Showing 63001 words to 66000 words out of 157081 words

Chapter 22 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

27

amshi kiran, ba Walid na domin Walid yana can fada, ya bar wayar babu charge. Sai Walid ya turo shi ya dauki wayar, anan yana jin haka, shi kuwa ya kira Gwaska dakare da Rilwani Yayari ya gaya musu, su ma domin cimma wata manufa nasu suka jefo irin da wayo.

Wannan abin ya musu dad'i, tana zuwa ya ce mata.."ki yi hakuri Walid Yayari ya ce na kai ni domin yana tare da Salmanu Faris." Jikinta bai yarda da shi ba, amma kuma bata son Mahaifiyarta ta ci galaba akan Zainab da Yaranta. Haka yasa babu shiri ta bishi, suka cigaba da tafiya sai dai suna zuwa karamin titin ya tsayar da motar ya koma wurinta ya ce mata.."idan aka ga muna tafiya a tare da ayi zargin wani abu ko zaki dauko daga motar ne ki shiga nawa? Idan yaso sai na saka a dawo dake nan!" Kamar zata ce mishi a'a amma yadda ya mata kwarjini sai ta fito da jakanta, ta bishi zuwa wurin motarshi ta shiga ya amshi key dinta ya nausa karamin titi, ya bar motar a wurin. Wannan tafiyar sai da suka yi na minti talatin da biyar, kafin suka isa tsohuwar masana'antu F&F,.kallon wurin tayi ta tuna suna Yara ana kawo su wannan masana'antu, jikinta ne yayi sanyi ta ce mishi.."Kuma suna ciki?" Ya hadiye yawun bakinta. "Eh mana! Ya kike abu kamar baki yarda da ni bane, taso muje!" "A'a ban yi tunanin suna nan ba ne!" "Ok zo muje " ya zaga ya bude mata motar sannan ya juya ya cilla key ɗin motarta, yayin da yayiwa daya cikin Yaran alama da kai, da babban yatsarshi, yana tafiya yana mishi misali da hannu yadda zai fahimta. A hankali suke tafiya har cikin wani lungu tafiya suke har suka isa wani karfe da zai kai mutum wani wuri na musamman. Suna tsaye ya kalle ta yana murmushi ya ce mata. "Sunana Mahfouz Nuru Yayari, me sunanki?" "Iram Junaid Gobir!" "Me yasa kike son tonawa Mahaifiyarki asiri?" "Ban san me yasa na gaji da wannan yanayin ba, amma duk mutumin kirki ka tab'a ganin anyi nasara akansa? Tun muna Yara take yunkurin cutar da Ikhlas bata taɓa nasara ba ka ga kenan duk wnada Allah ya bawa sa'a ba zaka tab'a iya nasara akanshi ba, kamar yadda ka dauko ni nan, nasan yadda n a shigo bai zama dole na fita da kafana ba sai dai gawata!" Ware idanu yayi yana kallon yadda ta san shirinsa. "Me yasa kika gano ni?" "Saboda wannan tsohuwar masana'anta ce, kuma mallakar Four Friends ne, nasan shi tun ina Yarinya yar shekaru biyar nake zuwa nan! Salmanu Faris ba zai tab'a zuwa nan domin ganawa da ni ba, Haka Walid Mamman yayari ba zai tab'a zuwa nan domin ya gana da ni ba bayan nasan he crushing on me!" Wani irin mari ya sakar mata kanta ya bugu da wani karfen jikin abin. "Ina abinda kika karbu daga hannun Alhaji Nafi'u da mahaifiyarki?" Dariya ta kama yi tana faɗin. "Saurin me kake ai tuni sakon ya isa ga Salmanu Faris Attahiru Shehu Yayari." Ta kama dariya tana faɗin. "Tun lokacin da ka dauki kiran na kara turawa....................

