Showing 69001 words to 72000 words out of 157081 words
gashi da Yarta ba. Ihu take tana faɗin. "Wallahi sai ka bani yata, na ji xan bar gidan amma ka bani ita!" Daga barandar wurina ya kwalawa Faruq kira yana shigowa ya ce min. "Kayi min waje da ita, kada ka sake ka bar min ita a nan!" Sannan ya shigo min da Yarinyar, sai da na ji zuciyata kamar zata buga. Yarinayr da dama yana shigowa da ita ta ga Yan uwanta. Sai gashi ya kawo min ita wai ta zauna ya ga abinda hali yayi. Har ga Allah ni bana son fitina kuma ya kawo min Yarshi nan gaba ya ce bana kula da ita ko me? Haka na kai zuciya nesa. Na hada Yaran na saka a cikin lissafina. Na hadata da Rabi. Sai Allah ya taimaka yarinyar bata da fitina idan na barta Yaran zan samu tana musu hira har da ismah ka samu tana karanta musu story book irin yadda Mamanta take koya mata, ni kuma ganin haka sai na daura mata karatu Alqur'ani da irin kananun karatun da zai zauna a kanta, musamman da na lura yarinyar kanta yana ja. Domin tana kusan shekara uku ne, sannan na haɗa har da azkar lokacin Sallah nayi zan tsaya kai da fata ita da rabi da take budurwa suyi sallah ina gyara musu.
Cikin ikon Allah Nadiyyah tana zanzabira, gidan ya samu zaman lafiya. A hankali Princess ta samu shiga rayuwata, domin kuwa tsayawar da na mata shi kansa cewa yake. "Da kece kika haifi Halimatu sadiyya, da ba zan tab'a hana idanuna barci saboda tarbiyyar da zata samu daga gare ki!" Murmushi nake na ce mishi. "Ka dai kara hakuri a duba lamarin mahaifiyarta." Hade rai yake yaki kula ni, haka abin ya cigaba da tafiya. Ban san me ya faru ba, ranar sai gasu Aneesah da matar Salim Dayyiba, sun zo mana wuni tunda suka zo wurin Ijlal suka zauna ni da Yaran muna parlourn kasa, na saka musu wani waka na huruffun ja'iyya da yake trending yanzu, don malami ne da yara suke karatun, sai na sauke a wayata na tura a laptop daga nan na sharing dinsa a drive na hada da tv na, ina kitchen da Rabi ita kuma Yarinyar ina jin muryanta tana wakar, har da tsallenta musamman inda yake faɗin. (Ba baitul Allah) Har da tsallenta, murmushi ya sake ina mikawa Rabi abincinsu ta juya ta fita nima na gama kome na fito, a babban parlourn na hango Dayyiba da Aneesah, kamar yadda suka kalle ni haka nima na kalle su na wuce abina na bayan na rufe kofar kitchen dina. Na shiga bangarena ina mai zama na rage karar tv na ce mata.."My princess, me yasa kika kara ƙarar?" "Mammy na fi da karfi ne!" "Oya zauna a ciki abinci!" Kin zama tayi na kashe tv ta ce min. "Mammy idan na ci daya zaki kunna min Tv din?" Gyada mata kai nayi amma na ce mata.." idan baki ci dayawa ba ba zan kunna miki na!" Jin haka sai ta zauna ta fara ci tana kallona. "Mammy yaushe Mommyna zata dawo?" Yadda tayi maganar sai na fahimci akwai abinda matuqar yaro ya rasa zai yi wahalar ya karb'eka a matsayin Uwarsa, ita uwa ce kaɗai zata iya wannan rayuwar ta manta da kanta tayiwa danta addu'a. Sai ta bani tausayi na ji zuciyata tayi nauyi. "Soon zata dawo!" Na bata amsa ina shafa kanta. A hankali ta cigaba da cin abincin, tana murmushi. Duk soyayyar da zaka yiwa Yaron matukar babu uwarsa a cikin gidan tow ba zai tab'a ganewa ba sai da Uwarsa a cikin gidan zai fi nutsuwa da kwanciyar hankali, haka muka cigaba da cin abincin, kamar ance na d'ago kai Ikram ce sai da gabana ya fadi na zuba mata idanun ina kiran sunan Allah. "Na zo ganinsu Princess da Prince ne!" "Ok yayi kyau!" Daga haka na cigaba da cin abincina, tana tsaye a kaina na gaji da nauyin da nake ji nace mata. "Fita min a bangarena!" Yadda nayi maganar na ga Isma itama ta mike tana gurnani. Babu shiri tayi waje, shegiya kanta wani irin fitar da hayaki yake na rasa dalilin haka.
