Showing 114001 words to 117000 words out of 157081 words

Chapter 39 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

35

zuciya na sauke tare da kallonsa na cigaba da lissafin da nake yi. "Ki barsu kawai idan wancan munafikin ya zo ki ce mishi ba zaki amince ba, ba zai miki dole ba domin akwai wata manufarshi akanki." Ware idanu nayi ina kallonshi. "A'a ba wani mugun manufa ba ne kawai dai na gaya miki dai!" A ranar bai gaya min gaskiya ba amma naga zallar gaskiya a idanunsa, bayan nasan duk abinda zai fada min gaskiya ce babu karya sai dai aka wayi gari ranar yaki gaya min gaskiya haka yasa ban takura mishi ba, Salim Ashe baya gari sai bayan kwana biyu ya zo akan maganar, na gaya mishi ban amince ba, murmushi yayi yana ajiye min karamin akwatin da ya zo da shi, ya ce min. "Gashi na Yarana ne. Ki musu hidima, sannan da kika ce baki amince ba, ba laifi domin duk abinda zai tab'a alumma yana da kyau kada ayi shi!" Gyada kai nayi ina mai jin nutsuwa da kwanciyar hankali akan maganarshi, sannan ya kara da cewa. "Ko sun miki barazana ne?" Girgixa kai nayi ina wasa da yatsuna, "sun miki barazana?" D'ago kai nayi ina jin kamar nayi kuka na gyada mishi kai. "Shi kenan ki yi hakuri, ya me jikin?" "Alhamdulillahi da sauki sosai." "Ki kula da shi kin ji!" Daga haka ya bar parlourn. Gidan Alhaji Nuru ya isa yayi ta dukar motocin gidan yana musu barna, fitowa Alhaji Nuru yayi ya ce mishi. "Baka da hankali ne?" "Daga asibitin mahaukata nake, ka fita hanyar gidan Salmanu Faris, idan ba haka na sai na baka mamaki." Daga haka ya juya ya fita, wasu abu da naga hankalin mutane bai kara kai wurin ba shine b'atan Yaransu, sun manta da batunsu don haka na cewa Ayaan. "Ina su Mahfouz?" "Suna can suna ta yawo da gararanba a cikin jinsin aljanu sun dauka mutane ne, har yau tafiya suke suna niman hanyar gida." Shiru nayi kafin na ce mishi. "Ka dawo da su gida!" "Ko an dawo da su, ba zasu kara lafiya ba, a can suke da lafiya domin suna ta mu'amala da wasu halittun suna dawowa haukacewa zasu gara a barsu kamar yadda suka saka mutane suka manta da wani shi sarki Salmanu baki yi mamakin haka ba!"

Shiru nayi ina kallon kasa ya ce min. "Na lura bakya cin abinci!" Murmushi nayi na ce . "Ina ci!" "Ko har yanzu mutuwar Abba bai sake ko ba ne?" Girgiza kai nayi, maganar ce kawai take ba ni wahala, a hankali na koma kan dogon kujera na kwanta tare da rufe idanuna. "Ki saka a kama su kawai." "Meye hujjar haka?" "Saboda zasu turo ayi miki barazana tare da yunkurin cin zarafinki!" Tashi zaune nayi ina kallonshi cike da mamaki. "Waye ta gaya maka?" "Nima na ji ne Nuru yana waya da Kabiru!" Kamar na tashi sama don kidima, dariya yayi ta min yana faɗin. "Ashe haka kike da tsoro? Tow maganar gaskiya abinda za ayi shine ki tattara kome naki, ki kawai ki fara gudu tunda ba zaki iya fuskantar matsalarki ba, ina nasihar da mahaifinki ya miki?"

