Showing 78001 words to 81000 words out of 157081 words
aka mata da bulala.
Cikin dare mai Babbar daki ta farka tana kallon Ayaan din zaune yana ta wasa har ta shiga ban daki ta fito yana wasa da abin wasansu yadda yake guda abin da kasa zaka rantse wasa. A lokacin Mai babbar daki ta kunna wutar dakin ta d'ago kai, a nan ne zuciyarta kamar zata buga domin idanunsa sun yi fari sol, murmushi yayi ya cigaba da dukan abin har can ya ga ta fara sallah ya sauko daga gadon ya zauna a gefenta, tana idar da sallah ta dauke shi ta cigaba da mishi addu'a har barci ya dauke shi daga nan suka dawo kan gadon suka kwanta. Da safe Ayaanah ta tashe su da kukan banza, zata sha kunu haka mai babbar daki ta hada mata tana sha Itama Ayaat ta farka tana nata ihun haka itama aka bata kafin Ayaaz yana tashi tuwo ya ga mai babbar daki na ci yana saukowa daga gadon ko wanke mishi baki bai yarda ana yi ba ya fara cin tuwon yana mita, yana gamawa ya koma gadon ya kwanta. Sarki a gida sarki adawa yana can yana barci ko farkawa bai yi ba sai karfe goma na safe, ya tashi duk suna parlourn haka ya fito yana kallon mai babbar daki, ya rarrafa wurinta ya zauna yana murmushi. Daukar shi tayi da kanta tayi mishi wanka ta saka mishi irin kayan yan uwansa sannan ta fito da shi ta bashi kunu ta sha ya ci dumamen tuwon dawa, daga nan ya cigaba da wasanshi.
Wato Salmanu Faris bai da kara, kiran Mahaifin Nadiyyah yayi ya gaya masa abinda ya faru, ba sai gashi nan da kanshi ba, a gaban Ubanta ya ce shi bai yarda da ko ciwon da take na karya ne, domin yadda ya saka kafa ta yi yunkurin kashe mishi Y'a ba zai yarda ba, haka aka yi ta fama ga cikinta na tsawon wata shida zai shiga na bakwai haka yake ta fama da shi, dakyar ya hakura ya barta amma ya dauki matakin fita harkanta ya cigaba da kula Ijlal ita kuwa ta kwantar da kai tana kwasar arziki daga jikinsa, domin kuwa duk abinda ta gani zata ce ya sayawa yaran bakiɗaya yadda take niman fada sai abin ya zo yadda take so, ikram da itama ta ga haka da kuɗinta take sayan kayan ta kawowa Mai Babbar daki, sanin cewa ba don Allah suke kome ba. Sai bata taɓa amfani da Kayansu ba, sai dai suna kawowa zata saka a nimo mata kalarsu sak tai kyauta da kayan da suka kawo, Mai Babbar daki tayi tsammanin zan kira na ce a dawo da su, sai da ta kira ni na ce mata ai na yaye su ma su zauna kawai kada a raba musu tunani nan ne dolensu. Abun ya dame ta, ta samu Abba da maganar ta wata ya ce ai zabin yana hannuna, duk abinda na yanke duk ɗaya..
Abin ya dame kowa ganin naki komawa, kuma naki cewa kome. Daga karshe ko wata ban yi ba aka fara yiwa Abba sallama idan har Aurena ne ya mutu suna cikin jerin manema, Abba ya same ni da cewa shi dai yanzu yana son ya sani da auren ko babu, dole aka hada zama bakiɗaya family biyun, aka hada su wuri guda da tambayar me yake faruwa? Abba ya ce musu. "Ni bani da matsala da Salman kawai shi da Zainab ce gata ta fadi bukatarta yau ina bayanta kuma ina tare da ita!" Tunda naji haka gabana ya fadi, shima a bangaren shi ya zuba min idanu yana kallon yadda nake shiru a parlourn. Alhaji Mamman Abba yayari ya ce min. "Fulani Babba kina jin abbank?" Gyada kai nayi ya sake murmushi ya ce min. "Me kike so?" "Rabuwa!" Bakiɗaya parlourn ya dauki salati. Kasa zama yayi ya mike yana wani irin tsuma ya dawo gabana ya zauna ya riko hannuna nayi maza na ja da baya, "kina nufin na rabu da ke?" Sai ya mike ya fara zaga parlourn, ya ce. "No no I can't let you go, wallahi na zan sake ki ba." Ya saka kai ya bar parlourn, ban tab'a ganin auren dole ba sai a wurin Salmanu Faris, can sai gashi da Yaransa suka zube a gabana. "Don