Bayan sallah isha, yana ɓangaren Ijlal sai gashi ya shigo, yana zuwa ya ce min. "Ina Princess?" Da mamaki nake kallonshi. "Tana wurin rabi!" "Ki daukota!" Ba musu na fita na daukota, a hankali na kawo ta tare da mika mishi ita, ya gama dubata har da cire mata kaya. Ina tsaye, "Aneesah da Dayyiba sun ce sun zo sun ga tana ta ihu!" Kura masa idanu nayi kafin na sake murmushi. "Bawa da bakinsa har a kasa tambayarshi gata nan ka duba ta!" Ina fadar haka na bar parlourn na juya dakina, na barshi da ita. A hankali wannan yanayin da na samu na amince, sai na fahimci Aneesah da Nadiyyah da Ijlal da Ikram suna son ruguza min, Nadiyyah bata gidan, amma yadda take zuba musu kudi da aika a kai- a kai. Sai ya zama kowannensu so yake yayi abinda Yaya zai fahimci ina cutar da Yarinyar. Kullum ya dawo sai ta tambaye ta ko an bata abinci, yarinyar na da wayo ce mishi tayi ita fa tana cin abinci a wurin Mammy da labi, take kiran Rabi. Ranar rabi ta wanke mata kayanta ta fitar da shi ta shanya, sai ta biya suka yi ta hawa da sauka. Abin mamaki dai muka rasa taya aka yi aka zuba mana liquid soap, yarinayr nan ta zame daga farkon step har zuwa kasa, kafin ta gama ihu har an kira shi wai na saka isma ta koro ta ta fado ba a sani ba ko mutuwa tayi. Ni jin ihunta da yanayin hayaniyar Rabi, na fito bata wani ji ciwo ba, na dauke ta zuwa sama a nan na ga ruwan sabulu na tambayi rabi ko ita ya zuba ta ce min a'a nan na fahimci ta bar kofar a bude aka shigo aka zuba, sai ban tab'a ba na wuce ha wanke mata inda ta buge na saka mata magani, sannan na dawo da ita parlourn na bata cake tana ci, sai gashi tun daga kasa yake min kiran mafarauta. Fitowa nayi ya ce min. "Ina Sadiya? Ai dama ba zaki tab'a riketa kamar yadda Uwarta zata rike ta ba, idan zalinci ne kema kin haifa zaki gani akan naki yar, haka kawai ki saka min yarinya a gaba saboda zafin kishi bayan na rabu da Uwarta duk saboda ke.!" "Saboda dai zata kashe ka ni yanzu ina ruwana? Matarka ce ka dawo da ita mai ya dame ni, Yaya ni da na iya ajiye ka a gefe kana tsammanin akwai macen da zan iya fitar da ita don kai? Wai ina ruwan samadara. Bani da wannan interest din da zan yi kishi da yar kishiya, dauke ta ka mai da ita duk inda ka so ko a jikin Bintu Junaid a da ne zan damu a yanzu ko babu zan rayu domin na yi farin ciki sannan ko da Yaran ka raba ni da su Alqur'an zan rayu da saboda na gani nima ina iya haihuwa ko ba da kai ba!" Daga haka na bar shi tsaye tare da nufar sama abina, sun dauka zan tsaya ne ya min haukar da. Cab dijam ai Ikhlas din yanzu bata da lokacin rigima da kowa har shi mijin ma. Ina kwance sai gashi nan ya shigo zai min hayagagga, na tashi xan fita ya dawo da ni gabanshi. "Ni fa ban san me yasa!" Zare hannuna nayi cikin nashi ina faɗin. "Ka sani mana kai fa ba giya ka sha ba, sannan ba wani abu ya buge ka ba gaya maka aka yi ina cutar da yarka hankalinka ya tashi so don haka ka dawo da Uwarta kada ka yi tunanin ni ka kai na sauka akan hanya saboda ina sonka, na gaya maka ni dai da ka sani ni ce fa ban sauya ba, kuma ba zan sauya ba, ka dauki yarka ka kai inda za a kula da ita kada na kashe ta!" Ina fadar haka na cigaba da harkan gabana.
Bai dauke yar ba, sai ma wani bina yake don mu shirya na tattara shi na watsar ni zai nunawa halin yan duniya. Mun yi haka da sati kusan biyar. Ina kwance da rana Allah yasa ba barci nake ba. Sai na ji muryan da take kirana kwanaki ana ta kirana. Amma can naji wani irin ihu tare da karaji, a hankali na cigaba da kwanciyata. Tun daga ranar ban kuma jin an kira ni ba, sai dai ya gaya min Ikram bata da lafiya iyayenta sun zo sun dauke ta. Ban san me ya faru ba amma tabbas ta ji jiki domin lokacin da ta dawo bayan wasu kwanaki na ga wani irin tsoro da firgici a tare da ita, duk da ya gaya min babu abinda yake faruwa a tsakaninsu amma kuma yadda take kara motsewa sai wani abu ya dirsu a raina, tunda babu abinda yake da ita ya sawwake mata mana, amma ina ko a cikin kwanakin na zargi yana shiga bangarenta ya kwana sammakon yadda Ijlal suka yi fada take cewa mata. "Ina nan da kika gama zamanki kika koma aka yi asirin sai gashi nan ya koma yana shiga dakinki ba, yar iska mayya! " Anan na kara yarda Yaya bai da kunya, ranar da ya dawo dakina kiri-kiri na ce mishi bani da lafiya, hauka nake zan yarda ya kwaso min damuwa ya kawo min. Ai kuwa yayi fushi har da zuciya.
