Showing 147001 words to 150000 words out of 157081 words
ya dace, nace Mata Allah ta ce min. "Zainaba ba don ke ta gari ba ce kin fito gidan da aka san da Allah kina tsammanin kome ba zai lalace ba ne? Gashi Allah gwanin hikima ya daura Ijlal hanya madaidaiciya, gata kowa sonta yake, har mamakin yadda take gudanar da rayuwarta nake, na sha farkawa cikin dare nayi ta addu'a Allah yasa kada ta kara kauce hanya
[8/28, 10:07 PM] Ramlat Manga41: 56
Saboda rashin zaman lafiya babu dad'i, kuma Allah da yake ba azzalumin sarki na ne sai ya daura ni akan ta duk abinda zata yi zata fara tuntubana, wani abinda ya kara min jin dadi da nutsuwa da ita kenan, ibada kuwa wallahi bata wasa da shi, duk wanda Allah ya so da arziki ko ana hamaza hamata sai yayi haka na gani akan Ijlal da Iram.
Mai Babbar daki ta kara tsayawa akan matsayinta, sannan duk abinda Aneesah take ita dai bata mata baki ba, sannan kuma bata shiga lamarinta ba, ta zuba mata idanu kamar bata lura da abinda yake faruwa, sannan tai kamar bata san da kome duk abinda yake tafiya tana sane, sai maganar Salim da Zainaba da take fada tana maimaitawa, tun ana jin abin bakon lamari har abin ya fara damunta domin ita kadai sai tayi ta surutu, da Mai Babbar daki tayiwa Salmanu Faris. Kin kulata yayi domin idan aka duba babu wani ciwon da yake damunta wanda ya wuce hassada wanda shima yana taimakawa wurin haifarwa da mutum haukata. Wanda shi kaɗai zai ta zabura da wasu abubuwan kamar mahaukaci nan kuwa lafiyarta lau ciwo ne da yake tab'a Imani da zuciya tare da hankali.
***
Wani ikon Allah cikin Ijlal wata wata biyar Nadiyyah ta fara laulayi, kamar ba zata kai ba. Ijlal tafi ni rashin hakuri domin cew tayi "malam Namamajo, daga dawowa Sai kuma ciki kai ko kunya baka ji ne? Matar da ta ke yunkurin ganin bayanka, shine daga dawowa har ka dirka mata ciki gaskiya baka da kunya kuma baka jin kunya."
"Ai gara ta gaya maka gaskiya ni har mamaki kake bani, domin gadon jarabtarka idan aka rabawa Yaranka wancan lusarin yaron zai fi kowa wahala. Amma kai ko a jikinki!" Inji Aryaan yana gefe yana kallonshi, kin kallon Aryaan yayi don yanzu sai ya manna mishi hauka, yayi kamar bai san yana yi ba shima ya koya a wurinsa. "Ina magana kayi banza da ni!" Kallonta yayi yana faɗin. "Me zance miki? Matata ce kuma kin san ba haramci ba ne, don haka ki bani wuri nayi aikina." Shiru tayi tana hararanshi. "Aikin kenan daga ka dirkawa mata ciki baka da wani kuzari sai na Fatari!" Murmushi yayi yana faɗin. "Ta nan kuwa babu namijin da zai gwada min iko da lafiya, domin bana zuwa daya ban ajiyewa mace jinina a maranta ba!" Haushi ya ƙara cika ta, ya fada yana kallon Aryaan da yayi shiru kafin ya ce mishi. "Aikin kenan baka iya kome, sai bin mata kana musu barbara!" Hannu ya saka a kunnenshi yana dan sosawa, yana murmushi ya zubawa Ijlal idanun ya ce mata. "Ni fa nafi karfin tuzuru ko Gwauron ko tsohon da ya shekaru aru-aru mara mata ma, ni daidai nake da namiji me mata huɗu, don haka idan baka san yadda ake zama da mace daya ba, kada a dinga sakawa namijin duniya irina baki a lamarin gidansa da na matansa, domin domin ko yanzu na ga Sa'ar Zaitunah zan aura, ashe ni zanci zamanina na ci na Yan Yarana yan mata da yan mazan, mamar twins me kika ce!" Ai kuwa haushi ya cikata, ta mike tare da barin dakin ya juya yana kallon Aryaan da ya tafi duniyar tunani domin da gasken gaske Salmanu Faris magana yAke gaya mishi tare da gori, wani juyawa yayi yana kallon yadda Salmanu Faris yana zabga murmushi, kamar bai san Aryaan yana parlourn, mikewa Aryaan yayi cikin takaici ya fara masifa. "Har ni zaka kalla ka ce zaka yiwa gorin aure? Ni zaka kalla ka kira ni tuzuru ko Gwauron, wato ni ne tsoho me shekaru aru aru, ka dube ni da girma da mutuncina, ka zauna kana cikin zarafina yau zai na koya maka hankali zaka san da ni kake niman magana."
