Showing 42001 words to 45000 words out of 157081 words

Chapter 15 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

29

gaya mata cewa Tauhid ya rasu tow idan mutum daya ne yayi wannan aikin ya zai yi? Wani irin tsoro ne ya cika mishi zuciya, idan har wannan abin ya faru kuma Zainab wani hali take ciki? Taci abinci? Ta sha ruwa? A wani yanayi take ciki. Kalman Nadiyyah kafin ya fito take cewa, "Na ji labarin idan Bandit suka kama mace da ciki, ko su nawa ne haka suke lalata da ita har sai dan cikinta ya mutu, waye yasan maza nawa suka hau suka sauka akanta, mu da yake karuwai ne amma mazan banza basu kawo mana hari sai matar auren da ake ta kare ta kada ayi lalata da ita." Bai kulata ba, amma tabbas idan ya koma zai san yadda zan yi da ita. Haka likitocin suka fara duba gawar da bincike akan gawar, kafin karfe uku na da har an gama binciken abinda ya yi sanadin mutuwarsa, aka gano wayar birki ce aka yanke masa wuya da ita, a cikin daren Hajiya Turai ta iso cikin asibitin, duk da rashin mutunci irin nata, lokacin da aka turo mata gawarshi, wani irin kuka take mai cike da ciwo da tashin hankali, bata taɓa kawo mishi mutuwa ba, bata tab'a wanin zai mutu a daren jiya ba, kuka take tana faɗin. "Ibrahima me yasa? Me yasa ka tafi me yasa ka tafi me yasa baka jira na tuba ba, kace kana son ka ga na tuba me yasa? Bireema me yasa me yasa kayi gaggawar tafiya, bayan kasan ina tare da kai bireema gaya min me xan gyara wallahi zan gyara me yasa suka kashe shi? Bayan barazana nace ayi mishi, me yasa zasu kashe min kai! Wayyo Allah na Wayyo Allah na, na shiga uku na lalace wayyo ni wayyo ni Turai sun kashe min d'ana!" Kafin karfe biyar na asuba Hajiya Turai ta suma ya kai sau uku, karfe biyar cib aka dauko gawar shi zuwa gida sannan suka tafi masallaci sallah asuba, anan suka sanar da rasuwar da jana'izarshi, inda Yan uwa mata suke. Lokacin da suka isa gidan zo ka ga abin tausayi musamman Iram da ta hango gawar a parlourn Malam Junaid, yankar jiki tayi ta zube aka yi ta mata fifita. Ta rarrafa da ta dawo hayyacinta, ta isa gabanshi tare da rungume shi, tana wani irin kuka. Duk mai imani ya ga yadda Iram take kuka sai zuciyarshi ta karaya, domin kuwa ta kashe zuciyar kowa da kuka tana faɗin. "Na daina duk abinda nake Ibrahim ka dawo wallahi na tuba, Ibrahim kai mutumin kirki, Abba kace ka tashi don Allah wallahi daga yau na daina kome Abba!" Bude mata hannu Malam Junaid yayi, ta ajiye gawar ta tafi ta kifa kanta a kirjinshi tana kuka ta ce mishi. "Abba Mommy ce ta saka aka kashe shi, Abba Mommy ce, Mommy monster ce ita take da hannu a dauke Ikhlas, duk ita ce Abba me yasa zata saka a kashe bawan Allah, wallahi Abba ya daina duk abinda yake yi, Abba idan mutumin kirki zai mutu a haka Abba ni da nake aikata sabon Allah fa? Abba ni ko ina ka kai ni, ka nisanta ni da Mommy nima zata iya sakawa a kashe ni!" Kuka take tana magana, "Ya isa haka!" Haka kowa ya shigo aka yi mishi wanka, a parlourn bayan matan sun fita sai Maluma da Umma da Ita Iram din, kuka take tana kallon shi tana tuna lokacin yana yaro, duk da shekarun tsakaninsu babu yawa.. amma tana tuna lokacin da take mishi wasa da ruwa yana dariya. Kuka take tana jin wani irin tashin hankali, idan har Yaron kirki irin Ibrahim zasu kashe saboda biyan buƙatar kansu tow itama bata tsira ba, don haka ta rabu da Mahaifiyarta har abada. Sutura aka yi mishi tare da shirya shi wurin karfe tara na safe an gama kome, aka fito da shi zuwa kofar Malam Junaid, aka mishi sallah, sannsn suka raka shi izuwa gidansa na gaskiya kowa ya watse ban da Malam Junaid da yaransa, da suke gaban kabarin suna jin kewarshi.

