Showing 45001 words to 48000 words out of 157081 words

Chapter 16 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

12

rasuwarshi ya samu aiki, Hajiya Turai ta bashi mota ya ce baya so, ya samu Malam Junaid da Abid ya addabi rayuwarsu, sai da aka nima mata wata Honda Accord ya kyale su, ana haka Khalisa Nafi'u Shaibah ta zo ganin gida, tambayar da ta mishi ya kama dariya ya ce mata. "Ina da mota amma bani da machine." "Ina zaka kai motar da aka saya maka?" Hajiya Turai ta tambaye shi. Dariya yayi ya ce mata."waye ya sani ko mabukata zan barwa idan na rasu a sayar a biyawa su Abdul da!" Fada tayi ta mishi har suka fito waje. Ya ce mata. "Mommy kece kika damu da duniya ni da kika ganni, abu daya nake tsoro mutuwa ban san yadda zata zo min ba, sai kuma haduwata da Allah, tow bana sata, bana zina, bana karya, ina sallah biyar amma ina dan shan syrup shima in sha Allah daga yau na daina, ina son na je gaban Allah ina mai tsafta da kamshi bana son na je ina tare da kazanta, bana son Mala'ikun rahama su juya min baya. Ina son ko mutuwa nayi matan huruul a'in su tawo irin dubu saba'in din nan suna faɗin, Habibi Tauhid Barka da zuwa mun jima!" Ruwa Maluma ta watsa mishi tana faɗin. "Mara kunya banza in sha Allah sai ka ajiye mana kyakyawan jika irinka mai kuzari da rikicin 20k!" Dariya yayi ya fita da gudu, malam Junaid yana jinsu, ko da dare da ya dawo haka ya tisasu a gaba da labarin mutuwa, da wata littafinsa yana faɗin. "Abba ka ga wannan idan na rasu ko yau na rasu a duba cikinsa akwai abubuwan da za a samu na shirin da nake son nayi, duk da na ga Ikhlas tafi kowa kudi a gidan nan ita ce mutum na farko da zata fara cika min wasiyya, ban yarda wani ya rigata ba!" Ya fara rubutu Umma da haushi ya ishe ta ta same shi ya buga mishi rankwashi a kai tana faɗin. "Allah ya shirya ka mutuwar abin arziki ce da kake kawowa kanka? Allah Ibrahim ka fita idanuna!" Ta shiga mishi fada, sai da ta gama ya kwashe da dariya yana faɗin. "Idan na mutu don Allah kada Mommy ta tab'a gawata, daga ke Abba Maluma, Iram ta tsaya akan gawar Allah yasa mutuwar ta zama aya akanta, ina so Ikhlas ta shafa min turare a kayana da gwiwata da hannuna da goshina Abba ka gaya mata!"

A hankali Malam Junaid ya bar wurin zaman ya dawo dakinsa ya rufe, ya fashe da kuka, yana jin wani irin ciwo da kunci a ransa, yanzu basu kashe shi ba suka kashe mishi Yaro karami da babu ruwansa Yaron da bai ji ba bai gani ba, Yaron da bai san kome a wannan rigimar ba me yasa? Me Ibrahim yayi musu? Haka yayi kukan har ya gani sannan ya dauki wayar shi ya kira Alhaji Nafi'u. Bugu daya yayi ya dauka. "Mai Tauhid yayi ka kashe shi? Na zata gabata da kai ne? Me yasa ka kashe min Yaron da babu ruwansa? Idan ni nayi laifi me yasa zaka hukunta Tauhid? Akan me yasa zaka kashe shi? Ka zo ka kashe ni amma me yasa sai shi?" Shiru yayi kafin ya hadiye yawun bakinsa ya ce mishi. "Tsakanina da kai mutuwa ce zata raba ko ni ko kai, amma ka sani ina Alfahari da Ibrahim da Khalisa, na san nayi wanka cikin kazanta amma wallahi Yaran nan guda biyu ina tsoron Allah kada ya$£ hukunta mu akansu, wallahi Billahi azmin, na rantse da Rabbul Ka'aba ban saka a kashe shi ba, zan dafa kur'ani duk da bani da banbanci da arne amma ban kashe shi ba, ko Zainab da take bana fatan ta rasa Rayuwarta, mutuwar Yaron nan ba iya kai ya tab'a ba, har da ni ban san yadda zan gya maka bane amma wallahi ni daya nasan yadda nake ji akan mutuwar nan. Kuma sai na gano wanda suka aikata haka sai na musu kisar gilla da duniya zata gani, ya zama abin jajjantawa da al'ajabi."

