Showing 144001 words to 147000 words out of 157081 words
min saboda ya yarda akwai mutanen da basu bukatar Yakubu daga cikin masarautar, kai ai an san ba zaka iya ba yasa aka barka da halinka na bibiyar matanka!" A matuƙar mamaki ya mike yana faɗin. "Me ya faru?" Riko hannunsa nayi na ce mishi. "Zauna!" Ba musu ya zauna yana kallona ranshi a b'ace. "Masarautar Zanzabira tamu ce, idan wani abu zai faru dole mu tsaya mu yi nazari kafin mu dauki mataki, sannan a san taya za a ɓullo musu ba aiki da zuciya ba, kada ka zuba Idanu akan abinda zai faru, kamata yayi kayi nazari yana bukatar tsaro, yana bukatar taimakon gaggawa domin rayuwarsa, sannan shima Gwamnan a tuna mishi fada ba wurin wasan Yaro ba ne, Zanzabira ba kanwar lasa ba ce. Idan kayi sakaci abinda ya faru da Ayaanah zai sake faruwa da shi." A take ya bada umurnin a saka tsaro a gidan Mai Martaba, tare da kwashe masu aiki a gidan a kawo wasu, musamman Yaran Mr Brandy, aka zuba su a gidan. Ba iya shi ba hatta su Hisham da Amir an saka ana bibiyarsu, domin mutanen hatsabibai ne.
Kwana biyu a tsakanin yaƙe gaya min cewa. Yadda suka yi da Jakadiya abin ya girgiza ni, ka bar mutum yadda yake kawai amma matar nan ta jima tana cutar da mutane. Sannan a wannan lokacin ya ke gaya min idanunsa yana kan Ajiyar Zanzabira da dan Malikin Zanzabira tare da Madaki, da Hajiya Malikah tare da Kanwar Alhaji Mamman Abba yayari wato Hajiya Nuratu.
Sai a wani binciken da aka yi an samu wanda ya kashe Tauhid, wanda ya tabbatar mishi shima kudi aka biya shi. Anan na san Yaya ta farka, sannan wani aikin da yake da ya gaya min sai da ya bani tausayi, na zata ko ya manta ya ke gaya min wnada ya kashe Abdullahi da Ayaanah mutum daya ne don haka yasa a nimo shi, a duk inda ya shiga a faɗin duniya, sannan wannan yawan tafiyar da Faruq yake da Yeemar idan aka ji labarin ne sai a sanar musu, shi yasa yake tafiyar da ita. Ya kara da cewa. "Idan na cigaba da rike mulki ba zan iya wannan aikin ba, shi yasa na koma asibiti hankalina yana kan wasu marasa mutunci."
Murmushi nayi na ja kumatunsa, ya buge hannuna yana murmushi. "Ni kada ki min fyade don Allah,"
"Waye target dinka.........
[8/28, 10:25 AM] Ramlat Manga41: 55
"Idan na gaya miki target dina, meye amfanin shirin? Kawai ki ji da goyanki!" Ya fada yana mikewa tare da ɗaukar hularsa. "Yaya!" "Me ?" Ya tambaye ni, "haka zaka fita ko chakulkuli ba zaka min ba!" Na fada kamar nayi kuka. "Idan nayi miki chakulkuli kika sake daukar ciki haushina zaki ji ai Aryaan ya gaya min cewa haushina kika ji da aka samu cikin Annur kin ga gara na rufawa kaina asiri ina da juyar mata da bata haihuwa zan sauke bukatata akanta." Yadda yayi maganar da gaske yake nufi haka ya bani haushi sosai. "Sai ka je ai!" Ganin yadda na fada a gatsale sai ya dawo ya zauna yana murmushi.."ba haka bane wasa nake miki, nutsuwa da kwanciyata hankali da nake samu a wurinki bana samu a wurin sauran matan don Allah kada ki ji haushina kin ji! Yaron nake so yayi kwari sai na san me zamu yi!" Da wannan ya rarrasheni ya fita, haka gidan ya samu zaman lafiya, da kanshi ya kara kai ni asibiti aka saka min implaner, sannan ya ƙara kai Ijlal aka duba mahaifarta, aka tabbatar tayi hakuri akwai lokaci.