Zama nayi nayi na ce mishi. "Ya zanyi to?" "Shine abinda ya dace ki tambaye ni, ba wai na yafe miki marin da kika min bane, nayi haka ne don na rike amanar da Mahaifinki ya bani ne, don haka yau xan bayan na a asalin Aryan dina, tare da abokina Aahil, zai taimaka min kada ki ce zaki yi wani motsi domin shi ba irina ba ne"

Hararanshi nayi na ce mishi, "fitar min a daki ina da abin yi!" "Bai kai wanda zan yi miki ba na gaya miki!"

Daga haka ya cigaba da cewa, "Zasu shigo domin an basu kayan aiki mai nauyi, idan har suka yi amfani da shi zasu yi barna, maganin barnan su kawai a sallami kowa yau kada su yi aikin dare, domin gidan ya kasance a bude." Sannan ya gaya min yadda zasu shigo gidan idan har gogaggun makasa ne, haka yasa na amince da shawararshi, bayan sallah isha na sallami kowa sai Faruq da nace ya tafi domin Yeemar tana da karamin ciki. Aure da rabo.

Da wuri na kwantar da Yaran suka yi barci wurin karfe daya na dare aka shigo gidan, wani abu da na kara fahimta a wannan lamarin ni ce ake nima na da karfi nayi yadda suke so. Nake cikin tashin hankali, sauran Matan basu san me ke faruwa a gidan ba, ni idanuna na kasa barci ga tsoro da fargaba da ya cika min cikina, tunda suka shigo gidan da yayi musu kama da irin gida mai abin tsoro nan amma don bakin zuciya haka suka shigo, a lokacin da suka bar wajen zasu shiga wani abu ya wuce wuf, na baya suka juya basu basu ga kome ba. Cikin parlourn gidan suka shigo, hango wani kujerar suka yi na zinari. Katon torch light ɗinsu mai haske suka haska kujeran, wani garjejen Zaki amma kamar gunki ne ba mai rai ba ne, suka gani a gefen kujeran sai kujeran wani Yaro mai ban sha'awa sanye da crown na zinari a kanshi yana wasa da wasu zinari. "Kai ina Mamanka?" Shiru yayi musu, daya cikin makasan ya nufe shi, sai ji yayi anyi sama da shi ihu yayi wanda daga haka bai kara ba, asalima baya nan, kamar ya b'ace bakiɗaya, suna sake haska torch light din suka ga babu zakin babu Yaron, wani irin ihu suka yi tare da curewa wuri guda sakamakon jin ana daure su a wuri guda. Bayan an gama daure su ƙaton Maciji ya fasa kai yana zare musu idanu, gefe guda kuwa Zaki nan ne yake ta zagaya su. Ayaan yana wasanshi kamar yana dakinsu. "Me kuka zo yi?" "Aiko mu aka ya mu razana Fulani Babba!" "Tow yanzu dai ku ne zaku razana Mammy?" Girgixa kai suka yi, suna faɗin. "Tuba muke ba zamu kara dawowa ba." "Ina son ku dawo, domin abu daya zai fitar daku macijin nan da Zaki nan abokai ne a daji suke amma basu tab'a dariya ba, yau nake son ku saka su dariya idan ba haka ba tow zamu zaɓi rayuwarku ko dariyarsu?"

Sake su macijin yayi suka zube a gaban shi. "Yallabai me zamu maka?" Gurnani Zakin yayi suka fasa ihu tare da rungume juna a lokaci guda. Suna ihu. Zane su ake ta ko ina suna yi ihu suna birgima, kafin aka kyale su cikin kuka daya cikinsu. "Amma ka cuce ni, Mugu gashi ka kawo ni inda ake so mu saka zaki dariya!"

Bakiɗaya suka rasa inda zasu saka ransu, taya zasu saka Zaki da Maciji dariya, nan aka yi ta ci Ubansu kai karshe aka samu wani ja'iri a cikinsu ya tashi cikin kundunbala ya fara rawa yadda kasan a sakawa katako riga nan yake rawa, da wata irin murya yana waka, tsulla mishi bulala aka yi ya fadi can, sai da suka yi ta fitowa daya bayan daya, karshe azaba da ba irin na mutane ba, kuka Babban cikinsu ya ke yana faɗin. "Mu dai ku kashe mu wallahi wannan bulalar kamar zai cire ran mutum yake."