***

Ikhlas.

"Ina zaka haka? Saurin me kake yi?" Dariya yayi min yana nuna min can inda na hango wasu mutane da fararen kaya suna ta tafiya.."Tafiya zamu yi mai nisa shine na tsaya mu yi bankwana sannan ki bani dubu ashirin!" Matashin kaina na dauka na maka mishi ina kokarin sauka daga gadon nace mishi.."Tauhid ka fita idanuna, ba na gaya maka idan kana son kudi ka cire a account din ba ne? Ko gulma ce ta sa kazo amsa ka saka kome ka cire ashirin. " Murmushi yayi ya ce min. "Tow kiyi hakuri, ni kan xan tafi ina sauri ne." Tashi zan yi ya ce min. "Koma ki kwanta abinki, amma ki yi addu'a Allah ya fitar dake daga nan, can gida Abba da sauran mutane suna jiranki. Na tafi!" "Tauhid din ina zaka?" Dariya yayi yana dan rausaya da kai ya ce min. "Zan tafi izuwa wurin mai kira ya kira ni, kuma kowa zai amsa kiran na shi, ki kula min da Iram da Mommy ki yi hakuri ke daya ce zaki iya wannan aikin bye!" Ya fada yana tafiya. A hankali na mike na fara binsa. "Ina zaka ?" "Garin mu da nisa, kada su tafi su bar ni!" Ya fada ina hango shi yayi ta tafiya, sai nayi kamar xan bi shi sai na ji na kasa d'aga kafana, haka ina ji ina gani ya b'acewa, sheka min ruwan ƙanƙara ya saka ni wani irin ajiyar zuciya ina ji wani azabaɓɓen sanyi yana ratsa ni, a hankali na bude udanuna da suka yi nauyi na kalle su. Wata mace ce katuwa kamar giwa a gabana. "Hmm Ikhlas kike?" Matar ta fada ina jin wani irin sanyi yana ratsa ni, na kalleta a hankali na kasa magana. "Tashi ba kwanciya kika zo yi ba." A hankali na mike tsaye, ruwa yana d'iga daga jikina mai sanyi. "Ku kara mata ruwa!" Ni dai ban san me ya faru ba kawai sai gani nayi matar tana ihu da kakari, kafin wani lokaci ta zube a kasa a sume. Kallon sauran matan nayi naga sun fara ja da baya, tare da cewa. "Ku fita kada ta zo kan mu!" Haka suka fita da gudu, tare da rufe kofar, kallon kofar nayi ina jin kamar na fasa ihu. Haka suka barni a rufe da matar da take kwance. Har lokacin ina jike, sauran ruwan sanyi na dauka na watsa mata itama ta ji yadda naji ihu take tana mai mikewa tare da cewa. "Wayyo Allah wayyo uwata wayyo Ni Mandiya!" Murmushi nayi mata, na ce mata. "Akan me zaki watsa min ruwan sanyi? Idan da ace lafiyata lau ne da sauki, amma zuba min ruwan sanyi kuskure ne." Na fada ina komawa na zauna ina kallon kayan jikina da suka jike, haka ta kasa motsi ashe wai ta ji ciwo a hannunta ne, ni ban sani ba. Haka yanayin ya kasance a cikin dakin babu dad'i, can aka kawo abinci tare da wasu gardawa guda uku suka biyu suka fitar da ita, daya ya ajiye min abinci da bindiga a hannunsa. Kallon da yake min haka nima nake mishi, zare idanu yake nima ina zare idanuna, wanda haka ya tilasta mishi fita babu shiri.

