Showing 27001 words to 30000 words out of 157081 words
karo da mota haka yasa suka zuba mata idanun, kamar masu tsoron tana ta kafa doka ita fa sai anyi biki, shi kuma daga fada ya ce babu biki, abin ya bata dariya don haka wurin karfe tara na dare, ta nufi fada ba tare da ta gayawa kowa zata ba, sai nimanta suka yi suka rasa. Lokacin da ta isa fadar da Faruq ta hadu, a hankali ta nufi inda yake sai dai wani ikon Allah kada isa wurin tayi, saboda wani irin zafin da yake wurin tana kallon faruq a hankali ta ga kamar ya fara juya mata wani wanda ta sani, dafe kirjinta tayi tana jin wani irin tsoro, tana ja da baya tare da cewa. "Lallai ashe wasar zai yi kyau ga Bargaga a kofar fada, ka mutu a bawa ka dawo a bawa!" Ya ciji bakinta tayi ta koma inda ta fito bayan ta ji haushi tana tafiya a bakin hanya wasu matasa a cikin mota suka yi ta binta suna mata horn amma bata kula ba, sai da ta ga babu jama'a babu mutane, a hankali ta tsaya tana murmushi. Bude mata mota suka yi ta shiga. Yadda ta shiga motar suka cigaba da tafiya.
**
Tun da nayi sallah isha barci yayi gaba da ni, wani irin murdaden mafarki nake, wai wata mata da ba zata wuce kamar ni ba, naga hannunta yana zubar da jini duk yadda naso isa gare ta, abin ya ci tura q hankali ta fara juyowa, a nan na farka ina haki domin yadda na ganta da alamu zata bada tsoro. Kallona Isma tayi tana mai lashe hannuna, can tayi wani mika tare da wata kuka kamar ta ga wani abin tsoro da gudu ta haura kaina tare da tsayawa tana wani irin gurnani. "Isma sauko daga saman nan kin ji!" Na faɗa ina sauko da ita daga kaina, a hankali na ga wutar dakin yana wani irin kawo wuta da daukewa. A hankali na d'ago kai na kalli bakin kofar, wani irin tsoro ne ya kamani, mace ce tsaye da Yara a gefenta. Kamar na san fuskarta. A hankali na dan so matsawa amma na kasa kamar an rike ni a wurin. Ta isa a hankali. Ta zauna a bakin gadon ta kai hannunta kan cikina. Tana murmushi ta ce min. "Kin san akwai rauhanai farare da bakake, ni ina cikin jinsin fararen kuma jinsin al'ummar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, nayiwa Awatif alƙawarin zan baki taimako a duk lokacin da haka ya taso. Babu Awatif yanayin da yake tare dake ne yasa ake ganin kamar ita ce ke. Amma ni kika gani a mafarki nan. Aojanah tana raye a jikin Ikram, ban san me zaki fahimta ba amma ku bil adam kuna da kafin basiran da mu rauhanai. Sannan baba titi yana tare da ke. Rundanar shaidanu tsakiyar birnin suna raye, babban addu'ar shine Allah ya sauke ki lafiya, kada ki yi fushi da mahaifinki, saboda ke yayi haka lokaci zai da zaki fahimci abinda yayi miki. Zan tafi amma ki gayawa Isma mu ba masu cutarwa ba ne, Aojanah ta kashe matasa uku yau din nan shine dalilin mafarkinki nan, saboda yanayin da Awatif yasa kika ji haka!"
