Showing 93001 words to 96000 words out of 157081 words

Chapter 32 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

44

nan ai." Daga haka yayi tashin sama yana tafiya kamar mai tafiya kasa saboda yarda da kai da yayi, lokacin da shiga parlourn ya samu ina cin abincin, hankali kwance kamar ban san me ya faru ba. "Ki bani hakurin marin da kika min kome ya wuce sai na yafe miki!" Murmushi nayi ina cin abincin karyawana." "Kada kayi hakuri ka ji!" Daga haka na na cigaba da abinda nake yi, can ya ce."Ummina tana kirana zan tafi!" "Allah ya tsare! Ka gaishe ta Allah ya kiyaye hanya" Kallona yayi yana mamakin yadda na yi maganar, kafin kuma ya kwanta, nayi mamakin yadda ya tafi bayan wani lokaci yaron yaron ya tashi. "Ummi yunwa!" Abinci na saka mishi, sai da yaci sosai sannan ya wuce wurin yan uwansa suka ci-gaba da wasa. Tausayi yake bani yaron bakiɗaya rayuwar shi ta koma wani iri.

Bayan Nadiyyah ta dawo, tsayawa tayi tana faɗin. "Kika zubar min cikina?" "Da alamu ciwon hauka ya fara kamaki, waye yake da lokacin ya bata lokacin shi akan cikinki? Look ni da bani da wani abinda xan dauka akanki!" Dariya Ijlal tayi tana faɗin. "Ashe ba dadi? Ni nan na zubar da cikinki, ko kina da abinda zaki yi?" Yadda tayi maganar da karfi da confidence, Kuma na hango iya gaskiyar don haka na kyale su, su sauke haushin juna. Nadiyyah ta tabbatar da cewa sai ta kashe Yaranta. Anan na ce musu, "Ya isa haka kowacce ta kama gabanta, batun kashe dan wani bai taso ba, idan har kuka kasance haka kanku zaku cutar domin shi akan dansa bai da lissafi!" "Uban waye saka ki a cikin maganar mu!" Wani mari aka dauke Nadiyyah da shi wnada yasa ta yin tsit. "Ni ba kanwar lasa ba ce, kika sake wani haukarki ya kara bani damar zagina sai kin ji a jikinki." Daga haka na bar parlourn, ita fa Ijlal kanta yana bala'in Ja, bata taɓa yarda ta zage ko aikata wani abu da za a tab'a lafiyarta.

***

Kusan wata guda aka ɗauka ana wannan rigimar, yau mun tashi da wani irin zafi ne a garin ko ina sai complain ake akan zafin haka yasa na mai da hankali wurin bude tagogin bangarena, kitchen na shiga na daura zobo. Yana dafuwa na juye shi na bar shi ya sha iska na tacce na juyo a cikin firiji sannan na koma dakina nayi wanka na biyu Ayaan ne ya shigo ya same ni a tsaye na fito ya ce min. "Abba kamar yayi hatsari!" Gabana ne ya fadi. Ina jin kamar zuciyata zata daga kirjina. "Waye ta gaya maka?" "Aryan yana can shi da icma!" Ciro doguwar rigana nayi na fito da sauri na nufi waje ban san yadda aka yi na fito a rikice ba kawai kuka na saka a hankali domin fitar da ya ce mana rangadi zai tafi ko da ya taso ya kira ni, don ya ce ba zai zauna ba. "Mammy ki jira a kawo shi." "A'a Ayaan! Ba zan iya jiya ba". Na fada ina kuka, sosai domin jikina rawa yake."Kada ki fita kema ana jiranki fita ne!" Cak na tsaya, wannan da yake min magana ba Aryan ba ne kuma ba Ayaan ba ne. Kamar yasan abinda nake tunani ya ce min. "Ni ba su bane, ni sunana Amir zan wuce na hango shi shine na sauko kema an saka miki tarko ana jiranki ne ki fito!" Jin haka yasa na koma na parlourn na zaunar. Ya biyo ni yana faɗin. "Sun shirya domin hallaka shi dake ne, amma in sha Allah ba abinda zai faru." Bayan minti goma sai ga Salim. "Fulani Babba ina sauran yan gidan?" Ya fada ko sallama bai yi ba, jikina yana rawa na ce mishi. "Suna ciki!" Daga nan ya kwala musu kira suka leko. "Mijinku yayi hatsari!" Ni dai kawai na ji shi amma tabbas zuciyata cike take da tashin hankali. Sai lokacin ya lura da kukan da nake yi, yayi shiru kafin ya ce min. "Ki yi hakuri zai dawo in sha Allah!" Ya fada yana kallon yadda nake shashekar kuka. Juyawa yayi ya bar parlourn.

