Showing 123001 words to 126000 words out of 157081 words
fada mishi kai tsaye, juyawar da zai yi muka yi idanu hudu da shi. Cikin girmamawa ya ce min. "Idan kika ce na kashe kaina zan aikata haka saboda adalci irin naki da sanin darajar kowa." Murmushi nayi na ce mishi. "Ka koma gare shi zai buƙace ka Bargaga, biyayyar da kayi mishi a baya har yau bai biya ka ba, ka koma gare shi, ni da kai shine ƙaddaranmu, idan muka janye daga jikinshi zai rasa kowa har da kanshi!" Daga haka na juya ina murmushi..
Aneesah abinda take nima kenan, zaman gidan, ni kuwa nayi kamar ban san tana yi ba, satin Yaya daya na saka Faruq ya dauko min Yaran cikin murna, amma wani ikon Allah Ayaan da muke gida daya yaƙi zuwa ganin Uban, ranar da na dauke shi wai na zo ya ga Yaya kamar wanda ya dauki dutse haka na ji yayi min nauyi na sake shi, ina faɗin.."Kai dai baka da kirki, muje ka gaida Abba!" "Ba fa inda zai je wancan lusarin mijin naki bamu maraba da shi.!" Yadda yayi maganar ya bani takaici sai na kyale shi, duk sauran Yaran suna wurinsa in fact saboda kewar shi da suka yi kwanan kwanaki uku suka yi suna kwana a wurinsa, Yaya yana son Yaranshi kamar zai zauce.
Amma haka Aryaan ya hana Ayaan zuwa asalima ko babu Aryaan sai na fahimci Yaron baya ta uban, sam kuma baya kula shi kamar yadda kowa ya sani. Haka abubuwan suka yi ta faruwa, Ayaan yaki zuwa duk yadda Uban yake son ganinsa amma yaki, nayi iya ƙoƙarina amma Ayaan yaki, ranar ina zaune sai ga Yaya da kanshi ya zo har dakin yana kallonshi yana wasa. "Ibrahim!" D'ago kai yayi yana kallonshi kafin ya cigaba da wasanshi. Uban ya riko hannunsa da sauri ya cire hannunsa yana mishi wani irin kallo. "Me yasa baka zo ka ganni ba!" Shiru Yaron yayi ya cigaba da wasanshi. "Kai!" Ya fisgo Yaron da babu tsoro a idanunsa ya ce mishi. "Abba ka daina tab'a ni!" Yadda yayi maganar sai da ya bani mamaki, "Ayaan!" "Ki gaya mishi ya bari tunda ba zai iya tsayawa da kafarshi ba akan me zai tab'a Ni...." "Aryaan!!" Yaya ya kira sunanshi, murmushi yayi yana faɗin.."ashe ka san ni ne?" Ya tambaye shi yana kallonshi. "Ina son ganin d'ana ne!" Dariya yayi yana faɗin. "Danka?" Ya tambaye shi yana kallonshi. "Ka sani ba zan iya ce maka yaron zai cigaba da kallon ka a matsayin mahaifinsa ba, domin baka da lissafi kan kome!"
"Akansu nake kome!"
