Showing 129001 words to 132000 words out of 157081 words
wani abu da na fahimta idan ka tara mata kowace da irin tarbiyyar da takewa iyalinta. Muna zaune da Yaran a parlourn kasa, Princess ta shigo ta zauna tana shan chocolate, Ayaat da Allah ya daura mata kwadayi tana gani tayi ta binta, ita kuma tana wani ture yarinyar ina kallonsu amma sai na ki basu attention dina, ina son ga yadda sauran yayun zasu yi. Ina kallon Ayaaz ya tawo tare da cewa. "Wuce ki zauna idan ta baki sai na gayawa Ayaan kada ya baki kayan dad'i " jin haka sai ta koma wurin Ayaanah da bata san me suke yi ba. Kallon Ayaaz tayi tana faɗin. "Mommy ta ce ku ba Yaran Daddy ba ne, Mammy kawo ku tayi." Kallon Yarinyar nayi da dukkan zuciyata. "Kika ce me?" "Mommy da Kawarta Aunty Linah ta ce su ba Yaran Daddy ba ne!" Sai nayi shiru, ban ce kome ba sai na tashi na bar su zuwa bangaren Nadiyyah da take ta fama da yogo, tana ganina ta sha jinin jikinta duk da bata san me ya kawo ni ba, amma tayi mamakin ganina, na ce mata.."me kika gayawa Saadiyyah ta gayawa Yarana?" "Ban gane ba?" Lekowa nayi na kira Princess din. Sai gata kuwa ta zo, na kara tambayaarta ta maimaita da kwarin gwiwarta. Ba sai ga Uwar tana zare idanu ba. "Ni yaushe ba faɗa!" Yarinyar ta ce mata. "Mommy ke da Aunty Linah!" Ganin yadda zata karyata yarinyar na kwashe ta da mari sai da ta zauna dabas. Na kara gabanta kamar na rufe ta da duka, kawai na ja jelar gashinta da karfi na ce mata. "Duk abinda kike yi ina sane fa, don ta tsamoki daga gutte ba yana nufin kina da tsafta ba ne, kika sake gayawa Yarki magana tayi approaching Yarana da shi, ni nafi Ijlal hauka tun kafin na auri Mijinki, ba yau muka fara ba ki sake gaya mata hauka wallahi wai na yi maganinki!" Ta ture ta ta fadi, fita nayi na barta tana ihu tare da kiran shi da ya tafi Fada. Wurin karfe biyar ya tara mu tare da tambayarmu me ya faru, da yake munafuka ce tsara yarinyar tayi ta sauya maganar, ni kuwa na zarewa yarinyar idanun sai gashi ta fada har da yadda Uwar ta shirya mata maganar, a yau yayi abin da ban tab'a zata ba, saboda ya mata tas sannan ya ce mata.."duk bala'in fitinar Ijlal ta fiki sanin ciwon kanta wawuya jaka!" Mikewa Ijlal tayi tana faɗin. "Ai gara a gaya mata kanta baya ja wallahi!" Daga haka muka barta sai ta ce ai mun hade mata kai, musamman ni baya son yayi min fada ko yayi min tsawa yanzu ya koma bayan mu da Ijlal.
