Showing 48001 words to 51000 words out of 157081 words

Chapter 17 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

22

vigilant suka nausa cikin gari, basu bar cikin gari ba sai ga motar kauraye da karnukansu, mutanen Goga domin yayi dawa can baya, suka nausa cikin dajin bayan sun yi tafiya mai nisa.

Wannan abin da kowa yake gudu na karyewan, munnunar sana'ar da aka jima ana yi, yau Allah ya hankad'o wurin da aka jima ana.zargi wanda babu wanda ya isa zuwa wurin.

Haka suka yi ta shiga dajin, har zuwa cikin ware house babu kowa a wurin sai dai wani ikon Allah an samu abubuwan da ya bawa kowa mamaki. An samu robar almajirai, an samu kayan yan mata irinsu Braziya. Yan kunnaye da wasu abubuwan da Allah kaɗai yasan yaushe aka fara. Don haka da aka shiga cikin gidan ma da karnukan wasu manya-manyan firiji aka samu shake da sassan dan adam, da wani daki da ake ajiye mutanen da suka mutu.. Faruq ya isar da sakon, ga Shugabanshi.

Kafin wani lokaci an turo masu bincike, ciro wani karamin towel din Zainab Faruq yayi ya durkusa gaban wani kare da tunda suka zo da shi yake zaune, "Goga kace naka ne?" "Eh Mai gida!" "Kuma dai iya biyo mana kamshin Fulani Babba?" "In sha Allah!" Saka mishi towel din yayi a hanci. Yayi wani haushi mai karfin gaske sannan ya ja da baya da gudu ya shiga bin wata hanya ana binsa a dai-dai wani wurin ya tsaya yayi haushi yayi haushi, wuri ne babu alamar kofa, haka Faruq ya shafa jikin bangon, kafin ya fara bubugawa, karar da yaji ya saka shi baya ya daki wurin amma bai bude ba. "Mai gida akwai wani abu ne?" "Kofa ce!" Haka suka yi ta ƙoƙarin buɗewa, har suka kasa, karen nan ya cigaba da duba wurin can yana zuwa wani waje kamar an tura shi wurin dai gashi kofar ya bude juyawa suka yi wurin kare suka ga ashe ya taka wani wuri ne da sauri wasu suka isa wurin suka matsar da shi, take kofar ta bude bakiɗaya Faruq ya saka hannu ya ciro bindigar shi a bayan wandonsa, sannan suka shiga cikin gidan.

Suna tafiya har cikin wani stair suka shiga sauka a cikin gidan, suna kiran sunanta. Wani irin kara faruq ya ji dakatawa suka yi ya ce musu.."ku koma akwai bom!" "Mai gida ai sai dai ya tashi damu." Suka fada bayan sun rufa mishi baya. "Fulani Babba!!" Ya kwala mata kira." "Ku taimake mu!" Suka ji ihun mutane, da sassarfa suka isa dakin. A hankali suka nufi inda aka saka suji ihun, yan mata ne a dakin sai bom da aka daura. A hankali Faruq ya yi baya ya dauki wayarshi. "Ku shirya masu kunce bom su shigo!"

Ban minti goma sai ga su, dole aka matsa musu suka warware bom din kafin suka buɗe musu kofar. "Kun ga wannan matar?" Faruq ya nuna musu hoton Ikhlas, wata cikin yan matan ta ce mishi. "Wata mai ciki ko?" "Eh ita ita!" "Sun fita da ita naji suna cewa za a kashe ta a cire abin cikin!" Wani irin hadiye yawu faruq yayi zuciyarsa tana rawa, ya dauki wayarshi ya kira shi. "Yallabai bata nan!" "Ina take?" "Wai sun fita da ita!" "Faruq try your best!" Ya fada da karfi, "ok Sir!" Haka ya koma wurin yan matan. "A ina aka ajiye ta!" Nuna mishi dakin suka yi. "Tunda aka kawo ta bata ci kome ba har ruwa bata sha ba." Shiga cikin dakin yayi yana kallon ranshi ne yayi wani irin b'aci, ya ga har da Camera a dakin. A hankali ya fito ya shiga bin dakunan har ya isa computer room din. Haka ya isa ya bude dakin ya duba abinda zai duba videon Ikhlas kasa gani yayi ya dauke kome na dakin ya fita, kiran Mai gidansa yayi ya ce mishi. "Sir sun san zaa faddaa bincike bamu san inda suka kaita ba!"