"A'a babu batun mutuwa ku gaya mana me ya kawo ku nan?" "Turo mu aka yi mu ci zarafin Fulani Babba!" Murmushi Aryan yayi ya mike tsaye akan iska ya nufi kofa dakin, wani irin ihu suka yi tare d curewa wuri guda suna ji kamar su mutu don tsoro. Buɗe kofar nayi na biyo stair na same su a cure wuri guda, zama nayi tare da cewa. "Barkanku da zuwa Aryan shine baka basu ruwa suka sha ba?"

"Tow Fulani Babba an gama!" Yana rufe baki sai ga kokon kan mutane cike da wani bakin ruwa yana tururi, ihu suka yi tare da kara mancewa da juna. "Ki tambaye mu kome ma? Zamu gaya miki gaskiya!" Juyawa nayi na kalli Aryan na ce mishi. "Ku da nace ku razana su, shine kuka firgita su?" "Fulani Babba ai da razanawa da firgitarwa duk abu daya ne?" "A'a ko daya kowanne da muhallinsa." Kuka suka fara suna faɗin. "Don Allah ki rufa mana asiri!" "Aryan a kawo musu abinci!" Ban rufe baki ba aka ajiye musu tire da kuraye, wani irin ihu suka yi daya cikinsu sai da ya suma, da bulala aka tashe su yana tashi da ihu ya zauna saboda tashin hankali.

Murmushi nayi na ce musu. "Waye ya turo ku?" "Alhaji Nuru Yayari;" "idan aka kai ku gaban alkali zaku maimaita?" Aryan ya kara tambayarsu, "Wallahi zamu yi! Zamu faɗi gaskiya!" " Aryan a kai su ajiye su kafin na gama shirin shigar da ƙarar shi,.laifi biyu kenan, na farko kashe Abba na biyu ya kara turo min mutane, bana raba daya biyun yana da hannu a kwanciyar Yaya, kwashe su aka yi nasan zuwa yanzu yana baza kunne ya ji labarin abinda ya faru. Amma Allah yafi shi.

Aka gyara gidan na wuce dakin Yaya nayi sallah na zauna a gabanshi,sai a lokacin naji kuka ya so min na zauna ina kuka kamar raina zai fita, a yanzu wannan ba fadar Yaya ba ne har da ni. A tambayar da muka yiwa Yaron ya ce Alhaji Nuru da Nafi'u suka bashi aiki,.haka nayi ta kukan kamar raina zai fita. Sai a lokacin mutuwar Abba ya dawo min sabo, bakiɗaya ji nake kamar ni daya ce na rasa Abba, ciro wayata nayi ina kallon hotonshi da yake kan wayata, wani irin kewar Abba nake ji, bakiɗaya na rasa meke min dad'i. Haka nayi ta kallon wayar cikin kauna da ban san ina yin sa ba sai yau, Abba ya tafi ya bar ni cike da Kaunarshi. Bakiɗaya sai nake jin kamar waɗanda suka kashe shi basu min adalci ba.....