Kamar yadda Aryaan ya fada sai na fahimci hatta ilimin addini gaskiya Ijlal babu, haka yasa na bata shawara tana bibiyar zauren Muslunci da ake budewa a telegram domin koyarwa addinin Muslunci, wannan abin ya zo min ba zata, duk da na fahimci wani abu Ijlal tana da zafin kishi. Duk ranar da abin ya motsa ko ɓangarena bata zuwa sai tayi kwana da kwanaki bata min magana ba, amma zata saka akawo Yaran wurin Aryaan, haka na dauke kai daga damuwarta, ana haka tafiya ta kama shi Scotland,.aka yi kuri'a wani ikon Allah sai ya fada kan Ijlal. Yadda take ihu da Murna sai ta bani tausayi, daga can zasu tayi Umura, ai kuwa sai ga Nadiyyah tana ihu bata yarda ba dama an shirya cutar ta, a sake kuri'a, ya ce ba zai sake ba tunda Allah ya ƙaddara da Ijlal za a tafi ba makawa haka ce zata tabbata, wani ikon Allah ana sakewa still ita ce dai zata nan ma ta ce bata yarda ba, aka sake yi garin ruwan idanun ta dauki na gaban Ijlal ita kuma Ijlal ta dauki wanda yake gefe dama tun farko da na ga ita ce ban kara cusa kaina ba, tana dauka ta bude ta mike tana faɗin. "Sai dai ayi kare jini biri jini domin wallahi ba xaka tafi da yar iska wata duniyar ba;" ina jin haka na bar parlourn ba sai ga rigima kamar zai make ta ba, ni ban san yadda suka kare ba, ina zaune bayan sallah asuba sai gashi ya shigo ina azkar ne, zama yayi yana kallon yadda nake ta addu'a, ai ban ci ta zama ba barawo ya saci gudu, yana ganin na gama addu'a, ya zauna yana jana da hira, ni kuwa barci nake ji na haura gadona nayi kwanciyata. Kallona yayi ya ga ina jan bargo na ce mishi. "Idan zaka fita ka kashe min hasken dakin!" Na rufe idanuna. "Zainaba nazo wurinki ne fa!" "Hmm ina jinka!" "Dama akan maganar tafiyar nan ne ko zaki taimaka min da kula da Yaran nan kafin nazo!" Wani irin dariya na rainin hankali ne ya zo min, na ce mishi. "Ka tafi idan na tashi sai ka tunbube ni naji yadda zan duba lamarin." "A'a ki tsaya mu yi magana!" "Bata da dangi ne? Sannan kana da yan uwa fa, ni na daina goyon dan wani ku san yadda zaku yi sai dai ko ta hakura da tafiyar ka tafi da Nadiyyah tunda ita Iyayenta suna Abuja!" "Don Allah ki taimaka min!" "Kul ki amshi yarta zumuncin da ke yi ma ya tsaya a haka, amma rikon Yaranta zai kara raunana dan zamantakewar da kuke, sannan ba zaki zauna lafiya ba domin shaid'aniyar kanwarshi zata lalata miki rai a kai, gaya mishi kai tsaye ba zaki rike ba ya nime wasu!" Inji Aryaan, ina fadar haka ya sha zuciya yayi waje, Aryaan ya ce mishi. "Hotiho aikin kenan mayen mata, mutum sai kace taure!" Daukar pillow nayi na wurgo mishi ya b'ace a dakin, na cigaba da nazarin kalman Yaya kafin barci ya dauke ni, ba sai ya kai zancen wurin mai babbar daki ba, itama anan ta ce a'a ya kaiwa danginta Irin azabar da nasha akan Yaran kowacce ta rike Yaranta babu amfanin takurawa juna, ai kuwa Aneesah ta ce musu."amma ace shi da gidansa bai isa yayi katabus ba, Ikhlas ta mallake kowa wallahi ka zuba mata idan ta ga ba sarki sai Allah zata kula da su " murmushi yayi ya ce mata. "Zainaba kaifi daya ce, idan ta ce a'a kaf duniya idan na Marigayi ba, babu me iya sauya mata abinda ta saka kanta, don haka kada ki yi tunanin zata kula su, don zuciyarta daya ce idan ta ce eh , eh ne. Idan ta ce a'a, a'a ne, ke zaki iya sauya ranki da wasu abubuwan Zainaba bata sauya abinda take so da wnada bata so. Bata karya kuma bata