Showing 99001 words to 102000 words out of 157081 words

Chapter 34 - Royal Politics Book 2 Complete Hausa Novel

Ramlat   

07 Nov 2025

58

dashi, haka na cigaba da hada kome, ranar ya kasance Monday, haka na kwana da nazari, washi gari ina shirin yiwa Ayaan wanka wannan dan iskan aljanin ya zo. "Gaskiya ba zaki mishi wanka ba, domin ba zaki ga girmana ba!" Takaici ya ishe ni na ce mishi. "Fita min a jikin Yaro ko na kwashe ka da mari!" Yadda nayi da hannuna yasa shi cewa. "Ai shi kenan." Ya juya ya fita, na dauki Yaron nayi mishi wanka, sannan na fito na shirya shi ya ce min. "Zan tafi wurin Ummin Fada!" Wato mai babbar daki, "kai ɗaya ka?" "Malama me kika mai da mu? Kawai ki bani hakuri na baki labari, an sake sakawa Mai Babbar daki abu a daki, sannan."

"Bana bukatar maganarka fita ku bani wuri!" Na cigaba da aikin da nake, kafin na shiga wanka.

Yaron nan yana fita suka sace shi, sai dai wani abu da ya basu mamaki, tunda suka saka shi a motar bai ko razana ba, bai kuma yi ihu ba asalima zama yayi yana mai daura daya akan ɗaya ya ce musu. "Tow muje ko?" Ai kuwa motar taki tashi, aka yi ta tashi taki, abin mamaki motar taki ko motsi. "Yanzu ya ake ciki motar taki tashi na sauka ne?" "A'a ance idan muka sace ka muka kashe ka." "Ayya Allah Sarki, yanzu ya ake ciki zaku iya sace ni ne?" "Kai Yaro ka min shiru!" Rike bakinsa yayi ya ce musu. "Tow na yi shiru!" Ya rike bakinsa, wasu suka sauka tare da tura motar, abin mamaki ko gizau kamar irin dutsen nan, dariya yayi ya ce musu. "Ai kun ji irinta ku zo muje office din Yan sanda." Kamar wanda ya musu wani abu suka shiga motar yana kallonsu yana dariya, haka suka isa police headquarters, suna shiga suka fito, sannan shima suka dauke shi, zuwa cikin office din. "Me ya kawo mu?" Ba tare da sun jira kome ba suka ce musu. "Mun sato shi ne zamu kashe shi." Abin sai ya zo kamar abin wasa kafin wani lokaci, an kira manya cikin yan sanda jahar Zanzabira.

Suka sake maimaita abinda suka fada dA farko, ai kuwa a take aka kira Salim domin ansan Uban Yaron bai da lafiya. Lokacin da Salim ya ji labarin sun zo shi da Faruq, sai Malam Junaid da Faruq ya gaya mishi.

***

Ina tsaye a gaban Yaya wayata tayi ƙara, dauka nayi na saka a kunne. "Kin ji labarin an sace Ayaan kuwa?" Inji Yeemar, "A'a tow wallahi Hubby ya kirani yana gaya min gasu a office din yan sanda mutanen sun kai kansu." "Basu suka sace shi ba, shi ya sace su ya kai ga yan sanda, Allah ya kyauta." Sai kuma abin ya bani mamaki da dariya, Ni daya kamar mahaukaciya nayi ta dariya a daki, kafin kuka ya zo min, nayi me isata kafin karfe biyu sai gasu hannunsa dauke da Popcorn, yana shigowa ya nime wuri ya kwanta ya fara bani labarin, "Amma na ce kada ka fitar min da Yaro ko?" "A'a ranki shi dade, ai basu mishi kome ba, domin ba zasu iya kome ba, tunda dai ni na sace su da sauki."