*I'm not perfect but royal politics is my favorite perfect story zaka yi ta tunanin shin Hausa novel ne ko English! Zaka ta tunanin haka a ranka anya ba wani drama aka juya ba Laaa baiwa ce da Allah yake bawa mutane musamman marubuta idan ya karkace ya rubuta labari zaka iya daukar shi a wani mataki na musamman, Royal politics yana kara min wani irin ilimi da sanin halin mutanen da suke around dinmu na godewa Allah da ya haɗa ni daku a duniyar makaranta wannan shine abinda zan iya yiwa Ubangiji godiya akan wannan baiwar da ya min dare ku ayi hakuri jiya na sayo power bank ne domin har yau babu wuta good morning beautiful ladies and Gentlemen*

*08130269641*

5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint 500₦

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 23

Cizon bakinshi yayi tare da kai mata duka a cikinta, sai da ta zube akan gwiwarta. Tana rike da cikinta..haka ya shako wuyarta har wani babban filin da ya haɗa Manyan mutanen fadar zanzabira, haka ya watsata a wurin ya shiga dukarta da kafarshi, haka tayi ta amai yana faɗin. "Wannan ba karuwar yarinyar nan ba ce, wai ashe itama wata kwaruwa ce!"

"Bar dukarta haka Son, ka sarrafa haushinka akan Salmanu Faris da Zainab, sai wadancan shegun da aka haifa ka tabbatar ka yi abinda ya dace, ita kuma ka san yadda zaka yi da ita domin idan Alhaji Nafi'u da Rilwanu Yayari suka sani case din zai kara zama wani abu na daban, ita din ba hostage din mu ba ce." "Idan na barta ta rayu zata tona mana asiri, sannan akwai alaka mai karfi tsakaninta da Walid Mamman yayari!" Ya kalli wani mutum da yake wurin zaune amma ya juya bayanshi, ba shi daya ba kusan duk wani da yake fadar sarki zanzabira yana wurin, amma basu yarda ta ga fuskarsu ba. Umarni aya bada tare da cewa. "Ku kashe ta sai ku kai gawarta inda za a samu da wurin!"

Gyada kansu suka ja ta zuwa waje aka jefa ta a cikin wata golf, suka bar masana'antar. Idanunta a rufe tana rike da hannunta da take tsammanin ya karye. Kafin. "Ya Allah ka kawo min dauki, Ya Allah na ambaci sunanka. Ya Allah ka bani damar na rayu domin gaskiya ta rayu." A hankali take addu'a, har ta kira sunan Isma wanda tayi ta kiran sunan tana, amma ta gama cire rai kawai zasu kashe ta haka suka kai ta karkashin gadar dam din zanzabira, suna zuwa wurin suka tsaya tare da fitar da ita daya cikinsu ya ce musu. "Gaskiya wannan karya ba zan iya kashe ta ban lashe zumar da yake tare da ita ba." "Gaskiya nima na yaba da haka!" Haka suka shiga cikin motar, kamar yadda Hajiya Turai take kai Yaran mutane ake lalata da su, ta sayar da wasu. Wasu kuma sun tafi kenan, sai dai kuma dab zasu cimma nasara akan kudirinsu, wani irin iska mai karfi da duduguwa daga ruwan ya tunkaro inda suka, da gudu daya daga cikinsu ya nufi hanyar barin wurin sama ina jifa aka yi da shi sai da kanshi ya bugu da wani dutse da yake can da da gabatar motarsu, na cikin motar ma yana fitowa jan shi cikin ruwan aka yi yana ihu yana kome, haka aka danna shi cikin ruwan, babu kowa a wurin wannan abin ya faru, da kyar ta fito daga cikin motar tana kallon ko ina amma bata ga kowa ba, haka ta dauki ƙaramar jakarta da wayarta. Ta shiga tafiya tana dingishi, gashi babu kowa a wurin, hannunta da ya karye ta rike tana kallon hanya kunna wayar tayi da ta ciro a cikin jakarta. Hawaye na zuba mata haka ta kunna wayar tana kunna wayar, text message bata gama tunani ba sai ga kiran Abbanta. Jikinta na rawa ta dauka. "Abba!" Ta kira sunanshi. Kafin ta fashe da kuka, "Abba kada ka zo da kowa daga Yan uwana kada ka zo da wani kada ka bada labarin inda nake Abba ka taimake ni ban yarda da kowa ba domin kashe ni zasu yi!" Ta fada tana niman inda zata boya, can ƙasar bututun da ake sake ruwan ta nufa ta tsuguna. "Abba kana jina?" "Eh ina jinki Iram!" "Abba idan kazo ka kira ni da karfi zan fito!"