Kamar ya dirko ta wayar yake ji, haka suka gama binciken, kafin suka fito wata cikin yan matan ta ce mishi. "Akwai inda almajirai suke ko zaku duba ba ne!" Kallon agogon hannunsa yayi, ya ce musu. "Maza a samu a ceto su!" Haka kuwa aka shiga bin inda suke dakyar aka samo su, a can gidan karkashin kasa, suma an saka musu bom din, sai da aka kunce ana fito da su, ware house din ya kama da wuta, haka suka fita a daidai lokacin da yan sanda suka iso, tare da bude wuta a sama. Wannan wani case ne na musamman..

***

Ni dai ban san inda aka kawo ni ba. Amma naji wurin kamar babu mutane sosai, sannan can can nesa da ni ina jin kamar karar mota ko karar wani abu, lokaci zuwa lokaci ana zuwa a duba ni, har lokacin yunwa nake ji. "Ki ci abinci, Mijinki yana can yana sauke masu rawanin fadarshi saboda ke, sannan."

D'ago kai nayi na ce mishi. "Na tambaye ka ne?" "Me yasa kike jin kanki ne kamar ke ce Sarki Faris?" "Jinin da ya hadu ne da ahalin malamai da ahalin sarauta, gaya min me kake bukata da ni?" A hankali ya tura min jakar abincin shagon Brandy. Juyar da kaina nayi domin yau ina jin cikina yana wani irin dunkule da buɗewa..

A ranshi yake cewa.

She fears absolutely nothing that's in front her knows exactly who's behind her. Murmushi yayi ya ce mata."me yasa baki jin tsoronmu?" "Ni ce zan ji tsoronku? Bayan ina da Allah da miji irin Salmanu Faris!"

"Ina sonki!" Ya furta yana kallona, murmushi nayi na ce mishi. "Mijina likitan ƙwaƙwalwa ne, sannan silently mahaukaci ne a kaina, ka addana kalaman domin ina ji kamar na kashe ka da hannuna!" Duk da fuskarshi a rufe yake, amma naji na tofa mishi yawun bakina, amma ina babu yawun ma sosai. "Da gaske ina sonki!" Ban san lokacin da na tofa mishi yawun ba, "are you wish your death?" Na tambaye shi, na ga yadda ya share yawun yana kallon inda nake ya dauki hanky dinsa ya goge sannan ya mai da aljuhunsa. "Ina sonki!" Ban san lokacin da na kifa mishi mari ba, domin wannan shine tozarcin da aka yi min a Rayuwata. "Still ina sonki!" Ban san lokacin da na fashe da wata irin kuka ba, mai yasa yake gaya min magana irin haka..ina dafe da cikina da yake wani irin juyawa. "Ba zan miki kome ba, sai dai ina jiran ranar da zaki kira ni, kin amshi soyayyata. Ni zan zame miki kamar bakar Inuwa ne!"

.. daga haka ya mike zai fita ya ce min. "Idan kin so zaki iya tafiya ba mai dakatar dake! Amma ki ci abinci!" Daga haka ya fita. A hankali ya nufi waje.

Salim Attahiru Shehu Yayari ya cire face mask din da ya saka, yana mai ciro hanky din da ta tofa mishi yawun bakinta, sai fuskarshi da ta mara. "Yarinyar nan zata fita a gidan nan, kada na ga wani a cikin gidan nan!"

