Showing 105001 words to 108000 words out of 157081 words

Chapter 36 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

50

yi? Ina miki nasiha da ki tsaya da kafarki, domin nimawa kanki mafita da Yaranki tare da mijinki, idan kika gaza zasu zo har gida sun kashe Mijinki, idan kika tsaya da kafarki zasu ji tsoron zuwa inda kike, zaki wayi gari ke daya ce gayya. A sauran wuraren mata basu da karfinki why not ki hada karfin wadancan da naki domin zama mace da zata tsaya da kafarta, idan har kika tsaya da kafarki zai matuƙar wahala wani yayi ihu a gabanki sai dai yayi a bayanki, Zainaba ko bana raye na saya miki jama'ar fada ga shi nan." Ya dauko min wasu takardu na musamman. Ya mika min, ya sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa. "Na sallame ki. Ki sani bayan ni akwai Abid zai iya tsaya miki amma kada ku rayu baki da namiji da zai baki kariya, ko ana hamaza hamata kada ki sake baki tsaya da kafarki ba, domin cikin duniyar da kike a yanzu daga ni sai Umar muke tare da ke, idan bana raye Maryamu tana tare da Umar suna tare ke, shi yasa nake son kada kiyi kuka kada a kawo labarin mutuwata ki yi kuka domin ta haka ne zasu fahimci gundarin nasarar da suka yi akanki, idan kika ji kuka ki shiga daki ko rufe ko ina ki kunna ruwa a ban daki , ki zauna ki yi kuka sosai zaki samu sassauci. Ni ina ji a jikina lokacina ya kusa ina ji kamar xan tafi nan da ba da jimawa ba.

Wato ban tab'a jimawa a gida irin na yau ba, domin mun dauki lokaci muna hira da Abba kuma na shiga damuwa amma daga baya da kanshi yayi ta bani dariya, har na manta na nuna mishi nasarar da na samu, da zan tafi har waje ya rako ni. Yana tsaye nima haka hira muke, har Ya Abid ya shigo budar bakinsa ya ce mishi. "Tauhid ka shigo, shiga ka jirani ai nima zan rike hannunka mu tafi." Zuba mishi idanun muka yi na ce mishi. "Abba Tauhid kuwa?" "Au Abid zance, don tauhid ne a raina." "To Abba xan tafi!" "To Allah ya tashe mu lafiya!" Ya fada yana kallona, "Amin Ya Allah!" Na wuce zan shiga mota ya ce min. "Jiya kin ga sakona ta E-mail?" "Eh na gani Abba, sannan na tura shi zuwa ga Faruq zai san yadda za ayi da kome."

"Shi kenan Allah ya miki albarka, ya albarkaci rayuwarki!" Ya fada yana kallona, shiga cikin motan nayi ya ce min. "Kin san yadda kome ya faru ki rike Allah kada yi wasa da Sallah, domin kiyayye sallah yana kare ka daga aikata kaba'irai manya da kanana. Kada ayi wasa da azkar safe da maraici, Allah yana tare dake fa kada ki yi wasa da sadaka ko ta ruwa ce ana rabawa sadaka."

"In sha Allah! Na gode sosai Abba!" Na shiga motar takowa yayi ya zuwa wurin motar ya ce min. "Allah ka so Zainab, Ya Allah ka so baiwarka, Ya Allah kasa bayinka na gari su so Zainab, Ya Allah ka bawa Zainab sa'a da nasara, Ya Allah ka kare Zainab daga miyagu mutane da miyagun shaidanu, Ya Allah ga Zainab ka bata nasara da sa'a!" "Amin Ya Allah, Abba dare yana yi je ka kwanta ka huta."