Ranar juma'a ina kwance bayan na gama karatun suratul Khaf nayi addu'a sosai domin har da zuriyata mamata sai da na musu addu'a, sai barci ya dauke ni. Da yake akan Abin sallah nake, ganin Ayaanah nayi ta shigo dakin ta fada kaina tana dariya. "Mammyn!" "Na'am Ayaanah, ke da waye?" Nuna min kofa tayi na juya, Tauhid ne da ya kara kyau, murmushi nayi na mike a hankali na rungume shi. "Daga ina kuka fito haka." "Mommy Turai!" Iya abinda ya fada kenan, ya mikawa Ayaanah hannu suka juya sai a lokacin na lura itama bata wani walwala. "Tauhid." Ratsa hasken dakin suka yi, wanda yayi daidai da farkawa, wani irin razana nayi domin al'amarin Ayaan ya fara bani tsoro na ce mishi. "Lafiya!" Murmushi yayi yana faɗin. "Mai hali ba zai fasa hali ba, yaushe zaki bani hakurin marin da kika min?" Wani irin takaici ne ya kamani, na zungure mishi goshi ya fada zaune na ce mishi. "Aryaan ka kyauta da ka tafi ka bar ni." "Ba tafiya nayi ba, amma Ayaan baki ga sauyin da ya samu ba ne? Akwai bawana Arfillah a tare da shi!" Ya nuna min gefenshi wani aljani ne shima cikin suffar mutane. Fari sosai matashin saurayi, kamar yasan lissafin da nake yi ya ce min. "Tow wannan da kike gani shekarunsa dari biyar da talatin, Malama ta ga wanda ya fi Mijinta kyau." "Mtsew!" Na ja tsaki na ce mishi. "Mutuwar Ayaanah ya kara bude shafi a ƙwaƙwalwar Ayaan, koda ban zauna a jikinshi akwai wasu da suke tare da shi. Ke kanki nasan kina jin tsoron abinda yake yi!"hararansa nayi na ce mishi. "Ni fa uwa ce idan ban shiga damuwa ba me zan yi? Jiya fa ɗaukar kujeran parlourna yayi ya dauki abin wasansa, saboda kawai ya fada kasar kujera."
"Shi ne Arfillah ya gaya min! Ban san yadda zan miki bayani ba, amma ni nasha mamaki da ga waɗanda suke tare da shi, Ikhlas ki yi hakuri, amma danki Allah ya zabe shi tun daga haihuwarshi, Zainaba danki mutuwar yar Uwarshi yasa baki na musamman sun bayyana a jikinshi, basu shiga jikinshi ba, amma wanda yake tare da shi, daya ne daga cikin shugabannin al'ummar musulman aljanu, mahaifinsa yayi zamani da wasu daga cikin Sahabban Manzon Allah, a cikin bil adam akwai sharifai, mu ma haka a cikin al'umma Aljanu akwai sharifai, bakon da yake tare da shi, kusan abokin Baba titi ne. Mahaifina a wurinsa ya fara karatu. Abu daya zaki yi, shine yau juma'a ki yi sadakar ruwa, fura da nono, sugar Mai iyali, sai shinkafa da wake, zasu amshi sadakar amma zasu dan ja baya kaɗan, amma ba zasu bar shi ba, baki ga idan ana wani abu sai ku ga ya ware kanshi ba?" Gyada kai nayi da mamaki. "Shi din shugaba ne yake tare da shi, ko ki ga yana yawan karatu."
