Showing 132001 words to 135000 words out of 157081 words
fara ruki'a kai ne zaka fadi, ni ina da gaskiya na ba irin ka ba ne, wanda ya tara mata ya kasa hakuri da fahimtarsu. Katon banza katon wofi wowowo katon banza!" "Ni ka zaga ka, kai ba kai ba hatta kakan Shehu yayari Ahmad Yayari, da uban Ahmadu, Abdullahi an zage su. Kayi duk abinda ka ga zaka iya shashasha, kawai katon banza mai katon kai, ka godewa Allah ina kaunar zamanku da ko cikin jikinta sai na zugata, ta zubar kuma ka min iskanci na nad'e ka kamar yadda ake nad'e kifi wallahi tsaf sai na saka ka, kuka a zauna mai shegen kai kamar Uwar yaki, baka san kome ba sai mata." Zagi na wulakanci Aryaan sai da yayiwa Salmanu hankalinsa ya kwanta, sannan yayi tafiyarsa. Barci nayi sosai kafin na tashi na samu Yaya yana zaune. Sallah na sauka nayi sannan na dawo dakin na samu Yaya sai cika yake yana batsewa. A hankali na shafa addu'a sannan na nufi waje na hada abin da zanci na dawo dakin, na zauna na fara sha ina lura da yadda yake cika da batsewa. Jikina ya bani sun yi yar hali da Aryaan, sai da na gama na zauna ina shan ruwa ya ce min.."ki gayawa dan iskan aljanin nan naki ya bar shigo min gida!" Kallonshi nayi kafin na ce mishi. "Me yasa baka gaya mishi ba?" Don nasan ba mamaki sun yi ba dad'i da shi ne, murya shi ta katse min tunanina ya ce min. "Na dai gaya miki wallahi zan dauki mataki a kanku;" "Allah ya baka sa'a Mai martaba!" Haka ta fita fuuuu. Ni babu abinda ya dame ni gashi ga Aryaan, wato idan kana niman mara mutunci ka samu Aryaan daga dan iska sai shi, ai tunda ya fahimci Yaya ba ganinsa yake ba balle ya samu hanyar kuntatta mishi, sai ya dauki kwallin da ya bani ya kai mishi daki, bayan ya juya ya koma kamar ni ya ce mishi. "Yaya ga wannan kwallin ka saka a idanunka zai taimaka maka!" Kallon aryaan yayi ya ce mishi. "Ajiye min a can kizo na baki labari!" Don shi ya dauka Zainab ce. Murmushi yayi ya ce mishi. "Idan ka saka kwalli zan zauna da kai." Da yake mayyen mata, tuni ya dauka ya saka yana faɗin. "Zan saka!" Yana saka a idanun daya kafin ya saka ya ji kamar an bude mishi wata kofa yana saka dayan ya ji shima haka, d'ago kai yayi yana kallon Aryaan da yake sanye da fararen kaya da rawani a kanshi. "Ka ga abinda nake son ka gani wnada ya fasa ni da kai Allah ya shirya shi!" Ya juya ya bar shi a zaune tare da rufe idanunshi. Tashi yayi a zafaffe ya fito parlourn yana kallon Aryaan da yake tsaye akan iska daidai inda Ayaan yake zaune, "kai ka fita min a gidana!" Dariya Aryaan din yayi yana faɗin. "Babu inda zan tafi zama daram inji me nakuda ta zauna a gado, ai mun zama dangin juna babu gudu babu ja da baya." Ya fada yana dariya, fada sosai Yaya yake wanda yayi sanadin da muka fito, ina kallon Yaya da Aryaan suna faɗa, abin dariya ya bani matanshi kuwa hankalinsu ne ya tashi, ba dai wani abu ba ne ya kara sun shi ba, musamman Nadiyyah da take da burin ta samu ciki ta haifi namiji duk rintsi sai jininta yayi sarauta. Don haka duk abinda zata yi sai ta kai wannan matsayin.