Zan iya cewa wannan shine karon farko da wani abu ya same shi, ban ga tashi hankali a tare da matansa ba, wurin karfe shida na yamma aka kawo shi gidan, Faruq an wuce da shi gidansa da yake bayan fadar. Tunda na ganshi nake kuka kanshi ya sha dauri sosai. Burinsa su kashe shi, haka yasa na kasa zaune na kasa tsaye, ina tsaye akan shi. Kwana nayi ina gayawa Allah halin da nake ciki, washi gari babu wani alamar jikinshi tana amsar yanayin, wurin karfe biyu na rana sai ga Faruq. Wanda shi ciwon shi bai kai na Yaya ba, ya zauna yana kallon halin da yake ciki. "Ku yi hakuri, hatsarin ya faru ina wata gaban motar, amma kariyar da take gaban motar babu a bayan motar." Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa. "Nayi ƙoƙarin na hana faruwan haka sai dai bayan faruwar lamarin wasu da ban san su waye ha sun kawowa motar hari ina zargin sune suke janyo hatsarin." Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa. "Sai dai Allah da ikonsa, a cikin wannan yanayin Allah ya turo wani zaki, daga nan ya tarwatsa mutane ban kuma sanin mai ya faru ba."

"Amma ance da kai aka ciro shi a cikin motar!?" Inji Mai Babbar daki, kasanshi a kasa ya ce min. "Ban san kome ba wallahi!" Taya zai san kome bayan ba yin kansa ba ne, shima shiga jikinshi aka yi, yayi wanan aikin bayan sun isa asibiti ya yanki jiki ya suma. Saboda buguwar da yayi. Faruwan lamarin Mai Babbar daki ta ce a dawo da shi cikin gidansa domin za a iya binsa, a cutar da shi tunda abin ya zama haka.

Hmm duk wani abinda za ayi na kula da shi anyi sannan an tabbatar da anyi ɗin, kawai shi din ne bai dawo ba, ba sai ga zaman jinyar shima ya zama abin kishi a kai ba, ni gaskiya ban sani ba kuma ban san me ke faruwa ba. Duk ranar duniya zan shiga na gyara mishi jiki na goge mishi jiki na mishi alola, wurin wanke mishi jiki dai na ga kamar anyi wani abu da shi. A wannan yanayin da yake ciki na rayuwa da mutuwa matansa suke kwanciya da shi, ban tab'a kawo kome a raina ba, nisan. Sai da nayi mafarki har sau biyu da Nadiyyah tana tarayya da shi, a cikin halin jinya, tsoro ya kama ni don haka yau da nayi mafarkin na tashi da sauri na sauka zuwa dakin, ina shiga na kunna wuta da sauri na ga Nadiyyah, wani irin tsoro da bugun zuciya na ji da ban tab'a jin irinsa ba, wani abu ne ya lullube min kai, na nufe ta gadan-gadan na fisgota ta fadi can. Hawaye cike da idanuna na ce mata.."Da yake dabi'ar karnuka kika taso a kai, shi yasa baki san idan mutum yana bakin mutuwa kyautata rayuwar shi ake ya tashi ko ya tafi kazama jaka jahila zaki zo kina hada shi da kazanta fita min a dakin!" Da yake bata da gaskiya haka ta mike tare da barin dakin, haka na dibo ruwa na wanke shi da towel don ma katifar akwai leda a ƙasar shi,.haka ni daya na wanke shi na cire duk wani abinda aka saka mishi. Sannan na nufi wardrobe dinsa na ciro kayanshi na saka mishi, na sauya zanin gadon, zama nayi a dakin ina kuka.. wani irin rayuwa matansa suka dauka ne, haka yasa na tsaka akanshi. Sai suka fara kawo min reni, ranar da suka min wani rashin mutunci, ai kuwa raina ya b'aci, bakiɗaya aka musu dan bura uban duka, ina jin ihunsu,ban ji ko dar ba, kamar zasu yi hauka haka na haramta musu ganin shi yadda suka fusata ranar kofar dakin suka je zasu ɓalle. Na fito ina kallonsu. "Wallahi tallahi billahi azim, kuka karya kofar nan ko hannun kofar nan zan nuna muku iyakarku, idan kuma kuna ganin karya ce Bismillah!" Daga haka na share su. Gani suke kamar ana tsoronsu.