"Kana da sauran lokaci, ka tuba ka daina shirka Allah zai yafe maka!" Ya kashe wayarshi, duk da Alhaji Nafi'u ba abin yarda ba ne sai dai ya tsinci gaskiyar da ba kowa zai yarda ba, ya hango bai da hannu a kisar da aka yiwa Tauhid, ya fahimci gaskiyarshi, duk da kasancewar shi mutumin banza amma har a kwanan gobe Malam Junaid bai cire mishi tsammani ba, sau biyu ya ga kukansa mutuwar Attahiru Shehu Yayari da kuma Mutuwar Tauhid haka ya jefa shi cikin wani irin rud'ani tow ya sa Nafi'u ya kama wancan tashar bayan kuwa yasan ba haka yake ba. Sai dai Nafi'u ba shi ba ne agende dinsa Zainab ita ce akan kome, ko da yau baya raye zai matuƙar wahala a nunawa Zainab yatsa. Wannan mutuwar Tauhid da irin yanayin da ake ciki ya karawa Zainab wata daraja.

Don haka zai yi amfani da damar da Allah ya bashi, ya kara cusa Zainab a cikin zuciyar dattawan fadar, babban addu'arshi ta ɗan jinkirta kafin ta bayyana haka ma wata nasara ce da Allah ya bashi ba tare da yayi ta bin mutanen Fada suna amfani da dukiyarshi da wata matsayinsa ba. Wannan shine asalin abinda yake bukata tausayi da adalci tare da soyayya da za a nunawa Zainab. Ta kafata yadda kamar yadda ake kafa pillar a cikin gini.

***

Wurin karfe uku na yamma, yana zaune tare da Mai Babbar daki wacce take kwance ana mata karin ruwa. Wayarshi ce tayi ƙara ya ɗauka.

"Kasan waye yake magana?" Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Kai ka saka a ka ɗauke min Mata?"

"Ashe kanka yana ja! Abu daya zaka yi ka yi murabus, kafin faduwar rana ni kuma zan tabbatar da matarka ta bayyana kafin hudowar alfijir! Idan ka ki kuwa masarautar Zanzabira zata koma koramar jini, ihu da kyarman mutane zai cika birnin tarihi zai sake maimaita kansa, xan ruguza tare da shafe duk wani tarihi na Zanzabira."

A wani irin fusace ya fara magana kamar haka.

"Idan ƙaddaranka ce ruguza zanzabira ƙaddara ta ce kare jinina! Ni Shago Ilu nayi rantsuwa da Ubangijina zan bawa zanzabira kariya ba iya zanzabira ba hatta takalmin Awatif sai na kare shi, kana da damar gudu ko ka boya, ni kuma zan farmake ka, kai da sauran shaidanun tsakiyar birnin zan yake ka zan kai ka kasa ka ajiye kalamai a duk matakin da kake ka boya ka yi gudu! Amma nasan tabbas zan farauce kamar yadda zaki yake farautar namun daji a dawa! Kaiiiii dan daudu mai boya a inuwar Mace fito idan har Uwarka da jini ta haife ka! Tsohon gaba ce idan kaso ka nemi sulhu idan kaso ka rike Awatif amma ka sake Uwar da Jariran suka samu tangard'a zanzabira zata yi ja madadin farin wata za'a samu jar wata na rantse da Ubangijina wannan shine sakona"

Dariya aka saka daga can gefen ana faɗin. "Kayya kamar namiji ai shi kenan! Mu zuba mu gani idan ka isa namiji ka binciko ni a cikin zanzabira ni kuma xan yi ƙoƙarin miƙa maka Matarka!"