***
A irin wannan yanayin muka bar kasar, ni dai bani da lafiya. Muna shiga kasar ni a lissafina mun baro shi a can, amma ina sai ga Aryaan a saman kayanmu zaune yana d'aga min gira, dauke kai nayi na cigaba da kallon gabana, ban san yadda aka yi Yaya ya ganshi ba cikin fada ya ce min. "Waye ya kawo mana shi? Waye ya kawo shi? Ba nace ki sallame shi ba." Yayi min kasa kasa. "Yaya ga ka gashi ka sallame mishi mana!" Kwafa yayi koda muka isa castle din fushi ya dauka ni dai bani da lafiya kuma bani da lokacinsu, kusan a wurin Ijlal ya tare, ya zata zan wani damu ne sai ya ga bani da lokacin kula su, wasa wasa sai ciwona ya karu, wani abu da tun fil azal nake da shi bana bin shi akan yana fushi, da kanshi yake saukowa ranar da muka cika kwana uku ba sai ga Nadiyyah ba, ita da Yarta. Na ji Yara suna ta murna Princess tazo amma ban ganta ba tunda ni daki nake, ranar a daren ruwanta suka yi fada da shi har ya ce mata shi da yabi ta mahaifinsa da bai zauna da ita ba, ita babu alkhairi a tare da ita ban da masifa da sharri babu abinda yake ranta, ita kuwa ta ce ai tasan yanzu ba yin kansa ba ne mallake shi aka yi Malam Junaid ya kashe kanshi domin ya mallakawa Yarshi Mijinta. Wannan maganar da tayi yasa shi kwashe ta da mari, fada dai fa ta kuma rantse ba zata bar garin ba sai ta cusa masa bakin ciki yaji amma bai damu ba, ita din ce dai bai da lokacinta.
Washi gari da na sauko muka hadu da masu girkin.muka gaisa sannan na haɗa abinda xan haka ina gani Mira da Mimi suna dauke da Ayaanah da Ayaat, sai hira suke musu, murmushi nayi na ce musu. "Ina Mary!" "Tana can bangarensu." Suka Bani amsa haka na tab'a abincin na fita na wuce daki na kwanta, yaran sun san bani da lafiya, don haka kasa suke saukowa su yi wasa tunda Nadiyyah ta zo ta janyo aka tattara yaran kowa ya zauna a dakinsu, yanzu haka Princess ta shigo suna wasa sai fada da zagi take, Ayaan da ya ji haushi ya mare tare da turo ta waje, shine ta fita tana ihu, da yake uwar ba hankali sai gata wai tazo rama mata sai aka yi da Uban ya shigo kenan, ai kuwa yayi tsalle ya ce bai iya ji ba, karshe fadar dai sai da ya wulakantata a gaban Yara, meye amfanin haka har yana gaya mata ita masifa ce da Bala'i a rayuwarshi, yayi dansanin aurenta da dukka zuciyarsa, wannan maganar yayi mata ciwo,don haka ta yi fushi ita da yarta suka bar gidan, karshe ko sati ba ayi ba muka sake ganinta ta dawo.
Ashe da shirinta, ta kuma dawowa domin ranar wata juma'a. Ina kwance naji ihu a wajen gidan, fitowa nayi muka iso waje. Ijlal ce da Mimi ban san me ya faru ba sai dai yarinyar ta fado daga sama wanda suka tabbatar Ijlal ce ya turo ta, ita kuma ta rantse da Allah ba ita ba ce Nadiyyah ce, abu dai sai da aka kira yan sanda suka tafi da su. Kiran Yaya aka yi ta nufi can office din Yan sanda karshe a yadda Nadiyyah ta bada statement din ta daure Ijlal, haka ya dawo gida da Nadiyyah, jikinshi a mace, yana zuwa ya fara masifa ina gida zaa yi kisan kai ban damu ba. "Saboda baka bani sandar kiwon matanka ba, ai shirin matarka ba akan Ijlal yake ba, ni ta so na fada kuma Allah ya ƙare ni!"