"Wallahi yawan karatunsa ya dame ni!" Yaron da ita abcd ake koyar musu yau sai na ji yana fassarawa yan uwansa abinda ake yi da turanci ko da French, dafe goshina nayi na ce mishi.."kana ganin zamu iya koransu?" "Ba zasu tafi ba, kamar yadda ba zan iya tafiya daga gare ku ba, amma bari zaki sha mamaki ki saka idanu!" Kamar yadda ya ce min haka nayi sadaka sannan ta kaf -kaf da Ayaan din. Ma shiga nayiwa Annur wanda yaro nan ya fita, abin ya bani mamaki domin ina zuwa na samu baya nan. Can sai gashi ya dawo yana kallona ya wuce abinsa bai ce min kome ba, na mishi. "Ina ka je?" "Baba Sarki an tura mishi wasu ne su razana shi, shine ni na razana su." Yana fadar haka ya wuce abinsa, wato wannan shi ake kira banza ta kori wofi.
" Na gaya miki dan baiwa ne shi!" "Tafi can ina baiwa anan." Karfe biyu saura ya shigo ya fara shirin zuwa masallacin, ya ce min. "Ki shirya min Yaran zamu tafi dasu Masallaci." "Tow!" Na fada ina shin wani abu yana ciwon rai na. Koda na shiga dakinsu Na samu Ijlal tana shirya Ayaad. "Ke kika shirya Ayaan!" "A'a na fada!" Ina kallonshi.."Sai da na ce mishi, yana jirana domin kada ya hautsina drower dinsa, tun case na maid da take lalata Yaran gidan aikinta nake tsoron su shirya su. Shi yasa na saka dokar duk Friday zan shigo da kaina, amma wannan mai taurin kan da halinsa irin ma wancan mai tsawo kamar isha!" "Maamah me yasa kullum baki da wnada kika rene sai Abba!" "Waye sana'a idan ba shi ba, ko Fulani Babba!" Murmushi yayi ya ce mata.."zuciyarki na da kyau, kuma zaki dace in sha Allah zaki haihu Yara maza kema! Waye ya sani ma ko Allah ya kawo!" Yana fadar haka ya dauki turaren da take fesa mishi ya fasa a jikin abin sallah. Ya kalle ni da nayi mutuwar tsaye, har ya kai bakin kofa ya ce mana. "Bari na baku labari baturiya zata dawo!" Daga haka muka kalli juna, "Nadiyyah!" Muka hada baki, ai kuwa Ijlal ta mike da sauri zata fita, wani irin ciwo ne ya rike ta, ta tsaya cak. "Ciwon ciki ko?" Rike maranta tayi a hankali ta zauna tana rintsa idanunta, "Na kira Munirah ne?" Girgiza kai tayi tana faɗin.."bari zai daina!" Yadda take maganar sai ta bani tausayi. "Wacce gulmar kuke yi?"
"Dama zaka dawo da Nadiyyah ne? Mu a zaton mu tayi wani auren tunda wata hudu kenan da barinta gidan nan!"
Sai lokacin na lura da shaddar jikinsa sabo ne fil duk da dama haka yake duk juma'a sabin kaya yake sakawa, amma na yau da renin hankali, dafa kafadarta nayi na ce mata. "Ina ruwanmu idan yaso ya dauko wacce bata kai Nadiyyah ba!" Murmushi yayi ya ce mana. "Idan na dawo da ita sai ku hade kanku a zauna lafiya." Ya fada yana barin dakin. "Ijlal bata da lafiya dai ka sani " dawowa yayi ya tsaya a gabanta. "Me damunki? Me ke miki ciwo?"
"Ka damu dama kake son dawo mana da alaƙaƙa."
"Kin ga ko ji da ciwonki!" Na fada mata, "bari na dawo sai na zo muje asibiti;" ya fada yana kallonta. "Kawai ka bamu izini mu tafi asibitin ba zan zauna jiranka ba!" "Ai na gaya miki zan dawo!" Ya faɗa, "idan baka wuce wurin daura maka aure da."
"Na ce zan dawo!" Fadar haka yasa muka kyale shi, ya tafi, ana saukowa juma'a da karfi tayi sallah, kuwa sai gashi suka nufi asibiti, Ikon Allah kawai zai a ce ya kawo cikin, amma wallahi sun sha mamaki sosai. Tunda suka dawo take kwance. A wannan takin nima sai ma ramawa kura aniyarta, sannan bangaren Nadiyyah bamu san ranar tarewarta ba, amma tabba mijinta ya gaya mana an daura auren,sai na mai da hankali akan Ijlal da hidimar gidan, ba karamin al'amari ba ne kula da miji yara, da sauran su.