Na tattara shi na watsar im not jealous type, na nuna mishi daga shi har matansa. Ana haka kwatsam ba sai ga Aneesah wai ta zo zata zauna mana a gida, da fari da tazo. Ni dai ban yarda da a zauna min ba naki bata fuska, sai ta koma wurin Ijlal. Tunda ta dawo take nuna min iko akan Princess, idan yarinyar tana barci zata zo tana duba min ita tana tashinta. Ko taci abinci yarinyar idan ta ce mata eh taci sai ta fita, ranar da ta ishe ni tana shigowa na fito tare da fisgo wuyar rigarta na turo ta waje. "Fita min a bangarena, ko shi wanda ya ajiye ni ba zai kawo min iyayi ba da yunwa nake barinta uwar munafikai!" Ya hankad'o ta waje, na rufe kofar wurina, can ina aiki a sama naji ana buga kofar, Rabi na saka ta bude kofar, haurowa yai da hayaniya. Yana shigowa na zuba mishi idanu, shiru yayi yana kallon yadda nake bishin da wani irin kallo. Sosa kai yayi yana faɗin." Da fatan kuna lafiya?" Murmushi nayi nace mishi. "Lafiya lau wani abu kake so?" "A'a kawai na zo duba ki ne." Ya karaso ya sumbaci bayana yana mai taya ni aikin, wato idan mace ta isa mace bata bukatar ihu, dambe ko tashin hankali akan namiji, ki yarda da kanki shine duk da muna rikici akan alakarshi sa Ikram, amma haka bai hana shi niman hanyar da zamu daidaita. Haka kuwa daren ranar da ya shigo ya mika min visa yana faɗin. "Zamu tafi Scotland, amma ita Nanny zamu barta a can gidansu Maluma ne daga ni sai ke!" Murmushi nayi nace mishi. "Allah ya kai mu!" Wannan shafin da ya bude na rarrashi yasa na hakura da kome na rungume shi, bayan na saka shi fara amfani da maganin infection domin har ga Allah ba zan bari ya dauko min ciwo ba, bai tashi fadawa yan gidan maganar tafiyar ba sai da ya rage saura kwanaki ƙalilan tafiyarki, ai kuwa na ga tashin hankali a fuskar Ikram kamar tayi hauka. A raina nace ba dole ba Yaya fa karya ya kwanta da mace bata haukace akanshi ba, Allah ya bashi lafiyar ji da kowacce yar iska. Sannan reni ko rashin kunya yayi sauki a tsakaninmu, abu daya yake cimin tuwo a kwarya, ita ce Aneesah da take min iskanci. Domin ranar ya gaya min dalilin zuwanta mai babbar daki ta kore ta shine ta dawo gidanmu da zama. Kuma wai a kaina ne tun lokacin da suka zo wai sun ga Princess a cikin yunwa, an yi haka da kwana biyu Mai Babbar daki ta zo, sannan muma muka je mata wuni bata ga kome tattare da Yarinyar ba, shine ta mata faɗa ta ce mata. Ai ta lura yadda take so na haka take son Yaranta ba. Ni fa sai na zama kishiyar Aneesah a wurin mai babbar daki, sannan duk wani abu da Ijlal ke gaya mata tow ni ce bani da gaskiya Ni ce mai laifi. Ina jin wannan labarin ne a bakin Jakadiya Iyaami.
Haka muka bar kasar, da Yarana a lokacin da Nadiyyah ta ji labarin abinda ya faru na mun bar kasar, kamar mahaukaciya haka tayi hauka da ihu. Wannan bai ishe ta ba sai da ta zo har Zanzabira, tayi ta rigima. Karshe ta zo gidanmu Abba ya mata tas ya kuma kore ta, wannan abin ya mata ciwo sosai ta dawo Jos ta kwana biyu sannan ta wuce Abuja. Haka ta saka Ubanta a gaba da riko ai kuwa ya shiga kitchen ya dauko muciya ya rufe ta da duka, wannan abin ya tashi hankalinta domin bata kawo zai mata irin wannan dukar ba. Ya ce ta bar mishi gidansa. Babu shiri ta bar gidan tana kuka domin bata kawo zai mata haka ba. Uwarta ma duk son da take mata sai da ta nuna mata iyakarta....
