Showing 111001 words to 114000 words out of 157081 words

Chapter 38 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

56

na dauko sauran Yaran na musu wanka suka kwanta. Laptop dina na bude na fara aiki, amma faduwar gaba ya hana ni sakewa, mikewa nayi na ga Isma da zaran Aryan yana nan bata zuwa, har sai bayan nan zata zo, shafa kanta nayi naga yadda take kuka hawaye na zuba mata. "Kema kina kewar Yaya ko?" Cusa kanta tayi a kirjina. Haka na cigaba da shafa bayanta, kwantar da ita nayi a gefen Ayaan, ta cigaba da kwanciya a wurin. Dakin Yaya na shiga na zauna ina kallonshi, tsoro nake kada ya tafi haka kawai. Ban san yadda aka yi na kasa barci ba, abin sallah na shimfida na fara nafilla ban san tsawon daren da na dauka ba. Amma har kusan asuba ban yi barci ba, sai da nake karatun Alqur'ani barci ya zo min, a hankali na kifa kaina a gefen gadon.

Barci me nauyi ya dauke ni, barci sosai nake domin kuwa ban san yadda aka yi barcin ya dauke ni ba. Kawai sai gani a filin Arfa, kowa da fararen kaya Abba da wasu mutane uku suma sun dauki harami. "Zainaba gamu nan!" Juyawa nayi na kalle shi, "Bani dubu ashirin dina!" Wani irin murna na kama tare da rungume shi nace mishi. "Ya aka yi ja girma haka kai Tauhid har da tumbi ka ajiye fa!" Na fada ina lallubar jakar kafadata. "Ka ga na barshi a masauki!" "Tow dai idan kika samu ki yi min sadaka da shi!" Murmushi nayi na ce mishi. "In sha Allah." Kallonsu Abba nayi da Mai Martaba da Alhaji Saddam. Sai na rasa dariya xan yi ko kuka duk sun sha harami. "Madalla da y'a ta gari" inji Mai Martaba, kallona yayi yana faɗin. "Sannu kin ji!" Inji Abba Saddam. "In sha Allah zaki iya zaki iya. Kece zaki iya zaki iya Allah ya amintar dake." Gyada kai nayi ina wasa da hannuna, "tow mu dai zamu tayi Allah ya baki sa'a!" Buga kofar da ake yi naji kamar ana kirana daga can nesa, juyawa nayi zan musu magana na ga ba kowa a inda suke, sake buga kofar aka yi na buɗe idanuna, na kalli kofar na hango haske a window yaushe nayi barci har haka da gari Ya waye. "Fulani Babba!" Naji muryan Ijlal, "Fulani Babba!" Tashi nayi a hankali na bude kofar ina kallonsu. "Ki zo muje!" Ta riko hannuna. "Ina zamu?" "Zo muje......

(Ban san me yasa nake kuka a wannan page din ba, ni kaina nasan nayi kewar Iyayena Royal politics ya tab'a ni yau, kowa zai mutu amma kewar masoyanmu abu ne da ba zamu manta ba, Ya Allah ka jikan iyayenmu bakiɗaya, am sorry ban san labarin zai tab'a ni da sauran kowa ba, but ina jin kewa kuma nasan zaku ji kewar rabuwar naku musamman Amintattunku)

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 39

Murmushi nayi mata na ce mata. "Yanzu ma sai ki cigaba da bibiyarsu ai!" Na fada ina kallon Ayaan da yake kallon Jakadiya. "Me kika sani akan mutuwar Attahiru Shehu Yayari?" Dariya ta saka tana kallonmu kafin ta ce min. "Ki godewa Allah da wannan shaidanin yana baki kariya." "Allah dai yake kare ta, ni bana mata kome, yanzu ba gashi kin same ta idanunta biyu ne ai gayawa mai rumfa ba tokare take, kin ga duk wanda zai zo wannan matakin gaya min ai baka isa kare shi ba domin tana da Allah." "Karya kake har da kai a cikin masu kare ta da kai da magen nan shi yasa na siffantu ta yanayin magen na rama!"