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 38

Mutuwa bata da dangi, amma tafi kowa zumunci, idan wanda kuke so ya mutu sai ka yi tsammanin ko Allah baya sonka ne ko baya kaunarka ne, in fact idan baka yi imani da Allah gani zaka yi kamar da wata nufi ake dauke mutum da suke da muhimmanci a rayuwarka ko wanda kake so a rayuwarka, nayi tsammanin ni ɗaya ce nake cikin firgici da dimuwa, kaduwa da tsoron waye next to Abba yasa na koma kamar wata wawuya, idan nace akwia mutuwar da ta gigita ni tow bayan na Tauhid Abba ne, sai nake jin wani irin. Guilty akan mutuwar, a lokacin da muka isa gidan ana ta wanke kofar gidan da jini ya b'ata na samu, Mai Babbar daki da sauran yan fada. A lokacin yadda Ijlal take jan hannuna zaka ɗauka mahaukaci ce ko mai irin laluran nan mara cikakken hankali ce, haka muka shiga cikin gidan, kowa ya ganni sai ya mike ni dai idanun nake bin su da shi a lokacin da na shiga cikin parlourn Abba, sai na zubawa gawata idanu daga Umma har Maluma kowacce tana cikin hijab ne, a hankali na sulale na zauna a gaban gawansa. Wani irin soya nake ji a kirjina kamar an wura wuta a zuciyata. Idanuna wani irin zafi yake min mai radadi da kuna, a hankali na sulale na kwanta a gefenshi, na lumshe idanuna. Shigowar Faruq da wani ne ya sani na tashi zaune na kalle su, kafin na kara kallon gawar Abba, sai na koma na kwanta ina ga mafarki nake, na lumshe idanuna. "Oga Faruq Yaron ne ya dawo kenan!" Ya fada a lokacin na kara bude idona a kansu na ce mishi. "Faruq kaima ka shigo mafarkin ne? Wai sun ce min Abba ya rasu ni kuma nasan Abba yana nan bai mutu ba!"

"Fulani Babba, you shud wakeup, Malam Junaid passing away!" Wani irin bugawa zuciyata tayi wanda na dafe hankali, tare da dafe kirjina. Ji nayi an rungume ni, ana shafa bayana a hankali, ina ma da Abba ne? Ina ma da Yaya ne? Ina ma da Tauhid ne? Duk lokaci guda nayi wannan nazarin ina ma da sune? Shafa bayana ake ina sauke ajiyar zuciya ina jin wani irin sanyi yana lullube ni kamar an lulluba min danyen fata, kunci hade da kaɗaici suka min dabaibayi, na ji wani irin tausayin kaina, sai aka daina kukan mutuwa Abba aka rufa min, Yes I'm daddy girl, amma yau babu shi babu alamarsa. Shafa bayana mai babbar daki take tana tofa min addu'a, a hankali nutsuwa ya zo min wanda har muka yi mishi addu'ar bankwana ban samu damar magana ba, kai haka aka yi ta dambe da ni na hana a fita da gawar, sannan na kasa furta koda kalma daya ne daga bakina, sai da Ya Yunus ya janyo ni dakin Umma ya bani ruwa na sha, Iram tana shigowa ta chaka min allura a damtsen hannuna, na juya na kalleta bakina yana motsi a hankali jikina ya sake ina ji ina gani suka saka ni barci me nauyi.

Wunin ranar barci nake babu wanda bai damu da halin da nake ciki ba, Hajja da tazo ta ga halin da nake ciki kuka take tana faɗin shi kenan sun kashe mata daya zasu kashe mata jika, bayan sallah isha na farka, wanka nayi na yi salolin kaina kafin na kwanta naji bakiɗaya duniyar ta min kunci,.ina kwance a dakin Umma naji SAJIDA tana faɗin. "Ance Yaro ne bai wuce sha takwas ba. Sunansa Kamal a tsohuwar unguwa yake irin yaran nan na getto area ne, shi yasa suka bashi kudi yayi wannan iskanci. Ai idan ba wani ikon Allah ba idan aka gama ihun da ake a gidan tv zaku ji an sake shi." Mikewa nayi a hankali na fito waje, duk da ina jin jiri saboda rashin kome a cikina. Dakin Maluma na samu na kalli Ayaan da yake kallona kamar zai yi kuka. "Ina Aryan?" Hannu ya saka a baki yana tsotso. "Ina Aryan?" Na kara tambayaar shi da karfi. Bai bani amsa ba. Wani irin tsawa na daka mishi tare da cewa. "Ina Aryan?" Nuna min bango yayi na bi hannun da idanu, yana tsaye sanye da irin kayan Ayaan yana kuka da idanunsa biyu, har da shashekar. "Sunansa Kamal! Ban damu ba ya mutu ko ya rayu daga shi har wanda ya saka su shi aikin a rufe tarihin sa sannan ka kawo min bincike akan wanda ya saka su. Yanzu nace." Gyada min kai yayi sannan ya b'ace. Zama nayi shiru daga nan na kwanta kaina ya fara sara min, haka naji na tsani kome, da kowa bana son magana. Idan na rufe idanuna kawai gawar Abba nake gani kwance a idanuna. Idan na bude idanuna shi nake gani idan na rufe idanuna shi nake gani, wani irin ciwon kai nake ji kamar kaina zai rabe biyu.