"An gama ranka ya dade, sarki mai jiran gado!" Sannan ya wuce yana mai kallon gawar mutumin da yake kwance. "Ku wurga shi can daji, dabbobi su cinye namarshi. "An gama ranka shi dade!" Wucewa wurin motar yayi ya shiga, ya kifa kanshi yayi a kan motar. A yanzu dole ya kyaleta ta bar dajin ta koma gidan ta haihu. Shi ya fara kaunarta tun daga ranar da suka je barkan haihuwarta, ya sha bawa Mahaifinsu labarin yadda yake son Ikhlas, amma mahaifinsu gaya musu yake ita din matar dan uwansa ce, dukar kan motar yayi yana faɗin."na ga samu na ga rashi a yanzu kuwa kowa sai dai ya rasa!"

Tsit garin ya dauko ko nace dajin ya dauka, hawaye da yake cike da idanuna suka zuba. Dafe cikina nayi a karo na biyu da naji yayi wani irin juyawa! Kallon dakin nayi da yake cike da duhu. Marana ne ya daure min, tun kwana uku da suka dauko ni nake jin wannan yanayin! Ji nayi kukan ma yaki zuwa. Na mike a hankali na leka babu kowa a kangon, a hankali na tab'a kofar naji a rufe to ina suka je? A hankali na ga kofar ya bude nima, fitowa nayi na ga babu kowa a gidan. Kafana ne ya rike tam. Na ciza lips dina na tsaya ina nishi. Can da ya sake ni na shiga tafiya ko gabana, bana gani saboda duhun dare sai kukan kwari. Ganin na fita a gidan na ji kamar ana hankad'a ni ina wani irin sauri kamar xan tashi sama, gudu gudu sassarfar sassarfa haka nake tafiyar, ban san karfe nawa na dare ba ne, amma nasan nayi tafiyar da ta kai dole ne fara jin abu yana bin kafana! D'ago kai nayi sama ina kallon garin yadda yayi duhu. "Yaya ba zaka zo ba? Yaya kana ina?" Na fada a matuƙar gajiye."

Haka na cigaba da tafiya a hankali ina jin ciwon na ta'azzara, kuma na kasa tsayawa. Haka na cigaba da tafiya har zuwa rabi da kusan kwatar dare. Hannuna na saka na shirfe zufar da take karyo min wanda ya kara min hango nisan daren sama da kowani dare a rayuwata. "Yaya kana ina?" Na kara fada a hankali saboda yadda cikin ya dunkule yayi ƙasa sosai. A daga nesa kadan na fara...

08130269641

5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint 500₦

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: Turaren wuta na daki

Turaren kaya (kabbasa or wardrobe balls)

Turaren jiki

Humra

Mopping musk

Turaren wanka

Halut *Hawaii *Sudanese kindakay *Kabba *Farce*Gabgab

*Oud balls *Dufr dollar

*Sudanese anfar

*Sudanese makmariyya

*Sudanese oils *Sandal

Ga masu sayan daya daya ko sari zasu iya tuntubar wannan number

07040840623

Hango haske madadin nayi farin ciki, sai na tsinci kaina da tsoron mai zai faru, haka yasa na shiga tafiya ina dafa bishiyar da yake gefena, Allah ya gani na gaji, jin kafana kamar an daure ni a wurin, yasa na fara zare idanuna..zamewa nayi tare da jingina a jikin bishiyar. Kalamanshi ne suka fara yawo a kunnena. _Ko ban kasance da ke ba, har Abada ba zan nisanta kaina da zama a gefenki ba Ikhlas, zan rike hannunku na taya ki haihuwa a duk halin da nake i will be on side!_ wani irin haki da nishi nake a lokaci guda na cire shegen pant din na wurga, na kara jinjina da bishiyar, tare da zamewa kaɗan. Na rasa mai zan rike, kiran Allah nake kawai bayan nan babu me taimako a cikin dajin nan. Babu kowa. "Ya Allah! Ya Allah!! Ya Allah!!! Kai kaɗai ka rage min! Allah ka kawo min sauki da sassauci!" Na fada da karfi, tare da sake wani irin nishi. Amma ina ciwon yaki zuwa sake mai da kaina baya nayi kamar zan mutu haka nake ji kai wannan zafin akwai abinda ya kai shi ciwo kuwa?