Kallon Juna muka yi da Aryan kafin na ce mata. "Ni me nayi miki?" Shiru tayi tana zare idanu. "Baki da amsar me na miki ne?" Shiru tayi tana kallon kasa cike da barin kunya kafin ta ce min. "Ni dai ki kyale ni tunda ban cutar dake ba." "Jakadiya zaki cutar da idan kika sami hali, yanzu ki gaya min me nayi miki?" Shiru tayi tana zare idanun kafin ta fara kuka tana faɗin. "Sharrin shaidan ne!" "Zaki iya tafiya!" "Kika kyale ta?" Ya tambaye ni, gyada kai nayi ina faɗin. "Eh ta je kawai." Fita tayi daga dakin, na shiga bayi nayi alola sannan na kara ɗaukar abin sallah na sauko kasa wurin Yaya na yi sallah a wurin, i feel alone. Haka na hada kaina da kafana ina mai kallon Yaya a kwance, a tunanina mutuwa zai yi a wancan ranar, ashe Abbana ne zai tafi ya bar ni, hawayen da nake son yi yaki zuwa bakiɗaya Mutuwa Abba ya mai da ni so wani iri bana son hayaniya, a wurin nayi sallah asuba da safe aka kawo min sako daga Fada, study room din Yaya na shiga na fara duba sakon, ba wani abu ba ne, amma kuma sako ne da yadda wasu kudaden suka yi missing. A cikin asusun masarautar ya kara bani mamaki, dama ana samun haka? Kiran Faruq nayi a waya muka yi magana kai tsaye ya gaya min eh shima Yaya yayi ta bincike amma bai samu yadda yake so ba, don haka ya hakura da binciken ya ajiye inda na kara fahimtar Yaya yana da rauni, da zaran ya fara abu ya ji ya gaji sai ya bari wanda a tsarin mulkin ba ayi mata haka, ajiyar zuciya na sauke tare da yin kasa da kaina, ina jin wani irin abu yana cika min rai, Allah kaɗai yake kare shi amma duk wani tsari na mulki yaya bai da ita a jininsa, anya shi din jinin sarauta ne? Domin kowa yana proud da bloodline dinsa amma ban da Yaya. Cizon lips dina nayi don na ji ko ni din ne, bayan na gama tunanin abinda zai yi kawai na shirya tsaf, sai da nayi kwana uku kafin na kira Faruq muka yi magana da Nuraim ya haɗa ni da manager na banki da yake da alaka da masarautar, nayi haka ne domin nasan Ya Nuraim yana aiki da UBA, ban wani samu matsala ba aka hada ni da manager, sannan yadda na bukaci taimakon bai ki ba, domin nima nayi wani amfani da wata dama na bude account a cikin bankin Abu daya suka bukata shaidar kotu. Shima sai na samu Kawar Mai Babbar Mrs Kudirat Obafemi Oloyokayemi, ta bamu wannan shaidar take aka yi copy aka fitar. Muka kai musu.

Ban yi mamakin yadda ake shige da fice na mahaukatan kuɗi daga cikin masarautar ba, abu daya na fara niman Ma'ajiyan Masarautar, ranar wata laraba na tuntubi Mai Babbar daki da wannan lamarin abu daya ta ce min. "Zainab kada ki zurfaffa dayawa, amma aikin da kike dauko ko mijinki bai yi irin wannan yunkurin ba, ki tuna muna tare da ke!" Gyada kai nayi ina mata godiya. Washi gari Alhamis na bawa Faruq yayi submitting rubutuna da kuma abinda nake bukata ayi a cikin satin na fitar da waɗanda suka yi badakalar. Cikin abinda bai fi awa uku ba aka yi ta kirana daga manyan fadar tare da min barazanar ai don Abba suke tare da ni zasu janye, na ji ciwo na ji zafi na kuma ji b'acin rai. Amma akwai wani abu da na karanta a lokacin aikin Jarida duk wani dan jarida idan har dan jaridar Gaskiya ne baya tab'a gudu a fagen fama, baya karaya barazana ko wani abu baya saka shi ya fasa aikinsa, an bamu labari da tarihin yan jaridu da suka sadaukar da kome nasu domin su isar da sako, sai aka yi dace ina da bala'in taurin kai da zuciya idan na ce xan yi abu bana jin tsoron aikatawa, banbancina da wasu kenan, haka na kafa kaina a wani maganar da mai babbar daki tayi min kamar itama an mata wani kashedi ne, ni kuma damuwata na ciro waye yake juya masarautar a cikinsu.

