Showing 81001 words to 84000 words out of 157081 words
son na koma ne mu cigaba daga yadda muka tsaya you're hungry ko?" "A'a wllahi ba shi ya kawo ni ba, ki yi hakuri don Allah." Wannan rudewar da yayi na rantse da Allah sai na ji ya dake ni, wani irin abu na ji ya tsaya min a rai dama haka na miji yake idan ka ɗauke mishi wuta. Ban yarda na kara kallonshi ba, sai na cigaba da shirun. Har can ya ce min. "Kiyi hakuri da idan baki shirya ba ko zauna Ali shirya a nutse ba gaggawa ake ba."
Daga haka ya mike ya zuba min kuɗi a gabana, "yaran sun ce zasu zauna ko? To ni zan tafi na gode da bani dama ta biyu na gode da taimakon da kika yi min, na gode da alfarman da kika yi min ....
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 30
Tunda ya fita sai na ji bakiɗaya jikina ya mutu, ko iya nan aka tafi ya nuna min alfarma nake mishi, sai na koma wurinsu Maluma na nutsu na fara ɗaukar haddasa akan zaman aure da wasu abubuwan da ban gane ba. Wasa wasa sai gashi ina kara hango inda nake da matsala, shiga harkansa da matansa, ove sabi sabi. Shishigewa dangin miji na hana su hango alkhairin kowa sai nawa, nuna isa da gadara ni ce matarso, da gaske wannan ya janyo min masifa a cikin gidan aurena, shiga hurumin mijina da matansa, nunawa su ba kome ba ne bayan wanda ya ajiye mu yana son kowacce, sannan yadda nake wasu abubuwan yasa shima yake tafiyar da ni haka. Kai ba sai gani a dakin Umma na ce mata. "Umma kinsan har da laifina a samun matsalar gidana?" Gyara zama tayi sosai ta sake dariya tana tafi. "Waye ya gaya miki?" Ta tambaye ni, zama ba gyara na ce mata.."Umma ni ce na gano haka ta dalilin maganar jiya da kuke cewa Yaran nan sun kwantar da hankalinsu a gidan Ubansu, saura ni ake jira na samar musu zaman lafiya da kwanciyar haka, sai.nayi tunanin me yasa sauran matan suke zaune basu da matsala da shi? Me yasa kome ya faru ni ce me laifi? Me yasa Ijlal bata katsalanda wa kowa? Me yasa Nadiyyah iya kishinta ta sani bata damu da kowa ba sai kanta? Ni kuma ina ganin idan na shiga harkansu kamar zaman lafiya za a samu ashe kashe kaina nake!"
"Yawwa Uwata bari na gaya miki wani abu akan Mijinku wanda na fahimci haka. Duk abinda yake so yana son a taya shi so. A gefe guda yana hango idan akwai wacce yake son ta taya shi son kome tow ke ce. Na biyu kin san rauninsa sama da kome amma kike taya shi fada akan matanshi idan matarsa ta yanka shi blind your eyes kamar baki gani ba, idan ya ce jini ne ki ce baki ga jini ba, sanan baki ga wani ciwo ba. Ta haka zaki taimaka kanki da zuciyarki. Amma ya ce jini kika ce jini yayi ihu kika yi ihu bayan ita matar bai iya samunta da magana ba, tow wallahi kin ji na rantse miki da Allah kika sake ya gano baki da hakuri akan shi tow zuciyarki zata buga, abin na munafunci ne ko ke ba zaki yi munafunci ba yi kokarin ki nuna mishi ba ruwanki kai baki jin Yaren da yake, babu wani batun matansa ko wani abu. Look at me kada ki yarda namiji ya kawo tsegumin kishiyarki, idan ya ce min fari nuna mishi baki san kome ba, ya kamata ace kin fahimci haka a cikin gidan nan!" Wallahi sai na ji kamar yanzu xan fara zaman aure yadda Umma take gaya min abun da nayi missing, washi gari aka zo har gida aka min gyaran jiki, Maluma tana gaya min cewa. "Idan na kula da kaina da Yarana, ina nan zaune matansa zasu ta rigima da juna, sannan nayi hakuri da shi fa.
