Showing 15001 words to 18000 words out of 157081 words

Chapter 6 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

51

zan iya cewa Isma ce ta san da bani da lafiya.

Fitowa mai babbar daki tayi suka gaisa, kanta a kasa hawaye na zuba mata ta ce mata.."Ummi don Allah ki saka baki ya bar ni ko yar walima nayi don Allah!" Murmushi Mai Babbar daki tayi ta ce mata. "Tunda ya ce kada ayi yana da kyau a girmama batunsa, ki yi hakuri ai azumi ne. Kuma kin yi sunan Fari tunda ya ce wannan baya so a bar shi ba hurumina ba ne na shiga mishi gidansa bayan nasan baya nan!" A hankali tayi ta mata nasiha, tare da nuna mata matuƙar tana son zaman lafiya ta yarda da abinda ya ce, sunan fari ya amince ayi amma na baya ko a masallaci kawai za a radd'a sauran kuma su hadu da wacce take gidan yi hira da raha sannan kada ta tara mishi mutane tunda ya fadi haka. Tayi mai babbar daki ne amma tunda basu wurin ina ruwanta, bata san kuwa shi ya gama shirinsa ba kafin ya bar garin.

Haka ta baro gidan ranta a jagule, tana zuwa ta gaya musu su kuwa suka ce zasu yi sunan. Sai dai kuma ranar sunan abin mamaki shine security da suka cika gidan haka yasa babu wanda ya samu damar shiga cikin, ranar sunan har dare sannan security suka bar gidan. Wannan abin yayiwa Ijlal ciwo, sannan washi gari suna Aneesah tazo ta amshi kayan sunan da ya haɗa ta kai ita ɗaya kamar mayya..

Ƙaddarata.

Tun daga ranar da kome ya faru, kaf zuriar Masarautar Zanzabira tare da bloodline na Yayari suka san da cikin jikina, na daina barci cikin kwanciyar hankali sai Ummi tayi da gaske a kaina nake barci, haka yasa ta kara komawa wurin Baba titi, ya bata rubutu, tana kawo min na fara barci idan na sha ko nayi wanka da shi zan yi barci. Idan ka ga na fita a gidan awo zan tafi gani ga Ismaha ikon Allah, domin tun da cikin ya fara bayyana magen nan ta tattara rayuwarta ta makalewa cikin jikina, da yake cikin wata na biyar, duk da azumi aka fara wani lokacin haka zan farka naga kanta a jikin cikina tana barci, idan kuma ina zaune zata shiga rigana ta jingina kanta a cikin, tayi ta juyi a jikin cikin. Da na gayawa Mai Babbar daki, ta kira Tasi'u ya haɗa ta da Baba titi dariya yayi ya ce mata. "Meramo Ishama ta samu shugaban mace ko namiji, zata kasance da su har ta koma ga Allah wannan shine dalilin mannewa cikin. Zaku ga abin al'ajabi zaku yi mamaki zaku yi farin ciki amma haka zai faru ne idan Allah ya so! Haka muke fatan kasancewa.

Bayan abinda ya faru, haka muka cigaba da azumi, ina gidan mai babbar daki da ta je har gidanmu ta gaya musu halin da nake ciki, ganin yadda Mai Babbar daki ta tsaya a kaina sai Iyayena suka mata yakanah suka dauke kansu akaina, amma duk bayan kwanan biyu suna zuwa ganina, har aka gama azumi bayan mun cika guda talatin cib kuma ikon nayi kaɗan daga karshe na ji cin ya ragu, sai na samu guda goman ƙarshe.

Haka muka yi sallah a watan na shiga wata shida cib, domin mai babbar daki ta ce na daina lissafi da watan boko na koma na mahammadiyya, kamar yadda Hajjah ta gaya mata, sai na fahimci akwai taran watan boko da na Muslunci.

Sallah da sati daya cib ya dawo, ni dai bana ganin girman cikina, amma ranar da ya dawo ya rike baki yana jinjina kai. Hade rai nayi domin ya fara bani haushi. "Ummi ni don Allah a kaina aka fara ciki ni bana ganin girmanshi amma sun wani dame ni." "Kiyi hakuri kada ki damu da su ni ban ga wani girman cikin ba!"