Kowacce ta kama kanta, haka nayi ta kula shi da taimakon abokan aikinsa da su Faruq da yan uwansa, aka samu ya fara motsawa. Sai dai har yau bai farka ba. A lokacin na samu kira daga Fada. A karon farko a rayuwata manyan mutanen fada suka kira ni, rike hannuna Ayaan yayi ya ce min. "Zasu ce miki, ki saka hannu a bawa wani rikon kwarya tunda an hana fita da shi? Sannan kece kike kula da shi. Tow abinda zai faru zasu ce ki saka hannu a bawa wani rikon kwarya kada ki saka hannu, duk wnada za a ce miki ki bashi kada ki amince, sai na biyu rayuwar al'ummar Zanzabira tana hannunki, Abbansu yana cikin doguwar suma ne. In sha Allah zai farka amma fa zai dauki lokaci yau ko gobe ko wata shida ko shekaru, wanan na Allah ne ke kuma naki ne ki cigaba da bawa kujeransa kariya. Yanzu zaki ga yadda mutane suke yau zaki shiga duniyar da kowa yake so wasu na gudu wasu na shiga, yana da kyau ki saka wannan kwallin."

Ya mika min, na amsa ina kallonshi. "Duniyar da zaki shiga, cike yake da ban mamaki al'ajabi." Daga haka ya juya ya bar ni tsaye da mamaki. Washi gari kamar lokacin da yake fita haka nima na fita na bar Aryan da Yaran sai Isma da ta koma kofar dakin Yaya ta kwanta. Sai da na shiga cikin gidan na gaida Ummi da ciwon kafa, sannan na wuce fadar. Aka bani kujera na zauna Faruq yana bayana, ga Abbana a can ina hango shi, shima a cikin manyan fadar. "Zainaba mun so mu je mu same ki, sai muka ga kamar zai fi dacewa a kira ki, dama akan ciwon Mijinki da kuma na kalmar fada ga zaɓe ya karato, sannan kin ga yadda aka samu matsala tsakanin Alhaji Nafi'u, wannan karon ma ana hasashen su zasu yi nasara. Shine muka hada kai bakiɗaya, domin Mijinki yayi wani aikin da ba a tab'a yi ba, sai muke ganin kamar ko zaki saka hannu a samu mai riƙon ƙwarya kafin ya farka." Shiru nayi ina jinsu kafin na kalli Abba da yayi shiru yana kallon yadda nake kokarin nazari. A matsayina na yar jarida wacce kuma ta tab'a aikin binciken da bata kammala ba, na ce musu. "Ba a bukatar rikon kwarya, duk wani abin da ake bukata a tuntubi Faruq zai gaya min, aikin da yake yi a daura daga inda aka tsaya, nima zan yi iya ƙoƙarina a kai naga mun daura daga inda yake."