Haka dai muka cigaba da tattaunawa har aka gyara min jikina aka min jar lalle. A hankali na tattara kome na rayuwar da na shirya na saka a gabana, sati biyu a tsakanin yazo da kanshi ya dauke ni, muka koma sai dai naki yarda da wannan rawan kan, wani abu da na kara yi shine zuwa asibiti aka saka min implaner, domin zaman gidan Salmanu Faris dole mace tayi takatsantsan. Wani irin tsoron daukar ciki ko wanu laulayi yasa naki sakewa na koma haka, na kuma mai da hankali na gyara jikina da lafiyata, gani ga Isma wacce ta guje ni ta koma wurin Ayaan, nima kuma na ji dadi koda na dawo ban nemi Yaran ba, domin suna wurin Mai Babbar daki, sai dai wani abu daya da na kasa fahimta zaman gidan ya koma wani irin zama ko kusa ban kawo ana kara'i ba, sai da na kwana uku da yamma na sauko kasa na fito waje, shan iska na hango Princess tana wasa a lilo me kula da ita tana gefe, Ijlal ta fito da Nana Aisha da Amirah, karatun Alqur'ani nake amma ina bibiyar lamarin Yaran, ita kuma Ijlal tana can tana waya, Princess ta ture Nana A'isha, ina kallonsu nayi kamar ban gani ba. Itama Nana A'isha tana tashi ta kaiwa Princess duka, kawai yaran nan suka shiga dukar juna, Amirah na kallonsu. Kamar xan yi magana sai ga me aikin Nadiya ta zo da gudu ta ture Nana A'isha sai da ta fadi, ita kuwa Nana A'isha ta kaiwa Princess cizo a wuya garin ta kwace ta faɗa kan Amirah da take ta ihu, abin sai ya bani mamaki Ijlal tana zuwa ta rufe mai aiki da duka, a hankali na zare jikina, na bar su wurin. Bayan sallah isha ina azkar ya shigo yana huci. Take na tsume nima na dauke kai, ni ina ruwana tun karfe shida yake bala'i har yanzu masifa yake. "Kina gidan nan haka ya faru?" D'ago kai nayi nace mishi. "Me ya faru da haka?" "Fisabiilillahi baki ga yadda kome ya faru ba ne? Wani irin rayuwa kika zab'a mana ne yanzu idan bana nan ba zaki hana aikata wani abu ba ne?" Ware idanun nayi kafin na kwashe da dariya na ce mishi. "Dama ka bani ajiyar iyalinka ne?" Kamar dai fashe da kuka ya ce min. "Yanzu baki fahimci irin abinda suka aikata ba?" "Look Mr Faris I'm not here domin na zama mai gadin gidanka, nothing concern me da lamarin gidanka, idan ka matsa min har ga Allah zamu samu matsala" daga haka na wuce zuwa dakina, daga haka ya sauka ina jin muryan Nadiyyah tana faɗin. "Annamimiya ba zata fadi gaskiya shegiya karuwa munafuka, da Yaranki aka yiwa haka ai da kina nan kin birkita hankalin mutane da gari, munafuka kanwar shaidan. Wallahi sai naga bayanki Ikhlas!" Lekowa nayi na kalleta daga saman baradan kofata na bude baki xan yi magana ya ce mata "Duk ranar da kika sake wani haukarki ya saka kika tab'a min mata ko Yarana wallahi billahi azim sai kin kare a jail idan kina