"Akan ka kake kome! Ba akan Zainab da Yaranta ba, idan wani ya ce maka zata aikatA mugun abu sai ka amsa? Ka sani Zainab mutum ce mai tsananin karamci da adalci, akwai mazan da suka fika kome Amma ta zauna da kai domin tana bin umarnin mahaifinta, tunda har Maryam ta ce zata kashe ta ni na kama alkawarin zan bata kyautar kiyayyar da takewa Zainab tunda har Bil Adam ya maka kashedi bata ji ba, ban san waye zai mata kashedi ta ji ba, tow bari na gwada mata yadda Aljanu suke kashedi!" "Kai waye da kake gaya min magana son ranka?" Yaya ya fada da karfi, cikin fusata Aryaan ya daka mishi tsawa da ni kaina sai da na daina ji na wani lokaci, wanda ya haifar min da zubar jini a kunnena, har sai da na durkusa kasa. Tasowa yayi ya toshe da hannunsa dukka biyu yana kallon Yaya yana huci. "Ka sake wani abu ya same ta, ba zan duba alaka ko kawazuci ba, zan shafe ahalinka bakiɗaya, wannan shine alkawarin da na dauka maka, ka sake tayi kuka ko ta ji ciwo bayan rasa Mahaifinta, zai hna ka sukuni da sakat sai na buwayeka na gallabe ka na hana ka jin dad'in rayuwa, kai!" Yadda yayi ihun sai da kome ya fashe a cikin gidan glass daga ko ina na cikin gidan suka nufi parlourn, su zagaye shi. "Ka sake baka dawo hankalinka ba, ka sake baka mai da bincike ya zama wajibi akanka ba, ka kara tab'a Zainab zan kashe ka!" Ya fada da karfi take glass din suka yi kan Yaya, dafe hannunsa nayi domin ina ganin yadda yake ihu maganar ce bana ji. "Kada ka cutar da shi, Mahaifin Ayaan ne!" Na fada da karfi. Zubewa kwalbar yayi, na ce mishi. "Abban Ayaan ne!" Na fada ina hawaye, girgiza kai nayi ina faɗin. "Kada ka cutar da shi, ka yi hakuri kada ka cutar da shi." Na faɗa a hankali ina jin kaina yana wani irin juyawa, a hankali na koma zan zube ya tare ni. "Ita mace ba kwanciyar sunnah take bukata daga namiji irinka ba, a tsaya a gefenta, ka tsaya mata ka tsaya a kusa da ita yadda ba zata yi kuka ba, Yayunta da Iyayenta mata sun yi nisa da ita, kai kuma da kake gefenta kana kara cusa mata bakin ciki, ina hankalinka yake? Ka samu macen da waninka yake bibiyarta tun tana Yarinya kana wulakanta ta! Da kasan abinda ta tsare maka da kai idan aka ce ka mata ihu zaka iya shiru har abada. Namijin kwarai magance matsalolinsa yake da na matansa, kai da ka gaza akan matarka su kuma Yaranka waye zai tsaya musu?" Sunkuyar da kai yayi, a hankali Aryaan ya kwantar da ita ya ce mishi. "Ka kula da kanka domin ta kuma samun Matsala da wani a cikin ahalinka kai zaka fi kowa sanin yadda abin yake!" Yana fadar haka ya fita a fusace a jikin Ayaan abinda ya janyowa Yaron faduwa a kasa, wanda idan dai fita kai yaron gado yake ya kwanta. Daukar Yaron yayi ya kwantar da shi a gefen Uwarshi, ya kamata yanzu yayiwa kansa fada kaka abinda yake faruwa.
Tun daga lokacin ya saka aransa ba zai kara wani abu ba tare da yayi bincike ba, wannan abin da ya faru ya saka mishi tsoron kada ya rasa Zainab din, anyi haka da kwana biyu sai ga Nadiyyah da wani sabon case wai bata ga Princess ba, Yaran da ko waje basu fita ita ce ma da Nana A'ishah za a saka su a makaranta, amma wai ta nime ta bata ganta ba, ita fada bakiɗaya zargina take. Da yake abinda ya faru ana ta aikin mai da glass na gidan, ni kuwa ina daki ina fama da ciwon kai, don har yanzu bai fara bin daki ba yana fama da jikinshi da yake ciwo aka bashi shawarar yana motsa jikinsa. Sai ga har dakin motsa jikin. "My lord ban ga Princess ba, kuma ni Zainab nake zargi!"