Ina daki ina bawa Annur magani da yake yana fama da mura, tun daga kasa nake jin muryan Aryaan yau kuma shi da waye? Haka Ayaan ya shigo yana kallona. "Mammy waye ya tab'a aboki?" "Hala Abba!" Kusan mikawa Madinah Yaron nayi na sauko kasa ni da Ayaan, dakin Yaya muka nufa, tunda Aryaan yake masifa Yaya bai d'ago kai ya kalli Aryaan balle ya ce da shi yake ba, da sallama na shiga dakin, Aryaan ya nad'e hannu rigarshi yana dukar kirjinshi yana faɗin. "Idan ka isa na miji taso mu gwada kashi!" "Abba!" Ayaan ya kira sunansa, Ni kuwa na kalli Aryaan na ce mishi. "Lafiya?" "Ban da rashin mutunci irin naku yan Adam ace kamar Mijinki ya kalle ni ya ce min tsoho me shekaru aru aru, bayan ya kira ni da tuzuru da Gwauro dube ni ta gidan Uwar waye na zama tsoho nawa shekaruna suke da zai kira ni mai shekaru dubu? Gaya min ta ya zai kalle ni ya ci zarafina yasan yadda cin zarafi yake da zafi?"
"Ya isa zauna mu yi magana kai me ya haɗa ku da Yaya?" "Taya zan baki labarin abinda yayi min gashi nan ki tambaye shi."
"Yaya me ya haɗa ka da Aryaan?" "Waye kenan?" Da mamaki nake kallonshi cike da mamaki na ce mishi. "Yaya baka ganin Aryaan ne?" "Waye kenan?" Anan na shiga rud'ani, na zuba mishi idanu. Kafin na kalli Aryaan, wanda shima ya shiga mamaki da al'ajabi ashe ba iya sune ba ne iya yan iska har da bil adam akwai yan iska da yan guguwa. Tashi yayi zuwa gaban Yaya ya saka hannu yayi yana nuna mishi hannun amma Yaya yayi kamar bai gani ba, nima na shiga rud'ani na ce. "Yaya baka ganinsa?" "Wai waye kike fada haka?" Lallai Yaya da gaske yake na juya ga Aryaan ina faɗin. "Shi bai ganka ba, bai kuma shiga harkanka ba, ina ga ka kwaso haushinka ne a wani wurin ko?" "Ni zaki cewa na kwaso haushi a wani wurin? Wannan mutumin zai iya cinye naman mutum ya kwana lafiya tabbas, wannan ba salmanu Faris da na sani ba ne wannan wani ne na daban." Murmushi Yaya yayi yana faɗin. "Ina ganinka kawai na nuna maka cewa zan iya sauyawa a kowani lokaci nayi kuma kamar ban san kome ba, don haka ka kula da abinda zaka yi. Batun ma kiraka tsoho waye ya ce ka gaya min magana da ba zan rama ba?" Zare idanun Aryaan yayi yana faɗin. "Wallahi kayi matuƙar rena min hankali, bari ka gani sai ka sha mamaki!" Ya nufi Yaya nayi maza na shiga tsakaninsu. "Kasan Allah ba zaka d'aga mana hankali muna zaman lafiya ka tafi sai da safe gobe ka dawo mu yi shara'a."