Murmushi yayi yana wasa da abinda mataimakin Kwamishinan yan sanda ya saya mishi, na dawo Parlourn muka zauna ina yiwa Salim godiya, murmushi yayi ya ce min. "Ba kome fa! Ya mai jikin dai?" "Alhamdulillahi!" Na fada daga haka muka yi shiru, kafin can ya mike yana faɗin. "Na bar baki a fada!" "Kamar ya ka bar baki a fada." Komawa yayi ya zauna ya ce min. "Kafin kwanciyar Yaya ne akwai wasu turawa da suka zo wurin Yaya akan wani filin farin kasa, tow dama ya ce zai gana da su har sau biyu bai samu hali ba shi ne yanzu suka zo!" "Ina file ɗinsu?" "Ai da yake daga gwamnatin Zanzabiran aka turo su, ba su zo da wani file ba, " ya fada yana murmushi. "Kamar yadda yaki ganawa da su, kai ma ban amince ka gana da su ba. Sai sun kawo file rubuce da wani saka hannun hukumar gwamnatin Zanzabiran, daga nan zasu gana da ni ne kafin musamman me yake tare da su." Yayi mamakin yadda na tsaya akan maganar lokaci guda, amma da yake ya iya takunsa sai ya ce min. "Tow ba damuwa in sha Allah zan musu bayani." Daga haka ya mike zai fita cikin sanyin murya na ce mishi. "Ya Salim!" A wani rikice ya juyo yana kallona, "dama zance maka na gode sosai da kulawa!" Girgiza kai yayi ya ce min. "Ba kome !" Ya fita daga gidan, lumshe idanuna nayi na kwantar da kai ina sauke ajiyar zuciya. "Mai martaba yaki ganawa da turawan ne saboda idan ya basu damar abinda suke bukata, ga zasu shigo da tashin hankali da masifa cikin zanzabira, shi yasa yaki ganawa da su, sannan ya gano akwai mutanen da suka basu goyan baya sosai haka yasa ya ce ba zai gana da su ba, a zahirance wannan wani yaki ne da ake tsakanin jami'an gwamnatin Zanzabiran da fada, domin su gwamnatin Zanzabiran ta amince da bukatarsu za a bawa Turawan damar yin yadda sune suke so! Sannan ko zuwa rangadi da hatsarin nan, ni yanzu na fara jin a jikina kamar har da wannan bukatar wnada ya ja kome." Inji Faruq,

Murmushi nayi ina kallon kofar da Salim ya fita da wani irin kallo, irin wanda yake cike da mamaki da takaici, wato sai da na fara binciken za a fara min wasa da hankalina, da farko an sace Yaron sannan yanzu wani abu na daban. "Ranki shi dade, matukar kika ce zaki razana tow ba zasu tab'a barinki ba zasu ta bibiyar ki ba dare ba rana, ranki shi dade kama yayi ki saka su gudu tunda suka fara haka zasu ta razana ki, yanzu haka zasu kara yin wani abu wanda zai saka dole ki hakura da binciken kin ga kenan sun yi nasara, amma daga lokacin da kika rintsa idanunki, kika fuskanci mutuwa da kansu zasu gudu Uwar Marayu Uwar Magajin zanzabira kece zaki saka su gudu kawai sai a zauna lafiya."

Gyada kai nayi, a daren ranar aka tura aka kashe Yaran nan, sai dai wani abu da basu sani ba Aryan ya sace daya cikin Yaran ya kawo shi cikin gidan ya ajiye mana shi, a bayan gidan yayi wurin yadda ba wanda zai iya tunanin da mutum a cikin wurin, ranar Laraba na nufi gida da Yarana muka wuni, suna parlourn wurinsu Umma ni kuma na samu Abba a dakinsa. "Abba na zo wurinka ne!" A hankali na warware mishi bincikena.

Murmushi yayi ya ce min.