Allah ku rufa min asiri da yaran nan, ki dawo rayuwarku!" Girgiza kai nayi na ce mishi. "Ko duniya muka haifa ba zan dawo gare ka ba, na baka lokaci ka yanke hukuncin da ya dace amma ni na hakura da kai har abada, na gaji ne kawai soyayyar da nake maka na hakura da shi sam bana kaunarka kamar da, idan ka ce dole sai na zauna da kai mutuwa zan yi iya hakurin da zan yi kenan." Ya rike hannuna kamar zai yi kuka ya ce min. "Gaya min idan na sake su zaki zauna da ni." Murmushi nayi na ce mishi. "Kana mai da al'amarin nan babban al'amari ka gane ni ko huruul a'in zaka zauna da ita bai dame ni ba, ai matanka ne fa ba Ni na aura maka su ba, taya xan damu ni dai ka taimaka min ka tafi da Yaranka wannan shine shamakin.da suka.hasa mu kawai ka ji ranka kamar namu tab'a haduwa ba a duniyar nan shi yasa na zabi na bar maka su na tafi abina. Ina da sauran rayuwa bal zan iya zama da kai ba, koma me nene na hakura da shi ka yi hakuri nima na tafi." Ban yarda nayi kuka ko wani abu ba da zai nuna karaya ta amma naki sai murmushi, wannan murmushin da nake gani yake kamar farin ciki nake, murmushi nake bakiɗaya yan parlourn babu wanda ya iya magana mikewa nayi xan bar parlourn ya taso ya rungume ni, baki daya suka sunkuyar da kai saboda kunya, "ina sonki ba zan iya rabuwa da ke ba, ina jin yadda hawayen shi yake sauka a gadon bayana. Haka na danne kukana na kwace kaina a jikinshi, na bar parlourn da gudu, durkushewa yayi a wurin, yana shashekar kuka......
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 29
Yadda yake shashekar yasa kowa a parlourn jin wani irin yanayi mara daɗi, domin abin ya zo musu ba zata. Duk abinda ya faru laifinsa ne bai da wani katabus a gidansa, sai yadda matansa suka yi da shi daga zarar mace ta saka shi a daki ta d'aga mishi kafa tow shi a wannan bangaren zai iya mata duk wata alfarmar da zata bukata gashi nan kiri-kiri zai rasa matarsa haka kowa yake gani, amma ba asan yadda shi yake ji ba, ba a san yadda yake fuskanta ba. Duk kokarin da yake yiwa matansa ace da irin sakayyar da zai kare kenan.
Mai Babbar daki ta fara barin parlourn, kafin Abbana ya fara barin parlourn, a kasan ranshi tausayinsa ne ya cika mishi rai, ba dad'i amma shi ya janyuwa kanshi. Sam bai da lissafi kome nashi, sai anyi mishi mutum kamar ba namiji ba, haka suka bar shi a parlourn, a yau yayi tir da alawadai na jarabar da take cinsa da Idan ya ga mace bai da hakuri yau a gaban jama'a Zainab ta gaya mishi ba zata zauna da shi ba kenan tun tuni alfarma take mishi, ba shi ya mata Alfarma zama da ita ba.
Har Abba ya fito muka bar gidan, naki yarda nayi kuka ko wani damuwa. A dab zamu shiga unguwarmu Abba ya ce min. "Ina ga ya kamata ki fuskanci wata damar daya!" Kallonshi nayi kafin na cigaba da kallon gefen. "Ba laifi bane niman saki, amma abinda zaki fuskanta zaki samu irin salmanu Faris? Ba dole nake miki ba fa, kawai ina nazarin yadda na ganshi ne yanzu da yadda na bar shi yanzu. He love you so much. Zaki iya fushi da tsaya akan ra'ayinki amma babban abinda nake son ki fahimta shi ne, Allah yana yafe mana idan muka roke shi balle mutum, ban ce lallai ki koma gidan Mijinki ba, kina da damar jan zarenki amma ki sani dama daya ce idan ka rasata har abada karasa abu me muhimmanci, yana son zama dake har karshen rayuwarshi amma bai san yadda zai iya zama dake ba, sannan ba umarni nake baki ba shawara ce. Ban ce lallai ki koma ba, ban ce kuma ki ga kamar ban miki adalci ba." Daga haka ya bude min kofar na fita, zuwa cikin gidan lokacin da na shiga cikin gidan babu wanda ya min magana domin yadda na haɗe rai, yasa babu wanda yayi min magana.
