Showing 138001 words to 141000 words out of 157081 words
da ya fito mutumin kirki ne, shine zai iya buge Musharraf, haka yasa muka goya mishi baya, anyi kome kamar yadda na tsara musu sannan a gefe guda, mun marawa dan takarar gwamna wanda ya fito a partyn Alhaji Saddam Tanimu Jatau, bakiɗaya ahalin aka goya mishi baya tare da al'ummar Zanzabira, kafin a zo wannan stage din sai da na samu Faruq muka yi wani squad team, yadda muka hada da vigilant yan taurin masarautar, yan sanda aka hada aka yi meeting, wanda ua janyo aka yi wani tsari na musamman. Sannan na kara da wani aiki daya na saka Aryaan ya sake Ahmad Rilwani Yayari, Mahfouz Nuru Yayari, Yaron da aka saka ya kashe Abba, sannan aka shafe musu tunaninsu da abinda ya faru, na kyale su domin akwai wani lissafi da nayi idan ja cigaba da riƙe su akwai abinda ban sani akan su ba da masu saka su aiki.
[8/26, 11:31 AM] Ramlat Manga41: 52
Ban san me yasa nake jin wani abu kamar zai faru da ni ba, lokacin da aka saka musu wannan kula fadar tare da security ta ko ina, abinda nq zata Jakadiya Iyaami, tana cikin masu wannan abin domin ko sati ba ayi ba aka kama Jakadiya Iyaami, amma matar nan ta nuna dama can ina bin ta da sharri ita da taso ni tsakaninta da Allah, wannan abin ya saka Mai Babbar daki sauran yan gidan suka ce tabbas ta fi ni gaskiya. "Ummi matar nan tana da hannu akan wasu abubuwan, ki kyale ta ayi mata hukuncin kada ki kare ta."
"Ke wacce irin taurin kai ne." Kallon Hajiya Malika Yayari nayi wacce jini ya mata lullubi har baka hango kanta sai bakinta da idanunta da kunnenta. "Ba zan kyale ta ba, idan kuma kina da abinda zaki kare kanki da ita sai ki yi magana, kin san yadda nake da taurin kai, tow ko kaina bana sauraro don haka ki ja bakinki ki yi min shiru duk wanda ya yi yunkurin dakatar da ni sai na saka a haɗa da shi." Na saka kai zan fita Mai Babbar daki ta ce min. "Ki kyale Iyaami, sama da shekaru aru-aru tana tare da mu."
Juyawa nayi na kalli mai babbar daki kafin na ce mata. "Akan me? Akan me xan barta idan na barta nima zata aikata kome domin babu Allah a cikin ranta." Ban san yadda aka yi ya shigo parlourn ba, nasan na bar shi yana barci ya ce min. "Ki kyale ta, kina janyo magana dayawa kina wuce makadi da rawa. Ke matar Sarki ce ba sarki ba kada ki sake shiga cikin zancen masarautar nan." D'ago kai nayi ina kallonshi cikin kunar rai, na zare hannun shi a saman nawa hawaye yana zubo min. "Zaka yi danasani." Na juya zan fita ya ce min. "Ki min alfarma daya kada ki juya min baya!" Fita nayi ina barin parlourn ya ce musu. "A tafi da Jakadiya Iyaami Faruq, tayi facing abinda ta aikata. Zainaba bata karya ko bata sonka ba zata tab'a maka sharri ba. Ya kalli Hajiya Malika Yayari ya ce mata. " Ki daina kare ta domin kema yana zuwa ta kanki." Daga haka ya juya ya bar parlourn, lokacin da na isa gida takaici yasa na shige daki, ko ta kan Yaran ban bi ba, tunda an yi musu kome, na shiga daki na kwanta. Gabana sai faduwa yake, na kira Umma muka sha hira kafin ta haɗa ni da Maluma, sai na ji sauki haka na kira Yayuna maza da mata har da Aunty Shukrah, kafin na kashe wayar. Ina kwance a wurin har aka kira sallah la'asar, na tashi na shiga ban daki nayi alola sannan na fito gabana yayi wani irin bugawa, dakyar na iya idar da sallah, ina addu'a amma bakiɗaya zuciyata kamar zata fado.