Sai tayi rashin dace nafi jinjirin jaki taurin kai, domin sau uku ana kai min hari a idan na fita wani uzurin, abu daya na gayawa musu a fadar. "Ni ba zan janye bincike na ba, sannan idan aka kuma min barazana da rayuwata ko na wani nawa. Zan yi wani abu daya da zai bawa kowa mamaki." Haka da nayi sai ya saka suka rena abin da na faɗa. Ayaaz suna wasa da Yara a cikin lambu aka nime Yaron haka rasa duk da na danne zuciyata kawai nake, amma kamar ta fashe don tsoro, ban ce kome ba har yamma, wurin karfe shida na yamma tsohuwar makabarta sarakunan Zanzabira aka samo Yaron a kwance wnada a fada mana yana wurin Aryan ne, wnada ya zo bayan hankalinki ya tashi,sai dai kuskuren da wnada yayi dauke ya aikata shine barin alamar farce purple kamar yadda aka samu a scenes din Hatsarin su Yaya, haka yasa na ce Faruq ya dauka ya mai a mana binciken shi, na shiga har bangaren Ikram na shiga har uwar ɗakinta na dauko Cumb dinta da brush na basu aka tafi da shi wurin bincike, an samu bai zo daya da yatsunta ba, kaina yayi murfi wani irin wuta yake fitarwa domin ban san cewa abin haka yake ba. Sai na kara tsannanta bincike abu daya na samu a nawa lissafin shine namiji ne yake wannan aikin da rakiyar mace, sannan akwai wani abu daya a jikin kayan Ayaaz akwai nau'o'in turare guda biyu, daya yana da sanyi da yana da karfi idan ka shinshina zai saka ka mura da atishawa. Ba tare da na kara wani lissafi ba na shiga bangaren Nadiyyah,tana parlourn kai tsaye na shige har uwar dakina, na fara shinshina turaren har na samo shi. Juyawa nayi na kalleta idanuna ya sauka akan farcen hannunta. "Ina farcen yake?" "Me ya kawo ko dakina?" Ta tambaye ni, sai ga Princess ta shigo budar bakin Yarinyar ta ce min. "Mammy Mommy ta mai da shi ko? Ita ta dauko shi ai!" Marin Nadiyyah zan yi amma sai na ga yadda Yar take kallona, na durkusa a gabanta. "Kin san Mamanki tayi laifi?" Gyada kai tayi tana faɗin. "Na sani babu kyau ka dauki mutum ka boye shi crime ne!" "Ki ce ta bamu hakuri a public!" "Mammy idan ta bada hakuri na za'a mata kome?" Yadda tayi maganar yasa na shafa kanta. Ta kara da cewa. "Mammy ki yi hakuri ba zata kara ba, idan ta kara zunubin zai yi yawa ki yafe mata!" Shafa kanta nayi na sake murmushi na ce mata. "Ya wuce Love!" Na isa gabanta da tayi tsuru-tsuru, "na barki da Allah, muna nan gidan da ke zaki ga abinda zai dame ki, kai Nadiyyah Allah ya isa tsaknina da ke Ubangiji ya daura miki abinda kika daura min na damuwa." Daga haka na fita ba bar parlourn, Yarana ban yarda na barsu Babu security ba, suna tare da su ban da ma Aryan yana kawo mana tsaiko.

Haka na cigaba da tsayawa akan ra'ayina abinda nayi ga manyan Fada da nasan akwai wani abinda ake basu a cikin masarautar sai na dakile, har na tsawon wata uku na ce kada akara basu wani abu, wannan tsarin da nayi sai ya kawo wani gagarumin sauyin da ban san zai zo a rayuwar masarautar ba, na farko sun ki bada hadin kai, ni kuma na hana a basu duk wani abu da ya dace,da yawansu hatta kudin ruwa da na wuta Masarautar take biya na saka aka yanke wutar da basu ruwan a cikin kwanaki ƙalilan suka fito zasu min bori ni kuwa na saka aka kafe min hoton wasu manya da yadda suke da alaka da Abbana. Ba sai gashi an fara fitar da marasa mutuncin cikinsu ba, abinda ya kara basu mamaki yadda nasan duk wani hanya na cutarwa a ruwan sanyi wani lokaci idan nayi wani abu sai na ga kamar akwai wani namijin aljani domin idan kaina ya cushe xan ji ina son barci da zaran nayi barci zan yi mafarkin Faruq da Yaya a cikin wata shiga na musamman suna aikin tsara yadda za a ji da mutanen Masarautar.

Ranar da na ce a fitar da su aka kuma bawa Alhaji Mamman Abba yayari sakon da na bada sai da ya karanta yafi sau uku sannan ya kira wasu a cikin masarautar ya nuna musu yadda nayi rubutun da kuma hausar da rubutun ajami ne,.haka yasa shi matukar mamaki, take ya saka aka sauke wasu daga kan muƙaminsu. Ba sai ga an fara ƙananan magana a cikin masarautar domin a cikin wanda aka sauke har da Alhaji Kabiru Hammud Yayari, Alhaji Dayyibu Hamza Yayari, Alhaji Ahmed Sani Yarima, da wasu fadawa a cikin fadar da duk wnada yake da alaka da Baitul Malin masarautar, sannan shima Ma'ajiyin aka dakatar da shi. Sai aka fara cewa an bawa yarinya damar saka idanun akan mulkin. Wannan abin ya matuƙar bawa kowa mamaki da haushi, a cikin masarautar Jakadiya Iyaami take fitar da wasu abubuwan, a can gidana kuwa na rasa yadda aka yi zancen na hana Nadiyya da Ijlal ganin Yaya basu kwana da shi sai ni ce nake kwana da shi, shima aka yi ta bugawa a jaridun ana hiran, idan na ji ana magana murmushi nake domin bana jin akwai kuskure, ni dai na kama Nadiyyah tana kwanciyar aure da shi, wnada haka kuskure ne da rashin adalci, sannan akwai masu ganin haka ba zai faru ba, yana faruwa domin na tab'a gani a wani documentary inda wani mai wanke gawa a cikin asubiti yake kwanciya da gawa mace, ashe ba shi daya ba ne akwai wata mace itama gawan maza suke kwanciya da su, wannan abin ya faru a New York ne a kasar Amurka, sannan shi mutum matukar yana kwance kuma kome nashi yana aiki tow ba makawa zai iya aikata kome.