ganin karya ne to ki tab'a min Zainaba ko Yarana, haukarki a kaina zaki iya yin shi zan dauke amma kika tab'a min mata ko Yarana zaki gane Allah da girma yaƙe foolish lady!" Ya wuce abinsa har zai shige ya ce musu. "Daga yau duk wacce ta kara min dambe a cikin gidana sai ta bar min gidan yan iska da Iyayenku suke nima muku alfarman a zauna da ku,.kuna min iskanci ita ɗaya ce nake zaune da ita domin tayi min Alfarma!" Tun kafin ya fara wannan bayanin ya bar shi da su a nan ina xan iya magana, ai kuwa haka sai ya kara rura wutar masifar da ake yi a gidan, ko kwana uku ba ayi ba Nadiyyah ta haihu ta samu da namiji, Allah yasa a kwanakin muna ta zirga-zirga maganar auren Yeemar da Faruq, wato tunda na tsaya daga parlourn kasa da suka dawo ba mata barka daga nesa, haka shima na yi mishi ban kara bin ta kansu ba, ya aka kwana a ragaya ban sani ba ranar dai ance min ta shirya wani irin gagarumin liyyafa akan ranar suna da burin zata kafa tarihi sai dai ranar da yaron ya cika kwana uku, cif ta shiga wanka ta ce dai ta ji an shigo amma bata fito ba, ita kuma mai zama da ita wai ta fita shanya, yaron nan ko kafin a isa asibiti ya ce ga garinku. Na tausaya mata domin hauka tayi tuburan, sai da akayi da gaske a kanta, ba sai ga Nadiyyah tana cewa tasan ni na saka a kashe mata Yaro ba, sai ta dauki fansa Ayaan idan bata kashe shi ba sai dai ta mutu, a wannan lokacin Iyayena, bangaren shi Mijin da Uwarsa da dangin Yayari bakiɗaya suka tsaya akan Yaron kai case har sai da aka hada da manya lauyoyinsa da na gidan sarauta da Yunus da kowani bangaren sai aka tsaya min suka ce batun kisa ba wasa ba, sannan da aka bincika a Cctv babu alamar an shiga dakin bakiɗaya. Case dai har sai da aka kwantar da ita asibitin ƙwaƙwalwa domin ta saka Yaron a ranta, abin sai godiya domin ta sha jinya kamar zata mutu sannan ta dawo ɗakinta, babu ruwana da harkansu kowa kaf kaf yake da dansa.
Yarana kuwa suna cikin tsarin Allah ina musu addu'a, Kakarsu tana kansu haka Ubansu yana tsaye akansu. Haka muka cigaba da shirin bikin Yeemar da Faruq, a daren ranar da aka daura auren a ranar na ga tulin hakurin Mai Martaba ya kasa hakuri, muryanshi tayi sanyi yake faɗa min. "Fulani Babba, har sai yaushe zaki duba lamarin bawan Allah!" Juyawa nayi na kalle shi kafin na ce mishi. "Wani lamari kenan?" Bai ce kome ba ya yayi shiru amma yana jin babu dad'i, na fahimci abinda yake nufi amma na share, a daren ban kyale shi ba, muka taru muka rufawa juna asiri.
Kwana biyu da muka yi a tare da kara fahimtar gundarin hakuri da kawaici irin nasa, amma duk wannan shagalin da aka yi ban yarda na nuna mishi ba, har bayan ya fita dakina na ga yadda jikinshi yake rawa da bari a kaina.