Haka na idar da sallah aka kira ni, wai Yaya ya fadi, hawaye ne ya zubo min dama abinda nake ji kenan, wani irin kuka ne ya zo min amma haka na daure na yi addu'a muka nufi asibiti, a ranar naga har Ayaanah ta damu da Daddynta, bakiɗaya Yaran hankalinsu ya tashi, haka muka zauna a asibitin har dare Faruq ya dawo da mu gidan, barci barawo ne ya dauke ni ga ciki ga damuwa, haka yasa na fara kumbura sakamakon damuwa da rashin barci. Haka yasa idan na zauna nayi nazari kamar rashin Abba ne yasa kome yake zuwa min da nauyi, amma idan na tuna akwai Allah, sai na ji kome ya zo min da sauki tun binciken nan da Aryaan yayi min, aka mishi kiran gaggawa ya tafi babu al'amarshi, haka yasa na fahimci wasu bakin lamari yana faruwa a kan Ayaan sai na rasa ganewa da Yaya zan ji ko da matsalar masarautar domin an hade min kai, tare da nuna na yiwa Jakadiya Iyaami sharri.
Kwanaki uku yaya ya farfaɗo, sai da yayi sati biyu aka dawo da shi gida, asalin rashin lafiya yake, ranar wata juma'a. Na nimo Sadi ya kai ni na ga Baba titi. Kallona yake yana faɗin. "Me yasa kika fito da nauyin jiki haka? Sannan kin bar yaran babu masu kulawa koda yake Akwai Isma da Arfillah ba abinda zai faru da shi, sannan ina miki ta'aziyar rashin da zaki yi a dan wannan tsukun, tabbas zaki yi rashi. Sannan kuma ki tsaya kada ki ji tsoron abinda zasu miki, zasu farmake ki yadda baki zata amma na hango kina murmushi bayan kin yi nasara, wannan rashin da zaku yi shi zai taimaka miki Mijinki ya farka shima basu kyale shi ba wannan kwanciyar da yayi sun tab'a shi amma in sha Allah zai farka ki yi hakuri. Wallahi ba rantse da Rabbul Ka'aba sai kunyi nasara, domin akwai garkuwa da zai kare ki koda yake shima." Shiru yayi kafin ya ce. "Ki yi hakuri ki kara hakuri! Ki koma dakinki, wannan lokacin yaki ne da zubar jini, amma fa Allah zai kawo babban ni'imar da zata wanke bakin ciki da takaici ayi ta farin ciki." Sannan ya rako ni na shiga motar na rike hannunsa, kuka ya zo min."idan kika ji kuka ki yi kin ji ko? Kada ki damu ki yi kukan in sha Allah zaki ji sauƙi."
Gyada kai nayi haka muka dawo gida nayi kuka na kara kuka, na rasa meke min dad'i,
Shima Baba titi sai da yayi kuka, jikokinsa suka zagaye shi da Yaransa suka yi ta tambayar shi. "Tausayi take bani bata da kowa sai Allah, ni na dakatar da Aryaan domin sun yi shiri akan shi, shi yasa na samu Iyayensa su mishi kira kuma ya koma sun rike shi, amma akwai Arfillah a tare d su, bata da kowa sai Allah. Amma konata da zasu yi shi zai kara mata girma da daraja wanda haka zai saka ta kara zama wacce ta san ciwon kanta, shima tab'a su da za'a yi shi zai saka ya san me yake mishi ciwo!" hawaye ya zubo mishi.