Bayan Abba ya shigo yake gaya musu yadda muka yi, sai shiru suka yi aka rasa mai mai magana, ni dai na yanke hukuncina ba zan koma gidanshi, ya jima kome bai same shi ba. Kwanaki biyu a tsakanin sai ga Bilqis da Daularh har da Salim, tunda suka zo na zauna a parlourn ina jinsu ga Yaran an kawo, nayi kewarsu amma na danne kome domin na kwace kaina. "Fulani Babba ki rufa mana asiri kada mu rasa dan uwanmu!" Murmushi nayi na ce musu. "Wane mutum inji mutuwa, kawai dai ina buƙatar ya sawwake min ma huta ne!" Zaro idanu Bilqis tayi tana faɗin. "Ba wani hutun da zaki yi, ka yi hakuri dai a koma a a rungumi juna ai yanzu mun zama yan uwan da dangin juna." Murmushi nayi domin na lura basu fahimci waye ɗan uwansu ba. Haka suka gama magana Salim ya ce min. "Kafin ka dauki duk wani step na rayuwa yana bukatar hakuri da kuma nazarin ina zaka saka kafarka, na zo on behalf of My kids ki yi hakuri ki duba lamarin nan, ban san yadda kike fuskantar matsalarki ba, but i feel your pain, ki yi hakuri ki yi nazari!"
Kaina a kasa ban yarda na d'ago kai ba, domin duk abinda ya fada gaskiya ne amma kuma bana son naji kamar dole aka yi min, bayan tafiyarsu sun bar min Yaran suka zauna a wurina.
****
A yadda yake jin zafin Zainab taki dawowa, ya tattara ya bar gidan bakiɗaya abu daya yake ta kokarin yi shi ne barin kujeran mulkin domin ya fahimci babu wani abinda yake iyawa banda shirme ba abinda yake yi. Kwanakin da suka shude sai da Mai Babbar daki ta kira shi tare da yi mishi barazanar saka mishi ba, ya dawo hankalinsa. Ranar da ya dawo kuwa Nadiyyah mai fama da ciwon kafa ita ta fara amsar hukuncinta, domin bakiɗaya ya kore su a gidan, ya ce baya kaunar ganinsu. Ya kuma barsu da Yaransu domin Zainab ta koya mishi ita bata cikin matan da zai yiwa barazana da Yaran da suka haifa.
Nadiyyah kan wurin mai babbar daki ta dawo, domin cikinta ya tsufa tayi nauyi sosai. A wannan tsakanin mai babbar daki watsar da su tayi itama da take zaune don Yaranta ne domin ko Khairat an mai da ta wurin dangin Ubanta. Haka mai babbar daki ta saka ya mai da Nadiyyah da sauran matan ta ce mishi. "Haka zaka zauna da su ba yadda ka iya dasu, wacce kake gogawa kashin kaza bata nan balle har ayi tinanin ita take koransu, gara ka koyi magance matsalolinka ranka shi dade."
Haka ya mai dasu, bakiɗaya suka dawo a hankali kwanaki suka cigaba da tafiya har aka samu wata gudu zuwa wata biyu, wanda yayi daidai da cikin Nadiyyah wata tara cif, ta gefe guda da kanshi yayi ta bin manyan hakimai da dagatai suna roka mishi Abban Zainab, ya bashi Zainab ya gyara, shi sai Malam Junaid bai ce musu kome ba, hatta malamai yan uwansa sai da suka saka baki, lamarin har Maradi wurin Dangin Malam Junaid haka ma Maluma da Umma duk inda suka shiga maganar kenan ayi hakuri a mai dawa Mai Martaba Matarshi.
**
Idan nace ban jin takaici nayi karya domin kuwa ba daren da ba zan amshi kiran mutane wasu daga ƙasashen waje wasu kuma a cikin gidan kasar hatta Ilham ta kirani tana kuka nayi hakuri, bakiɗaya aka daure ni da jijiyana, ina zaune Babban limamin masallacin jami'ar ya zo bayan sallah juma'a, yayi min nasiha tare da cewa. "Zuwa yanzu ya dace ki san yadda kike da daraja a zuciyar Mijinki da alumma, aurenki da shi kamar wata babbar nasara ce da Allah ya bawa Mahaifinki, yana da kyau ki yi hakuri ki rungume kome kamar ba kome ba, sannan ki kara yawan addu'ar da kike yi a yanzu da haka ya faru wallahi nayi imani da wanda rayuwata da mutuwata take hannunsa, Salmanu Faris ya biyu yadda kike so, domin ko shekaranjiya sai da aka danne shi akan wata tashin hankalin da ya faru tsakanin matansa biyu da suka jiwa kansu ciwo, sannan wani abin dad'i Mahaifinki dai shi ya iya tankwara shi suka koma dakinki su, kin san saboda me yasa? Saboda girma da darajar da kike da shi a zuciyarshi. Ya yarda ya amince duk abinda zai yi matuƙar mahaifinki zai ce a'a zai hakura da shi. Har yau Mahaifinki bai ce mishi ya sake ki ba, da zai gaya mishi haka tow sai dai ya hakura da kome akan ya sake ki, tsoron kada mahaifinki ya ce mishi ya gaji ta sake ki yasa yake mugun kiyayye abinda za a mishi magana a kai, mutumin da ya zaɓi shirun mahaifinki da maganarshi ki duba mana,sannan ki duba girma da Soyayyar Uwa da takewa danta Mai Babbar daki tana bayanki kamar rai da rayuwa akwai abinda ya kai hana halacci? Wadannan mutane biyun sun miki kome kuma ya kamata ko biya su, ke mace ce kin san hanyar da zaki kwaci kanki mun yi miki duk wani abinda zamu miki na goyon bayanki. Ki nuna ke din babba ce domin dattako kawai zaki yi musan tabbas min haifi Y'a mace kuma mata mai halin manya!"kaina a kasa na rasa mai ke min dadi nasiharshi tana shiga jikina a wata uku zuwa hudu da nayi tabbas na ga kauna da soyayya daga wurin dangina da danginsa har da wasu mutanen, na gyara zama na ce mishi. "Baba liman zan koma gidansa!" "Alhamdulillahi Fulani Babba a kodayaushe ita babba ce. Ina jin ki kamar bakin nan da magana."
