Showing 24001 words to 27000 words out of 157081 words
naji kome ya tsaya min, cikina ya koma gefe, murmushi yayi yana faɗin. "Yes screaming out loud, yi kukan dadi da ihu i need it badly!" Wani irin laushi nayi, kafin ya mai da ni gefe tare da d'aga kafana ta gefe ya shiga aikin lada, yadda jikinsa yake rawa na fahimci Yaya ya jima ba ayi bayin ruwa ba. Ya haukace a jikina ya gigice, kamar zai zauce haka yake sambata da yadda ta yi kewata. Hawaye na ji yana zuba daga idanuna, na lumshe idanuna nayi shiru. Sosai ya gajiyar dani, sai da ya nutsu ya komo gabana yana kallona ina kallonshi ya ce min.."Last haduwarmu cikinki bai shiga wata biyar ba, yau kina shirin shiga wata takwas, nayi hakuri ko ban yi ba?!" Ya fada yana shafa cikin jikina da ya dunkule wuri guda. "Shi yasa nake son Ummi ta barni na koma dake wurina zan kula da ke!" Ya fada yana sumbatar goshina yayi yana faɗin. "Sannu kin ji,!" Ban daki ya shiga ya haɗa min ruwan zafi sannan ya fito ya taimaka min cikin yayi ƙasa sosai, sai wani irin nauyi da suka yi, ya ce min. "Gama mu je asibiti a duba cikin nan girman yayi yawa!" "A'a anyi min scanner tun wata shida!" "Anya kuwa?" "Zan maka karya ne?" Na fada ina shiga cikin abin wankar na bude kafana ina bin wani irin dad'i yana ratsa ni, domin gabana wani ciwo yake min ba dad'i. Sai da na gama jin dadin ruwan na kara fita na sake shiga sai da anyi sau uku na ji dadin sannan ya sake tara ruwan ya shigo muka yi ta wasa da ruwa, a hankali duk wani fushi da b'acin rai suka tafi kamar ban tab'a fushi ba, duk yadda naso na tuna sharrinsa wannan soyayyar da alkhiarinsa ya danne kome, kallonshi nayi ta yi ina jin kamar nayi kudi ko ban yi ba." Amma wani sashi na zuciyata taki bani damar haka, kusan tare muka yi wanka muka fito sannan ya ciro min wata doguwar riga da mayafinta. Ya taya ni sakawa kafin ya ce min. "Ina takardan scanner din!" Duba gefen gadon nayi na mika mishi, ya buɗe a hankali yana duba bayanin a hankali ya kalle ni, ya kuma kalli cikin yana faɗin. "Duk cikinki ya dauki yaran nan?" Tura baki nayi nace mishi. "Ni dai ka rufa min asiri kada kasa a zo a kashe ni!" "No Baby gurl kawai kudirar Allah nake dubawa!" Sannan ya ce min. "EDD dinki zai kama Early November, yanzu muna karshen watan takwas kenan ." "Kyale su da karyansu." Na fada ya shiga nima min takalmi ya ciro min wani mai saukin tafiya da nake tafiya awo da shi, ya saka min. Ya d'agani na mike sannan na kama tafiya a hankali, har muka bar dakin ya ce min . "Zauna bari na gyara dakin nan!" Haka ya gyara dakin, ya dauko Isma ya rab'ata a kafad'arshi. Muka shiga fita daga cikin parlourn. "Daga yau idan yamma yayi zan zo muna zaga cikin gidan ko!" Gyada kai nayi. Ya kai ni wurin matan gidan duk da suka shigowa duk bayan sallah asuba su gaida Mai Babbar daki, na gaishe su suka min fatan sauka lafiya. Sannan muka fito bai ajiye kai ni ko ina ba sai tsohuwar ganuwa, wanda aka zuba kuɗi kamar ba a kaunarsu. Na kalli ginin da kyau nace mishi. "Yaya!" "Na'am!" Dukka gidan sama kenan?" "Eh kowa ta zauna a sama baku ga juna ba balle ayi faɗa, parlourn kasa akwai kitchen na part din kowacce mace. Ni kusan ga nawa part din anan kai ni na ga dakunan guda uku wanda a ƙalla zai dauki gado biyu, ya nuna min wani daki. "Wannan dakin Yarana maza ne saboda tare zamu na zuwa masallaci da asuba, wannan kuma dakin karatu ne za a fara zuba kayan idan sun iso, wannan kuma dakina ne, ke daya zan barwa key ɗin saboda akwai dakin