"Meye hujjarki da ita ta sace miki Y'a? Idan baki da hujja ita kuma zata iya maka ki kara kotu kuma zata nima mata hakkinta!" Shiru tayi. Kafin ya cigaba da cewa. "Ina da abin yi!" Da yake yar balaja'u ce, sai ga ta ta biyo ta kaina, ai kuwa tayi ta masifa Aneesah tana taya ta, ni dai ina kwance ina fama da kai da ciwon kai. "Ke!" Aka ce mata tana juyawa ta ga kwarangwal ce, ihu ta saka ya ce mata. "Nazo ki koya min yadda ake masifa ce yau shekaru na dari da daya ina son na koyi yadda ake masifa na kasa sai da na ganki na ji a raina na samu Malama!" Wani uban gudun da ta saka tare da nufar kasa, ai rufe kofar yayi ya sauko inda take ihu tana faɗin a bude mata, zama yayi a step ya zuba tagumi, ta kuma juya ta saka ihu shima ya saka ihu, ta suma a wurin. "Shegen rashin kunya kin iya fada baku iya kwatar kanku ba!" Daga hakan ya nuna kofar ya nunata da yatsa tayi waje, ya kuma juya ina murmushi yana faɗin. "Kafira mai taurin kan tsiya!" Daga haka ya koma sama abinsa, Nadiyyah kan a sume haka Mijinta ya same ta, ya buga tsawa da tasa yan gidan fitowa musamman masu bayin suka fito aka dauke ta zuwa ɗakinta. Ya dawo dakina ina kwance, hawa gadon yayi ya d'aga ni yana me rungume ni. "Sannu ya jikin naki?" "Da sauki!" Hada goshinmu yayi yana faɗin. "Do you know!" "Yaya bani da lafiya kuma nasan kayi miss dina!" Domin nasan gaba labarin na wanka da tsarki ne, duk yadda naso kwacewa Yaya sai da ya more ni tare da zuba min idanu ya mike a hankali ya buɗe wardrobe ya dauki First aid din dakina, ya zauna ya duba abinda zai duba kafin ya min allura ya tsaga inda na saka implaner din ya cire a hankali, sannan ya tabbatar ya tsayar da jinin, kafin ya min alluran kashe zafi, daga nan da ciwon hannuna Yaya sai da ya turmushe ni son ranshi, kafin ya kyale ni yana shafa kaina. Ya ce min. "Ina son kara hada jini dake.......
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 46
Shafa wurin yayi ina kallonshi, ina lumshe idanuna, a hankali na sauke ajiyar zuciya, "tashi ki yi wanka zama da datti babu kyau!" Haka na tashi nayi wanka na sauya kayana na dawo da kwanta ina jin kamar na tashi na tsagalgale shi da masifa, amma kuma idan ma tuna bai min kome ba duk masifata dole na haka na share shi nayi barci. Ko sauran matan sun fahimci wani abu ne a tsakaninmu, sai suka taddata bori musamman Nadiyyah, ita ijlal abinda ya sa tayi sanyi saboda Yarta Jinyar yarta yana wani irin tab'a silently yadda yake cin ruhinta da zuciyarta ba karamin al'amari ba ne, musamman da ta gama zagaye duk inda zata aka ce mata ciwon nata ba na warkewa ba ne hatta malamai sai da ta kai yarinyar kuma da yake Allah bai so a ciki kuɗinta ba, aka gaya mata Jinyar yarinyar ba wani shafar Aljanu ko asiri, ciwo ne da aka haife ta da shi, wani lokacin takan saka Yarinyar a gaba tayi ta kuka musamman da ta fara girma ga kyau ga nasibi amma babu lafiya, ga mace har mace idan da zata girma ba karamin kyau da girma zata yi ba, idan har kana niman ƙasaitacciyar mace, Amiratul Zaitunah ce domin kuwa duk wani zubi da halitta na mace Allah ya mata halittar mata, zuwa yanzu ita da kanta take fitowa da ita wurin yan uwanta, ta bar su ban san waye ya mata fada ba, amma naga kamar Ijlal tayi sanyi, sannan tana yawan kawo su da kayan kwadayi, wanda na lura sam Ayaan da sauran yan uwansa haka bai dame su ba, ita kanta idan ta kawo Yarinyar da idan ta ga yan uwanta kamar ta tashi tayi ta tsalle saboda jin dadi da farin ciki. Amma ni haka bai saka na zuba idanun akan su ba, domin ina matuƙar kare Yarana tunda nasan tayiwa Nadiyyah illa ba zan so nima na zama victim ba, domin babban tashin hankali shine ka zama victim kaima.