Dakyar muka rabu da shi, nima da na fita sai na tsaya na dawo cikin gidan yana tafiya na ce mishi. "Abbana!" Juyowa nayi na isa wurinshi da gudu na fada jikinshi ina jin wani irin kuka na zuwa min. "Abba na gode sosai!" "Allah ya miki albarka!" Da kanshi ya kai ni wurin motana, na shiga ya ce min, "je ki Allah ya tsaya a gabanki da bayanki ya baki kariya gabar da yamma. Idan har ban zalunci kowa in sha Allah babu me cutar dake, sai Abinda Allah ya ƙaddara miki!" Haka na bar gidan ina kuka, ban bar unguwar ba na kira shi. Yana ɗauka nace mishi.."Abba ina kewarka!" "To ba gashi kin kira ni!" Har na bar unguwar na kusan wuce g.r.a, muna waya kusan har na isa gida, na kifa kaina akan motar ina jin wani irin kuka yana zuwa min. A lokacin na samu Mai Bauchi da Salim, Yaran suka zo da gudu suka rungume ni. "Ina kika je haka? Tun tuni kin bar Yara a gidan nan bayan kin san gidan ba wani safe!" Inji Salim, ya fada yana wani haɗe rai. Kaina a sunkuye na ce mishi, "na je wurin Abbana ne!" Sai kuma yayi shiru, haka na shiga gidan suna bin bayana. Har dakin da Yaya yake na bude musu, suka shiga cikin suna mishi fatan samun lafiya. Ina tsaye ina jin yadda Mai Bauchi yake mishi, fitowa nayi na koma dakina. Can ciki na shiga ina kuka, haka na zauna nayi kuka sosai, kiran sallah Magariba, domin kiran sallah, ban daki na shiga nayi alola sannan na fito, ina shimfida abin sallah, sai da nayi idar kafin na fito waje, na samu sun tafi sallah, sai Ayaan da suke cin abincin na ga Princess tana bakin kofarsu itama Nana Aisha, yadda na fahimci Yaran Babansu suke son gani. Kiran Yaran nayi da hannuna, suka sauko da sauri na saka su a gaba har da su Ayaanah, muka shiga dakin. "Daddy!" Princess ta kira sunanshi, a hankali Ayaan ya bar dakin ina ga ba shi bane, suna tsaye sai kallon Uban suke Nana Aisha ta rike hannuna ta ce min. "Mammy daddy yana barci ne?" Sai na ji hawaye ya cika min idanu. "Eh My Princess!" Na fada ina mai durkusawa a gabanta, Saadiyyah ta ce min. "Mammy I miss daddy alot!" Mai da hawayen da yake zuba min nayi nace musu. "Me too I miss him!" Ina kallon shi, bakiɗaya zuciya tana gaya min wannan shine kallon ƙarshen da xan mishi domin ina ji kamar xan rasa shi a kowani lokaci. "Nana!" Muryan Ijlal da ya ratso dakin na juya ina kallonta. Shigowa tayi tana ƙoƙarin riko hannun Yarinyar ta koma bayana. Sake fusata tayi zata riko hannun yar na rike hannunta. "Ki je zan kawo miki ita!" Yadda na rike hannunta. A hankali nake jin wani abu me karfi kura mata idanu nayi da jini a hannunta. Da fuskartar. "Zan kawo ta ki kawo Amiratul Zaitunah ta zo ta ganshi." Gyada kai tayi sannan ta fita daga dakin can sai gata da yarinyar, ta kawo ta tana ganin Uban ta fara buga kirjinta. "Da....da....da....da ....da..daa.dah" ta daki kirjinta ta juya kanta, ta rasa inda zata cusa kanta don murna tana hawaye, Yarinyar tana kewarshi. Idan Ummi first love dinsa ce, Amirah ita ce second love dinsa ce. Son Yarinyar rubutacciyar kauna ce a zuciyarshi, ɗaukarta nayi na nufe shi na hada hannunsa da nata, wani irin zillo take tana faɗin. "Daaada!" Mikawa Uwarta nayi ita, naki yarda mu hada idanun da kowa a dakin na fito nasa Rebecca ta rufe kofar idan suka fito domin dukkanmu muna dakin ne, ita kanta da take security hawaye take sharewa tana faɗin. "Allah ya tashi kafad'arshi Queen!" Suna gama ganinsa suka fito, tare da rufe kofar dakin. A daki na samu Aryan yana ganina ya juya min baya. Zama nayi a bakin gado, yadda muka gan shi ya kara karya mana zuciya. Haka nayi sallah isha, na dauki Alqur'ani ina karantawa ya zo ya zauna a gefena. "Kiyi hakuri! Kiyi kuka ki yi kuka ki yi kuka yanzu, gobe sai ki shanye kukan ya zame miki makamin yakar kowa zan koma wurin Ummina, amma ina tare da ku Kamar yadda Inuwarku take haɗe da ku. " Gyada kai nayi. "Na gode sosai Aryan ka gaida Ummarka!"