"Abu daya na sani akan auren Khalifa da Ikram aka fara wannan tashin hankalin, duk da dama mun san cewa Nafi'u ya kauce hanya ya zabi abinda ba zasu iya tsaya mishi ba, na farko kenan amma a haka bamu guje shi ba muna tare da shi, na biyu yaron ya lalace domin yana lalata da yan mata Minor sannan idan ya tashi ya kashe su, babu uba na gari da zai dauki yarshi a cikin wannan ahalin da suka yi wanka da kazanta, sai na uku goyan bayan Saddam akan rigimar da suka samu na makalewar kayansu da muka biyan kudin da Nafi'u yake binsa, sai na biyar yadda muka kara bawa Saddam Tanimu Jatau goyan bayan ya tsaya ya kafa gwamnati, ina ga wannan sune abinda ya faru."

Shiru yayi kafin ya kalle ni, sannan ya ce min. "Me kike tunani a kai?" "Dole ayi rubutu akan wannan lamarin, ta haka ne zan san motsinsu, Abba bayan nan akwai wasu mutane da nake nima, idan aka yi rubutun tow zasu iya boya su ki bani hadin kai, sai idan kuma na same su dole zan yi rubutun. Na farko waye mutum na musamman ga Alhaji Saddam wanda yake tare da shi dare da rana?"

"Malam Barau, shine drivensa kuma yana rasuwa aka ce ya koma garinsu." Ya fada yana niman wani abu a wayarshi ya min. "Wannan mutumin shine kusan p.a dinsa." Gyada kai nayi na tura a wayata, bayan na tsayar da record din da nake yi. "Sannu da aiki!" Murmushi nayi na ce mishi. "Abba kasan harin da aka kaiwa Yaya, akwai wasu abubuwan da na fahimta yanzu? Yanzu bincike biyu nake na farko abotarku na biyu Yaya, idan har na samu yadda nake so zan kara zuwa gare ka Abba baka gaya min wani gari Malam Barau yake ba." Gyada kai yayi yana faɗin.

"Shi din dan garin kafancha na jahar kaduna ne." Gyada kai nayi na ce mishi "kun tab'a zuwa ne can?" Gyada kai yayi yana faɗin. "Eh mun je wani lokaci can da jima mun je mishi ta'aziyar rasuwar Matarshi."

Gyada kai nayi ina sauke ajiyar zuciya, kafin na dawo na ce mishi. "Abba Baban su Yaya fa waye na kusa da shi?" "Sallama shine drivensa kuma na kusa da shi, kaf duniya babu wnada bai san sallama ba." "Yanzu baya nan ko zan san inda yake?" Shiru yayi kafin ya ce min. "Shi din dan garin garin farin kasa ne!" Jinjina kai nayi na ce mishi. "Abba akwai wani alaka ce tsakanin Jakadiya Iyaami da Babansu Yaya ne?" Shiru yayi yana nazarin kafin ya ce min. "Zainaba zaki iya tabbas zaki iya wannan lokacin ya dace ki sake mikawa fa! Jakadiya Iyaami ita ce ta reni Rulwanu Yayari, amma daga baya ta dawo aiki a bangaren Alhaji Shehu Yayari Mahaifin Attahiru Yayari, abinda na sani Iyaami tana kula da Rulwanu, daga lokacin da aka bawa Alhaji Shehu Yayari mulki ta dawo bangarensu, tunda dama can ita take dawainiyya da Surukanki, tana muka renon Yaran Abubakar Yayari. Kasancewar gidan sarautar ba a kebewa kowa wanda zai kula da su ba kowa ma zai iya hidima, daga lokacin da aka bawa Shehu Yayari mulki ta koma bakiɗaya, sai dai wani abu da ya faruwa wanda abin ta daki zuciyar Jakadiya Iyaami, shine tana da y'a budurwa da take matukar kauna da kulawa da ita, sannan kuma ta kiyaye yarinayr da shiga cikin gidan Sarautar, sai dai daga baya aka rasa waye a cikin gidan Yayari yayiwa Yarinyar fyade, wanda daga baya aka yi ta gulma da kananan magana akan mai Martaba Shehu Yayari ne, sai dai da yake akwai karfin mulki a lokacin an rufe zancen itama yarinayr garin jinya ta rasa ranta, wanan kiyayyar da jin zafi tare da rashin bincike yake damun Jakadiya Iyaami, domin ko bayan rasuwar Alhaji Shehu Yayari, an so tuhumarta sai ni da Alhaji Saddam da Nafi'u muka ce barta kawai ba zata aikata kome ba, domin yadda take kuka yasa muka amince, me yasa kika kawo zancenta?"