Gyada kai nayi na kalle shi na watsa mishi harara tare da murgud'a baki, shima bakin nawa kamar yayi ciki domin girma yayi hatta siririn hancina kato ya dawo. Nifa na daina kallon kaina a madubi domin na gaji da ganin madubi yana zagina.

Washi gari kafin ya shiga fada da sassafe,.ya kai ni awo, bayan ya kai ni aka gama min, sannan ya wuce da ni gidanmu. Kallona yayi ya ce min. "Ke daya nake dauka na kai ko ina sauran duk kai su ake yi. Ban san me yasa nake jin ki sama da kowa a rayuwata?" "Yaya kace dai abin ya motsa an kwana biyu ba a turmushe yar baiwa ba, shine za a dauko emotional love moment a kawo cikin lamarin nan, yanzu kai yaya ban da rashin imani a wannan tulelen cikin nawa idan na kwanta taya zaka shiga jikina? Don Allah ka tafi ka bar ni ba huta na gaji da zama gabana ciwo yake!" A rikice ya ce min. "Kamar ya?" "Kawai idan na zauna na dan lokaci sai na ji gabana yana ciwo kamar kashin gaban zai fashe!"

"Me yasa baki fada ba? Sai da na.kawo ki gida!" "Ni yanzu kwanciya nake son yi!" Da sauri ya bude wurinsa ya zo ya bude min, na fito a hankali. Ina dan bude kafana, domin zaman da nayi na ganin likita da sauransu. Rike jakata yayi muka shiga cikin gidan, daidai Mommy Turai zata fita. "Masoyan zamani!" "Ya batun kudina?" Ya tambaye ta, kallonshi nayi na kalleta. Wani shock ta shiga ya ce mata.."na baki awa uku ina jiran kudina ko ki sha mamaki!" Daga haka ya wuce da ni cikin gidan domin na fara zargin da wani abu da fitsarin da nake ji, hakan muka shiga na ce mishi. "Ya aka yi kudinka ya shiga hannunta?" Ba fada ina jefa kafana ko ina, "zan miki bayani idan mun koma gida!" Na fada ina mai wucewa parlourn Umma da sauri ina kwad'a musu sallama, ban tsaya ko ina ba sai bn dakin parlourn, na yi fitsarina, na huta bayan na fito na nufi parlourn Abba inda na ji muryanshi, ina shiga na wurga da Hijab din na kwanta ina nishi. "Abba sannunku ina kwana anyi sallah lafiya!" "Alhamdulillahi!" Shigowa Hajjah tayi tana faɗin.."Salamunu faransa ka dawo lafiya? Ya ibada? Naga tsaraba Allah ya jikan mahaifinka ya shirya maka Zuriar ka!" "Amin Hajja zan tafi ga kawarki nan!" "Ba kome xan kula da ita!" Ta fada Maluma da Umma sai godiya suke mishi, Abba ma haka bayan tafiyarsa da na raka shi. A harabar gidanmu ya ce min.." A ci kadan kada a ci dayawa!" "Allah ya tsare!" Sai da ya bar gidan na juya zuwa cikin gidan, na hango Iram tsaye tana kallona. "Ciki kike da shi dama?" "Ba gashi kin gani ba!" Na fada ina wuce ta zuwa cikin gida. A parlourn Abba na kara kwanciya. "