Ni dai ban iya ko motsi har ta gama ta juya zata fita. "Isma aiki yana kyau babu me zuwa sai da izinin Allah!" A hankali ta b'ace, ajiyar zuciya na sauke domin wannan shine karo na biyu da nake ganin wasu abubuwan da na gayawa Mai Babbar daki ta ce saboda ina tare da Isma. Bayan wasu yan mintina na sauke ajiyar zuciya, ban daki na shiga nayi alola ba fito nayi sallah shafa'i da wutir, na jima ina addu'a musamman abin cikina da mahaifinsa, don ni har yanzu ban yarda yan biyu zan haifa ba, bayan na idar ya shigo ya kalle ni ganin ina addu'a ya zauna ya shafa sannan ya zauna yana kallon yadda nake cizon bakina. Yau wuni nayi marana yana bala'in ciwo, "anya ba zan fada maganar auren nan ba kuwa ina ganin bayan kin haihu sai shi yi." Tab'e baki nayi ina hararanshi na ce mishi. "Kamar da gaske ji yadda kake wani zancen sai kace zaka iya idan baka zage ni baka jin daɗin!" Murmushi yayi ya zauna tare da daura kafana akan cibiyarshi yana ja min kafar yana kara, bayan ya gama ya ce min. "Ina son na kai ki Abuja ki haihu amma Ummi ta ce a'a ban san me xan yi ta gane ina son haihuwa tare, amma in sha Allah tare muka fara kuma tare zamu haihu, in sha Allah a duk inda nake, ki yi ƙoƙarin kirana ni kuma xan zo gare ki!" Murmushi nayi na ce mishi. "Tow SuperMan ko nace Spider Man, kawai sai na ganka kazo min!" Murmushi yayi yana cewa. "Soyayyar da take tsakanina da ke tsakaninmu, in sha Allah zaki gani domin kuwa ina jin kamar mun rayu tsohon shekaru masu yawan gaske, ina kallon kamar na san ki a wata rayuwar. Ko kawai dejuv ne yake damuna a duk lokacin da na kalleki sai na ji kamar na sanki!"riko kunnenshi nayi tare da cewa. "Tatsuniyar ya isa haka." Hannunshi ya kai cikin rigana yana tab'a cikin d'aga rigar yayi ya sumbaci cikin yana kallon yadda yake motsi kamar zai ruso min, "bana miki ciwo?" "Tura baki nayi na ce mishi. "Wani ciwo kuma ba wani ciwon fa." "Hmmm haka kika ce amma yadda kike d'aga kafa yau na ga kamar ko cizon yazo ne!" "Eh yau na tashi da wani irin ciwo ne, amma da sauki fa!" "Allah ya baki lafiya ya kuma sauke ki lafiya!" "Amin Ya Allah Yayana!" Ya cigaba wasa da cikin yana tab'a inda ya ga motsin cikin, wayarshi ce tayi ƙara ya dauka ya saka a kunne. "Wai kana nufin haka zaka aureni babu biki babu kome kamar yar tsuntuwa?"
Jin yayi shiru ta cigaba da cewa. "Idan ka yi min haka ka bani mamaki da kunya, har abada kuwa ba zaka tab'a zama namiji a idanuna.." "idan nace na fasa aurenki fa!" "Kace me?" "Abinda kika ji!" "Allah ya baka hakuri!" Kashe wayar yayi yana faɗin. "Jaka kawai! Na tsani yarinyar nan, da ina da yadda xan boye ta a daina jin batunta ta balle labarinta da nayi wallahi na tsani yarinyar bata kaunar ta sam, kamar masifa haka nake kallonta a cikin rayuwata." Yadda yake fadar ni dai jin shi nake domin dai a shekaru da nake da shi na dauki ilmin rayuwa a wurin Yaya yace baya son mace gobe ki ga mace da ciki, ban gama wannan nazarin ba sai ga kiran Nadiyyah. "Yaya ka tafi gidanka na gaji da yawa barci nake ji!"