"Zata ji!" Daga haka ya kwanta barci ya dauke shi, haka na dauko sauran Yaran na musu wanka suka kwanta. Laptop dina na bude na fara aiki, amma faduwar gaba ya hana ni sakewa, mikewa nayi na ga Isma da zaran Aryan yana nan bata zuwa, har sai bayan nan zata zo, shafa kanta nayi naga yadda take kuka hawaye na zuba mata. "Kema kina kewar Yaya ko?" Cusa kanta tayi a kirjina. Haka na cigaba da shafa bayanta, kwantar da ita nayi a gefen Ayaan, ta cigaba da kwanciya a wurin. Dakin Yaya na shiga na zauna ina kallonshi, tsoro nake kada ya tafi haka kawai. Ban san yadda aka yi na kasa barci ba, abin sallah na shimfida na fara nafilla ban san tsawon daren da na dauka ba. Amma har kusan asuba ban yi barci ba, sai da nake karatun Alqur'ani barci ya zo min, a hankali na kifa kaina a gefen gadon.

Barci me nauyi ya dauke ni, barci sosai nake domin kuwa ban san yadda aka yi barcin ya dauke ni ba. Kawai sai gani a filin Arfa, kowa da fararen kaya Abba da wasu mutane uku suma sun dauki harami. "Zainaba gamu nan!" Juyawa nayi na kalle shi, "Bani dubu ashirin dina!" Wani irin murna na kama tare da rungume shi nace mishi. "Ya aka yi ja girma haka kai Tauhid har da tumbi ka ajiye fa!" Na fada ina lallubar jakar kafadata. "Ka ga na barshi a masauki!" "Tow dai idan kika samu ki yi min sadaka da shi!" Murmushi nayi na ce mishi. "In sha Allah." Kallonsu Abba nayi da Mai Martaba da Alhaji Saddam. Sai na rasa dariya xan yi ko kuka duk sun sha harami. "Madalla da y'a ta gari" inji Mai Martaba, kallona yayi yana faɗin. "Sannu kin ji!" Inji Abba Saddam. "In sha Allah zaki iya zaki iya. Kece zaki iya zaki iya Allah ya amintar dake." Gyada kai nayi ina wasa da hannuna, "tow mu dai zamu tayi Allah ya baki sa'a!" Buga kofar da ake yi naji kamar ana kirana daga can nesa, juyawa nayi zan musu magana na ga ba kowa a inda suke, sake buga kofar aka yi na buɗe idanuna, na kalli kofar na hango haske a window yaushe nayi barci har haka da gari Ya waye. "Fulani Babba!" Naji muryan Ijlal, "Fulani Babba!" Tashi nayi a hankali na bude kofar ina kallonsu. "Ki zo muje!" Ta riko hannuna. "Ina zamu?" "Zo muje......