Umma ta ce min. "Bakya iya zama ne?" "Umma zaman ba dadi!" Allo Maluma ta kawo Abba ya fara rubutu da farin zuma ya wanke min da zam-zam na sha na kwaye cikin na shafa girgiza kai yayi yana faɗin.."yaushe zaki yi hankali?" Tow Allah yasa riga da zani ce. Washe baki nayi nace mishi.."ai riga da zani ce." Su kansu dariya suke min yadda suke dariya yasa na tsargu. "Abba dariya me su Maluma suke?" "Dariyar ranar da kika fara al'ada ba." Rufe fuska nayi da hannuna na fashe da kuka, idan faɗin. "Abba ai Yaranta ce ko? Kuma lokacin ai ban san ciwon kaina ba ne, Abba da wayo ai ba zan yi ba!" Dariya yayi yana faɗin. "Tow naji daina kuka Maluma da Umma ku daina kuka!" Shigowa Hajjah tayi tana mai mika min ruwa a kofi. Karba nayi na sha ruwan zartsi. Na ce mata.."wannan ruwan fa?" "Da kaina na je Unguwar Dawaki na amso miki ruwan doki yana maganin tsinku-tsinku." "Gaskiya matar nan baki yi ba!" Na fada ina tura baki!" Matar nan haka bai mata ba sai ga ta da tafasasshen barekata wai na sha, ni naga zobo na kuwa kifa kai ba kome dai citta kanunfari, haka na ajiye mata ranar a parlourn Abba na wuni Ya Yunus da Nawwas sun zo, sai Ya Abid..kafin wani lokaci gidan ya cika haka yasa Iram ta fito cikinmu tana mai sakewa. Domin bata kawo zamu barta a cikinmu ba, amma Tauhid yana zuwa aka bude shafin hira.

Wurin La'asar Aunty Shukrah da Aunty Sajidah suka iso, Basu jima ba sai ga Aunty Nu'aymah, gidan ya cika sai lokacin ake hiran an kai sadakin Nawwas da Yunus. Murna kamar me za a sake aure a gidanmu.

Wunin yau ban ga Isma ba, haka na ji kewarta. Bayan sallah isha ya zo daukata a lokacin ya kawowa Hajjah Kilishi da dambun nama, Faruq yake dauke da shi, haka ya kawo suka yi ta hira, kallon Hajjah nayi na ce mata. "Kawata ba zaki bani ba ne?" Rausaya kai tayi tana faɗin. "Ko iyayenki ba zan basu ba, wannan abin daga Tarasulu sai jikanta ki je can mijinki ya baki!" "Hajjah ba don halinta ba!". Inji Aunty Nu'aymah, harara ta watsa mata ta ɗan dubulo dambun ta mika min na saka roba na amsa sai Kilishin da ta yanka min, shima na amsa ina godiya, sai kuma tayi murmushi ta ce min. "Ayi ta addu'a, ba a zama haka!" Na mike ina daukar hijab dina. " Ce min ki gaida min yar magenki ga sakonta nan!" Ta kulla mata nata a leda tana murmushi jin dadi domin tasan magena. Haka na baro gidan da kayan kwadayi rabi kafin na isa cikin gidan na cinye shima dariya yake min haka suka suka taya ni daukar kayan ina faɗin. "Ai mu yi sauri na samu nayi fitsari!" Muna shiga Mai Babbar daki ta tare mu da lale ban tsaya na na wuce nayi fitsari, sannan na fito ina mai shan ruwa na sauke ajiyar zuciya.

*

Nadiyyah..

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 06

Nadiyyah

Idan da wani zai ce mata Ijlal zata iya mata abinda tayi zata iya cewa makiyinta ne, kuma ba zata tab'a yarda da shi ba. Yanzu ta fahimci irin kallon da Baban Princess da Ikhlas suke mata, ashe kallon mahaukaciya suke mata shi yasan abinda Ijlal take nufi da ita, Ikhlas ta fahimci yadda karshen tafiyar zata koma. Tayi kuka ta tsani kanta da kuma cin alwashin sai ta koma ta koyawa Ijlal hankali. Ko iyayenta bata gayawa haka tayi ta fadi tashi, amma ba dama har aka yi sallah ta rasa waye zata kama ya mai da ta gidanta?.