Sai dai yadda zuciyarta tayi taushi musamman yadda Ayaan yake zama yana rike hannun Zaitunah yana mata kamar tausa domin yadda yake sonta yasa Aryaan yake kula da yarinyar inda Ayaan zai zauna da ita zai zo ya shiga jikinshi ko kuma ya zauna a gefe yana kula da motsinta, idan yana yi wani lokaci har zaka ga kamar wurin yana motsi da aiki. Shi ya fara gano cewa bata gani sosai, wata juma'a, sun fito daga dakina suka sauko daga kasa, sai niman shi take tana murna tare da cewa. "Aya" tsayawa yayi can gefe ya ce mata. "Adda Gimbiya!" Sai ta fara nimanshi tana wani kura idanunta ita tana nimanshi daidai fitowar Uwarta daga kitchen, zata yi magana ya ce mata."Shiiiiii!" Cak ta tsaya ya kara kiran sunanta, tayi ta nimanshi bata ganshi ba karshe ya hakura ya kalli Uwar ya ce mata. "Ciwonta ya shafi ganinta, ki yiwa Abbansu magana." Ya cigaba da tafiya ya isa gabanta, ya d'ago kai yana kallonta idanunsa cike da kwalla ya ce mata. "Addar Aya!" Wangale baki tayi tana dariya, ya riko hannunta. Hawayen da yake dannewa ne ya zubo mishi. "Ba ruwanta, amma kaddaranki shi ya kaita inda ba zata gudu ba, gashi tana rayuwa a cikinku amma faɗin cikinta kaɗan ne."
, Aryaan baya kuka amma yau kukan da yayi na tausayin Amiratul Zaitunah, ya ce Ijlal. "Ki ajiye kishi ki kula da yarki, ki tuba kofar Allah a bude take ki yarda shi ya baki Zaitunah kuma ya jabarabce ki, kiyi hakuri laifinki yana kan nan, ban hana ki fada da dambe da Zainab da Nadiyyah ba, amma ki sani babu asirin da zaki yi ya kara kama wani, sannan ki nime yafiyar Nadiyyah akan abinda kika aikata, sannan ki kula da yarki ita ce abin tausayawa domin idan kika ci gaba ita ce zata cigaba da wahala, sannan kema bai zama dole ki samu yadda kike so ba, ita Amirah daya ce amma ba za a kara samun irinta ba."
Kallonshi take baki a sake yau ta gano dalilin da Zainab take kaf-kaf da Yaron ashe ba shi daya ba ne, domin maganar da yake bata yara ba ce ta manya masu hankali da hangen nesa ce, zama tayi zuciyarta tana wani irin harbawa. "Na gaya miki, ki san gaskiya ki san yadda zaki zauna da kanki Zainab ba zata tab'a cutar dake ba, ko da kuwa da wasa ne. Amma idanunki yana kanta." Daga haka ya fita a jikin Ayaan sai yaron yayi laushi a hankali ya zare hannunsa a jikin Yarinyar ya koma kujera ya kwanta yana mata murmushi.
Abubuwa da take ganin kamar ba kome ba ne, kome ne tunda gashi nan ta sanadin Zainab da take ki ana bata shawara. Sannan ita kanta yanzu ta dawo daga rakiyar kowa. Ihun Nadiyyah ya saka ta d'ago kai tana kallon sama, ihu take tana faɗin. "Baka da lafiya? Ka shiga wurin Zainab kake kwana da ita? Baka da lafiya kake cin mace."