"Wani shari'ar kaniya? Kallona yayi ya ce min tsoho?" Ni kaina sai na naji abin ya ban dariya, na kalli Yaya na kalli Aryaan da yake huci, ban san lokacin da dariya ya kwace min ba. "Tow kai ba tsoho ba ne?" Kambu da nasan wannan maganar zai kara wani rigimar da nayi shiru, ai kuwa ya kankanta idanunsa. "Zainaba ni kikewa dariya?" Gimtse dariyar nayi na ce mishi.."Ni ba da kai nake ba da Yaya nake!" "Zainaba da ni kike, kawai da shi kike ba." Ya fada kamar yayi kuka Ayaan ya ce mishi. "Zo muje Abokina!" Ya mika mishi hannu, haka ya rike hannun Ayaan suka bar parlourn, ya juyo ya zabga min harara ya ce min. "Zamu haɗu tunda halinki ne ko cigaba da goya mishi baya!" Ya bar dakin. "Kallon Yaya nayi a hankali na ce mishi.."me yasa kayi mishi haka? Bai taba cutar da kowa ba me yasa?" "Ban yi don na bashi haushi ba sai don ba yadda na iya ne shakiyancinsa yayi yawa ne yana da kyau a nuna mishi ba shi daya yake da damar yayiwa kowa yadda yake so!"
Sai kuma na yarda da maganar Yaya, da nazo dakina na same su shi da Ayaan sun yi shiru kamar akwai abinda yake suke tattauanawa, shiga dakin nayi na zauna ina kallonsu, murmushi nayi na ce mishi. "Yaya ya ce na baka hakuri Ubangiji ya huci zuciyarka."
"Munafuncin banza nan kika sharara min mari ko a mafarki baki tab'a bani hakuri ba. Sai yanzu da yake babu kunya a cikin lamarinki zaki wani hakuri da rashin tsoron Allah kin zo bani hakuri." "Yanzu kai me mutum zai yi ya maka gwaninta!" Dauke kai yayi kamar bai san ina yi ba, wato Aryaan idan yana jin niman magana ba abinda ba zai yi, muna haka sai danne dariyar nake ya d'ago kai muka kalli juna ai kuwa na kwashe da dariya, wani haɗe rai. Tare da ɗaukar kanshi kamar na kwanta a kasa, wannan ne karo na biyu da na ga fushinsa, muna zaune Yaya ya shigo yana faɗin. "Zan rufe gidana, akwai yan waje su fita zan rufe gidan!" Shiru Aryaan yayi ya mike kamar wanda yake zaune akan ƙaya. "Malam kada ka bi bango ka bi hanya kamar yadda shari'ar Muslunci ya tanadar, ai kaima musulmi!" Wani irin fushi yayi tare da fita fuuuu kamar kububuwa, yayi waje wato Ubangiji shi kaɗai yayi halittar Mutum da aljan, a fitar da aryaan yayi sai na ga kamar da siffar doki kamar maciji ko me ni dai kamar fitar numfashi haka na ga fitar Aryaan, sai nayi ta mamaki dama haka suma suke. Maganar gaskiya sai na kasa barci, duk da ranar a dakin Nadiyyah yake. Cikin dare ina kwance sai naji kamar ana buga kofar kasa, bugawa sosai haka na fito na na ga Babu wnada ya fito a lokacin, wani ikon Allah ina saukowa na ga Ayaan shima ya fito yana murza idanunsa. Kallona yayi ya tako inda nake, ya ce min. "Koma ki kwanta ba, bakinki ba ne nawa ne!" Ya fada yana nufar kofar, kafin ya isa kofar kofar ya bude kanshi. Wata bakar guguwa ce daga ciki nake hangota bakakirin, kamar na koma na dauke Yarona, amma wani ikon Allah sai na ga kamar guguwar tana yin baya. Dawowa guguwar tayi da gudu,kamar zata lullube shi. Wani irin ƙara yayi mai shegen ƙarfi sai ga shi guguwar ta b'ace. Juyawa yayi zuwa cikin gidan, ya nufi hanyar dakinsu. "Ibrahim