Kwanciya nayi na ji barci yayi gaba da ni, wurin karfe sha biyu ina parlourn na ji muryan Aryan a gabana.."Gasu can na kai su wuriin da Faruq yake ajiye baki, ga kofar nan ki shiga ta ciki." Mikewa nayi na shiga ban daki na kama ruwa na zo na gabatar da sallah shafa'i da wutir, sannan na bi kofar sai ga ni a wani babban gida. Ahmad Rilwani Yayari, Mahfouz Nuru Yayari, sai mutum biyun Yaron da ya kashe Abba da kuma wani dan daba. Ni dai ban ce kome ba amma na cigaba da zuba musu idanu. "Fulani Babba gasu nan!" Ya fada min yana kallonsu. "Me ya dace ayi musu?"

"A kai su dajin da bai da karshe balle farko, sannan a jiye su a can su cigaba da rayuwa har mutuwa ya cimma su." Daga haka na juya na dawo kofar. "Me yasa kika ce haka?" "Idan suka san babu su babu alamar dawowa zata ta kokarin ceton kansu, sannan na dasawa danginsu bakin cikin da suka dasa min har duniya ta tashi zata zasu ta ƙoƙarin niman inda suke amma ba zasu tab'a reaching dinsu ba, zasu rayu da begen son ganinsu amma lokaci ya kure musu, ba zan yi fada da kowa ba. Lokacin da na fito, a parlourn na samu Maluma tana kallona. "Ke da waye kike magana a kitchen, "babu kowa!" Daga haka na wuce daki na kwanta, har gari yayi tsit ban iya rintsawa ba karshe sallah dare na kama, zan iya cewa tun da nayi magana har ranar da Abba ya cika sati daya magana bai kara hada ni da wani abu, bana ma iya dogon gaisuwa Mai Babbar daki kullum tana gidan, haka Yaran hatta Aneesah na ganta tazo. Karshe komawa bangaren Mommy Turai nayi inda itama ta dawo gidan ayi zaman makoki da ita amma babu aurenta da Abba, tayi kuka tayi wani irin razana domin cewa take. "Abbanku ya tafi bamu gana ba, ban nime Yafiyarshi ba, yanzu ya zan yi da hakkin Malam Junaid, ya zan da hakkinshi. Innalillahi wainnalihir rajoun." Akwai wani da Mommy Turai ta boye wanda ana jibi zai rasu ya turo, garin na tura ayi print dinsa na gani nima abin ya dame ni, na kara kiranshi na ji da gaske ne ya tabbatar min da eh haka. Wnada iya shi kawai ya isa Mommy Turai ta ji kamar ta mutu da ranta. Idan aka nime mutumin kirki tow Abba ne na farko a duniya ta, Yasan Tauhid ne kawai jininsa da ya haɗa da Mommy Turai, amma ya rungume Yarta da aure ya bashi domin ya aureta da cikin Iram wata biyu ne, ya ce duk sauran abinda ya faru kafin haihuwar mu, duk kirkira ne don a zauna lafiya, sannan wani abin da ya kara min amince akan Iyayena mata yadda suka rufa ido akan kome

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login