(Ban san me yasa nake kuka a wannan page din ba, ni kaina nasan nayi kewar Iyayena Royal politics ya tab'a ni yau, kowa zai mutu amma kewar masoyanmu abu ne da ba zamu manta ba, Ya Allah ka jikan iyayenmu bakiɗaya, am sorry ban san labarin zai tab'a ni da sauran kowa ba, but ina jin kewa kuma nasan zaku ji kewar rabuwar naku musamman Amintattunku)

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 41

Kukan da nake yi mai dan ƙarfi da sauti, amma ba can ba yasa ya ɗan motsa tare da bude idanunsa. Ƙarar motsin yasa na dakatar da kukan da nake na d'ago kai ina kallonshi, da sauri na isa gare shi. "Yaya!" Sake lumshe idanunshi yayi, turo kofar aka yi na juya ina kallon Ayaan ne tsaye ya shigo. "Malama shi fa Mijinki ko ya farka ba zai iya kome ba wallahi, gara ki barshi yayi ta dogon sumarshi. Idan ya farka sai kin gwammaci da mutuwa kika yi kika bi Babanki, ni kuma ba zan tab'a lamuntar mutuwarki ba. Bayan baki bani hakurin da ya da ce ba. Kalla har yau kunyar kallon fuskata nake a Madubi, gaskiya baki da imani inda masu imani suka bi, ke ba ki ba kuma ba ki san hanyar da suka bi ba, kawai ki ce min Malam Aryan da girmanka, ka yafe min marin da nayi maka!" Yadda ya sake baki yana magana kamar wani mutum can. Murmushi na sake mishi na ce mishi. "Kayi hakuri Malam Aryan!" Wani dafe kirji yayi tare da komawa ya manne a bango, yana haki kamar wanda aka yiwa wani abu. "Ni kika kira Malam Aryan?" Ya kara kallona dA kyau, kafin ya kara leka ni yana duba yadda nake tsaye komawa baya yayi, yana wani kankanta idanunsa, irin ya gano da gaske ne, ni ce ko wata ne kara leka fuskata yake yana ƙara yin baya. "Meye haka?" Gyara tsayuwarsa yayi yana kara kallona. "Dubawa nake ko ba ke bace!" Yadda yayi maganar sai abin ya bani dariya, na girgiza kai ina faɗin. "Kai kanka baka yarda zan baka hakuri a cikin lalluba ba, tow ka ji da kyau ba zan tab'a baka hakuri ba, wuce ka fita ka bar min Yaro yayi barci." Na fada ina hade rai, "Haba yanzu na ji batu, ki bani hakuri ko me zaki yi nasan ba a tab'a sauyawa tuwo suna, sunanki na Fulani Babba ai ba zai tashi a banza ba, dube ki har zaki bani hakuri hala ko fitowa nayi a siffata ba zaku bani hakuri ba." Wani irin takaici ya kama ni, sai kuma murmushi ya zo min nayi kasa da kaina, kafin na d'ago na juya na gyarawa Yaya kwanciyarshi. Na saka mishi Pillow a bayanshi saboda idan ya gaji ya ji dadin kwanciya da gefen. "Aryan je sai da safe!" A hankali na kwanta a dogon kujeran dakin. Kashe wutan dakin yayi sannan ya fita can na ji an sake bude kofar shine dauke da bargo yana zuwa ya lullube ni da shi, ya ce min. "A cire zancen wasa, kina cin abinci bakiɗaya baki da karfi." Murmushi nayi na ce mishi. "Ba na jin yunwa ne ka ji!" Girgiza kai yayi ya ce min. "Ba hujja bane, kin ga yadda kika koma kuwa?" Murmushi nayi na ce mishi. "Ka tafi gida ka bar Ayaan ya huta kana bawa jikinshi wahala da safe sai yayi ta barci, don Allah ka sassauta mishi Yaro ne, yayi kankanta da handle dinka!" Murmushi yayi ya ce min. "Ba zan iya rabuwa da shi ba, domin ba don Allah ya ƙaddara zai rayu ba, a wannan daren da Isma tayi tsalle a kan kirjinsa da kune ba zaku tab'a tsayawa mishi haka ba. Kin san me?" Girgiza kai nayi ina jan bargon. "Idan Mijinku ya farka zaa yi ta haihuwa a cikin gidan nan." Juya mishi baya nayi tare da faɗin. "Barci nake ji!" Nayi kwanciyata, ko da zai fita sai da ya tab'a kaina yana faɗin. "Tsigai!" A hankali na ji wani irin barci mai karfi ya dauke ni, ba don ya min haka ba, da zan kwana ina juyi ne.