Tsaki Ijlal tayi tana faɗin, "Mahaukaciya har yanzu bata yi hankali ba!" Ta fada tana jan tsaki, wasu abubuwan baka bukatar mahaukata a cikin lamarinka, amma ita yanzu ta fahimci Nadiyyah kwanton bauna tayi yanzu da ta samu dama bari ta baza Capacity son ranta, tsaki tayi a ranta tana ji kamar ta rufe shegiya ta barta ta mutu , ita yanzu bata jin zafin Zainab akan kome domin duk wnada za a yiwa laifi bayan ita ce.
Kusan kwana a aka yi ana wanan rigimar, washi gari ya raba mana kwana ni kan nace mishi. "Na yafe nawa Allah ya baka lafiya, sai ka dawo." "Munafuka taya zaki yafe tunda yanzu kin samu yadda kike so ba zan yafe ba sai.." tass ta ji an wanke matA fuska da mari, tayi cak tana kallon wanda yayi marin, amma aka rasa. "Waye ya mare ni!" Kamar an ce na d'aga kai, Aryaan ne tsaye ya tsinka mata mafi, "idan kika cigaba da zagina ba mari ba har abinda ya fi mari zaki ji!"
Na tashi na bar wurin tana ihu da Bala'i, shi kan bai yi magana ba, wannan abin da ya faru sai take ganin kamar tunda ya tashi na juya mishi tunani ne, shi yasa baya ganin laifina, tow meye nayi haka zaman ya cigaba da turawa wani ikon Allah da ya raba kwanan kan Ijlal ya fara sauka domin anyi lissafin ranar da ya fita a dakina. Zai shiga dakin Ijlal, haka kuwa aka yi ya koma ɗakinta, matar nan kamar tayi hauka. Ita kan Ijlal bata ta mijin kanta take fama da shi na ciwon Amiraah, kamar wasa sai gashi Nadiyyah tana hakikancewa ana zalintattar, wani abu da na kara yarda Ijlal ta yarta take shine bata da lokacin rigima da kowa, idan ka ganta a kasa ta dauko da Yar ne, ba sai haka ta bawa Nadiyyah da Princess damar yin yadda suke so, ranar dai ban san me suka yiwa yarinyar ba. Amma tayi ta kuka uwar ta rasa yadda zata yi da ita. Haka ta hauro sama da ita tana nishi ta ajiye min ita tana faɗin. "Ikhlas ina Ayaan Addarshi tana kuka na rasa yadda zan yi d ita!" Da gaske bamu san me ya same ta ba, sai da Ayaan din suka fito da na kira shi ya karaso wurinta ya zauna yana kallonta. "Addana!" Ya furta a hankali yana riko Hannunta, kuka ta cigaba da yi har da hawaye ya ce min. "Mammy ki mata tsarki!" Kallon Ijlal nayi naga ta dauke ta ta shiga ban dakin da yake parlourn. Ya Ilahi wacce irin zuciya ce a kirjin Nadiyyah me yasa take haka me? Yarinyar ta cusawa attarugu fa." Shi yasa take wani irin kuka me cin rai. Rike hannun Yarinyar nayi lokacin da Uwar take tsuma. "Wallahi Nadiyyah sai tayi danasani, ko xan yi yawo tsirara sai na ga bayanta da abinda ta haifa."
"A'a ba zaki yi haka ba kowanni mutum da ƙaddaransa, ki kyale ta da ƙaddaranta ma ya ishe ta!" Aryaan ya fada yana rarrashin yarinyar ya shafa kanta yana faɗin. "Zata yi barci ki kunna mata fanka, Attahiru Shehu Yayari yasan wata rana zata zo da irin haka zai faru, gara da tayi haka kaɗai zai nuna tarbiyyarta. Kin ga illar sharri ba dan aike ne, ka tura wani wurin ya dawo ya wani wurin. Meye amfanin haka?" Kuka ta saka tana jin ciwo haka ta dauki yar ta fita da ita. "Ba ruwanki, ki tsaya inda take. Ba zaki koma ga Allah ba sai kowacce ta zo gabanki domin niman mafita. In sha Allah!" Gyada kai nayi ya koma gefe ya ce min. "Yaushe xaki bani hakuri?"