Sannan cikin ya saka mata tsanar mijin kullum rigima, tun ina damuwa har na daina, domin wata rana Ayaan yana zaune shi da Aryaan suna karatu, sai na ji tana faɗin. "Tunda ka iya dawo da wacce zata hallaka ka, ka tafi gare ta mana dole sai ni ce." Zan yi magana Ayaan ya ce min.."da dai kin warke daga haukar shiga abinda bai dame ki ba, wannan ma haka ki dauke kai ciki ne ya hadu da kishi!" Budar bakin Aryaan ya ce. "Allah shi gafarta malam ya ka mata kayi wani abu?" "Zata zauna a gidan, ita din da wancan sune tsaye a gidan, sai dai ita da kanta zata girbi abinda ta aikata, ko bana wannan nahiyar zai faru domin hakki zai bibiye ta."
Daga haka suka cigaba da karatu, haka lamarin ya kasance, sati uku sai ga Nadiyyah da Matan alfarma abin dariya har da Ikram, ranar da ta dawo na sake mafarkin Tauhid yana zaune kasar bishi cikin damuwa da kunci, na ce mishi.."Wai meke damunka ne?" "Mommy Turai!" Ina farkawa ana kiran sallah farko, alola nayi na fara nafilla,har aka yi sallah asuba. Da safe da ya shigo ban kalle shi ba na gaya mishi. "Ki daina wani dauke kai kamar baki ganni ba, Zainaba fushin ya isa haka don Allah idan ban dawo da ita ba ya zan yi? Sai bin dangi suke har wurin Mai Martaba suka je shi kuwa ya ga musu alkawarin dawo da ita." Shiru nayi kamar na rufe shi da duka nace mishi shine sai da ka kwanta da ita, sai na tuna ba hurimina bane, haka muka rabu a dakin Ijlal rigima suka yi, dole a rayuwa aka bukatar dan iska a gefenka, Ijlal irin matan nan ne marasa hakuri da hayagagga, ni sai yanzu na fahimci ita fa abinda zata mallaka nata ita daya take yiwa yaki, bayan nan bata bin wani abu ko me shi kuwa.
Ta nutsu ta kama aurenta, sannan wani abin da yaya yayi tunda ya ga kowa ya juya mata baya sai yayi ta kyautata musu, yanzu ba a wata daya su Aunty Fa'iza da sauran yan uwanta sun zo. Haka yaya ya dauki nauyin Jinyar Hajiya Mardiya, bayan la'asar da xan fita na same ta a parlourn kasa tana kwance na ce mata. "Bari na fita!" "Ke dai da bakin hali kike, ban da son zuciya me saka gidan yari ya cika, taya zaki gida ki tafi ke daya? Su yaran idan ba zaki da su ba, ni ai kin dauki rakiyata." "Mammy zamu bi ki!" Itama mikewa tayi ta kwalawa Madinah kira ta ce ta dauko mata mayafinta. Dama Nadiyyah tun da ta dawo ta dauke Yarta, babu wnada ya nuna ya damu idan ta kuma lalata yar ita ta sani koda yake shima yaya yana tsaye idan ya shiga wurinsu yana kawo yarinyar ya haɗa da Madinah gari na wayewa Uwar zata zo ta dauki Yarta, sau biyu ina ganinsu, ban ce mata kome ba nasan bai sani ba ne, tana jin ihun zasu bi Ni unguwar Malamai itama ta sauko da gudu tana faɗin. "Maamah ki je da ni!" Kallon sama Ijlal tayi ya ce mata.."kin tambayi Mummy dinki." "Zata hana ni zuwa." Ta faɗa makalewa bayan Ijlal. Ita kuwa ta riko da suka fita, nima na riko hannun Yarima Annur muka fita abin mu.