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 10
Ba zai kwaso gulmarshi yazo ya dame ni shi da matansa ba, zuba min idanu yayi kafin ya ce min. "Korata kike Yan mata saura kwana nawa ki dawo wurin Yayanki?" "Ni dai rufa min asiri." Na fada daidai Ijlal tana kiranshi, kamar haɗin baki yau matansa har da wacce zai aura suke kiranshi, "ni fa anan zan kwana" ya fada yana murmushi, bayan ya kashe wayar. Ya mike tare da kashe wutar dakin. Ya zo ya kwanta a gefena yana latsa min cikina. "Yaya ka ji tsoron Allah ka tafi gidanka!" Mikewa yayi ya fito parlourn har da jin haushin daga cewa ya ji tsoron Allah ya tafi gidansa, shine zai wani tafi babu wani jan aji ai dama nasan duk abinda yake faɗa kawai bukata yake nima ya biya idan ya samu shi kenan, zai tattara ni ya watsar gefe guda ga sabon wuri fresh ina zai yi rawan jiki akan local. Ina gama tunanin sai gashi ya dawo, kunna wutar dakin yayi ya ware idanu nayi cike da mamaki dama bai tafi ba ne? Yadda fuskana yayi sai da ya sake murmushi, "kina tsammanin na tafi ne yan mata?" Daukar pillow nayi na rufe fuskana, ina jin wani irin yanayi, kashe wutar yayi ya zo ya sauya kayan jikinshi, ban daki ya shiga ya watsa ruwa ya fito, sauka nayi a gadon na tsaya a tsaye sai naga cikin yayi min wani irin rumdundun irin katon abu kamar randa, kunna wutar dakin yayi a karo na uku ganin yadda nake kallon cikin na tallafe shi da hannuna, ina son n a shiga ban daki amma na kasa saboda abu biyu na farko yanayin da nake ciki na yadda cikin ya girma na dame ni, sam bani da wani fasali duk wata mace tana son ta burge Mijinta, amma idan tana da ciki wani irin muni take, haka yasa nake jin kamar ba ni ba. "Ke bar wannan tunanin Mijinki yafi sonki da katon ciki!" Ya fada yana mai dawowa bayana yana mai kara tallafar cikin, a hankali na juya ina kallonshi da fuskarsa da yake kan wuyana. "Ba zolayata kake ba? Anya akwai wani kyau da nake da shi da wannan randar cikin.." sumbtar kunnena yayi yana faɗin. "Ina sonki a haka! Duk cikina ya mai dake haka, taya zan ki kayana! Ina sonki muje ki yi wanka!" Ya dawo gefena ya tallafe ni, har ban dakin kallonshi nayi nace mishi. "Yaya jikina ya tara suma." "Eh na gani shekaranjiya, na san Zainab dina bata tara suma bari zan gyara miki yanzu!" "Na gode sosai Yaya!" D'ago kai yayi ya sumbaci bakina, yana faɗin.."A duk lokacin da kike bukatana tow baki bukatar sai kin yi min godiya ai ni mallakanki ne!" "Yaya kalamanka yana bani tsoro, yadda kake tsarani haka kake tsara sauran matan ko?" D'ago kai nayi yana dariya, ya shiga abinda yake bayan ya ɗauki shaving stick ya fara goga min shaveer, sannan ya bi yana kwashe gashin. "Ina son mace, amma ni ba bawan kowacce mace ba ne sai ke da uwata da kannena da Yarana, babu macen da na tab'a mata wannan aikin sai ke, nasan ba zaki yarda ba, domin kuwa kina tunanin shirga miki karya nake ni kuwa nasan me nake fada har cikin zuciyata." Shafa kanshi nayi ina faɗin. "D'an nan zaka yi albarka!" D'ago kai yayi kafin ya ja min hancina yana fadin. "Kin bala'in rena ni yar nan!" Dariya muka saka. Haka ya gama min na d'ago hammata na ya kwashe na, sannan ya taya ni nayi wanka, muna fitowa ya dauko min