Washi gari.

Hayaniyar da nake ji yasa na fito domin tun da nayi sallah asuba, na koma na kwanta yanzu karfe daya saura, sanye da Hijab na fito parlourn Ijlal da Nadiyya ne, a tsaye suna kallon Ikram zata haura sama, ban san yadda aka yi ba, kai ban tab'a sanin ina da wannan zafin namar ba, ji nayi na hada ta da bangon. Dambe sosai ya kwashe mu kamar zamu hargitsa gidan, ji nayi an kwashe min kafa, Nadiyyah ta rufe ni da duka, wannan shine kuskuren da tayi, Ijlal kan komawa gefe tayi tana faɗin. "Nadiyyah kin manta waye a tare da ita Allah ya jikanki Nadiyyah!" Bata rufe baki ba, kawai Nadiyyah ta fasa wani irin ihu tare da gantsarewa, kafin tayi gefe can tana burgima da alamar zane ta ake na kuma samu damar juya Ikram, idanuna ya rufe dukarta nake ina hada kanta da kasa, ban san yadda xan gaya muku yadda nake ji ba, yadda na tsani yarinyar nan kamar na kashe ta kaf gidan aka rasa me raba mu, ashe lokacin Ya Nuraim ya zo da Matanshi Abidah, ai kuwa yana sallama ya ga ta'asar da nake cak ya dauke ni a kanta tare da rungume yana buga bayana, kuka nake son nayi amma na kasa sai ajiyar zuciya nake. Yana shafa bayana kafin na fashe da kuka, ita kan azaba da ciwo tare da zane ta da ake yasa ko ihu bata yi. Jana yayi zuwa Parlourn kasa. Inda Ijlal ta nuna mishi."zauna;" ya fito zuwa waje yaga Ijlal tana dariya ya ce mata. "Don Allah kitchen?" Nuna mishi tayi yana zuwa ya ga a rufe dawowa yayi ya ga key ɗin a center table, ya dauka ya je ya kawo min ruwa. Addu'a yayi ta tofawa kafin ya mika min, sai da na shanye tas, sannan na ajiye goran ina haki. "Wallahi sai ta bar gidan nan, ba zata zo ta karasa mana shi ba." "Ki yi hakuri!" Kukan da nake son nayi ne ya zo min, ina kukan tare da dukar kirjina. "Na kara ganinta sai na kashe ta, domin ita din tauraruwa mai wutsiya ce" yadda na fada ya kara riko hannuna. "List to me!" Ya fada yana bubuga bayana, kuka na sake kawai na rasa gane me yake min dad'i. Sai nake ganin kamar ni daya nake azabtuwa da abinda yake faruwa. Kamar babu me fahimtar kome a yadda nake ji. "Ya isa haka, ga Abidah nan na kawo miki ita." Kasa magana nayi ina kuka ni kaɗai nasan yadda nake jin how im hurting, bit by bit haka nake ji, zama tayi a kusa da ni cikin kulawa take faɗin. "Ya isa haka Fulani Babba, ki ga yadda Yaran suka zuba miki idanu, kin san yadda suke ji a ransa? Please kada ki saka musu damuwa da rashin walwala, sorry my Queen!" D'ago kai nayi ina kallonta. "Did you know..." Kalmar ce kawai amma na kasa furta kome, ji nayi zuciyata tayi nauyi, rike hannuna tayi tana faɗin. "Na miki wata misali da Allah yayi a cikin Alqur'ani?" Kallon ta nake hawaye na zubo min, Ta gyara zama ta ce min.."Allah maɗaukakin sarki ya ce, ayari ne na masu fatauci, sai suka shiga cikin jirgin ruwa, a cikin jirgin ruwan nan akwai hawa biyu ne, sai na kasan jirgin suka ce a basu ruwa zasu sha, sai na sama suka ce a'a ba zasu basu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login