"Zaki iya ji da matsalar Zanzabira?" Alhaji Kabiru Hammud Yayari, kallonshi nayi da kyau jinin da nake gani a hannunsa yasa na kara murmushi na ce mishi. "Xan iya da yardan Allah!" "Mace a zanzabira?" Ya kuma magana mai babbar daki da ta shigo ta ce mishi. "Ba yau aka fara ba, farkon jinyar Marigayi Attahiru Shehu Yayari na amshi kula da harkokin masarautar, ba lallai sai ta zo fada ba a tura mata kome, Allah zai bata sa'a."

Daga haka ta zauna a zauna a gefena. A hankali Alhaji Kabiru Hammud Yayari ya ce.

"Bana goyon bayan kome za ayi sai an sami Zainab Junaid Gobir, idan kana tare da ni, ka tashi tsaye idan kana tare da ita ka zauna." Abin mamaki babu wanda ya mike. Murmushi mai babbar daki tayi tare da cewa. "Kenan kuna tare da ita?" Murmushi nayi na ce mishi. "Abinda nake son a fara shine Hamis Yusuf Yayari da Alhaji Mamman, ku yi binciken inda aka yi hatsarin Mai Babbar, sannan idan akwai kudi a cikin asusun masarautar a ware fara gina asibiti ina son aikin ya kasance cikin kwana hamsin da yarda Allah. Ba zan dauki kuskure ko laifin wasu ba, ni mace ce kuma dalibar jarida. Ayi min aiki cikin kwanakin da ya dace. Masarautar Zanzabira tana zaune da mutane dari uku da wani abu, ace babu Asibitin da za a kula da mara lafiya ko ta emergency ce." Daga haka na kalli Abba na ce mishi. "Malam Junaid ka haɗa min tsofin files na masarautar ka bawa Faruq ya bani, Salim ka kasance a shirye ba mamaki za a samu bijirewa daga gwamnatin Zanzabiran, ko al'umma ka zama mai shiga tsakani, sauran manyan fada irinsu Tafida, Ajiyar Zanzabira a hada duk wani abu da yake gudana a bawa Faruq ya duba min." Ajiyar zuciya na sauke ina jin wani abu yana taso min kamar ba ni ba. Na kalli kowa a fadar waɗanda suke tare da ni ban ga kome a tare dasu ba, amma akwai wanda suna son su tashi amma tsoron, hatta Salim da yake gabana hannunsa dauke da jini, tow jinin waye haka a hannunsu? Jinin iri daya ne da Alhaji Kabiru Hammud Yayari, shiru nayi kafin na ce musu. "Ina jiran duk wasu bayanai nan da awa ashirin da huɗu!" Sannan na fita daga cikin zauren tattaunawar.

Ina shiga parlourn Mai Babbar daki na zube a dogon kujera na kama barci, Mai Babbar daki ta zauna. Hawaye ne yake zuba mata. "Awatif!" Bude idanun tayi tana murmushi ta ce. "Maryamu, zan kasance da ita har ranar da zai samu lafiya. " Daga haka ta lumshe idanu tayi, ta cigaba da barci.

Karfe biyu na farka, na zauna ina kallon mai babbar daki na ce mata.."Me yasa nake ganin mutanen fada har da dogarai hannunsu dauke da jini?" Kallona tayi tana faɗin. "Jini Zainab?" Gyada mata kai nayi. "Allah yasa ba wani zubar da jinin zaa yi ba." A hankali Jakadiya Iyaami ta shigo ta zauna a gefena, ita kan bakiɗaya jikinta wanka tayi da jinin tayi. Kallon ta nayi ina murmushi na ce mata. "Jakadiya kin ci zamaninki kin ci na Yayanki, cin na jikokin. " "Haka nake Fulani Babba, shi yasa nake ta rokon ko bani damar na kula da Mai Martaba, tunda ke kina fada."