"In sha Allah!" Haka ya fada tare da kashe wayar, kuka take a hankali. Sannan ta saka wayarta a silent yadda tana kallon babu wanda zai kira ta ɗauka. Haka aka yi ta kiranta da layuka daban-daban har zuwa wani lokaci. Abban ya kirata ta ɗauka.."A ina kike?" "Abba ina dam din zanzabira!" "Tow shi kenan gani nan!" Ya faɗa yana kashe wayar.

Malam Junaid da Salmanu Faris da Faruq, da Abid. Haka suka tawo a motar Salmanu Faris tare da wasu jami'an tsaro, tafiyar minti talatin suka yi a cikin minti sha biyar domin gudu suke kamar zasu tashi sama, kafin suka isa kasar dam din, tana kasar wurin bata fito ba duk da taji karar motar da suka zo wurin amma bata fito ba, sai da ta ji suna kiranta. A hankali ta kira number Abba tace mishi. "Abba gani a bayanka!" Juyawa yayi yana kallon bayanshi a hankali take fitowa daga cikin ramin Faruq ya haska torch light din da yake hannunsa. Hango mata tana fitowa ganin zata koma Malam Junaid ya ce mata. "Tare muke Faruq ne!" Haka yasa ta fito daga ramin, Abid ya isa inda take ya rikota, a hankali ta mika mishi hannun mai lafiyar, "me ya samu hannu ɗayan?" "Sun karya shi!" Ta fada tana murmushin karfin hali, haka ya dauko ta cak ya fito da ita yana mai ɗaukarta bakiɗaya har wurin motar, Malam Junaid ya ya ce mata. "Garin Yaya haka ya faru?" Hawaye ne ya zubo mata, ta kalli Faruq. "Sakon ya iso gare ka?" Gyada mata kai yayi ta mika mishi hannu. A hankali ya dauko ya bata, ta mikawa Salmanu Faris ta ce mishi.."Gashi nan a kanshi ne, kuskuren nawa ne!" Haka Faruq yasa Goga ya ja motar suka bar wurin kai tsaye Gidan Malam Junaid suka wuce,

Ina ganin Iram na fashe da kuka, rungume ta nayi ina faɗin. "Sannu!" Baki daya ta sakar min nauyinta. Amai take aman jini, wani irin tsoro ne ya kama ni a hankali aka wuce da ita asibiti, ina rike da hanunta, haka muka wuce asibitin. Kafin wani lokaci labarin ya karade an ganta. Mommy Turai kamar mahaukaciya haka ta zo asibitin. Muna zaune ta zo ni kan kuka nake yi, na rasa me ke min dadi. Ganin Iram a cikin wannan yanayin yana firgita ni gani nake kamar zan rasa ta ne kamar yadda na rasa Tauhid, kaina yana kafad'arshi. Haka muka zauna har wurin karfe daya na dare sai da Maluma ta kira Abba ya zo ya min magana, a hankali na mike Yaya ya rike hannuna muka bar parlourn har xan wuce na dawo na goge hawayen da yake zuba min. Kalaman Iram ya dawo min. "Duk halin da zan shiga kada ki bari Mommy ta shiga inda nake don Allah ke ce zaki iya mata wannan maganar ki ce kin san kome."