Gyara zama nayi na ce mishi. "Abba hannunta da jikinta lullube yake da jini. Ba ita ba akwai mutane dayawa da na ga jini lullube da su, Abba idan har abinda nake fahimta anan shine Jinin Shehu Yayari da kuma...." Wayata ce tayi ƙara na saka a kunnena. "Na turo miki file din ta email ki duba!" "Ya Salim kai ne?" "Eh ranki shi dade Barka dai na shiga gidan aka ce baki nan." "Ayya nazo ganin gida, an jima zan dawo ai." "Tow ki bari na zo na dauke ki mana!" "A'a da ka barshi zamu dawo!" "A'a zan dai idan dai ba korata ake yi ba." "Haba ai baa yi haka ba, Allah ya kawo ka!" Nan muka gama na kashe wayar, na kalli Abba da yake nuna damuwa a fuskarshi. "Bana son alakarki da shi fa." "Abba ba zan yanke alakata da shi ba, akwai jinin da ya tab'a domin tana wanke da shi don haka ba xan rasa wannan damar ba, Abba Yaya yana kwance bai san waye akan shi ba, taya ba xan yi approaching duk mai hannu a kanshi ba, kada ka damu ba zan yi wasa da kimata ba, amma kowa ya nuna mishi yatsa sai na karya hannunshi."

"Allah ya kare ki ya kuma taya ki kare martabarki!"

"Malam Junaid, ka cewa Yarka ta bani hakurin marina da tayi."

"Waye kuma wannan?" Takaici ya sani kama kunnenshi ina faɗin. " Aryan ka koma duniyarku bana son ganinka!" "Ai fa sai ki yi ko godewa Allah danki ba mace ba ne da abinda zan miki sai kin yi kuka domin aure shi xan yi. Amma yanzu ma takaici na ma ya ishe ki sai kin bani hakuri ko nayi ta miki rashin mutunci!" Talle keyarshi nayi ya juya a fusace har ina hango wuta a cikin idanunsa,. "Malam Junaid ka ga iskancin da take min ta shammace ni ta kwatsama min mari ko ta shantale min keyana! Kana gani dai akan idanunta ta wanke min keya da mari, gaskiya ban yafe wannan lamarin ba, ka gaya mata ta bani hakuri."

"Ki bashi hakuri shi kenan kome sai ya wuce." Sai da na galla mishi harara kafin na ce mishi. "Allah ya baka hakuri!" Nad'e hannu yayi a kirji yana faɗin. "Wannan ba hakuri kika bani ba, ki kira sunana da girmamawa ki ce min Yallabai Aryan Imran Malami ka yi hakuri da marin da na yi maka na zan kara ba." Sake baki nayi ina kallonshi kafin na ce mishi. "Allah ya min tsari da baka hakuri har na girmamaka."

"Ka ga girman kan yarka ko?" Yayi abin yana wani nuna hannunsa a kasa sannan ya ce mishi. "Macen bil adam akwai kafirin taurin kai, yarinyar nan tayi laifi hatta mijinta sai da ya bani hakuri amma shegen girman kai ya hanata ta ce min. Yallabai Aryan abokin Yarima Ayaan ka yi hakuri ko don kula da Yaron nan da nake mata, yau da a duniyarmu aka falle ni da mari ai da ba a ga zaman lafiya gaskiya ta bani hakuri na cigaba da ganinta da mutunci!"