"Gaya mishi dai don na lura basirar ta toshe, Nadiyyah da ta kulla sharrin ai gata can tana dariya a daki saura ke don haka zamanki a daki shine abinda ya dace!" Takaici yasa na rufe ni, na shiga dakin ban kuma fitowa ba sai dare, a can dakin kuwa fada suka yi wnada yayi mata duka, wato da na sake Yaya yakai hannu jikina da na shiga uku, sai na fahimci suma sun fi gane ya dake su, haka ya koma tare da ɗaukar Attorney suka yi ta fama, Allah ya so yarinyar ta farka da hankalinta ita take gaya musu Nadiyyah ce ta turo ta Ijlal ta je taimakonta ne ya amma bata turo ta ba, dole aka zo aka tafi da Nadiyyah, wannan abinda ya faru ya kara saka min yardan Ijlal ta sauka daga inda nake tsammani ko zargi domin da ta dawo a ranar a dakina ta zauna tayi ta kuka tana faɗin. "Ki yafe min!"
Abinda tayi ta fada kenan har ta bani sa'a, daga nan na ce ta koma ɗakinta. Kwanakin Nadiyyah biyar Kakanta ya zo dakyar suka kyale ta bayan ta dauki nauyin jinyar Mimi, sanan aka yi banner passport dinta, saboda abinda tayi aka haramta mata shigowa kasar har abada. Wannan abinda ya mata ciwo taso idan za a haramta mata zuwa bakiɗaya ahalin Salmanu Faris ne amma ina ita ɗaya haka ta bar kasar, shi kuma da yafi ta iskanci yaki bata Yarta, ba ruwana da Yar kowa, yawwa tunda na fahimci niman jona min ita yake tuni na ki, haka yasa ya bar Yarinyar da Yaran Ijlal itama kamar wacce muka haɗa baki ta ce bata ji bata gani ba, karshe haka ya kawo min ita, hmmm kusan wani abu? Ni dai a tsarina Yara basu kwana da ni, koda zasu kwana a tare da ni, nayi wani abu daya shine bana yarda da Ubansu a dakin, akwai wani abu da yake cikin scenes na sex wato moans da Groans wannan abu biyu ko barci yaro yake yana iya farkawar saboda yanayi ne da ba kowa yake iya danne na shi ba, balle kuma Nadiyyah da Yaya da suke abu kamar Porn stars, idan ana abu yarinyar tana ji, ina kwance shi Yana tare da Ijlal, sai na ke ganin kamar mafarki nake ko ido biyu ne oho dai ni dai ganni yarinaya nayi tana cire kayan ta tare da yin wasu abubuwan tana ƙoƙarin nufar Ayaaz, bude idanun nayi na nufi dakinsu ina shiga ban yi wata wata ba na kuna wuta haka ne, abinda ta ga Uwar take tana saka hannu a gabanta. Wani irin razana na shiga na ce mata. "Ke" na daka mata tsawa, a tsorace ta koma can tana zare idanu, wayar charge na ɗauka na shiga tsuga mata a cikin daren, domin kuwa hankalina ya tashi kamar zan mutu, a'a ba zai yiwu ba ihunta ya taso uban ganin yadda nake zane ta ya kwace wayar yana shiga tsakanin bakiɗaya Yarinyar nan shekarunta uku da wata shiga sha daya. "Me kika yi haka? Me tayi miki? Dama kun yi haka ne don ku kori Uwarta!" "Eh sai me? Nace kawo min ita ne?......
