sai ta shigo. " Daga haka ta bar zancen cikin ruwan sanyi Mai Babbar daki ta kashe zancen ta kuma tura mishi text ya shigo ya gaida Hajjah.
Bayan sallah juma'a, ina kwance Isma a gefena, tana dungure idan ta ji cikin yayi motsi itama zata dungura. Shafa kanta nayi na ce mata. "Isma kin ga hajja ta dame ni ya zamu yi da ita ne?" Kamar ta fahimci maganar da nake mata, ta lumshe idanun tana shafa kanta a goshina, tare da lashe gefen fuskana tana kananun kuka, "ta dame ni, sai bani kunya take!" Sake shafa kaina tayi da kanta irin rarrashin nan. "Kina nufin na kyale ta?" Tsayawa tayi cak, tana kallona yadda ta lumshe idanun ta bude na ce mata. "Shi kenan na kyale ta idan ta kara min iyayi sai na bar gidan nan!" Wani irin tsalle tayi tare da doro, ƙafafuwanta suka wani mike kamar zasu huda gadon. "Ai shi kenan tunda kin hanani magana." Ta fada tana rausaya, idan ta Hajjah