Cikin wani irin zafin rai ya mike tsaye, ya fito tare da kiran Faruq. "A bincika ko ina na gidan nan a tabbatar da an fitar da wayar kowa ka tabbatar da an bincika layin da ya kira ni minti biyu da wani abu a kawo min tsinannen nan na sare kanshi!"

Ya fada a fusace, yana mai kaiwa da komowa. Kafin wani lokaci fadar ta dauki wani irin tashin hankali ashe ba baya wasa ne, domin gida gida ake bi ana binciken nan.

***

Dattawa uku ne a zauna sun juya bayansu, Alhaji Nafi'u yana gefe can yayi shiru.."Mai yasa zaka ce a kyale ta? Bayan muna gab da cika burinmu?"

"Barinta a hannunmu yana bani wani irin yanayi mara daɗi, su kaita gidan gonan Attahiru Shehu Yayari su ajiye ta daga nan zata iya kai kanta ga matsirata!"

"Jinin nake so kuma zan farmake ta."

"Ba zaka iya mata kome ba, domin shigowar ta ware house sai da kome ya tsaya cak, ba ita ba ce matsalar cikin jikinta yafi karfin kanta balle mu. Idan ka ce zaka yi wani abu kai ne zaka mutu!"

"Karya kake munafiki!" "Tow shi kenan" kiran kiran wani yayi ya ce mishi.."Ku bi Yarinyar nan ku farke cikinta ku kawo min abin cikin!"

"An gama;" ya fita da gudu. Ko minti biyu bai dauka da bada umarni, aka kira shi waya aka kuka. A rude ya ce. "Gaya min Nusrah lafiya mene faruwa ne? Nusrah menene? Nusrah.....

Daga inda Alhaji Nafi'u yake ya ce mishi.."daga lokacin da kake shirin yaki ka fara sanin waye abokin gabarka da waye zaka yaki da shi....

***

A can Yayari housing Estate, gobara ce ta kama daya daga cikin gidanjen Alhaji.......

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 17

Gobara ce sosai, ta kama shahararren gidajen zamani da shagunan zamani, mallakin ahalin Yayari bakiɗaya. Asalin wannan ginin zamanin na mallakar Attahiru Shehu Yayari ne, amma bakiɗaya ahalin Yayari suka yi ta rigima har ya bar musu akan yafi kowa dukiya cikinsu, Malam Junaid da Alhaji Saddam suka ta bashi hakuri ya bar musu filin karshe wani tudu wani gangare aka dawo da rigima tsakanin yan uwa wnada ya haifar da wasu suka suka yi ta sayar da filin wa Alhaji Mamman Abba yayari, wanda dayawan mutane suna ganin kamar nashi ne, amma a yadda abin yake filin ba nashi ba ne, sannan mamallakin filin yana nan a tsakanin mutane uku mafiya karfi a cikin familyn Yayari.

Motar fire service suka tawo akan lokaci, aka kashe wutar a lokacin dayawa na dattawan Yayari sun iso cikin tashin hankali, domin kuwa ba ƙaramar tafka asara suka yi ba, haka yasa abin ya zame musu babban iftila'in da ya kusan zautar da kowa, wannan abin da ya faru baa ga Kafar Mai Martaba, domin yana cike da tashin hankalin rashin Matarshi da yayi. Sannan labarin asarar ya shafi mijin Aneesah, rashin ganin Mai Martaba sai abin ya tunzira yan gidan Alhaji Sani Yayari Mahaifin Mijinta, wannan yasa shi shigo gidan a fusace ya cewa ɗansa. "Ammar idan ni na haife ka, dole ka sake ta yau ba gobe ba!"