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 26
Tunda muka isa kasar na fahimci yanayin kasar ya amshi Yaran, yan gidan ganina da nawa Yaran suka yi ta murna. Dama daga ni sai shi sai Isma. Da muke tare da ita. Sai wani nutsuwa suke samu, babu tashin hankali babu rikici a yanzu suna niman wata biyar, wanda yayi daidai da wata biyu da dawowa na gida. Zama kuwa har sun fara domin tun a gidanmu ana jingina su, da na dawo kuwa na cigaba da dan musu dabarar. Masu wayon tsakanin Ayaan da Ayaaz ne, matan kuwa me wayon Ayyanah ce, amma Takwaran hajja ai sai godiyar Allah, domin Ubanta sai da ya kaita asibiti yasa a duba mishi ita, rashin wayon yayi yawa. Ayaan bai da karaji da hayaniya amma akwai karfi da hakuri, idan ya zauna a wurin matukar ba ni na dauke shi ba ko rabi ko Abbansu, tow zai matuƙar wahala ka ga yayi kuka ko mita, Ayaaz kuwa mita lalaci da son jiki idan ya gaji da zaman kwanciya yake yayi ta danna min ihu, ita kuwa Ayyanah hannu take sakawa a baki ko kuma ta damke Isma a hannunta ita kuwa tayi ta xille mata ta sakata wahalar, Ayaat sarki kallo da rashin wayo, sai tayi ta kallon abu daga can ya fashe da kuka. Ita kuwa Princess, zama take tana saka musu abin wasa. Idan abcd ne tow ita zata yi ta fama nan ita ce malamarsu, idan kuma huruffun ja'iyya ne nan ma, haka zata azkar da kananun surar da take koya musu. Su kuma suna ganinta zasu ta murna yayarsu ce.
Zaman yanayin garin ya sa na kara maka shi a wannan amma lokacin da na tuna baya rena mace sai na tsinci kaina da ƙyamar shi, har ranar ya ce min. "Me yasa kike gudana?" "Yaya kai fa abin gudu ne, ace kowacce mace a cikin gidanka ka sannan yadda take!" Murmushi yayi ya ce min. " Ba dai kowacce mace ba, domin kuwa akwai wacce ko hannunta ban tab'a rikewa ba, idan ina son abu ina so amma idan na ce bana so ina nufin bana so ne.". "Ya shiga ta nan ya fita ta can!" Tsaki yayi ya ce min. "Ku mata haka kuke, kin san me yasa nake kwana a dakin Ikram? " Girgixa mishi kai nayi, ina kallonshi. "Zan gaya miki gaskiya ne ba wai don ina son wani abu daga gare ki ba, a'a xan wanke miki wannan karamin brain din naki ne!" Ya fada yana zungure min shigo, kallonshi nake ya ce min. "Ba zan iya boye miki gaskiya ba don tun a Nigeria na fahimci kina kyama na!" Ya fada yana murmushi, kuma gaskiya ne hatta kiss sai dai ya yiwa wuyata ina Dalili, yadda na san idan yana mu'amalar aure kamar zai mai da mace jikinshi. Matse hannuna yayi ya ce min. "Kina tare da ni?" Gyada mishi kai nayi, kamar nayi kuka. "Kin tuna fadar da suka yi da Ijlal ta ce sai dai ta kare a gadin gidan?" Gyada masa kai nayi ya cigaba da cewa.."tun wannan ranar na tattara na shiga lamarinta. Take shiga dakina ta kwana, amma Allah shine shaidana wallahi ban tab'a rike hannunta ba, kowacce mace tana da yadda nake bukata a tare da ita amma ke rayuwata tana take da wani abu da kike da shi, shi yasa bana gajiya da ke bana kuma jin kin gundire ni, ke abincin marmarina ce, ina ci ina kara jin yunwarki, sauran kuwa kowacce da yadda take!" Yadda na kalli cikin idanunshi, sai na kasa gano gaskiya yake faɗa ko karya ne, sai na kasa yarda da shi. A hankali bakina ya bude nace mishi. "Baka tunanin haka zai iya zama illa ga rayuwarta?" Matse hannuna yayi ya ce min. "Gaya min illar ta nawa? Gara Ijlal bata taɓa zina ba, idan kika ce min rayuwar da suke na karnuka na sani amma kin san yadda abin yake? Kin san sau nawa tana fita tana haduwa da wasu mazan? Kin san wasu mazan nawa suke biyanta."
"Kuma kake tare da ita?" "A'a Abbanki ya ce na ajiye ta a wurin aiki muke na musamman a kanta, na gaya miki gaskiya ne ba don ki yarda da ni ba, sai don na