sirri a cikin dakin," ya kai ni cikin dakin da gaske sai ga wani wall kamar ba kome yana zuwa gefen wardrobe din ya tab'a ba sai gashi dakin ya buɗe ba, a hankali ya riko hannuna. Ya shigar dani, babban tv ne daga ko ina na cikin zanzabira kana gani hatta wnada ya dauki hanyar Sir Abubakar tafawa balewa akwai wani tv ya kunna sai ga aslalin garin zanzabira a cikin ko ina ya kasu. "Yaya kai intelligent agent ne?" Girgiza kai yayi ya ce min. "Dan uwanki Faruq ya bani shawara na saka ayi wannan aikin!Shima a akwai bangarenshi a can baya akwai irin wannan dakin, yana ganin kome. " Kasa tsayuwa nayi na zauna nace mishi.."me yasa ka yi haka?" "Wata rana zaki fahimci haka!" Gyada kai nayi ta riko hannuna muka fito a hankali har zuwa gidan farko, ya nuna min ya ce min. "Ni bana son nan bangaren. " Haka ya kai ni daya ya ce shi baya so, kafin ya kai ni daya na kusa da shi sosai. "Ina son wannan kin fi kusa da Yarana, kin fi kusa da ni, sannan parlournmu ta kasa a hade yake!" Ya bude min parlour kasa glass ce a tsakaninmu da shi. "Why Yaya?" "Because I need you a gefena." Murmushi nayi nace mishi. "Sauran matan fa?" "Kece kawai baki buƙatar kome daga gare ni sai abinda na baki, Nadiyyah bata damu da sunana ba sai lafiyata idan zan kwana ina kwanciya da ita ba zata gaji ba, Ijlal sunana matsayina lafiyata, in fact Ijlal ta gayyato min Ikram rayuwata, tunda na hada tarayya da ke na fahimci mata suna suka tara, macen da nake samun nutsuwa da ita kece, daga abinci abin sha a wurinki nake da nutsuwa na ci, zuwa yanzu na ƙara fahimtar dalilin da Abba ya rasa rayuwarsa har da hannun mace. Don haka Brandy zai dawo, sannan kayan cikin kitchen din da yake wurin faruq zan saka azurfa, sannan akwai wani tukunya da idan aka jefa kwaya yana iya nuna alamun, Zainaba na shirya zama da kune yanzu a matsayin namiji ba a matsayin sauna ba, duk abinda aka yi akwai Camera bana bukatar explanation domin xan gani kuma Faruq zai gani. Nayi haka ne don kada na na sake aikata irin kuskurena da nayi a baya. Shafa fuskarshi nayi na ce mishi. "Ina ne bangaren Amarya!" Nuna min yayi yana faɗin. "Ita da aminiyarta ga wurinsu nan, Nadiyyah ga wurinta nan." Sai yanzu na fahimci tsarin gidan kowa a rabe aka yi sannan aka haɗe kome a tsakiya, "sannu Yaya ka kashe kudi!" Murmushi yayi yana faɗin. "Muje ki ga wajen!" Haka muka fito, ya rike hannuna har zuwa bayan gidan ga bangaren Faruq da wani katon kitchen a wurin, muka shiga kitchen din manyan firiza guda biyu ne, sai gas cooker da aka saka kusan kai shida da alamu masu aikin da za a karo wannan lokacin zasu kai mutane goma sha biyu. "I don't need maid tun akan Wildat nake gudun kada a kara samun wanda zasu cutar da min ke, sannan wannan karon ba zaki shiga kitchen ba, idan ma kina so tow sai don ayi min abincin irin naki mai dad'i." Ya fada yana sumbatar bayana. "Yaya kayan kitchen din ya min kyau!" "Daularh da Bilqis na bawa odan kome kuma nasan zasu yi kome the best!" Haka muka wuce play background nan na ga har wani camp aka yi a wurin da abin wasa sai na tsaya ina kallonshi. "Yaya you are so sweet for me!" Ya sumbaci kumatuna, ya ce min. "Dominki da Yarana!" Gaba muka yi na ga babban swimming pool ne, ga na yara can gefe, gabana ne ya fadi na ce mishi. "Ni dai ba zan bar Yarana su zo nan ba kada su fada a cikin ruwa!" Dariya ya sakan min yana faɗin. "Muje na kai ki gida Magariba tayi, muka ya rufe gidan, yana faɗin. "Kin kyauta amma ni na saka ne domin shan iska."