Bayan sati biyu da haka, Alhaji Kabiru Hammud Yayari ya zo gidan. Banyi mamaki ba domin yadda yake jini na zagaye da shi na bashi wuri ya shigo, zama yayi yana murmushi ya zauna can sai ga Alhaji Nuru Yayari. Ya zauna yana murmushi shima, zama nayi na daura daya a kan daya Faruq ya zo ya tsaya a bayana. "Yarinya kina ta wasu abubuwan kamar kin hada jini da Yayari!" Wasa da yatsuna nayi na ce mishi. "Alhaji Kabiru Hammud Yayari ni ban hada jini da Yayari ba. Amma na haifi Ibrahim Salman Attahiru Shehu Yayari, na haifi Attahiru Salman Attahiru Shehu Yayari, Na haifi Maryam Salman Attahiru Shehu Yayari, na kuma Haifi Zainab Salman Attahiru Shehu Yayari, ka ga idan aka tashi ni nake da kaso mai girma a cikin gidan Yayari da jikokinsa, gaya min me ke tafe da ku?"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce min, "Wannan sune tsarin da zamu kawo a cikin zanzabira, ina son ki saka hannu akwai wasu filayen talakawa ana so za ayi kamfani a wurin shine na zo na same ki ko zaki tsaya mana ta hanyar saka hannu da bawa al'umma shawara su amince kin san yanzu ba a cika damuwa da zancen gwamnati kamar zancen ku ba!"

Murmushi nayi ina mai wasa da yatsun hannuna na ce mishi.......

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 40

Barazana yake min fa! Na fada a raina kafin na kalle shi na ce mishi. "Duk wannan na me nene?" "Ki saka amince mu kuma zamu baki goyan bayan da kike bukata?" "Ina salim yake?" Na tambaye su, shiru suka yi kafin na cigaba da cewa. "Ina ganin ku same shi sai ya zo mu yi magana!" Kallona suka yi wani irin kallo me dauke da wasu abubuwan wanda ni dai ban fahimci na meye ba ne, amma sun amince sannan sun tafi, shiru nayi Faruq ya ce min. "Wannan aikin yana da matuƙar buƙatar nutsuwarki domin ta haka ne zaki gane illar da za ayiwa alumma, sannan idan kika ce kai tsaye zaki sakar musu kome tow zasu iya baki mamaki, ki yi nazari koda Salim ya zo ne idan da hali ki tuntubi Yallabai Abid! Ki ji me zaki ce!" Gyada kai nayi, na kuma dauki shawarar Faruq, bayan sallah isha ina zaune na kira Ya Abid muka dan gaisa kafin na gaya mishi halin da nake ciki, ya ce min. "Auta ina ga ki dan bani lokaci, nayi nazarin zuwa gobe zan miki magana ko ban kira ki ba zan tura miki sako ta email," "Allah ya kai mu!" Na ce mishi ya amsa da Amin, haka bar zancen, yau da kaina nayiwa Nadiyyah magana ta kwana a wurin Mijinta amma ta sani duk abinda take yi Allah yana ganinta, da wannan na kyale su, suka kula da mijin, ni kuma na koma kan teburin nazari da binciken masarautar.

Kamar yadda Ya Abid ya ce washi gari sai ga kiranshi muka yi magana, ya gaya min yadda aikin zai shafi muhalli da rayuwar al'umma, ba laifi ba ne gina Zanzabira amma kuma kuskuren shine kamar sayar da Zanzabiran ce, haka yasa tsoro ya shige ni, na kasa zaune na kasa tsaye. A haka Ayaan ya shigo ya zauna a kujeran dakina. "Ba zaki iya gaya musu ba zaki saka hannu ba ko?" Juyawa nayi na ganshi zaune a iska. Zama nayi a bakin gadon ya ce min.."Ki auna a hankali aikin nan abu biyu ne wasa da rayuwar al'umma ko kuma wasa da rayuwarki, idan kika dauki risking zaki karawa Mijinki farin jini da soyayyar al'umma, idan kika kawar da kai aka cutar da al'umma tow ki sani ba mamaki tsinuwar da al'umma zasu yi akanki da Mijinki zai sauka."

Ajiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login