"Abba me yasa?" Aneesah ta tambaye shi a rikice, kwad'awa ɗansa mari yayi wnada ya ja shi furta saki ɗaya ga Aneesah. "Duk lalacewarmu, mun fi wancan yarinyar da ya kasa takowa yazo ya ga irin asarar da ahalin Yayari suka yi, don haka fita ki koma inda kika fito!" Wannan abin ya daki zuciyar Aneesah dama tana jin haushin Zainab gashi nan an sake ta saboda Yayanta Bai zo musu jajje ba. Wai ma tukun ya suke so yayi? Ya ji da mutuwar da aka yi na kanin Zainab din ko kuma yaji da threating dinsa da ake yi da waya ne? Hakan ta baro gidan hankalinta a tashe dama tun b'atar Zainab din sau daya ta zo, wurin karfe goma sha daya ta shigo ganin yadda kowa yake curko-curko yasa ta shiga cikin bangaren Mai Babbar daki, da take shan magani, ta fashe da kuka tana faɗin. "Ni kan mai na tsarewa Yaya ne da bai je ya musu jajjen gobarar da aka yi na Yayari Estate? Gashi nan akan yar iskar yarinyar na...." Tass aka wanke ta da mari, da yasa ta hantsilawa, sai da aka yakushe fuskar bayan marin, Isma ce tana lashe hannunta. A rikice Aneesah ta yi baya tana faɗin.."Waye ya mare ni?" "Gata nan!" mai Babbar daki ta nuna mata Isma da yake gabanta tana wani irin, irin wanda kana ganin kasan haushi magen take ji,.marin ya shige ta wani irin tsoro ne ya kamata ta koma tare da makalewa a saman kujeran. "Dama can sun shirya sake ki! Ai sun san me ya faru da shi,.zuwa yanzu ko yaya abu ya faru dole ayi mishi uzuri"

"Amma ai ko da Kanin Zainab din ya mutu ba ya je ba a cikin daren ni gashi nan ya janyo min na rasa aurena!"

"Mutuwa daban gobara daban, hakki suka tab'a kin san ma tarihin inda yake konan ma kuwa? Na mahaifinku ne mahaukaciya, sannan shi Kanin Zainab kin san yadda yake a zuciyar Zainab din? Kin san waye shi a rayuwarta? Da kin san girma da Soyayyar da yake tsakaninsu ba zaki tab'a cewa yaki zuwa ba, gobaran da iya dukiya ya tab'a bai tab'a rayuwar kowa ba ba." Ganin yadda Mai Babbar daki take shiga take fita yasa Aneesah tayi shiru domin tsoron tsiya ne da ita.

Har kusan asuba ba wani labari, washi gari bayan anyi addu'ar uku, Malam Junaid ya zo fada yayi musu Jajje, sannan yayi shiru. Cikin sanyin murya ya cewa Mai Martaba. "Ina ga zuwa yanzu ya kamata mu cire rai da ita, domin kuwa bata raye da tana raye da sun sake ta, ka yi hakuri ka fuskanci al'ummarka, ka manta da Zainab tunda ba ita ɗaya ba ne! Matarka!" Wannan abin da Malam Junaid yayi yasa Alhaji Kabiru Hammud Yayari, ya ce mishi.."Malam Junaid Gobir kasan me kake yi kuwa? Taya.zaka ce ya hakura da Matarshi da take dauke da juna biyu? Ko jiya Sani Yayari da yayi wani hauka ya fahimci yadda gaskiya take, Salmanun Faris bai zai tab'a hakura da matar aurenshi ba, sai dai idan gawarta aka kawo mishi, mu fada muna tare da Zainab Salmanun Faris, ba zamu tab'a juya mata baya, Malam Junaid kayi abinda ba kowa yake iya yi ba, ka bashi Yarka ka kara tsaya mishi a cikin gidansa hatta matsalar iyayensa kai ne a kai, karshe saboda a zauna lafiya yar amininka ta ce mijin Yarka take so ka hakura da farin cikin Yarka ka bawa mijin Yarka auren yar abokinka, wacce irin zuciya gare ka da bata damu da kanta da abinda nata yake so ba? Gaskiya ka cika adalin Uba adaline, wanda bai damu da kanshi da abinda Yaransa suke ba, gashi yau danka aka kashe ka zo kana cewa a sake auren Yarka da aka sace ta rasu. Ubangiji ya kara maka hakuri da lafiya. Balle wannan sakaran gobara ya kasa hakuri don bai ga Salmanu Faris a wurin ba yasa dansa ya sake Matarshi!"