zalinci, Zainaba mutum ce sukutum da guda!". Yana gama fadar haka ya bar parlourn, duk yadda yake tsammanin abin ba haka ba ne, karshe sai ya nimawa Yaran visa, ba iya su ba hatta ni sai ya shirya tafiyar da mu bakiɗaya, amma ban da Nadiyyah, Wayyo Allah na, sai ga gurmi ya tashi. Ita kanta Ijlal ɗin sai da na fuskanci bata ji dadin yadda ya shirya tafiyar ba, shi dalilinsa na shirya tafiyar Yaransu saba da juna, ya ga duk wannan rigimar amma Amiratul Zaitunah tana rigimar Aya, haka yasa a matsayinsa na likitan ƙwaƙwalwa ya fahimci har da Yaran suna taimaka mata, sai ya haɗa tafiyar, da yake tunda ya mata duka take bala'in tsoronshi, sai da ta kasa hakuri ta mishi magana muna cin abinci. "Abban Amirah suddenly sai ka haɗa tafiyar da su Ayaanah da Mamansu?" "Eh nayi haka ne don kaina, sannan bata shiga harkan kowa ba, kowa ma ya yi abinda zai iya idan ba zaki ba, zaki iya hakura da tafiyar. Ita kanta bata san da tafiyar ba, sai yanzu da kika faɗa ta ji." Kishi halal ne ban ga laifinta ba, shi mafitar shi da ta Yaransa take bi, bayan nan bai cika damuwa da yayi wani taking action akan irin wannan abin ba, amma akan lafiyar Yarshi yana ƙoƙarin inganta hanyar da zata samu lafiya. Sannan maganar gaskiya ban san da tafiyar ba, taya zan sani yanxu fa tunda Aryaan ya saka shi a gaba yake tabuka abin arziki baya sauraren kowa sai ranshi, don a baya ko zan cutu zai min abu kuma ta hau kaina, amma yanzu baya yi sai ma ta share ni yaki kula ni, sannan akaina ya tsaya yana cin Uban Nadiyyah da duk wnada zasu ce yafi kula da ni, akansu sai na samu sauki da sassauci akan lamarin gidansa, amma da nace ba zan rike mishi Yara ba sai da ya ji haushina tare da kaurace min a shimfida, idan na shiga dakinsa sai ya tsiro aiki. Haka xan gama kwana biyu na a tsaye, da na fahimci haka da girkina ya zagaye sai na hakura da zuwa dakinsa abin har mamaki yayi ta bashi, sai ga zancen kuma zai tafi damu zuwa Scotland,.
Bayan mun watse ta fara faɗin. "Fisabiilillahi ke Mammy baki da kirki, kawai sai ki shiga tafiyarmu! Anya Makaminki bai tsaya akanki ba!" Murmushi nayi don nasan magana ta gaya min na ce mata. "Malami dai, ai na wuce wannan ajin, ni kuma bani da lokacin biyan kudina a banza!" Na fada xan wuce ta kuma cewa. "Amma kin ci lokacinki me yasa zaki amince da tafiyar?" Sai na fahimci ita fa tana son hutawa da mijinta ne, ni kuma ina fama da kaina, bana jin dadin kaina da jikina. Na ce mata. "Ijlal ki ce mishi ya soke tafiyar bana son damuwa!" Zare idanun tayi tana faɗin. "Kambu amma kin ce ya kashe ni da duka, kaf cikinmu ke ce baya yunkurin duka fa, amma daga ni har Nadiyyah dukarmu yake musamman ma ni!" "Ayya!" Na fada ina barin parlourn, na wuce dakina na kwanta jikina ciwo yake ga abincin tashin zuciya ya sani na kwanta ina lumshe idanuna. Shigowa yayi ya same ni a dogon kujeran parlourn. "Sannu kinji na fahimci kamar bakya jin dad'i!" Ya fada yana shafa tafin ƙafana. Yana min sannu. "Ni lafiyata lau!" Na fada ina kallon Ayaat da ta shigo tana faɗin. "Mammy tea." "Ki je Madinah ta haɗa muku!" Na cigaba da lumshe idanuna. "Uric acid!" Ya furta, ni dai ban ce mishi kome ba, ya cigaba da matsa min har barci ya dauke ni, gyara min kwanciya yayi yana faɗin. "Allah ya baki lafiya, amma kuma ina tsammanin ciki ne!" Barcin da bai yi nauyi ba haka na bude idanuna ina kallonshi, cikin lafiya hauka ne.