su waye?" "Mammyn idan na gaya miki yau sai min shiga ban daki sau goma kafin gari ya waye!" "Gara ka gaya mata dama ta ishe ni haushi suke bani." Kallon Aryaan nayi da yake tsaye. "Wai kai cibiyar ka yana gidan nan ne?" "Yana nan mara mutunci, ai tunda kuka ci mutuncina ke da Mijinki, ku je da halinku, tunda haka muka zabawa kanku. Masu mugun hali!" Dariyar da banyi niyya ba na fara ina kallon Aryaan. Wucewa daki nayi na kwanta ina mamakin Ayaan barci zai dauke ni, kwaci kaina nayi sallah na jima a wurin ina gayawa Allah kukana, washi gari da wuri na farka na nufi dakin Yaran na tashe su suka yi wanka da sallah, karfi bakwai na nufi dinner room, muka ci abinci da Yaran Yaya bai fito ba, princess ta fara saukowa da shigar makaranta tana zaune a gefena. Tana ta wani shiru-shiru. "Yaya dai Yan mata?" "Mammy akwai wata ne." Ajiye cokalin hannuna nayi ina kallon Yarinyar cikin nutsuwa na ce mata. "Ina jin ki!" "Mammy dukana take yi tana kwace min abincina!"
"Yar gidan Uban waye?" Inji Ijlal da ta shigo dakin tana ajiye wayarta a kusa dani, na kalli yarinyar na ce mata. "Kin gayawa Ayaan?" "Yace Ba ruwansa da ni!" Kallonshi nayi na ce. "Baba Hassan me yasa?" "Itama kafin duniya ta mata atishawar tsaki haka take musu laifi ne don sunyi mata abinda tayi ne yake bibiyarta." Shiru Ijlal tai tana mai kallon kasa, sai da na dafa ta, ta dawo hankalinta tana faɗin. "Tabbas rayuwar yana koya mana darasi, idan kuka tafi yau ka basu hakuri,.nima nayiwa Mammy laifi kuma ina rokon Allah ya yafe min idan ta yafe min!" Dan mangaje ta nayi ina faɗin. "Kina da lafiya kuwa ba wani abinda kika min Ni ce ma nake ta muku iyaka da wasu abubuwan da yake naku.....
[8/29, 3:59 PM] Ramlat Manga41: 57
Yadda take kallona da mamaki irin like, dama suma na cutar da su tow amma ai ba su ga abinda ya faru ba. Murmushi nayi na ce mata. "Daga ni har Yarana sai da nayi ta shigowa kowa domin a ga ni nafi kowa kirki, sannan nayi ta cusawa Yaya halin kirki da ya ce nafi kowa kirki, na kasa fahimtar cewa kowacce mace tana da damar tayi kome cikin gidan nan, kin ga kenan idan da ban cusa kaina ba kowa zai zauna lafiya a cikin gidan nan da dangin mijinmu, ni kaina nayi kuskure nunawa nafi kowa iyawa. Ba mamaki shi yasa Allah yayi ta hukutani da laifin da na aikata ba tare da na sani ba, ku yafe min domin nima nayi kuskure." Girgiza kai tayi tana faɗin. "Ni baki tab'a min kome ba, kuma ai dukkanmu babu wacce take da burin ki zauna da Yaya, domin kin tattara abubuwan da mu kanmu bamu da shi, Allah ya gani har labe na sha miki!"
Mikewa nayi domin ita fa kan gaskiya bata kunyar fadar duk abinda ya fito bakinta kamar bata jin kunya ko nauyin fadarsa kai tsaye take fada sai dai ka mutu. "Tun bayan rasuwar Abba nasan idan Aurena ya mutu ko Babana ba zai iya dawo da ni ta sauki ba, shi yasa na rankwashi kaina na zauna a dakina Allah na tuba rayuwa da babu tabbas yanxu sai duniya ta maka atishawar tsaki. Bana son ko bayan raina wani ya karba min Yarana da sunan riko a barwa Ubansu da ke, Allah zai taya ki riko."