"Kada ki shiga inda take don Allah, idan ba haka ba zan fasa abinda kika aikata domin na san kome!" Ja da baya tayi tana mai dakewa, cikin kuka na ce mata. "Ki kyale min ita haka, wallahi ita ɗaya nake kallo a matsayin Tauhid, Mommy ki barta haka don Allah, don Allah ki kyale ta, itama ta huta. Idan wani abu ya faru da Iram Mommy zan aikata kome kada ki sake ki yi wasan da kika yi da rayuwar Tauhid. Don Allah ki tayi!" Haka ta juya ba musu tana tafiya,.kamar zata fadi haka ta jingina da bangon tana hakki ta ce min.."Waye ya kashe min innocent soul? Waye yake bin Yarana?" A hankali na fito ina kallonta, a hankali na ce Mata.."Hakkin jini ne, jinin da kika zubar hakkin al'umma da basu ba basu gani ba, shine yake ki." Na bata amsa na barta a wurin. Kuka na sha tun a motar a hankali Yaya suka kai ni gida har cikin gidan, sai da suka ga na rufe kofar suka dawo, a parlourn na samu Maluma da Umma suna goge da Ayaat dama na san ita zata saka na dawo ba wani ba, ita da Ayaaz shima haka yake da rigima. Haka na zauna na basu nono sannan na shiga daki na kwanta, kusan kwana nayi ina gayawa Allah kukanmu da abinda yake faruwa da Iram Allah ya kawo mata mafita da sassauci, washi gari da wuri na shirya zuwa asibiti, dan barcin da ban nayi ba sai kaina ya fara ciwo, shiga daki nayi kafin Nuraim ya shirya ina shiga ba sai na fara barci ba, haka da Maluma ta gani ta ce mishi yayi tafiyarsa kawai nayi barci.

Ban tashi farkawa ba sai karfe biyu na rana, nasan nayi barci murmushi Umma tayi tana faɗin. "Daga ina zuwa sai barci!" Haka na sosa kaina. "Ga abincin nan ki ci!" Haka na zauna na fara ci, muna maganar Aunty Nu'aymah da tayi sarin wasu kayan kitchen tana zuwa bawa a mall dina tana sayarwa, murmushi nayi na ce mata. "Ai na hada ta da wani agent a china shine kankat a wurin kawo kayan kitchen," murmushi tayi tana faɗin. "Kuma kin ga ya amshe ta tunda wancan karon ba karamin kayan ta kawo ba." "Eh wallhi!" Haka muka yi ta tattauna har Maluma da Hajjah da Abba suka dawo. "Ina ga Hajjah jibi zata koma ɗakinta, wankar ya isa haka su je can na gaji da barci da idanu daya!" Murmushi tayi tana faɗin. "Ai in sha Allah zulumi ya ƙare, " tunda naji an ce xan koma naji hankalina ya tashi, domin kuwa ban san yadda xan ji da miji da kishiyoyina? Bakiɗaya na rasa duk wani karsashina, haka nayi ta zulumi. Kwanaki biyu da suka biyo baya an gama shirya min kayana, aka min kitso da gyaran jiki, dole Abba ya kara mana sati biyu muka shirya, da kyau kafin lokaci kwananki Iram biyar aka sallame ta, ana jibi zan koma. Babu ya gaya min dalilin b'atar Iram amma na share da ta dawo haka Maluma da Umma suka yi ta kula da ita. Yarana kuwa so Masha Allah, haka nayi ta shiri wani shirin da Hajjah ta bani ban san yadda zance ba amma wallahi saboda tsananin kulawa sai da na ji har jikina yana rawa, ana gobe zan koma aka min lalle hannu da kafa, ina kwance ranar wayar da muka yi washi gari wurin karfe uku na yamma Yan uwana har da Iram suka raka ni, gidan Salmanu Faris tare da Hajjah da Tarasulu suka raka ni. Tun daga yanayin bangaren gidan Tarasulu take ambaton Allah, ta kalli Hajjah murmushi tayi hawaye na zuba mata ta ce mata. "Yar nan zata sha gwagwarmayar, amma karshe ita kaɗai zata cire tuta!" "Allah ko kawata?" Gyada mata kai tayi tana faɗin. "Don ma akwai irin juda a tare da ita, sai dai makirci ba dai sihiri ko tsafi zata ga rayuwa." "Tow yanzu ya zamu yi?" "Sharrinsu zai koma gare su kawata!" Yan uwansa har da Ilham da bata zo ba, suka rungume ni tare da wata da na ga yadda take wani shan kamshi, haka suka amshi Yaran ina ta murmushi. "Ya Ummina?" "Tace su huta kafin su zo ganin Abba karami!" Cikin gidan muka shiga, muna hira kamar zasu tsaga gidan, lokacin da muka isa parlour kasa kowa mamaki yake Aunty Shukrah ta ce min. "Amma Mijinku nan sai shi halinsa kalli yadda ya bude kofar da zai haɗaku!" Murmushi nayi haka muka haura sama, matan babu wacce ta fito sai Ikram. Bakin cikin da take ji ba na wasa ba. Haka muka ta zaga gidan aka yi ta min addu'a zaman lafiya. Bayan Magariba aka watse sai jikar Tarasulu da aka kawo min ita wata yar kurma da ita, sai tsafta ta ga gidan wai. Amma Umma ta ce a barta kawai.