Ana haka aka yi wani bikin nadin sarauta a cikin fadar zanzabira, a ranar na ji labarin da ya bani tsoro domin ni dai bana wurin amma an ce min Yaya ya tafi da Ayaan, inda Faruq ya dauke shi. Abin mamaki shigar Ayaan pada ana taro, hankalin kowa ya tafi ga abinda ake yi, amma an ga lokacin da Faruq yake nimansa, shi kuma yana gudu yana bin lungu, can Faruq ya hango shi yana rike da wani bakin abu. Takawa Faruq yayi wurin ya ce mishi. "Little King zo muje ko?" Juyawar da yaron yayi idanunsa suka koma sak na Isma, dariya yayi da hakorinsa guda shida ya ce mishi. "Wasa ne!" Ya mika mishi katon Black Cobra da ya kama shi ya rike mishi wuyarshi. "Ajiye shi Ayaan kada ya cutar da kai!" "A'a yin wasa da shi ne!" Ya kara shake wuyar macijin, yana dariya kafin Faruq ya riko shi ya kaiwa faruq wani irin duka a cinyarsa, wurgi aka yi da faruq can, ya sake murmushi yana faɗin. "Wasa ne!" Yayi cikin al'ummar fada, da karfi Faruq ya ce.."Mai Martaba kayi wani abu!" Juyawa inda Yaron yake yayi, yana wangale mishi baki, wato wani abu Salamanun Faransa yaji da daki zuciyarsa, kamar ya daka tsalle ya bar padar, tuni aka dare dayawa sun fita saboda tashin hankali. A hankali ya tsaya a gaban uban ya ce mishi. "Unnnn wasa ne" ya mikawa Uban, "in cico ba!" Wato ba zai yi cizo ba." A hankali a bayan kunnen Mai Martaba aka ce mishi, karba da sunan Allah ka mai dawa me aiki aikensa." Ana fadar haka aka yi shiru, ya juya yana kallon mutanen fadar, amsa macijin yayi wanda yayi wani irin zafi ya ce mishi. "Ka koma inda aka aiko ka,.ka gaya musu Sarki Hassan yana nan a raye!" Ya sake macijin ya fita da gudu. Yaron ya fashe da dariya yana faɗin. "Wasa ya gudu!" Wani irin ajiyar zuciya Uban ya sake, sai lokacin aka lura da halin da Faruq yake ciki, wato cinyar ta samu matsala. Tabbas wannan yaron idan ya daki mutum mutuwa zai yi, haka aka kai shi asibiti aka daure cinyar domin kashin ya tsage ne.
A hankali yaron ya koma kan cinyar Uban ya zauna yana wasa da hannunsa a baki. "Ranka shi dade ba za akai shi a wanke mishi hannu ba macijin da ya tab'a mai hatsari ne kuma kamar aiko shi aka yi!"
Murmushi yayi ya kalle su ya ce musu. "Babu abinda ya faru domin shi kansa macijin ya razana." Ai kuwa ba a tashi daga fada ba. Aka samu labarin Alhaji Tahir Abbas Yayari ya fadi sakamakon sarar da Maciji ya mishi, a hankali kowa ya kama kansa, Ayaan din ta tafi gaban Alhaji Mamman Abba yayari, ya ce mishi. "Ciwo kafa!" Gyada mishi kai yayi ya ce. "Eh kakanmu ciwon kafa yaki barina tun da kuruciya!" Kallon Baban yayi ya ce mishi. "Ababa tatan!" Wato yana nufin takalminsa. Mikewa Mai Martaba yayi ya dauki dan yana faɗin.."Baba Mamman ka shigo cikin gidan!" Haka aka watse a fadar. Har cikin gidan a parlourn mai babbar daki suka zube, yaron ya fito waje ya dauki takalmin Mamman Abba yayari, ya shigo da shi parlourn ya zauna yana budewa a hankali, har ya bare takalmin da karfin tsiya, Isma ta zo tana lashe hannunsa tana kukan jin dad'i. "Cima!" Wato Isma Goga kanta tayi a jikinshi a hankali yaron ya bare takalmin nan sai ga kashi a cikin takalmin da kwalba, sai wasu irin layyu kanana, ya bare a hankali ya mikawa isma ta cinye tas, kafin ta fita waje tayi amansa, ya yarda takalmin ya dawo gaban Alhaji Mamman Abba yayari ya fara shafa kafar yana tsaye. "Ciwo akafi?" Wato ciwo da zafi, murmushi mai babbar daki tayi ya ce mishi. "Ubana da zafi kai!" "Connu!" Yana gamawa ya wuce dakin Mai Babbar daki ya dauko kwalbar man zafinsa ya tsaya yawunsa ya cikin man ya shafa mishi.. "Cima ashe kafa!" Ita kuwa ta kashe kafar tass. Ai Alhaji Mamman Abba yayari bai bar parlourn ba sai da yaji kamar an zare mishi allura a kafarshi, sannan yayi ta godiya yana yiwa Yaron addu'a.