Ganin ban da niyyar magana yasa shi fita, can ya dawo yana faɗin. "Saura kwanaki ƙalilan ayi bikin bude asibitin duk da anyi amfani da shi zamu bude shi amma!" Ban ce mishi kome ba, haka ya cigaba da niman magana yadda ranshi ya so sannan ya bar dakin, maganar shi na ciki ne sai ya saka ni a cikin damuwa ciki kuma? Yaushe aka hadu har an yi cikin? Shiru nayi sai kuma na mike na nufi asalin dakina da yake sama na shiga ban daki, na bude first aid box na ciro abin test na ciki, na fara gwadawa, sannan na cire shi zuwa gobe da safe. Dukka dukka ko wata ba'ayin ba, wancan satin nayi period tunda ya cire min abin, sai tsoro ya kama ni bayan nayi na kwanaki uku, ranar da Ijlal take girki na fara, na gama ranar da ya dawo dakina, gabana ne ya fadi na dafe goshina. Shi kenan na kwaso magana. To kuma idan ba shi bane? Yau bakiɗaya sati uku kenan zuwa hudu. Abin sai ya kara min takaici da ciwon da nake ji, haka na kwanta ina jin zazzaɓi kamar an kara min. Kwanakin da yayi ya dawo dakina aka bude asibitin, tun ranar da nayi test ban duba ba, sai yau da muka hadu da Salim ya kasa boye damuwarshi a gaban Mutane yake tambayata. "Baki da lafiya ne? Meke damunki? Kin ga likita kuwa? Ko zaki je asibiti ne!" Sai kunya ya rufe ni na ce mishi. "Lafiyata lau na gaji ne abubuwa sun min Yawwa!"
Daga haka na bar zancen bayan fitarshi Bilqis ta ce min.."Duk wanda ya ganki dole ya damu fuskarki ta rame, kin yi wani irin haske kamar baki da jini!" Anan ne na zargi kaina, haka yasa ina dawowa gida na shiga ban daki na duba test din Aryaan ya ce min. "Kada ki yi sauri ciki ne ma fa" da wani mamaki da tashin hankali na zauna ina jin kamar zuciyata ta fita, wani abu da na kasa fahimta ina son Yaya amma haka kawai nake jin kamar Yaran da na haifa da shi is ok ba sai na kara tila mishi wasu Yaran ba, sai na ji ni kaina i hate myself, balle shi mutumin da bai da future balle na Yaranshi.....
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 49
" Ki ma bar wani tunanin banza domin lafiyarki da rayuwarki tana da muhimmanci, idan kika cigaba da sakawa ranki damuwa zai shafi lafiyarki da ta Yaranki, mutum irin Mijinku sai addu'a domin bai da lissafi kamar kowa idan yana tare da ke tow kina bin ra'ayinshi ne, idan baya tare dake wancan tana bin ra'ayinshi ce. Yana da kyau ki yi hakuri duk abinda yake faruwa zai wuce kamar yadda iska yake kwashe kura ya tafi da shi, haihuwa kuwa zaki yi da shi. Hakuri da juriya zaki kara akan wanda kike yi." Hawayen da nake dannewa ne ya zubo min wani chapter ya kara buɗewa a rayuwata, ni na gaji wallahi iya gajiya na gaji.
"Haka zaki yi hakuri ba a gajiya da bautar Allah, da shiga rai wasu abubuwan suke amma idan kika yi hakuri zai wuce abu daya zan yi miki ba zan tab'a barin wani ya cutar dake, wannan shine alkawarina akanki!" Haka nayi kuka sosai, bayan na gama na zauna a parlourn ina shiru kafin na cigaba da kwanciyata a parlourn, bargo ya dauko ya lullube ni da shi yana faɗin. "Yau naga barci kike son yi a parlournki." Gyara kwanciyar nayi na kwanta kamar yasan dama ina son daukar bargon yadda na cigaba da kwanciyata a wurin Yaya ya shigo da Yara suka yi ta min ihu kamar nayi kuka na kalle shi da Yaransa kamar na rufe su da duka. Sai hira suke yana biye musu amma hankalinsa yana kaina.