***

Kallon Faruq ASP Daniel Johnson Tufka yayi, yana murmushi ya ce mishi. "Me ya kawo ka nan, Sir Faruq Hamza!" Cike da mamaki yake kallonsa. Murmushi yayi ya cigaba da bada umarnin abinda yake gabansa. "Sir CP ya turo ni akan maganar shiga wannan wurin da aka yi!" "Ka gaya mishi Mai Martaba Sir Salmanun Faris ya turo ni,." Daga haka ya wuce ya cigaba da bada umarnin sannan suka fitar da kayan zuwa cikin gidan da yake ci da wuta kafin wani lokaci ya rushe sai kura da yake tashi, sannan suka fita daga dajin da yayi wani irin yanayi na sanyi da zafi saboda karfin lalacewar tsafin da yake cikin dajin. Lokacin da aka iso cikin garin a nan Aka wuce da Yan matan asibiti, amma madadin ayi farin ciki sai ga hukumar yan sanda sun cika fadar ana kalubalantar Salmanu Faris akan abinda ya bada umarni, haka yasa ranshi yayi azabar b'aci, ya ce su bar fada ko kuma ya basu mamaki, dayawan mutane basu yarda zai iya daukar mataki ba, sai da suka ga motar jami'an tsaro ya kama da wuta, haka yasa kowa ya ja da baya, daga saman hasumiyar ya cewa Faruq. "Ba sai kayi magana ba, kada na dawo nan na ga koda dan sanda daya ne!" Ya juya ya fita, bai tsaya ba can tsohuwar ganuwa ya isa. Bai tsaya ba kai tsaye dakin Ikram ya nufa. "Ya same ta kamar yadda ya daure ta, ya ja kujeran ya zauna. "Kwana biyu kafin b'atar Zainab kin fita daga wannan tambayar ba zan kara miki wani ba amma tabbas zaki gane Allah da girma yaƙe gaya min, ai nasan aljanar da take tare da ke."

Cikin azabar da take ciki ta ce mishi. "Ba zaka iya min kome ba,.sannan idan Junaid Gobir yasan da abinda kake min kana tsammanin zai kyale yarsa ce?" Dariya abin ya bawa Salmanu Faris ya ce mata.."Allah kin haukace, waye ya gaya miki ba zai ce wani abu? Ai shi yanzu yadda yayi amfani da ke ya kafar yarsa kaf duniya babu wanda ya isa shiga fadar kamar yadda Malam Junaid ya shigar da yarsa, kina wasa da Malamai ance miki zai kyale ki ne, ki lalata auren yarshi? Mahaukaciya idan na sake ki darajarshi ce zata zube, amma zan barki ki ga yadda Uba yake tsayawa yarsa!" Ya kunce ta yana murmushi ya ce mata.."ina jin zaki kara gudu ki gudu domin zata dawo!" Daga haka ya juya ya fita, ita fa tunda ya warware mata maqarqashiya da Malam Junaid ya mata sai da ji ashe kaf duniya babu wanda ya rena mata hankali, kamar ta fasa ihu sai da ta ji kamar bata da zuciya a kirjinta, duk da taki magana amma kuma tayi mamakin yadda aka yi ya samu kwarin gwiwa har haka.

Har zuwa dare babu wani labarin, wurin karfe shida na yamma Salim Attahiru Shehu Yayari ya iso masarautar Zanzabira a matuƙar gajiye, yana mai nufar bangaren Mai Babbar daki, ya zauna yana jajjantawa kamar bai san kome ba. "Allah ya bayyanata, ya tona asirin duk mai hannu cikin wannan lamarin, na ji ashe kaninta ya rasu shima, Innalillahi wainnalihir rajoun!" "Wallahi kuwa abin ba a magana sai godiya!"