**

Yau baki muka yi yan gidansu, Uwais har da Ikram. Kallo daya muka yiwa juna muka yi, ni dai bata kaina. Sannan bata gabana. Abu daya na sani shine harkan gabana. Gaishe da Mahaifiyar Uwais nayi amma na gagara mata ta'aziyar rasuwarshi, kaina a sunkuye ina shafa Isma da itama bata jima da fitowa parlour ba, cikin girmamawa suka gaishe ni har da ita Ikram din. "Zainab sun zo gaishe ki ne fa." "Ni kuma Ummi!" Na kalle su, sai na juya gare ta. Gyada min kai tayi tana faɗin. "Tun jiya Maman Ikram ta kira ni ta gaya min zasu zo!" "Ayya na gode!" Na fada ina kallon mai babbar daki, kafin na juya ina kallonsu. Aka yi ta shirya musu abin tab'awa. Muna zaune ya shigo daga fada. Domin yau ya tashi da wuri. Bayan sallah azhar. Idanunsa a kaina ya shigo murmushi yayi min kamar bai ji yadda ake gaishe shi ba, hannu ya d'aga musu ya kalle ni ya ce min. "Ya jikin naki?" Murmushi nayi na ce mishi. "Da sauki fa!" Na fada ina kara shafa bayan isma, shima tab'a ta yayi yana faɗin. "Isma ta ji dadin zama a jikinki fa!" D'ago kaina nayi na kalle shi tare da cewa. "Baka jin yunwa ne?" "Yau Alhamis ina azumi!" Ya fada yana kashe min ido ɗaya!" Murmushi nayi na ce mishi. "Dakyau jarumin maza?" "Ke kika mai dani Jarumi ai!" "Anya? Baka ga baki a parlourn ba ne?" "Wallahi na gansu amma ba zan iya ce miki ga yanayinsu ba domin idanuna yana kanki!" "Ummi fa!" "Ai ita Uwar zamani ce ba ruwanta tasan me take yi!" "Sannu My lord!" Ta fada cikin wata shaid'aniyar murya, murmushi nayi mishi na ce mishi. "Kayi kasuwa!" Juyawa yayi yana kallon inda take, "yawwa!" Daga haka ya cigaba da shafa bayan isma, "Ummi anya Isma tana da lafiya kuwa?" Wato magen nan kamar jira take yayi magana ta wani mike tsaye tayi mika sannan ta juya tana shafa kanta a jikin cikina, tana kad'a bindinta. Kafin ta juya kan Ikram wani irin kallo take yiwa Ikram ɗin, ban tab'a sanin Isma yar bala'i ba ce sai da ta fada kan kayan abincin da aka basu ta karkad'e jikinta sannan ta fito tana wani yi musu kallon banza. Anya Isma lafiyarta kuwa? Yadda take yunkurin hawa kan Ikram yasa ni daka mata tsawa. "Isma!" Juyawa tayi ta dawo inda nake tana wani gurnani. "Wayyo Allah na." Ta fada tana kallon hannunta da magen ta yakusa. Kamar nayi kuka tana, "Mage ce fa!" Mamanta ta fada, haka suka gama hiransu suka bar gidan.

Ni dai na ma manta da wani zuwansu, hmm bayan kwana uku da zuwansu na ga ya shigo hankalinsa a tashe, ya samu Ummi a daki, ban san me suka tattauna ba amma tabbas na ga yadda ta fusata ta ce mishi. "Na gidan baka gama da su ba, har akwai abinda zai d'aga maka hankali? Wallahi ka d'aga mata hankali da tsohon cikinta sai na sab'a maka!" Ban san me ya tuna ba, sai na ga ya ce mata. "Ki yi hakuri Ummi!" Daga nan ban kuma sanin me yake faruwa ba, tunda ba a koya min saka ido da son sanin kome yake gudana a rayuwar wasu ba.