Yanayin da nake ciki ni kaina nasan ba zan iya gane inda nake ba, wayata babu network. Gata nan dai amma bata da amfani, cikin gida ne irin zururu nan ne, sai dai duk motsin da wani zai yi Zaka ji, domin kuwa dakin yana da dan fadi mutane biyu zuwa uku suke ci, ni kuwa kamar an san da zuwana dakin ni daya ce, sai inda aka ajiye min wasu abin bukata, dakin akwai toilet da wurin wanka amma akwai Camera mai ɗaukar duk abinda kake yi, haka yasa tunda na gani na kasa nutsuwa idan zan yi uzuri kamar akan idanunsu zan yi, idan kana niman tozarci shine wannan abin da suka yi min, gashi wurin da zafi haka zan ji kamar nayi hauka, haka yasa bana iya kome idan zafi ya dame ni haka nake sakarwa kaina ruwan sanyi da yake cikin ban dakin, duk na jika ko ina sannan na kwanta.

A cikin kwana ɗaya da wuni guda, na tsani kome na rayuwar duniya duk matsayinka da darajarka kai ba a bakin kome bane, ina jin ihun yan mata da yara, daren ranar da nake da wuni kwana ɗaya da wuni, ina zaune bayan na gama sallah wanda ban san yadda matsayinta yake, haka nake sallah da kome idan ina jin fitsari haka xan cire Jalbab dina, sai na saka pant dina da under skirt ina na yi fitsari a jikinshi, idan na gama sai na saka Jalbab din, sai na wanke jikina. Cikin dare ina kwance na ji an bude kofar dakin. Tashi nayi zaune ina kallon kofar, wasu mutane ne, da jajjayen kaya. Kuna wutar dakin yayi Alhaji Nafi'u, murmushi nayi ina kallonshi. "Me yasa baki roki a sake ki ba!" "Akan me zai saka na yi haka?" Na tambaye shi ina mai gyara zamana, ina kallonshi. "Wannan alfaharin fa?" "Na jinin Yayari ne da yake jikina, ba zan ce ka sake ni ba, amma nasan ba zan kara kwana ba anan zan fita ko kaki ko ka so. Zan fita zan bar gidan nan, amma ka sani ka gudu domin kanka da rayuwarka." Yana zuwa ya d'aga hannu zai mare ni, ya ji hannun kamar an rike mishi. Ta baya har kamar da a karya. "Me kike takama da shi?" Murmushi nayi me haɗe da dariya na ce mishi.."Allah!" Na janyo Yar jakata na ciro kayan kwadayin da suke jakar. "Me yasa ba zaki ci abinci ba?" "Me yasa ka damu bayan ina ganin guba kace na ci abincin, ka ga ni ba zan shiga harkanka ba, amma kace zaka takalo mijina da rigima zaka san ka yi kuskure, ka fita. " Na nuna mishi hanya, kofar da kanta ta bude kanta su kansu sun razana, musamman da nake yin abinda ba kasafai normal Dan Adam yake yi ba.

"Zan dawo kanki bari na je ga Mijinki!" Murmushi nayi na ce mishi. "Wancan ai murucin kan dutse ne bai fito ba sai da ya shirya, idan kana ganin zaka iya Bismillah mana, da alamu zaka sha mamaki!" Cikin d'aga murya zai yi magana aka rike mishi wuya ya kasa magana sai tari yaƙe. Daga nan cikin asalin ware house din suka shiga, inda suka sami SAN suhaila tana ganinsu cikin d'aga murya ta ce."wani dan iska ne zai kawo mana ita cikin gidan nan? Bayan kun san yanayin jininta rashin anfahinsa yafi amfaninsa yawa, kun san yadda zaku yi ku fitar mana da ita domin wallahi kuka sake wani abu ya faru zan zare hannuna na koma gefe kamar ban san ku ba!"