"Allah ya ganar da ke, ya gaya miki kin kusan mutuwa ne?" "Amma ai dai dole dan adam ya tuna da makomarsa dai ko?" Ta fada tana hararata. Nadiyyah ta sauko tana tsaki. "Eh haka ne amma kuma ai shi mutuwa zata zo ko da girma ko ba girma tabi dan tayin da yake cikin ciki balle mutum!"
"Fatan nayi bari kike min? Ikhlas fatan nayi bari kike so? Me nayi miki!" "Kun ga wata makakiya, me cikinki yayi mana da zamu damu da shi? Ai idan akwai babban damuwa shine ki haife shi mu ganshi ya zo duniya mu taka kallonshi a matsayin bakon cikinmu, kin ga ki yi sabgarki mu yi namu!" Daga nan muka cigaba da hira, ashe kiran Mijinta tayi, ya gaya mishi muna zaune sai gashi ya dawo ya kalli Ijlal da take watsa mishi harara. "Wai me ya faru ne?" "Kawai muna hira ta zo ta kama zage-zage waye zai kula kare?" Girgixa kai yayi ya juya yana kallon Nadiyyah da take tsaye ya ce mata. "Jira ni ina zuwa!" Dakinsa ya shige can sai gashi da laptop ya ajiye duk abinda ya faru, sai gashi yana gani ya ce mata. "Me yasa bakya son zaman lafiya? Duk yadda na so a zauna lafiya sai kin nuna min iyakata cikin gidan nan? Allah ya gani na fita hakkinki kuma na fita na kowa ban san me kike so nayi miki ba? Idan na kara dawowa na samu tashin hankali ko kika kirani zan kira Babanki da su tafi dake wallahi na gaji da wnada aka yi a baya." Jin haka yasa tayi shiru tana kame-kame. Don dama fitina ce kuma ya daina biyewa kowa a cikinmu.
Muna gama abinda muke Aryaan ya zo ya tsaya a gefena, sai kallona yake yana cika yana batsewa nima sai na mishi na Yaya kamar ban san yana wurin ba. Tsaki yayi ya ce min. "Dama labari nazo na baki kuma tunda kika ki shi kenan!". "Je da abinka bana so!" Na fada ina kallon shi.
"Ina jinka me kake tafe da shi?"
"Mijinki zai koma mulkinsa wallahi, domin ga can dan uwansa yana ajiye muƙamin?"
Zare idanun nayi nace mishi. "A ina ka samo wannan labarin?" Dariya yayi yana faɗin. "Ai yanzu naje na wuce na ji yana kuka shi baya so, domin tunda ya hau ya daina barci cikin Salama. " "Akan me?" Na kuma wurga mishi tambayar. "Saboda mulkin ba na shi ba ne, kuma ai ba a fadawa kowa cewa Mijinki ya ajiye mulki ba rikon kwarya aka bawa dan uwansa yanzu kuma zai dawo da shi. Kin san me?" Girgiza kai nayi ya ce min. "Jiya abinda kika gani nan, wallahi Mijinku ake farmakam saboda ya tashi da kafarshi amma ina mai baki shawara kada ki damu da abinda zai je ya dawo in sha Allah wannan karon zai yi aiki da gaske, akwai wani aikin da yayi ya bani mamaki, zuwa yanzu ya saka a nimo mishi Rilwanu Abubakar Yayari da Alhaji Nafi'u."
Lashe bakina nayi tare da cewa. "A yanzu aikinsa ne ya kare masarautar domin gwamnatin Zanzabira an zugota."
Ban yarda da abinda Aryaan ya gaya min ba, sai da yaya ya dawo yake ƙara fada min da halin da yake ciki, ya kira Nadiyyah da Ijlal ya basu labarin abinda yake faruwa. "Me Mammy ta ce?" "Ba tace kome ba!" "Mammyn Yara me kike ce?" "Maaman yan mata, ina gani ya amsa bamu san me haka yake nufi ba, kuma da alamu ba shi yake bin mulki ba shi mulki yake bi, yayi addu'a ya nime zabin Allah sai mu ga abinda ya dace." Gyada kai tayi shima kuma ya gamsu, tsaki Nadiyyah