[8/26, 5:37 PM] Ramlat Manga41: 50
"Ko nace dole sai na rike maka yarka? Kun lalata tarbiyyar yarinya karama ina zaka zauna da hakkinta? Anya kai uba ne ko mugu? Yaya na gaji da zama da kai, na gaji da halinka ba zan iya zama da kai ba, idan na cigaba da zama da kai dare daya zan mutu!" Na fada tare da fashewa da kuka, ina jin wani irin ciwo a raina. "Kun kashe Yarku, kun gama da rayuwarta idan baku gyara ba gaba kai zaka yi danasani." Daga haka na tattara kayanta na watsar musu, na ce su fita min a daki, kuma gobe zan koma gida, saka mata kaya yayi suka bar parlourn, gari na wayewa na fara shirin barin masa gidan, Aryaan ya ce min. "Babu inda zaki ki kyale shi. Ya dai san yadda zai yi da yarta, Zainab iyayenki mutanen kirki ne shi yasa Allah yake tare dake, ban da iyayenki suna tsaye akanki da wasu abin sai yafi haka muni shi Mijinku yana da son kai. Idan bukatarshi ta biya baya damuwa da kowa sai kanshi. Don haka kada ki bar mishi gidan ai yanzu kin ci guda da fili balle wannan gidan naki ne ba na wani ba." Bayan mun gama magana na kira Maluma ina kuka, kafin na gaya mata ciki nake da shi, nayi kewar Abba ne, ja na da hira tayi ta yi har nayi shiru, kafin na fara sakewa muka yi hira da ita. Ashe fushi yayi ta tattara kayanshi ya tafi da Yarinyar wurin Uwarta, ai gani yake kamar sharri ne da kuma bana son zama da yarinyar, a lokacin da suka isa Uwar ta ga jikin Yarta kamar tayi hauka, har da cewa zata shigar da ni kara shi dai ya lallabata, ma rasa gane wani irin makalewa juna suke da Nadiyyah, haka yasa muka zuba mishi idanun. Sai da ya shafe wata guda kafin ya dawo, yana dawowa da wani iyayi wai yana niman wani abu yadda na yi tsalle nace ba wannan maganar fada sosai muka yi. Ban san yadda aka yi ba Itama Ijlal tabi sawuna muka watsar da shi,.haka muka kwashe wata biyu a haka kafin ya fara shirin mu dawo gida don na ga yadda yake wani ruwan kai na san Nadiyyah ta dawo, sai na bar shi yaya ba zai sauya ba, haka yasa da muka fara shirin dawowa nayi sayayyar haihuwa don ma cikin watansa hudu kenan, wata mu uku bamu kasarmu.
Ranar wata talata muka dawo gida, Nadiyyah muka samu, a gida har lokacin bata san ina da ciki ba. Don ko Ijlal shi ya gaya mata tayi ta murna da cewa za a saka sauran Yaran a makaranta tunda ita dai mahaifarta ba halin haihuwa sai bayan shekaru biyar, sai ta bani tausayi. Haka da muka dawo kowa ta kama gabanta muka barwa masu renon Yaran muka huta. A wannan karon naga yayi wani abin mamaki Yara mazan ya tattara su suka koma bangarenshi, yan matan kuma ya bar mana su, wani lokacin idan nayi wani abu sai naga Ijlal tana yin kusan haka, ashe yarinyar nan ta iya kitso, haka take kama kan Yan mata ta musu kitso, Madinah kuma.ta musu lalle. Haka yasa sai muka samu wani irin shakuwa duk da bana shiga mata amma ita fa tana tare da ni, haka zata kwashe Yaran zuwa wurin mai babbar daki, su wuni ko su kwana ta koma ta kwaso su zuwa gida, a hankali na samu saukin dawainiyyar yaran, kuma naga yanzu kamar islamiyya take zuwa Asabar da Lahadi. Sannan akwai wata malama da take zuwa musu karatu da karfe tara na safe.