Haka suka ta jajjantawa shi da Jakadiya Iyaami domin kuwa mai babbar daki bata iya magana mai tsawo ba tare da kanta ya amsa, sai Aneesah da take ta chat dinta abinta, kallonta Salim Attahiru Shehu Yayari ya yi ya ce mata. "Ke baki damu da halin da ake ciki bane?" Mikewa tayi ta ja tsaki ta ce mishi. "Allah yasa bandits din su kashe yar iska tunda dama can yar iska ce!" Ya bar dakin ji yayi kamar ta watsa mishi wuta, ya bita da idanu. Yana jin wani abu yana yawo a jikinsa, ya mata a goge mata zeron da yake kanta.

Haka ya bar parlourn ya nufi bangaren mahaifiyarsa.

***

Kaf ahalin gidan Yayari suna cikin dimuwa domin Sarki Shago ya hana kowa barci kai baka isa ka koma daki ba kowa na tsaye akan kafarshi. "Ina Ikhlas take? Ina ta shiga?" Inji Hajiya Kubrah da hankalinta yake tashe, yau kwana uku amma babu ita babu labarinta. Ƙarar motar yan sanda ne ya cika gidan. "Kai Faruq kace kada su ketare wannan iyakar su juya! Awatif tana hanya." Haka aka suka hana yan sanda shiga gidan. Suka juya.

Yana tsaye a hasumiyar masarautar sanye yake da shigar sarauta. Mai Bauchi ya shigo wurin. "Allah ya baka nasara mai babbar daki ta farka!" "Hmmm!" Ya ce idanunsa yana kan hanyar shiga birnin! "Ranka ya dade!" Hannu ya d'aga mishi, a hankali ya dafe gefen zuciyarsa. "Tana kirana!" Haka ya wuce mai Bauchi ya fito waje, dagarai da bayi basu san me yasa suke wani irin biyayya a gare shi ba, amma tabbas babu me iya koda tari ne a cikinsu. Kowa tsoron wannan sarkin yake ya sauya bakiɗaya. Tare shi Faruq yayi yana faɗin. "Ba zaka fita ba sai dai ka sare kaina sai ka wuce!" Wani irin riko wuyar Faruq yayi cak sama ya ce. "Kul Bargaga!" Ya cilla shi can, ya juya ya bar wurin Faruq ya tashi da kyar ya bi bayanshi. Koda ya fito ya hango shi ne can yana tafiya da gudu ya bi bayanshi, yana mai cewa.."Yallabai ka kashe ni domin ba zan iya barinka a wannan yanayin ba." Wani naushi ya yiwa Faruq a ciki ya fadi can, sannan ya cigaba da tafiya, haka ya sake bin shi.

"Ya Allah ka gafarta min zunubaina, Ya Allah ka kawo sauki da dauki Ya Allah ka kare Zainab da abin cikinta! Ya Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkaka, Ya Allah nayi imani da kai, na yarda da kai Ya Allah ka kawo min dauki bani da tsimmi ba ni da dabara!" Jin wannan addu'ar da yake yi yasa faruwar mikewa ya cigaba da binsa, har suka iso wajen gari a kafa shi mamaki ma yake yadda tafiyar kamar an rage musu ita tsakanin wajen gari da cikin gari akwai tafiyar kusan rabin sa'a

**

A daidai gabbar da na gama cire raina da samun ceto, a lokacin na ga Ismaha a gefena, tana min kuka itama. Cikin azabar ciwo na ce mata. "Ismaha kece?" Wani irin doro ta yi min tare da kuka mai karfi a hankali wuta ya kama dajin, azabar ciwon da nake ji bai hana ni fahimtar kofar gidan da nake ba, "Ya Allah!" Muryan Baba titi ya ratsa dodon kunnena, "Tasi'u? Zaka iya kawo mana shi a wannan lokacin?" "Eh Kaka!" Ya fada cikin wani irin murya, hannu na mikawa baba titi ina niman abinda zan rike na samu na fitar da abinda ya tokare min gabana, aiki aka ce da ayi min saboda yaran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login