Murmushi nayi na ce mata. "Mai martaba yana samun kulawar da tafi tawa, domin ko kuda bai isa ya ratsa inda yake ba." Zaburar da tayi jinin ya kara watsawa a hankali, sannan suka kara komawa jikinta. A hankali ta sosa wuyarta. Mikewa nayi na nufi dakin Mai Babbar daki na wanke fuskana da alola na fito ina jin ciwon, haka nayi sallah na jima ina addu'a, ina cikin addu'ar na ji wani irin kauri a hankali na juya a dakin Mai Babbar daki wani abu a bayan gadonta. A hankali na shafa na nufi wurin, matsar da gadon nayi wnada ni kaina nayi mamaki. Kashi cinyar akuya aka yi wani abu da bakin kyalle, a hankali na ciro shi dai-dai shigowar Jakadiya Iyaami. "Ke kika ajiye?" A tafin hannuna na rike shi, sannan na sake murmushi na ce mata. "Kin san me shi Kenan?" "A'a wallahi!" Ta fada tana zare idanu. Damke shi nayi take ya kone. "Duk wnada ya aikata zai koma kanshi." "Haba sai dai idan bai san kanshi ba, amma idan ya san kanshi kullum a tsaye yake." "Jakadiya Iyaami kina wani abu kamar akwai wata a kasa." Murmushi tayi tana faɗin. "Ni ɗin? A'a wallahi ban san kome ba!" Ta nufo ni da sauri, nuna mata yatsa nayi ta juya da sauri. "Kul kada ki tab'a." Ina takowa tana baya, ina takowa tana baya har ta fadi a bakin Kofar. "Ni ba ruwana da ke! Fita ki bani hanya."

A hankali na fita bayan ta fita daga cikin dakin, na nufi wurin mai babbar daki da take cewa.."Kin ga gwiwata da take ciwo kamar an zare min ciwon." Aneesah ce ta shigo, kusan yadda na ga Jakadiya haka na ga Aneesah. Abin mamaki a cikin gidan nan wannan abin yake faruwa meye ya kawo jinin jikinsu?

Haka na dawo gida na sama an gama kome Faruq ya kula da shi sannan ya bawa Yaran abinci, Aryan da yake jikin Ayaan yana ta iskanci, yana ganina ya ce min. "Yau kin ga bakin lamari xan gaya miki kome amma ko bani hakurin marin da kika kwatsama min, kawai sai na yafe miki." Tsaki nayi na wuce shi ina faɗin. "Sai dai ka kare da jin haushina!" "Awatif tayi aikin da ta san shago zai yi malama taimakon da nayi miki, ki kawo na goro." "Fita min a jikin Yaro kada ka saka shi ya fara tunanin wani abin arziki ne......."

"Jinin da kika gani a jikin Jakadiya.....

(Ayi hakuri na rufe wayar don nayi typing ne, wallahi tun 4am har na fara gashi ko karyawa ban yi ba kada ku ce kome ku yi hakuri don Allah....)

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: Cak na tsaya sai kuma ya kyakyale da dariya irin na renin hankali ya ce min. "Ba zan gaya miki ba, ki nimo jinin waye yake bibiyarsu daga lokacin da kika sani nasan zaki so jin. yadda aka yi jinin ya ke bibiyarsu."

Banza nayi da shi na wuce yana bina a hankali yana dariya. Tunda na shiga daki zai bi ni na tsaya na ce mishi. "Kada ka sake raina ya ƙara ɓaci akan wanda nake ciki domin zan baka mamaki." Ba musu ya gangaro daga bina da yake ya shiga daki na zauna a kujeran parlourn, nayi shiru. Hayaniyar da nake ji a kasa yasa na mike tare da lekowa Ijlal ce Aryan ya mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login