Kusan sati uku da zuwansu Ikram, yau na tafi awo, da wuri na dawo na samu Abbanmu da Baba Mamman, a parlourn gaishe su nayi na wuce Abba ya mika min leda amsa nayi ina fadin. "Allah ya kara lafiya da nisan kwana Abbana!" "Amin yar Abbanta!" Suka fada suna murmushi. Tunda na shiga na ji kamar bawa mai babbar daki hakuri ake tayi shiru, can aka kira wayar aka bata nan ma hakuri ake bata ban san me yake faruwa ba, amma da alamu Abba aka saka a tsakiyar lamarin. "Shi kenan Malam Junaid, tunda ka saka baki amma ka sani bana bukatar wata Y'ar kuma zan tsaya kai da fata na kare y'ata, ba zan tab'a barin wani abu ya same ta ba matukar ina raye, Yaya Mamman ku yi kome a gidanka kada a kawo min kowacce y'a gidan nan kowa tazo da kafarta zata zauna ba dai gidan Salmanu Faris ba ne, gashi can an kusan gama ginin." A hankali na d'ago labulen dakin na ga kamar kuka take, ji nayi jikina yayi sanyi ko dai Nadiyyah zata dawo ne, kalaman Abba ya dawo da ni daga tunanin tunani. "Alhamdulillahi Alhaji Jamil Chiroma mun gama kome, amma ta yi hakuri da tarewan sai an gama gini!" Tab'e baki nayi na cigaba da harkan gabana, da Abba zai tafi ya kira ni yana tambayata. "Kina bukatar wani abu ne?" Wannan dabi'ar iyaye ne, duk kulawar da za ayiwa dansu bai cika gamsar dasu ba, sannan ba wai sun rena abinda ake yi ba ne, so idan da hali suna kwantar da hankalin Yaransu ne. "Mijinku ya ce yana son ayi suna a sabon gidan, Mamanku tace ita a'a me yasa ba zaki bi Mijinki ba?" Dariya nayi nace mishi. "Abba ita Ummi tasan mai ta hango ka barta tayi ikonta shima Yaya ba naji matarsa zata dawo na ai shi kenan!" Murmushi yayi yana faɗin. "Mata kenan, shi kenan za a sauya miki kayan kitchen dinki da na dakin baki daya Ummanki zata Dubai sayan kayan aure!" "Abba!!" Na fada da karfi, "Abba wani Dubai kuma? Kayan da suke store fa? Ina zan kai su kawai ku bani odar kayan!" Murmushi suka yi suna jin yadda nake rigimar a bani odar. "Shi kenan tunda Sajida da Shukrah ne a wurin sai ta musu magana!" "Ko kai fa, dan gidan Hajjah kawar Tarasulu!" "Allah ya shirya min ke!" "Amin Ya Allah!" Haka suka tafi, na dawo parlourn na zauna ina mai bude kafana domin mai babbar daki ta gaya min babu kyau na rufe kafana. "Sailuba kawo mata abinci!" Tana kawo min Isma tana zuwa wurin ta zauna haka na fara ci ina kallon Mai Babbar daki da take dauke kanta.."Wai Nadiyyah zata dawo ne!" Ta fada min. "Ummi shine na damuwa? Ɗakinta ne fa, sannan idan bata dawo ba nasan zai matuƙar wahala Yaya bai karo wata ba. Ummi da ace yana watsewa a waje, gara sau dubu ya karo matan a gidan mu zauna, ni gaskiya ba zan iya fitina ba, na fison shi da zaman lafiya, sannan idan yau ya sake Nadiyyah har abada sunanmu da na shi ya lalace, kuma ko don albarkacin Saadiya ya dawo da ita, ya za ayi haka rayuwar take yau dad'i gobe mad'aci ina ga gara ya dawo da Matarsa shima zai fi samun nutsuwa da ace kullum tana zirya ita da iyayenta, ni a bangarena kuwa ma shiga makarantar ta nutsu, ba a cizon mumuni sau biyu a rami ɗaya ya zauna, na koyi darasi mai girma a wurinsu don haka ki kyale shi ya dawo da ita tunda naji kina cewa yanayin ginin an yi kowa da Part dinsa ko? Ni da." Sai nayi shiru ina wasa da yatsuna. "Ke da Yaranki babu ruwanku da kowa ko?" "Hmm!" Na fada ina sunkuyar da kai, Allah ka gode da ban cika raina da soyayyar Yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login