"Baba liman ka gaya mishi ina da sharadi biyu, zuwa uku." "Ina jin ki Yar nan!"
"Sharadi na farko kada ya sakani cikin sha'anin gidansa, sharadi na biyu kada ya takura min akan lallai sai na shiga matsalar Matanshi da Aurenshi! Sharadi na uku kowacce mace ta rike Yaranta nima na rike nawa kowa ya zauna a inda yake!" Gyada kai yayi ya ce min. "In sha Allah an gama wannan!" "Nima Kuma zan yi kokarin fita harkan kowa har da shi kansa!" Haka ya tafi yana saka min albarka, da na koma cikin gidan na gayawa Umma da Maluma yadda muka yi Hajja tana Maradi bata san meke faruwa ba, haka Umma da Maluma suka yi ta min fada da babu ruwana da matanshi harkan gabana da Yarana ya ishe ni. Gashi Maluma taji dama ni da Yunus ina maganar komawa master haka dai ya mata dad'i ta ce mana."ko ba kome yanzu baki da lokacin kowa Yaranki suna wurin kakansu idan kika tafi kika dawo zaki huta baki san m yake faruwa ba, wannan horon da kika yi ba shi zai baki damar kara sakewa da shi ba, a'a tsayawa zaki yi ki yaki kanki da matansa ya san fa kina da daraja."
Ba laifi Maluma sun wanke kin kaina, haka ya turo min sako da cewa. *Na amince da sharuddanki?* Ban yi mamaki ba domin nasan zai iya amsa. Haka Mai Babbar daki da ta ji sai da ta kirani tayi ta min addu'a kamar har da kuka take wallahi dai da jikina yayi bala'in sanyi domin na ji tausayin matar nan ya cika min rai, ita nata jarabawar kenan. Kwana goma a tsakanin sai gashi da Yamma da yake na mai da musu yaran suna ta kiran Jadda wato Mai Babbar daki, na mai da musu yaran nima bana da lokacin su sai na barci. Lokacin da ya shigo parlourn baki ya zauna yana wasa da Yaran da suka shigo cikin gidan Ayaanah tana ganina ta fara murmushi tana min wasu irin magana, ɗaukarta nayi na ce mata. "Mamana ban san Yaren da kike ba wallahi wannan Yaren naki sai Mai Babbar daki ita kaɗai zata fassara mana!" "Maluma ta ce mana." "Ai fa ina ruwan tafinta, ki kai mishi ruwa mana!" Sharewa nayi kamar ba zan je ba can na dauki goran ruwan na nufi bangaren da yake na ajiye mishi ba kome na kome haka ya dauka ya sha yana tsammanin zan gaishe shi nayi wani fuska. "Barka dai Fulani Babba!" Nan ma kamar ban ji ba na share. "Ya hutu da jin dadi?" A lokacin na d'ago kai na zuba mishi idanu. "Abinda ya kawo kenan?" Murmushi yayi yana faɗin. " A'a kawai nazo na kara bada hakuri ne, sannan idan da hali a yafe min!" Shiru nayi na cigaba da jin sa har ya gama maganarshi. "Baki ce kome ba?" "Allah ya kyauta!" Daga haka na ja baki na tsuke kamar me, can ya ce min. "Maganar komawanki makaranta shima na amsa!" Da sauri na kalle shi kafin na dauke kai, ko jiya Aunty Shukrah take gaya min an kara girman mall dina saboda yadda yake ake cika. Musamman idan lokacin sallah ko Kiristamas da kuma lokacin Mauludi ana sayan kaya. "And!" Zuba mishi idanu nayi wnada yasa shi dole yayi shiru. "Na ji!" Na fada ban kara cewa kome ba. "Yaushe xaki koma?" Takaici ne ya kara kamani ban ce mishi kome na na cigaba da wasa da yatsuna. "In sha Allah ba zaki kara kamani da laifi ba." "Kana