***
Ni da Yarana, sai da na zama kamar wata zarariya akansu domin ta ko ina kare su nake, a wannan lokacin hatta waya da turo min sako sai da ya shiga firgita ni, domin idan aka turo min gargadi ne akan ka kyale Jakadiya Iyaami, amma nayi biris da su, a cikin wanda basu juya min baya har da Salim da Abdulhafiz, Alhaji Mamman Abba yayari, Hisham wnada ya dawo gidan da Amir, suka mara min baya. Kwanaki suna ta shudewa, haka yasa na hakura da tashin hankalin da me zai faru da ni.
Yau Laraba tana cikin kwanakin da ba zan manta ba a rayuwata, Yara suna waje tare da Ijlal da Nadiyyah, ni kuwa ina dakin Yaya ina bashi magani, muna cikin dakin muka ji ihun Ijlal tana kiran sunana, sai da gabana ya fadi ya kalle ni. "Me ya faru?" "Bari na duba!" Haka muka fito ina rike da hannunsa, muka fito Amiratul Zaitunah take aman jini da kumfa, fa ciki ga nauyin da nake ji haka na dauki Yarinayr muka nufi asibiti shi kuma ya xauna da sauran Yaran kanshi a sunkuye. Bayan mun bar gidan ya kalli Nadiyyah da take zaune ko a jikinta. "Me kike so Nadiyyah? Ina sane da ke, duk yadda nayi pretending kamar ban san kome ba!"
Zare idanun tayi tana faɗin. "Me nayi kuma?" "Kina nufin ba ke bace kika bawa Amiratul Zaitunah wani abu ba ne?" Kallonshi tayi tana mamakin yadda aka yi yasan da haka. "Na sani na ga haka tun daga dakina, na ga lokacin da kike saka mata abu a baki. Me kike so?"
"Kashe min Yaron cikina ta kashe min, ta kuma yi min duka sai da cikin jikina ya zube gaya min idan ban kunsa mata bakin ciki me zan yi?" "Kema ai min mata illa ko kin manta ne akan ki na dake ba halin ta sake haihuwa? Ke wacce irin son zuciya ce take damunki, yanzu idan wani abu ya sami cikin jikinki fa? Baki san Allah zai saka mata ba!" Yadda yayi mata magana yasa tayi shiru, mikewa yayi ya koma cikin inda ya tara Yaransa a dakinsa, haka na dawo na kara hada kayan da zasu bukata, na bada Madinah ta kai musu, na shiga dakin ya kalle ni. "Ya jikinta?" "Da sauki sosai!" Zama nayi ban ce mishi kome ba. ",ki yi hakuri!" Murmushi nayi na ce mishi. "Ijlal zaka bawa hakuri ita ke cuta ba ni ba" na fada ina mikewa, na nufi dakina na kwanta Yaran suka zo suna tambayata ya jikin Amiratul Zaitunah, murmushi nayi nace musu da sauki, haka nayi ta musu hira na gaji amma haka nayi wanka da sallah muka ci abinci har da Nana A'ishah. Bayan ishe a dakina suka kwana dukkansu.
Na gaji ainun, haka na kwanta ina barci cikin dare Ya shigo ya tashe ni, na bishi dakinsa, duk da bai da lafiya amma fa generator dinsa yana service yadda ya dace, lokacin da na fito dakin na ga Nadiyyah a tsaye a barandarta. "Duk da ciki ai a hakura da juna!" Ban kulata ba, na wuce nayi wanka na tashi yaran suka yi fitsari, da wuri muka wuce Asibiti da Yaran duk da Allah ya jarabci yarinyar da jinya mun same ta ta warware kamar ba ita ba, muka yi ta mata wasa sai Yamma muka bar asibitin yan gidanmu sun zo duba ta, domin Ijlal ta koma kamar wata yar gida, bayan mun dawo take gaya min Iram da Ya Abid sun zo .nayi ta murna kamar nayi Yaya.. washi gari aka sallame ta. Ni dai abin na ta damuna karshe na ce mata. "Wai me yasa kika daina daukar zafi a kaina?".