wata rigar barci mai nauyi ya saka min, sannan ya gyara min gadon, ya kwanta a bayana yana min hira, a hankali barci ya dauke ni, ban daki ya koma ya dauro alola ya zo ya shimfida abin sallah, ya jima yana Sallah tare da niman sa'a da nasara a rayuwarshi Allah ya sauke ni lafiya. Kafin ta dawo gadon ya kwanta a bayana hannunsa akan cikina, barci yayi gaba da mu, da Asuba Jakadiya Iyaami ta buga kofar, haka muka tashi shi ya tafi masallaci, ni kuma ta kawo min madara mai zafi na sha sannan sai zuma da dabino na ci, kafin na sauka a gadon. Sai da nayi gyatsa ta ce min. "Kina bukatar abinci ne?" "A'a Jakadiya yanzu ai cin yaragu!" "Alhamdulillahi shi kenan ki yi sallah lafiya!" Ta fada tana murmushi, haka na wuce ban dakin nayi alola sannan na zo ma kwanta, duk bayan sallah asuba Mai Babbar daki tana fitowa parlour ta zauna amma yau tunda ta san danta ya bokare duk koran da tayi mishi a wurina ya kwanta ta kwashe kafaffunta, ta addaba a ɗakinta, ta sani tsaf ba kunya ce a shi ba. Ita tausayi cikin da uwar take amma ta lura kishi ya rufe min idanu, ban damu ba kome zai yi kuma ni kaina bana jin haushi a zahiri amma a cikin raina kallon duk abinda yake yi kamar karya ce. Bayan sallah asuba ya shigo, anan na ga rashin hakurinsa. Domin yana dawowa na ga yadda jikinsa yake rawa, na gano ta ciyo shi, haka ba bashi damar yayi yadda yake so da ni, zai dai wannan karon ya kuwa lakato min damuwa, domin lokaci guda na ji kamar kome na jikina zai yi waje, ai ba san lokacin da nayi ta kai mishi duka ina ture shi, shi kuwa ya ga zama ya ga banza ya kuwa kwashi gara da dad'i, sai da ya ga na fara fita hayacina yayi maza ya zare jikinsa a nawa. "Sorry!" Ni dai ban iya magana, haka ya taimaka min na shiga ban daki nayi wanka na zauna cikin ruwan zafin da ya tara min kafafuna ciwo suke min. Dakyar na fito tare da tsayawa ina hararanshi, "sorry!" Wucewa gadon nayi na kwanta, barci yayi gaba da ni. Shima wanka yayi ya zo ya kwanta a gefena yana latsa kunnena. "Don Allah meye ne haka Yaya?" "Sai an jima zan koma gida ne!" Shiru nayi ban kara ce mishi kome ba, ya saka hannunsa a cikin nawa kafin ya min sai anjima, yana fita sai n a kasa barcin da nake ji, a hankali na ji raina ba dad'i wurin Ijlal zai je ya kara samun nutsuwa dama nasan yaudarata yayi, hmm namiji ne kenan..
Bayan tafiyarshi da kyar barci yayi gaba da ni, sai karfe sha biyu saura na farka shima don yunwa nake ji, a hankali na shiga ban daki nayi wanka na zo na saka doguwar riga mara nauyi yau ai jina nake cikin nutsuwa bayan an kawo min abin karyawa na karya, aka kwashe ina zaune a tsakiyar gadon da Sailuba ta gyara min, sai ga sallamar Bilqis da Daulah, sai Kubrah da suka zo. "Sannu da kaya!" Hararansu nayi ina gyara zaman da nake kokarin yi, "kwanta abinki gaya mana me kike so?" "Duk abinda kuka ga ya dace, kin san dai ba fita zan ya kasuwa ba, sannan shima kan shi Mai Martaba ba zai bar ni ba, duk abinda kuka ga ya dace ku saya kawai waye ya sani ana ta kai, karshe azo a ce babu ni ko yara..." Rufe min baki Daularh tayi tana faɗin. "In sha Allah zaki shayar da Yaranki da yaran domin cikin nan yayi kama da Uwar uku!" "Daya ne fa!" "Haka dai kika ce