**

Bai samu zama ba sai yau, domin shekaranjiya da jiya bai da nutsuwa, kallon Nadiyyah yayi da kyau tana zaune sai wani yauki take, shi kuma maganar b'atar Zainab yake turawa babban cibiyar bincike da yadda zasu taimaka mishi. " My Big bomb!" Kurban tea din da Faruq ya ajiye mishi yayi kafin ya kalle, bai kulata ba. "Wai har yanzu kana kan bincike akan b'atar Matar da ba mamaki da kanta ta gudu!"

"Nadiyyah tsakaninki da Allah me yasa kika sauya?" Tsaki tayi tana faɗin. "Taya ba zan sauya ba, ina ji ina gani ka sauya kana nuna mana bamu da amfani!" "Ni yaushe nace baku amfani a rayuwata?" Shiru tayi bata iya magana ba, "tsakanina da ku Alkhairi ce, haka Zainab tsakaninta da ku Alkhairi ce me yasa kike murna da sace ta da aka yi? Na zata kece mutum na farko da zaki fara kuka da tashin hankali!" "Allah ya sawwaka nayi kuka. Tab" daga haka ta juya mishi keya. "Kin yi magana ranar, amma na bar ki da halinki abinda ka shuka wata rana shi zaka girba, mai kyau ko mara kyau yadda kika juyawa Zainab baya kema haka abubuwanki zaki ji yadda ake ji."

"Ba dai baki kake min ba? Ba dai Sara min baki kake ba? Ba dai baki kake min." Hawayen da ta gani cike a idanunshi yasa jikinta yayi sanyi. "Matata da ciki aka sace kike min fata ranar ban ce miki kome ba, yau ke nace Allah ya nuna miki yadda ake butulci kike fadar haka Nadiyyah a da can ban yi niyyar dawo dake ba, saboda maganar da zainab tayi tare da nuna muhimmancin yarki na dawo dake, ba wai don ba zan iya hakura da ke ba ne, ba wai don ba zan iya rabuwa da ke ba ne, Nadiyyah Kanin Zainab ta rasa duk da haukar Ikram da Ijlal sun je ta'aziyar Yaron da jajjen b'atar Zainab amma Nadiyyah sannu bai fito a bakin mutanen da suka saka miki farin ciki a cikin zuciyarki ba, idan ban kira ki butulu ba ban san me xan kira ki da shi, ke azzalima ce da kanta kawai ta sani!" Wani sarawa kanshi yayi yana dafe kan ya daka mata tsawa. "Fitar min daki, muguntarki shine ajalinki, na tausaya miki irin munnunar karshen da zaki yi a cikin gidan nan zaki ga bakin cikin da zai saka ki gwammaci mutuwa kika yi akan abinda idanunki zai gani fita butulu kaza mai manta alkhairin da aka mata.......

Yau na sha rubutu fa Allah rashin comments yana damuna.....🥺

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 16

Da sauri ta fita, ranta a b'ace tana fitowa ta hango Ikram da Ijlal. "Allah ka raba mu da masu fuska biyu mutanen da zaka musu alkhairi su takaraka da sharrin!" Inji Ikram. Tana fadar haka ta wuce bangarenta. Ijlal kuwa sai da ta kusan shiga bangarenta ya rage kofa zata shiga ta juya tana kallon Nady ta ce mata. "Butulci irin naki gaskiya ko a tarihi sai an yi da gaske a samu butulu irinki, miji ma ya san kai din butulu ne ashe girman ne ba wayo, ina ruwan kazar agric." Ta fada tana mai rufe kofarta, don tunda nady ta dake su kowa yake tsoron yatsawa a kusa da ita, duk da baya kaunar Ikram amma yadda ta damu zaka ɗauka har cikin ranta ne, kuma ko da wasa maganar banza bai fito daga bakinta ba, duk da wannan aikin ba na su Alhaji Nafi'u ba ne har da ita a cikin amma gani take kamar bai wani damu da Zainab din, ita abin har mamaki yake bata ta yadda babu wani damu akan b'atar Zainab din. Abinda bata sani ba, ya danne ne damuwar Zainab ne domin yana son mutane irinta su fito da kansu. Sai dai suma a waye suke domin ba zasu yarda su yi wani motsin da zai saka su fito domin kuwa a boye daga gefe zai saka wasan yayi armashi.