"Saboda Mutumin da yake tsaya min ko Aurena yana watagaliliya ya rasu. Shi ɗaya yake tsayawa wanda bai haifa ba, sai na fahimci yasan ina kishi da ke amma kuma bai daina min fatan na shiryu na zauna lafiya da ke ba, ya sha gaya min idan nayi yaji ya ce min na yi hakuri na zauna da ke baki da matsala sai taurin kai da kafiya! Akan me ba zan sauya ba, ko Uwata da ban santa ba. Ban ji mutuwarta kamar na Abba ba, idan har wannan ita ce shirya tow Abba ya jima yana min fatar ma shiryu kuma na daina sai dai ban sani ba domin kishi dai ina da shi, kuma ina takaicin ganin kun shiga kun rufe ko..." Ganin Nana A'ishah da gudu na ce mata "ya isa mai b'arota!" Dariya tayi tana faɗin. "Shi Namamajon fa!"
"Ijlal munafuncin da ake fada kuna yi ashe da gaske ne!" Juyawa nayi na kalle shi kafin nace mishi. "Munafunci kuma ai bamu yi kama masu yi ba!" "Mammy ina Ayaanah?" Inji Ayaan "Ba suna wasa da keke da Ayaaz ba?" Babansu ya bashi amsa, "Mammy ina Ayaanah?" Sake kallonshi nayi fuskarshi tayi wani irin ja, gabana ne ya faɗi na fito da sauri na ga Princess a zaune wuri guda kamar wacce take kallon wani abu, tab'a nayi ta kwala ihu tare da rungume ni. "Mene ne?" "Ba zan fada na rantse ba zan fada ba, ban ga kome ba kada a yanka ni.." ta kai maganar tana mai zubewa a jikina, gabana ne ya tsananta faduwa, haka ya dauki Yarinayr yayi cikin gidan da ita ni da Ijlal muka shiga niman Ayaanah muna kiranta amma ina, haka na gaji na zauna bakiɗaya tausayin yarinayr ya cika min rai, haka aka yi ta zaga gidan ana niman Ayaanah amma babu alamarta. Cikina wata bakwai da sati uku ne, ina ga tashin hankalin da nake ciki ya janyo min nakuda Babu shiri, a ranar Yaya ya duba Cctv babu iyaka, ga dai lokacin da take wasa akan keke ita da sauran Yaran, ga lokacin da take kallon wurin ita da Princess ta bar wurin, ita kuma fuskarta da fara'a ta nufi wurin, daga nan daukar yatsa cak, a ranar na san cewa wato duk abinda yake yana sane iskanci ne da renin wayo domin yau bakiɗaya ya tara yan gidan ya ce musu. "Ku fito min da Yarinyar da dayanku ya dauke ta, idan kuka sake aka fito sallah azhar babu ita wallahi sai na saka a muku yanka rago.........
[8/27, 6:48 AM] Ramlat Manga41: 53
Sun zata wasa yake sai da ya saka kiraasa manya guard da suke kula da harkokin team ɗinsu na tsaro hankalin kowa ya tashi suka fara rantsuwa bashi bane bai ga kome ba, ai kuwa ya bada umurnin ayi ta gana musu azaba a cikinsu har da Madinah, dama haka abin yake? Ganin za'a hallaka su, daya cikin masu aikin girkin ya ce musu. "Na ga Jakadiya Iyaami ta zo, ban san yadda aka yi ta fita ba! Amma tazo gidan nan iya abinda na gani kenan wallahi." Yana fadar cewa ya ga Jakadiya Iyaami a cikin gidan Laminu daya daga cikin masu tsaron kofar ya mike tare da ciro abu a kugunsa, kafin ayi wani yunkuri ya yanke wuyarshi ya fadi a wurin cikin jini. "Faruq kada ka bari a fita daga cikin masarautar nan, a binciko Jakadiya Iyaami duk inda ta shiga, ita kuma Zainab kada labari ya je mata!" Ya mike ya fita shima, aka bazama niman Jakadiya