Bakiɗaya sai gashi mutanen Fadar sun ciyawa Malam Junaid baya, tare da dakatar da shi batun raba Salmanu Faris da Zainab ɗin. Wannan takin Malam Junaid yake bukata ko da ace akwai mai son ganin bayan Zainab din, ya san zuwa yanzu ya boye gillin da yake ranshi, sannan yana tare da masu goyon bayan din. Haka suka gama maganar Salmanu Faris yana zaune idanunsa lumshe kamar mai barci.."Mai martaba baka ce kome ba?"

"Ina mai bada umarnin duk wnada yake da hannu a cikin wannan lamarin ya sake min matata domin ba daga waje aka dauke ta ba, idan aka sake abin cikinta da ita kanta suka samu matsala duniya zata ji mu!" Daga haka ya mike zai bar fadar Alhaji Nuru Yayari ya ce mishi. "Batar Matarka ya kai ace baka mana jajjen gobarar da aka yi mana ba ne?" A fusace ya juya yana kallon shi. "Idan baku dawo min da matata ba kayan jikinki sai kun rasa, na gaya muku." Ai kuwa a fusace Alhaji Nuru Yayari ya mike shi kuwa ya daka mishi tsawa. "Zauna!" Ya fada mishi da karfi wani irin tsoron Salmanu Faris ne ya cika mishi idanun. Akwai wani al'amari da yake fitowa a muryanshi da zaran ya fusata. Hatta sauran dattawan fadar sunkuyar da kai suka yi.."Da ace Matarka ce aka sace da gobara wanne zaka zab'a?" Shiru fadar yayi a hankali ya taka har gaban Alhaji Nuru Yayari ya ce mishi. "Matata aka sace da tsohon cikin haihuwa ko yau ko gobe, gaya min kasan yadda nake tunanin me zai same ta?" "Hattara dai talaka matsiyincin banza Mai Martaba Allah ya huci zuciyarka Zakin Zanzabira!"

"Idan yarka aka sace ya zaka ji? Yarsa aka sace bayan ka kashe mishi d'a gaya min me zaka ji idan ka fahimci kaine a matsayinsa? Gobara hakkin Allah ce da ba a cire ba, Matata da abin cikinta gaya min me ye laifinsu?" Yadda ya yi maganar da karfi sai da fadar ta wani girgiza. "Nayi ƙoƙarin, na danne zuciyata amma yanzu na fahimci dalilin da yasa na zama shugabanku ciwon da yake cikin ran wasunku ba zai tab'a boyiwa ba shi yasa kuka fara ta kan Zainab idan mutum.ya cika d'a namiji ba dan daudu ba, baya boya a bayan mace fitowa yake a faffata da shi, na kara jin wani ya kara min wani magana, sai na datse harshenshi! Ku dakatar da Nuru Yayari a matsayinsa na waiban Zanzabira Ina Turaki! Alhaji Rabi'u Yayari A dakatar da Nuru Yayari." Da gudu Isma ta nufo shi ya dauke ta tare da rab'ata a kafad'arshi ta zauna yana takawa tana zaune. Har ya isa cikin gidan. Zama yayi yana huci. "Allah ya huci zuciyarka, Allah ya bayyana Fulani Babba!" "Jakadiya bani ruwan sanyi!" Fita tayi Mai Babbar daki ta cigaba da kallonsa wani irin zabura yayi ya bar dakin kafin Jakadiya Iyaami ta dawo yayi waje, kai tsaye ya wuce hasumiyar Masarautar ya tsaya cak. Yana kallon cikin garin Zanzabira. Lumshe idanun yayi kafin ya bude ya juya ya ga Faruq yana tsaye. "A shiga dajin biri akwai wani hayaki yana tashi duk da bata wurin a shiga a ga meke faruwa!" "An gama ranka shi dade!" Faruq ya fita, ya kira team ɗinsu, da na wasu yan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login