"A'a yaya ni dai oo!"
Haka ya kawo ni gida yana dariya, muka samu mai Babbar daki ta dawo, shiga dakin nayi na yi alola na gabatar da sallah, Jakadiya ta kawo min abinci na ci na sha madara, na zauna ina karatun da nasa ba.
***
Ikram
Wayarta ta dauka ta kira.
"Mommy Turai na amince ina jiranki, " wurin karfe takwas ta kirata ta ce ga ta nan, ba musu Ikram ta fita daga cikin gidan, ta nufi waje. Sai da suka isa gidan ta ce Mata. "Ki shiga!" A hankali ta fita daga motar ta shiga gidan, ba kowa a parlourn can kuwa wata mata da nikka ta fito, ta ajiye mata ruwa tana faɗin. "Naji dadin amincewa da kika yi sha ruwa shine cikon yardan da zan yi da ke!" Ba musu ta dauki ruwan ta kurba a hankali sannan ta ajiye bayan kamar minti goma ta ji kome ya tsaya mata daga nan bata kuma sanin inda take ba, ta zube. Daukarta tayi zuwa wani daki ta kwabe tsirara ta kunna wutar runshi sai ta fara rawa a gaban ruwan tana kirari da ihu da kuka tana saka wuka tana tamkar fatar jikinta, tana faɗin."na bada jinina Aojanah fito ga gangan jikin da babu kazamta babu datti zo ki duba wannan ita ce irin da kike jira na tsawon ƙarni, ita ce zata shiga a matsayin mata ta huɗu a gidan mai girma Shago." Ihu take tana kuka tana faduwa, can kuwa ta sokawa kanta wukar sai ga jini ya watsu a cikin wutar ya kama da karfi, sai ga wutar ya taso cikin wani irin tartsatsi ya nufi.sama yana yawo har ya kan Ikram.
-----
Cikin tsananin duhun dare, take kallon wutar da yake ci a hankali. Gani take wutar na rabuwa gida biyu-biyu. Zubewa tayi tana mai da numfashi a hankali. "Me kika aikata min? Me kika min?" Ta fada da wani irin amo, kafin ta lumshe idanunta, bata kara buɗewa ba sai bayan awa daya, kafin ta bude idanunta a hankali. Wanda yake ci da wuta kamar yadda wutar gabanta yake ciki. "Kada ki manta ruhi biyu ne a jikinki, akwai mai girma Aojanah. Wacce ta kasance mai tsarki ce ita ɗin, shi yasa ta zab'e ki. Sai abu na gama ina son na tuna miki fansar mahaifinki ko kin yafe musu ne? Ko kin yafe mutuwar dan uwanki ne? Idan har kin yarda kin amince zaku kasance da mai girma Aojanah har karshen rayuwarki wannan shine dalilin, sannan itama tana da burin domin shagon ya farka da ba zai kara komawa ba. Wannan ne lokacinki kafin Awatif ta kara dawowa a gare ki! Domin ba Mai Babbar daki kaɗai ke taimakawa ba har da wasu ruhannin!"