Iyaami, ni kuma na nufi cikin gidan, can inda aka tanadi ruwan wanka a swimming pool, can naji kamar ana tunkud'a ni, ina isa wurin na ga yarinyar a saman ruwa, ji nayi abu yana zuba a kasana, na dafe cikin, saboda tsananin azaba, niman kuka nayi na rasa bakiɗaya na rasa me yasa sai ni ni ni, me innocent soul tayi da za a kashe ta? Durkusawa nayi a wurin, ina kallon gawar yarinyar cikin wani irin so da kauna. Idanunta yayi wuri-wuri, kallonta nake cike da tausayi domin naga tsoro da firgici a cikin idanunta, da alamu kisar karfi aka mata, ina durkushe na rarrafa da kyar na nufi bakin ruwan na saka hannuna a cikin ruwan. A hankali na janyo kafana na fada cikin ruwan, nayi ta ninkaya na isa inda take na rungume ta, a jikina. "Mariama! Ga Mammynki! Mariama na zo kin ta niman ceto ko?" Na rungume ta ina jin hawaye na zuba min. Ihun Ijlal na ji tana faɗin.."Miko min ita Ikhlas, Innalillahi wainnalihir rajoun, Wayyo Allah na, me angel tayi musu!" Wani lokacin haka take kiranta wai sunan suruka ce, kasa mika mata yarinyar nayi, ji nake kamar zan ji numfashinta, amma ina haka ta juya da gudu ta kira security, aka zo amma naki basu yar ina rungume da ita, can suka kira Yaya, shima ya zo tare da Mai Babbar daki, amma naki kula kowa, ina rungume da ita ina jiran ko zata yi numfashi, na tabbatar musu bata mutu ba, nafi awa daya a cikin ruwan domin har sun fara kwashe ruwan ana zubarwa. Ina rungume da yarinyar a kirjina, ga cikina da yake juyawa jiran lokaci yake ya zo duniya. Shigowa cikin ruwan Maluma da Umma suka yi, Umma ta amshi Yar a hankali tana faɗin. "Masu hakuri suna tare da Allah, da sannu Ubangiji zai miki sakayya!" A hankali na sake mata yar na dafe cikina, mai babbar daki ta ce musu. "Ku watse!" Ba musu suka bar wurin. Hatta Nadiyyah da hankalinta yayi mugun tashi, haki nake Maluma tana rike da ni, durkusawa zan yi ta kira shi ya dauke ni cak ya kwantar da ni a saman, Maluma ta fito ta ce mishi. "Kazo bayanta! Babu lokaci ku Mai Babbar daki hado mana kayan karban haihuwa." "Shi Kenan!" Ta koma ciki, ita kuma ta cigaba da yi min yan dabarbaru tana tambayarshi. "Wata nawa ne cikin?" "Bakwai da sati uku!" "Ba matsala ai!" Zuba yake karyo min, ta ko ina jinsu tana tambayar shi yadda aka yi yana bata amsa cikin jimami, zuwan Mai Babbar daki da wani kit wanda Ijlal ta nuna mata, domin tazo sau biyu tana ganin ina hada kayan, haka ta bata, hankalinta a matuƙar tashe. A can cikin gidan Umma da su Bilqis da Daulah suka cigaba da hada ruwan wankan gawa.
"Maluma!" Na kira sunanta da karfi, d'ago kai tayi tana kallona.."Maluma sun kashe min Y'a!" "Ki fuskanci matsalar da yake gabanki kin ji!" Damke hannunsa nayi da karfi xan yi magana naji numfashina da kome yayi wani irin zuwa da ƙarfi kamar zai bar gangan jikina, a hankali abin cikin ya fado a hannun Maluma, ta dauka a hankali tana mai nad'e shi cikin mayafi. "Mace ko Namiji!" Yaya ya tambaya, Dariya tayi ta ce mishi. "Ba mamaki Abdullahi aka samu;" ta fada tana murmushi, jikinsa ne yayi sanyi, a hankali tayi ta tausa