Da gaske Yaya ya kullace ni, haka yasa na ki yarda na biye mishi. Haka muka cigaba cikina yana shiga wata biyar wata yammacin Laraba na fito shan iska Ijlal tana karatu da yara a garden, ni kuma ina zaune da Ayaanah da Ayaat, Nana A'ishah tana nata drawing din saboda ya taimakawa rayuwarmu ya saka su a makaranta, Yaran suna da kashin girma, ina kwance Princess ta zo tayi ta wasa yaran kowa yaki kulata, sai Nana A'ishah ta cewa Uwarta. Maamah xan yi fitsari!" "Ki sami Madinah ta kai ki, kuma ta wanke miki jikinki da kyau." Na fada saboda naga Uwar sai famar shigar da hadda take, kamar kaftu da Bismillah Princess ta bita, kamar wasa suka bata shiru, na kalli Ijlal na ce mata. "Ba zaki bi sawun yarinyar nan ba, ta jima fa." Kallona tayi ta ce min. "Kuma haka ne!" Ta ajiye littafin ta yi cikin gidan Dogarai na gaishe ta, haka ta wuce tana gyara zaman myafinta, haka ta shiga bangarenta, tana haura sama, akwai wani abu da idan Allah yana sonka da rahama sai ya kawo maka dauki, koda ta shiga ban dakin da Yaran bata ciki bata dakin, can ta wuce ban dakinta. Nan ma shiru haka yasa ta sauko. Dakin kasa ta nufa anan ta ji muryan Nana A'ishah tana faɗin. "Mammyn ta ce idan aka yi Allah zai kona mutum a wuta ni dai ina tsoro!" "Ki cire pant ɗinki zan nuna miki yadda Daddy Da Mommy suke yi ne. Ina jin Daddy yana faɗin akwai dad'i." Ƙafafuwanta ne suka gaza daukarta ta fashe da kuka da gudu ta shiga ban dakin. Ita Nana A'ishah tana makale a bango tana kallon princess da take kokarin cire wandonta, ai kuwa itama Ijlal ta manmaketa tare da korota waje. Da yake tasan tayi laifi kasa kuka tayi sai da ta je wurin Uwar ta kama kuka, ita kuma da yake halinsu daya da Uban sai gata, nan tazo zata ramawa Yarta, fada ya kaure dambe Allah ya bawa Ijlal sa'a ta makata da ƙasa, ihun Madinah na ji haka yasa na taso, na zo aka raba da su da kyar. Kafin wani lokaci jini ya ballewa Nadiyyah, ai kuwa yana zuwa ya ce sai dai Ijlal ta bar gidan, ita kuwa ta ce mishi. "Ba zan bar gidan ba, kayi kaɗan ka yi tsararo. Idan duka ne ka jima baka dake ni ba, ba zai yiwu na ga yarka zata lalata min tarbiyyar Ya na kyale ba, wallahi kayi kaɗan kayi tsararo." "Ke tarbiyyar ce da ke, yaushe kika daina lesbian?" A nan na kasa hakuri na ce mishi. "Ka ji kunya ka kad'e har buzunka, gara ki magana nima haka tazo zata min akan Yarana, shi ne aka dawo kanki, idan kai ne da wuta da aljanna sai ka hana mu shiga!" Nima na shigar mata fadar, yana fada ina fada sosai muka yi rigima budar bakinsa ya ce min. "Ki je sai na nime ki!" "Kaci karya ka kwana da yunwa babu inda xan tafi da wannan cikin wallahi na gaya maka kuma ka sani ranar da na haifa maka zan nuna maka Gobirawa suka haife ni!" Wannan masifar yasa shi shiga hankalinsa, na kasa gayawa kowa, na bar maganar a raina.
Kwanan Nadiyyah daya ta dawo, tare da alwashin da ta ciwa ranta, Ijlal dai ta daki banza, kuma ina bayanta kwanan biyu da dawowarta ina parlourn kasa Daularh da Kubrah tare da Yeemar sun zo wuni ganin yadda muke shiri da Ijlal itama ta shigo cikinsu aka zauna lafiya, haka yasa ta shiga cikinsu ana ta hira ni kuma ina kitchen ina girki, na kawo musu ana ta ci