Kallonshi nayi cike da takaici na ce mish. "Waye yake bukatar mutuncinka? Kai din ne zaka ganin ni da mutumci amma mafarki kake ko kasha giyarku na aljanu ne? Ta ka ji da kyau ba zan wani baka hakuri ba domin ban ce ka fitar min da Yarona cikin dare ba, kai baka ji kunya ba yadda ka zo ka makale jikin Yaro karami kana gyara kuruciyarka." Hannu ya saka a bakinsa cike da mamaki yana kallona ya ce. "Amma ke dai baki da tsoron Allah,ba zaki bani hakuri sai ki min sharri!" Murgud'a mishi baki nayi tare da juya mishi keya shima yayi haka tare da naushin bangon parlourn Abba sai da ya burma Abba ya ce mishi, "kayi hakuri ai wannan bata wuce jikar jikarka ta biyar ko ta shida ba!" Wani tsalle yayi ya makale a bango yana zare idanun tare da dafe kirjinshi. "Ni saurayi ne har yau ban yi aure ba zaka kiran min jikar Jikar ta shida, ina ka kai min samartakana? Tunda nan tab'a!" "Don Allah ka yiwa mutane shiru magagannane banza da wofi ka fita daga jikin Yaro na gaya maka kuma an kira ka Tsoho mai shekaru dubu ba saurayi ba....

[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 36

Dirowansa yayi gabana yana kallona. Ni fa kallon Ayaan dina nake mishi, shi yasa ban wani dauki lamarinsa da muhimmanci ba, haka yau ma Abba ya shiga tsakaninmu yayi ta rarrashinsa da nuna mishi ai ni ba sa'arshi ba ce ni yarinya ce mara wayo, gashi ban san kome ba, yadda Abba yake lallaba shi yasa na fita daga dakin don ya bani haushi, su kare can ni babu ruwana.

Wurinsu Maluma na koma muka yi ta hira, ina basu labarin yadda kome yake tafiya, sannan ina bukatar addu'arsu a koda yaushe, haka yasa tun nan bar gidan ba, aka jika shinkafa za ayi masa da sugar sadaka, a yamma Maluma ta aika aka sayo mata jakar pure water har goma ta ce a kai massalaci ko alola aka yi Allah zai bada lada ya kuma sa a dace. Bayan Magariba Salim ya zo ya dauke ni da Yaran, sai da nayi ya rarrashin Aryan kada yayi magana, domin kuwa akwai irin kallon da Salim yake mishi wanda nake ji a raina kallon tuhuma ce ko zargi yake son ya tabbatar amma abin ya kasa yiwa. "Fulani Babba."

"Na'am!" Na amsa mishi, "dama akan abinda kike yi ne ko zaki dakatar da wasu abubuwan musamman bincike?" Kallon titin nayi a hankali ina murmushi na ce mishi. "Ban san me yasa ba, ko don ba a koya min tsoro ba ne, ko don ban san yadda zan sarrafa tsorona ba ne, amma tabbas binciken nan rufe shi sai dai idan bana numfashi. Amma matuƙar ina numfashi tow koda shine na ƙarshe zan tabbatar da na karasa aikin da na fara."

Na fada ina kallonshi, murmushi yayi yana faɗin. "Kuma gaskiya ne, yana da kyau mu baki goyan baya ki yi aikin nan cikin nasara!" Ya fada yana kokarin murmushi. "Na zata kai ma kana cikin masu son dakatarwa ne?" Na tambaye shi irin ban san me ke faruwa ba, cikin yake ya ce min. "Akan me? Akan me zan dakatar da ke? Ni mai bada rayuwata ne akan naki, kada ki ji kome ki yi binciken ki, idan kina bukatar wani abu ki tuntube ni." Fadar haka yasa ni, kallonshi a hankali can na ce mishi.."Idan kana ganin akwai matsala ba hakura da shi mana, ni bana cikin tashin hankali. Idan da hali kawai na hakura da kome." "A'a ba zaki hakura ba yanzu kika fara bincikenki ina mai baki goyan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login