mu ma haka muke ce." Inji Kubra, duk wani abinda suka zo nace ina so naki, su na bawa damar domin nasan idan gidanmu na kai suma hada su da aiki nayi Sannan bana son rashin yarda ta shiga tsakaninmu da Yaya, idan yan uwansa ne duk abinda suka ga ta dace shi zasu yi, haka suka yi lissafin kayan haihuwa kaiwa , a take Kubrah ta musu lissafin dubu dari takwas, Daularha ta ce mata.. "anya takwas din nan bai yi sauki ba, na ga dai kayan Nadiyyah miliyan daya da wani abu ya bata " rike ta nayi na ce mata. "A saya haka tunda na haihuwa ce, idan bai isa ba kada ku tambaye shi kun ga biki ne a gabansa ga Atm dina ku kara da shi!" Buge hannuna Daularh tayi tana faɗin. "Bana ciki da takaici, waye ya gaya miki yana son auren nan ne? Shegiyar Yarinyar don ubanta wai har da shan guba zata kashe kanta!" Kwafa Bilqis ta yi tana faɗin. "Na sha mamaki da na ga DM dina na Twitter ana ta min magana don Allah nayiwa Mai Martaba magnaa ya yi accepting proposal dinta, domin tayi video tana kuka." Sake baki nayi ina kallonsu, sannan suka nuna min videon, a wani posting da aka yi a Instagram, wata ta ce a kasar comments din. Munafuka ta ga yadda yake kula da Fulani Babba ne, ita ɗaya ce bamu ji an same ta da hauka akan kishi ba, yarinya karama da halin manya., comments kala kala, na kalli Daularh cikin zoyala na ce mata. "Amma dai yayanku yayi kasuwa ashe haka mata suke ƙoƙarin kashe kansu akan shi?" "Allah ni babban abun farin cikina da aka ce bani yi fushi ko rashin hankali akan auren ba, nace wannan matar tasan ciwon kanta gaskiya ba banza Allah ya zabe ki a matsayin Fulani Babba ba " inji Kubrah, dariya na kama musu duk da ina jin ba dad'i amma na share na cigaba da tsokanarsu, "Ai mai babbar daki ta gani ta ce saboda ranar da suka zo ta ga yadda yake damuwa akanki shine ." Murmushi nayi na ce mata." Yayanku ya zama Namamajo, kawai ku daina wani kare shi " " Allah na ji ance Nadiyyah ma zata dawo?" "Eh ba wai bane da gaske zata dawo ne, kuma idan ya rabu da ita za a ce ya zalunce ta ta zauna da shi ba tare da sanin cewa shi din wani ne ba, kin ga kenan babu amfanin sakin da zai mata, Allah ya bamu zaman lafiyar da yake ta fatan."
"Shegiyar yarinya na ji ance Abbanki da Alhaji Mamman suka hada kayan lefen. Ya ce ba za ayi biki ba amma yar Iska ta dage sai tayi bikin Allah ya sa ya ce ta fasa!"
"Ba Amin ba wallahi! Ku da Yayanku zai kawo muku wata auntyn!" Tsaki suka yi tare da bar min dakin, ina jin su a parlourn suna gayawa Mai Babbar daki da Jakadiya wai naki basu goyan bayan a lalata auren, Mai Babbar daki ta ce musu. "Ai da yake ita din yar albarka ce taya zata lalata tarbiyyar gidansu ta hanyar warzaga auren da zai yi ko bai auri Ikram ba dole zai yi aure ai. Ku barta a matsayinta na Queen ta nuna darajarta, duk wasu da zasu biyo bayanta a matsayin kwarkwarah zasu zo, ku dai ku mata addu'a Allah ya bata ikon Ansar jarabawarta kawai!" "Amin Ya Allah!" Suka fada, na cire damuwr Yaya da aurensa. Ranar wuni nayi hankalina kwance, bayan sallah isha sai ga kiran wata number bayan na dauka muka gaisa sai naji muryan Ikram ce. "Ke ki gayawa Salmanun Faris ya tawo ina son ganinsa?" "Kika ce me?" Na tambaye ta a nutse,