"Kamar bakya jin dadi muje asibiti!" "A'a da sauki!" Na fada mishi domin haushi yake bani bana kaunar ya kara min magana ji nake kamar na rufe shi da duka, ni dai yanzu haushi yake bani, kwanciyata a parlourn sai ya fara damuwa domin hayaniyarsu, don wasa yake da Yaran kamar yaro shima, a hankali na lallaba tsumar rayuwata na gudu daki na barsu. "Ka zauna cikin yara kana da shiririta, sakaran sarki!" Tashi yayi zaune yana kallon Ayaan da yake gabza mishi harara. "Kai kasan waye ni?" Yaya ta tambaye shi, "mtseew kai din banza Sarkin da bai amsa sarki ba, idan kayi wasa sace ka zan yi na shiga jikinka." Jin haka sai ya share shi. Cikin jin haushi Aryaan ya ce mishi. "Ya zaka yi mata haka?" Share Aryaan din yayi domin bai fahimci akan me yake magana ba, ya ce mishi.."me yasa zaka kawo Jakadiya cikin lamarin gidanka!" Kamar wanda aka mitsine shi ya tashi zaune ya ce mishi. "Ba ruwanka da lamarin gidana! Abinda nayi niyya shi zan yi!" Kamar ya rufe Salman da duka, ya ce mishi. "Lamarin gidanka kace? Kasan aikin da muka yi kana kwance? Kasan yadda muka rage fitinar cikin gidan nan? Kawai daga zuwanka zaka lalata mana shirinmu?"
"Na saku ne? Na aike ku ne? Kasan abinda nake shiryawa ne? Kasan me ka koma duniyarku ka kyale ni da mulkina, ba abinda ya dame ku." Daga haka ya mike ya shigo dakin ya tsaya a kaina zai zazzaga min fada ji yayi an shake wuyarshi. Wani irin ihu Aryaan yayi da karfi wanda yayi sanadin da na bude idanuna da ƙarfi tare da wani irin ciwon kai da na ji ƙwaƙwalwata tana wani irin ciwo da zafi lokaci guda, haka jini yayi ta zubowa daga hancina. "Aryaan!" Na kira sunanshi a hankali, juyawa yayi ya ga yadda nake ƙoƙarin tashi, sake Yaya yayi ya tawo da gudu, ya durkusa a gabana. Yana na xuwa ai kuwa bai yi wata-wata ba kawai ya fada jikin Yaya. "Sannu tsigai!" Ya fada tare da riko ni yana faɗin. "Sannu Zainab! Ni ne Aryaan ba shi bane!" "Ka fita ka bar shi ka ji!" "A'a Zainab kan yake ciwo ko?" Ya fada tare da kama kan ya rike da karfi yana min addu'a, har sai da ya ga nayi shiru barci ya dauke ni, sannan ya kwantar da ni. A hankali yA fita a jikinshi, ya zuba mishi yana kallona. Kamar wanda aka yiwa wani abu sai gashi yana kallon gefe da gefe, tabbas ya ganni ya kuma ga wani sabon duniya da ya zauna a cikin idanunsa. A hankali ya rike hannunta yana shafawa. Hawaye ya zubo mishi, shigowa Ayaan aryaan ya shiga jikinshi. "Kada ka kaita asibiti, ba zasu iya kome kanta ba, domin muryata ta ji!" Kallon Ayaan yayi. "Yanzu ka fahimci baka da wani amfani a rayuwarta? Duk yadda zaka zauna a rayuwarta cutarwa ce, don Allah ka tafi daga rayuwarmu!" Wani irin kallon yakewa Salmanu Faris, kafin ya ce mishi. "Kishina kake don ina tare da ita?" Haushi ya ƙara kama shi ya hayayyako mishi. "Sai ka yi sahorami, kuma ba zan tab'a fita ba wallahi ka ji na gaya maka. Sai dai ka mutu."
"Na gaya maka ka fita kafin na saka a maka ruki'a." Wani kallon banza yayi mishi. "Sai dai a maka domin na rantse ana