Mikewa tayi tare da nufar kofar a hankali, ta juya tana kallon matar da take cikin duhun ta ce mata. "Haka kawai ba zaki tashe ni daga barci ba meye buƙatarki?" "Mulkin zanzabira ya dawo hannunmu." Murmushi tayi tana mai fitowa parlourn a hankali, ta samu parlourn da mutane wasu fuskarsu a rufe bakiɗaya suka zube a gabanta. "Barka da dawowa sabuwar rayuwa Barka da tashi daga barci mu dakarun tsakiyar birnin mun yi miki mubaya'a a matsayinki na shugaban rundunar shaidanun tsakiyar birnin, mai girma Aojanah."
"Alhaji Nafi'u waye yake saka ka aikin nan ne? Nima ina son sanin waye ne a cikin ahalin Yayari? Idan har zan shiga cikin masarautar Yayari dole sai na kirkiro yar karamar wasan kwaikwayo tunda abar wasannin mu ta gama mana aiki!"
"Ki je ki shirya akansa Salmanun Faris da kika sani da can ba shi bane anan, wanda yake nan fusatacce ne"
Dariya tayi tana faɗin"kasan me yasa Aojanah ta zabe Ni? Saboda ita din tsarkakakiya ce. Nima ban tab'a haɗa hanya da kazantarku ba. Fansa tawa biyan bukata taku!" Daga haka ta dauki jakarta ta bar parlourn tana wani irin tafiya mai jan hankali. Wanda idan ka ganta she look sexy, tabbas an sake haihuwar ta jin ta take a cikin jikin da yayi mata dai-dai. Wani iskar yanci ta shaka....
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 09
Washi gari.
Umma suka kawo kayan Nadiyyah, aka wuce da shi Jos saboda bata koma can Abuja ba ta zauna a jos ne ko da zakaranta zai yi carar alkhairi, sai dai shi wannan Salmanun Faris da nake gani kamar ba shi na sani a baya ba, wanda na sani a baya ya bai tsaya akan kome, amma wannan ya tattara kome ya watsar kamar bai damu da abinda yake faruwa. Bai da lokacin da zai d'aga hankalinsa, koda ya ji labarin yan kai kayan Nadiyyah, shigowa yayi ya same ni, a dakin Jakadiya Iyaami tana bani labarin yadda aka yi ta zama Jakadiya sai dariya nake mata sauti. Mikewa tayi tana gaishe shi, zama yayi yana faɗin. "Barka da hutawa Gimbiya Zainab!" Murmushi nayi na ce mishi. "Ango mai jiran gado!" Annurin fuskarsa ce ta ɗauke ya haɗe rai, a tashi nima da son niman magana, na ce mishi. "Ya da b'ata rai, na ga ba wani abu na ce maka ba. Kawai na dai ga kamar yana da kyau ina tuna maka da kai fa kana da wasu matan uku rus ruguza-ruguza masu kayan aiki da makamai, ba irinmu kamar mun rako mata duniya ba."
Murmushi yayi yana faɗin. "Baki yarda da da zancen na ba ko? Hmmm!" Ya fada yajan hannuna suna kara, murmushi nayi idanuna suka cika da kwalla, yadda yake fadar abinda yake bakin shi he take long time for the confess how is he feeling, murmushi nayi na d'ago kai nace mishi baka ga yadda nayi muni ba ne? " "I'm ready love from thousands years! No matter how im still love you, and I'm still waiting for you lu'ulu'a Awatif!" Ya sumbaci goshina, wani irin kwalla ne ya zuba min kamar kada na daina kukan da nake jin zan yi na kauda kai na gefe, haka kawai sai nake tausayinshi da dukkan zuciyata, amma nasan halin Yaya tsaf yanzu dai ta iya shayar da mamaki, don haka sai na mai da kwallana kada wata rana nayi dan danasanin ganin abinda zai yi, haka yasa na zare hannuna daga cikin nashi ya ce min. "Baki yi magana akan haihuwarki ba, dukkansu kowacce kudi take amsa amma ke har yanzu baki yi magana ba." Murmushi nayi na shafa kanshi da ya daura akan cinyata. "Ka bawa Bilqis da Daularh su saya min sun fi ni sani kome!" "Kina ganin haka zai yi miki?" "Idan ka bani kudin kome zai iya tsaya min tunda ban san kome ba akan haka, amma idan su ne kome zasu iya saya kome!"