Bayan wanda ya kawo ta ya tafi Yaya da ya shigo bayan isha muna zaune a parlourn kasa ya shigo na taka na riko hannunshi, muka wuce parlournshi. Kwantar da kaina nayi a kirjinshi. "Yaya tsoro nake ji;" sumbatar goshina yayi ya ce min. "Gani nan!" Kwantar da kaina nayi a kirjinshi ina murmushi. Wani irin buga kofar aka yi, wnada ya razana mu bakiɗaya sai dai wani irin ihun da muka ji yasa bakiɗaya muka fito har sauran matan, isma ce a saman wuyar Nadiyyah tana yakushinta tana wani irin gurnani. "Sauko Yata kyale ta mahaukaciya ce!" Ya fada yana mikawa Isma hannu tayi tsalle bayan ta yakushe mata fuskarta sai da ta kwarzane fatar fuskar kuwa. Murmushi nayi ina kallon yadda take ihu da kururuwa, ta fita da gudu. Wani irin tsoro ne ya kama Ijlal ganin yadda Nadiyyah take ihu, komawa ciki muka bar su a wurin, anan. Tunda na shiga na zauna shiru ina zaune. "Yaya!" "Ba sai kin ce kome ba! Watannin da baki gidan nan na fahimci halin kowa, Zainab idan nayi kuskure ki taya ni dawo dani kan hanya, Zainab bakiɗaya ja gaji kamar na bude idanu na ga bana raye a duniyar nan, Iram ta gaya min kome. Yanzu haka wani ya fito yana son auren Iram kin san waye?" Girgiza kai nayi ina jin damuwa. "Walid Mamman yayari, da gaske yake sonta!" "Ina tsoron kada wani abu ya kara samunta, Abba ma nasan ba zai yarda ba!" "Shine dai muke fama da shi, amma yaki sam yaki amince." Daga haka ya bar zancen, wayarshi ce tayi ƙara ya dauka yana faɗin.. "kawo min bangaren Fulani babba!" Haka ya iso kofar Parlourna yayi sallama, ya fito ya shigo da katon tire da abinci ya kuma fita sai gashi da basket da kaya kwadayi, haka muka kwashe muka wuce bangarenshi, sallah muka yi na godiyar Allah, kafin ya rako ni muka ɗauki Yaran bakiɗaya zuwa dakinsa, ban ajiye yaran ba sai da nace mishi. "Matanka suna zuwa dakin nan ne?" Juyawa yayi yana min wani irin kallo irin da gaske kike tambaya. "Eh wani abu ne?" Juyawa nayi da Yarana na kai dakina na ajiye su sannan na koma na dauko sauran. "Me kike nufi?" Juyawa nayi na ce mishi.."Miji nake da ra'ayin mu raba da su, ba makwanci ba. Ni tun fil azal ba zan bi dakin miji ba " daga haka na wuce dakina, na je na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login