Ai a ranar da naji labarin a bakin Sailuba a daren na d'aga mishi hankali ya dauko min Yaron domin kuka nayi ta yi. Ashe wani sabon tashin hankalin ma dauko shi nayi. Washi gari da aka kawo min shi yan uwansa suka biyo shi. Ban san me ya faru na dai rufe su a parlourn kasa na shiga kitchen ina musu abincin, kawai na ji ihun Ayaat Allah ya daura mata son yan uwanta. Wai ta ga Princess ne ta bita shine Uwar ta wurgota daga step, duk muka fito, har Ijlal da Ikram. "Yanzu Nadiyyah abinda kika yi mai hankali zai yi? Wannan wacce irin dabbancin ne!" "Mammy ciyo!" Ayaan ya fada min yana dariya, yadda ta turo yarinyar haka itama aka yi ta janyo ya ana kwalata da kasa, na rantse da wani ya gaya min ba zan yarda ba, amma akan idanuna yayi ta majajawa da ita yana molata da kasa, Tsoron da na gani a idanun Ijlal wnada ya haifar mata da guduwa dakinta. Ta shiga kiranshi amma wani ikon Allah ya nime wayar babu shi, haka Ikram. Ni kuwa idan na bude baki xan yi magana sai na ji na manta kome, haka ina ji ina gani Yaron nan ya sumar a Nadiyyah kafin ya shafe mana tunanin mu bakiɗaya muka manta da faruwan lamarin, sai da na kwanta barci Bayan azhar nayi mafarkin abin, shine zaune yana gefena yana shafa goshina. "Mammy akuyi!" Wato nayi hakuri, "Ibrahim me yasa ka yi haka?" Ya fada yana kallona, sai a lokacin kome ta dawo min, dafe goshina, a take na fara tunanin zuwa wurin Baba titi, wallhi ban isa ba.
Haka na yi sallah la'asar, ina addu'a ya shigo parlourn ya kalle ni. "Fulani me ya sami Nadiyyah wai itama ta manta yadda ta fado daga step!" Kallon Yaron nayi yana kan kujerar parlourn ya daura daya akan ɗaya yana kallon Cartoon abinsa. Kamar nayi kuka haka na yi shiru Ayaan ko jidali. Anyi haka washi gari a wurin karyawa, Nana A'ishah ta kwad'awa Ayaanah cokali. Ya ce mata.."A bata akuyi!" Kallonshi nayi wato Nana A'isha ta bata hakuri, uban shima kallonshi yake nace mishi. "Kyale ta ba da saninta ba ne!" "Gangane" na ce mata.."Nana A'isha bata hakuri ki ce Sorry!" Yarinyar ta ce min. "Ba zance mayya kawai!" Wani irin mari ya dauke da shi sai da ta kifa akan bowl din farfesun ya ce. "Ace Mammy akuyi.!" Da gaske yarinyar ta ki bada hakuri sai ihu take, ai kuwa ya d'aga ta sama, abin da ya razana Nadiyyah kenan ta tashi zata gudu ya dawo da ita. "Mammy aku yi Aicha!" Da sauri Uwar ta ce min. "Don Allah ki yi hakuri!" "Ayaan dina, Hassan Ibrahim dina kyaleta tauhid dina!" A hankali ya saukar da ita daga sama ya juya zai fita. "Zo ka ci abincinka!" "Ya koshi!" Aka fada da wata ƙatuwar murya, da sauri na mike ya datse kofar da zai kawo ni wurinsa. Kallon Yaya nayi ya sake murmushi ya ce min. "Adalci yayi fa, kowa aka tab'a masa uwa ba zai yi hakuri ba. Sannan wannan ya rage naku, kuyi wayiwa Yaranku kyakyawar tarbiyya ko kuma shi zai zame min mataimakin idan bana nan!" Ya mike yana mai barin dakin cin abincin. Babu