**

Kwana biyu da rasuwar Ibrahim, ga batun b'atar Zainab da har yanzu yan sanda suke ta fama da bincike amma har yau babu wani labari, rasuwar Tauhid bai hana su sadaka da duk wani abun da ya dace, sai dai kuma yau da ake da kwana biyu Cp na yan sanda ya zo yiwa Malam Junaid ta'aziyar rasuwar Tauhid din a yadda ya kebe da shi ya mika mishi takardun binciken da aka yi ya ce mishi. "Malam ba zan manta da alkhairin da ka tab'a min ba a rayuwata shi yasa na kawo maka wannan binciken, mun yi bincike amma ka yi hakuri ban so haka ya faru ba, domin na samu sauyin wurin aiki daga ranar da aka yi rasuwar don Allah Malam ka yi hakuri, lamarin rasuwar Yaron nan akwai saka hannun wasu na jikin gwamnati, idan na cigaba da zama a garin nan abubuwa zasu faru ba, ba ma iya shi ba hatta b'atar yarka akwai wani abun da na gaza fahimta na yi ƙoƙarin ganin mun yi magana da Mai Martaba amma abin ya ci tura sun ki bani dama, don Allah ga wannan ka bashi wannan kuma na binciken b'atar yarka ce shima!" "Na gode sosai, Haris ka gama min kome na gode sosai da alkhairin da ka yi min." Ya mika mishi hannu suka yi musabaha, sannan ya mishi sallama ya bar gidan. Har zai shiga mota ya dawo ya ce mishi. "An sake mahaifiyar Yaron nan fa, tun jiya bayan an rufeta, Alhaji Nafi'u ya turo lauyoyinsa suka fita da ita! Sai dai kuma;" yayi shiru kafin ya cigaba da cewa., "an wuce da ita asibiti domin jiya ita ɗaya tayi ta dariya da kuka, kayi hakuri ban gaya maka da wuri ba, nasan zaka iya sani ne shi yasa ban gaya maka ba, na gode!" Sannan ya bar gidan, Ba zai manta da Junaid ba a rayuwarshi domin ya mishi abinda ba kowa zai iya mishi ba, a lokacin yana ƙoƙarin hada kudin shiga makarantar horan da Yan sanda, a lokacin kome ya tsaya mishi, iyayenshi ma basu da karfin da zasu iya daukar nauyin karatun, haka Junaid ya bashi aron kudin saura kiris a rufe kome Malam Junaid ya biya mishi koda ya biya mishi bayan ya dawo ya kawo mishi kuɗinsa ya ce ya bar mishi ne, wannan ba iya shi ba mutanen dayawa Malam Junaid ya musu alfarma da haka yasa basu iya cutar da shi, haka ya koma wurin zaman makokin wanda a son ranshi da an fara.

Haka mutane maza da mata manya da yara suke ta zuwa yiwa Malam da su Umma gaisuwa, su fa a kallon mara jin magana suka dauki Tauhid sai ga shi Yaron nan yana samu kyakkyawar shaida daga wurin Al'umma, a nan suka ji labarin ai dubu ashirin da yake amsa wutinsu ba a kanshi yake kashewa ba, wa mabukata yake bawa musamman yara masu wata nakasa, a madadin su fita bara yake biya musu duk wani abu, kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login