"Kayan unisex za a saya ko?" "Eh!" Na fada ya ciro wayarshi zai min magana sai ga sakon Ikram, dauke kai nayi kamar ban gani ba, sai ya kira Bilqis suka gama magana har ya bani wayar ina mata tsiya tare da cewa. "Ai kece unguwar zoman idan haihuwar tazo sai ta jira ki, sannan xan kyale ta." Murmushi tayi yadda tayi kamar shine, ahalin Yayari kome nasu daya daga shi har yan uwansa, shafa kasumbarshi nayi ina faɗin. "Ba don yana tare da ni ba da nace anya ba shi ba ne." Murmushi nayi na ce mata. "Duk abinda zaki fada daya ne." Na fada ina wasa da gemun shi, rike hannuna yayi yana faɗin. "Baby girl kuna gulmar sarki guda, Ya Allah Mai gadon zinari kina gulmar mai Martaba dole na hukunta wakilin birnin zanzabira tunda matarshi ta yi gulmar Mai Martaba." Dariya ta saka wani mai sauti tana faɗin. "Allah ya taimaki zakin zanzabira!" Shafa kanshi. "Ni dai ba ruwana!" Na mata sallama don tace zata kira Hadiza da Daulah su saka ranar zuwa.
A can gidanmu kuwa Hajja har da guntun yajin zuwa gidan Tarasulu sai da ta kwashe sati daya kai karewa Maluma da Umma suka tafi bikonta, da kyar ta baro gidan Tarasulu da yamma kuwa tana dawowa suka hadu da Hajiya Turai wacce ta tsaya ya gaida Hajjah sannan ta tsaya tana son cusawa Umma da Maluma haushi. Ta ce musu, "Sai kuma aka na ji labarin Sarkin Zanzabira zai kara auren Ikram Saddam Tanimu Jatau, kuma na ga duk kawaye ne fa!" Umma da ta san kan duniya ta ce mata.."Au ashe wanda ya baki labarin bai iya bada labari ba, domin anan muka hada kayan auren ni fa Shukrah da Sajida da Nu'aymah, ita kuma da yake zinariyar Surukatarta a can aka hada mata kayan fadar kishiya har da rai miliyan biyar ko nake tunani, Hajjah bata san da labarin. Ai kuwa ta rangad'a gud'a tana rawa tare da cewa. "Kai yanzu na san na haifi jarumar jika wacce ta ci sunan Fulani." Ta kama rawa kamar ana mata kid'a rawa sosai, kamar munafuka haka Mommy Turai ta wuce Maluma ta ce mata. "Ai kune iyayen Hajiya Jamilah kawarki ce na amana, amma ki gaya mata kada kishin ya koma gidan da aka yi na makaranta ya dawo gidan Salmanu Faris, domin nasan wacece na kai gidan!"
"Kina tsoro ne ko ba zata iya kwatar kanta ba ne?" Dariya Maluma tayi tana faɗin. "Ina ai ni nasan cewa tabbas ita din ba raguwa ba ce zai matuƙar wahala mace ta razana ta, sai dai ta basu tsoro Fulani Babba wasa ce!" Daga haka ta wuce ta bar Hajiya Turai tana cizon yatsa.
"Zaku ga yadda xan yi waje da ita kuwa na saka ya watso ta titi!"
***
Hajiya Jamilah mahaifiyar Ikram, bakiɗaya ta ga yarinyar ta sauya musamman Yayunta Halima da Safiyya, ba su dai yi magana ba sai da tayiwa Tanim rashin mutunci, ya rufe ta da duka. Ai kuwa washi gari haka ya tashi ko ina a jikinsa ya kumbura, kamar wanda yayi