Wasa gaske Nadiyyah ta fito ta samu yarta bata nan, nan ta fara masifa da jidali ta kira shi, ya ce mata sai me? Da bata nan su waye suka kula da yar? Idan ta ce zata d'aga mishi hannu sai ya sake ta, wallahi ba zata saka mishi damuwa da Matanshi ana zaune lafiya ba, sanin daya ya rage sai ta yi kasa da murya ya ce ita fa ba'a gaya mata ba, ya ce mata. "Saboda yanzu gidana baka iya banbance Dan Ikhlas da Yaran Ijlal ɗuk daya suke a wurin matana da ni kaina!" Wannan masifar da yayi ta mata babu ji babu gani yasa ta kashe wayar, kamar yadda muka yi na bar Ijlal da su Umma da Yaran na dauki Iram da jami'an tsaro muka nufi gidan Alhaji Nafi'u, aka dauko Mommy Turai da saura kiris ta mutu, muka nufi asibiti iram ta ce min.."Ikhlas, dama kin san Abba ba shi ya haife ni ba " toshe mata baki nayi ina kallonta. "Ki dauka jininmu daya!" Dariya tayi tana faɗin. "Sai kuma aka yi yaya?" Ta cigaba da wasa da hannunta. "Maluma da Umma suka ce Ya Nuraim ya rufa min asiri ya aure ni." Ji nayi kaina yayi wani irin kato, na ce mata "yaushe aka ci amanata?" Hawaye ya zubo mata ta ce min. "Nima na ji kunya amma shi yadda na fahimce shi ya amsa hannu bibbiyu, ashe ni ce Abba yaso ya aura ba Abidah ba, me yasa Abba yake sona haka?" "Saboda yasan kaf duniya Yayanshi ne zasu rike ki, kamar kanwarsu kuma matarsu, duk wnada ya aure ki zai tausaya miki kuma zai ji kanki, sannan zai kaunace ki domin Abba yana sonki, Mijinki zai so ki. Ki yarda da Allah zai so ki, nasan wacece Umma tunda ta yarda ayi auren har ta nuna miki tana sonki, wallhi bata duba kome akanki, su fa Umma da Maluma, a sabon Allah ne ba zasu yiwa Abba biyayya ba, amma idan har abin Allah ne duk abinda ya fada ba su ja akanshi, jikinsu yana rawa suka amincewa da kome don haka kada ki damu kanki. Muma muna sonki kuma zamu zauna dake a matsayin Yar uwa kuma surukanmu!"
Na ji dadi na yi farin ciki, kuma na yarda gidammu dattawa ne, domin babu wnada ya damu da Iram tayi wani abu, kawai hidimar bikin ake tayi, Ya Abid ya tsaya a matsayin Baban wa kuma Uba. Kasancewar ta zama daya daga cikinmu, ba ayi wani yunkuri ba a Maradi aka dauro auren, Mommy Turai kuwa anata kula da jinyarta da ta fara samun sauki sai dai depression ya shigo cikin lamarin inda ya hadu jinya, abin tausayi idan ka ganta. Tun daga lokacin da na tsaya aka kawo ta asibiti aka mata jinya ban kara ganin Tauhid ba, na ce a raina dama ita yake son mu taimakawa.
Haka aka yi bikin Iram, manya kawaye ana laulayi, da yake yar bidi'a ce, tana jinya amma sai da tayi anko, bikin da ciki ya hanata zuwa, haka muka yi ta sintiri da Yaran ranar Wuni kowa ya dame ni ina Ijlal na ce tana gida Yaya ya jika mata aiki, sai aka yi ta murna, abin ya bani mamaki ashe tana son haihuwa har haka domin har su take gayawa, yadda take fatan Allah ya kara mata ko daya ne, Yan uwan Yaya sun zo, har da Mai Babbar daki da take gaya min, nayi hakuri tuntuni ta saka ana ta mana saukar Kur'ani, ita ko da minti ɗaya bata tab'a cire hannunta akan lamarinmu ba, ta bar ni nayi ƙoƙarina ne kada ta shigo nace tana ganin na gaza ne, sai gashi kuwa ana bata mamaki na tashi yaya daga barci yayi abinda